Last chapter
JARIRAI*
*ƘARSHE*
Daga Masallacin kai tsaye gidan Yayan Nuratu na nufa, na ci sa'a ina zuwa na same shi ya na ƙoƙarin shiga gida, shi ma dawowarsa kenan daga Sallar.
Mu ka gaisa sannan na soma rattabo masa jawaban da ke tafe da ni, a ƙashe na rufe da cewa idan har ya na son cigaba da zamana da Nuratu to ya gaggauta shigowa cikin lamarin dan ɗaukar mataki, in ba haka ba kuwa babu abin da zai hana ni ɗaga mata jan kati, dan na gaji da abubuwan da su ke faruwa.
Ga dukkan alamu barazanar tawa ta yi tasiri a zuciyarsa dan yadda naga ya ruɗe da ya ji zancen saki ya shigo lamarin, kasancewar shi ne kadai ya ragewa Nuratu shaƙiƙi wanda ya ke jiɓantar lamuranta.
Nan ya shiga kwantar min da hankali tare da tabbatar min da komai ya zo karshe insha Allah.
Daga nan kai tsaye gidan wani shahararren Malami muka nufa, da kaina na yi masa jawabin duk abin da ke faruwa, nan ya tabbatar min da zai je ya gwada sa'arshi ko za a dace.
Nan mu ka rankaya gaba ɗayan mu har Malamin da kuma wasu almajiransa guda biyu.
Koda muka isa gida sai muka nemi Nuratu sama ko ƙasa muka rasa, ba ta ba alamarta a cikin gidan. Nan fa na tashi hankalina saboda yadda Nuratu ke son gocewa wannan tarkon da na ɗana mata.
Malamin ya shiga kwantar min da hankali tare da tabbatar min da cewa akwai dabarun da suke yi wajen kiran Aljanu, kuma koda a bangon duniya suke sai sun zo.
Nan ya baje kayan aikinsa, su ka shiga karatu shi da Almajiransa.
Wucewar wasu mintoci sai ga wata guguwa mai ƙarfi ta taso ta dinga yawo da labulayen ɗakin tamkar za ta cizge su, jim kadan kuma komai ya lafa, sai ga wata murya mai ƙarfi da amsa amo ta soma magana.
"Fatuhu! Ka yi kuskure da ka ke tunanin wannan ita ce mafita a gare ka, ka sani ka ragewa kan ka lokacin tonuwar asirinka ne, dan kuwa ba zan taba bayyana ba har sai ka kirawo Mahaifiyarka da sauran 'yan uwanka an yi komai a kan idanunsu..."
Yaya Murtala, Malami da sauran Almajiransa suka zubo min idanu, nan da nan na ji numfashina na neman daukewa, ina mai tabbatar muku da cewa tashin hankalin da na ji a lokacin ban taba jin makamancin sa ba, dan ko abubuwan da suka faffaru tsakani na da Nuratu ba su tayar min da hankali kamar wannan sharadi na wannan Aljana ba.
Ba kuma komai ne ya tayar min da hankalin ba face tonuwar asirina, da kuma abubuwan da za su faru bayan haka, ya ya duniya za ta cigaba da kallona? Ya ya zan kubuta daga fushin da zan fuskanta daga mahaifiyata?
Innalillahi... Ban taba jin nadama cikin ayyukana ba sai yau, ashe dama abin da Nuratu ta shirya aikata min kenan? Ashe so ta ke ta tona min asiri a idanun duniya? Kai wannan tashin hankali da me ya yi kama? Allah na tuba!
Jikina ya dinga tsuma zuciyata ta dinga rawa tana tsalle tana barazanar ficewa daga ƙirjina.
Yaya Murtala ne ya yi maganar da ta dawo min da saiti. "To kai Fatuhu mai ka ke aikatawa ne haka? dama ni nasan duk wannan abun da ka ke ta faɗin yana faruwa na san akwai wani dalili."
"Yanzu sai ka gaggauta kiran 'yan uwan naka su zo mu yi aikin mu mu tafi." shima Malam ya yi magana.
Na riga na gama saddakarwa karshena ya zo, dole lokacin tonuwar asirina ya yi, dama duk nisan dare dole gari zai waye.
Haka na dauki wayata cikin rawar jiki na kira kanina Jamilu na fada mishi ya dauko Mamanmu su zo gidan, na kira Yayana shi ma na sanar masa.
Falon ya cika maƙil, na yi mamakin wanda ya kira ƙanin mahaifiyata sai gashi tare da matarsa, shi ma Yayana da tashi matar ya zo.
Malam tare da Almajiransa su ka cigaba da aiki, nan da nan sai ga Nuratu ta bayyana, babu wanda bai tsorata ba a falon in ka cire Malamin da Almajiransa sai kuma ni da na riga na saba da wannan aljanancin.
Kuka sosai Nuratu ta ke tana rokon Malamin kan kar ya cutar da ita, ita ba muguwa ba ce, sun zo ne dan yin taimakon da su ka saba yi ga bil-Adama.
"Ya kai Malam Ahmad Asib, ina rokonka da ka barni in gabatar da komai cikin nutsuwa dan kowa ya san wanene Fatuhu da abin da ya ke aikatawa."
Malamin ya gyada kai yace, "Muna sauraron ki."
"Tabbas ni ba Nuratu ba ce! Nuratu mun dauke ta tana can karkarshin kulawarmu, mun yi amfani da surara jikinta ne dan samun kusanci ga Fatuhu, amma ina tabbatar muku Nuratu tana can cikin koshin lafiya."
Cikina ya dinga hautsinawa, ashe da Aljanar gaske na ke artabu tsawon wasu kwanaki ban sani ba?, wayyo Allah na.
Hannu na dora aka ina shirin fasa ihu kamar yadda na ji kwakwalwata na ba ni umarni. Babu wanda ya kula da hanlin da na ke ciki dukkan hankalinsu ya na ga Aljanar Nuratu wacce ta ke cigaba da cewa.
"Ni sunana Zinatul Iman, na kasance 'ya a cikin Rundunarmu, kuma ni ce wacce ta ke jagorantar tawagar da ke bibiyar rayuwar marayun 'ya'ya da Jariran da aka salwantar musu da rayuwarsu ta wani mummunan sanadi... kuma ban shigo rayuwar Fatuhu dan in cutar da shi sai dai dan in dauki fansar ran bayin Allah sannan in bayyanawa duniya kullin da su ke kullawa a bayan fage ba tare da mutane sun farga da abin da ya ke aikatawa ba, ina so kai Fatuhu ka yi bayanin abin da ka ke aikatawa da bakin ka kowa ya ji ka."
Nan kowa ya zuba min idanu, ji na ke tamkar kasa ta tsage in shige ciki, kuka na soma yi mai cike da da-na-sani da nadama, me ya fi wannan titsiyen tashin hankali saboda Allah!
"Kai mu ke saurare Fatuhu." Na tsinkayi muryar Mamanmu.
Cikin kuka na shiga bayani, "Kamar yadda ku ka sani, ni likita ne bangaren mata da yara, to baya ga haka kuma ina aikin Abortion wato zubar da ciki, na kai akalla shekaru goma ina wannan aikin ba tare da na taba fuskantar wata matsala ba sai a kan wata yarinya Bilkisu, wacce ta rasa ranta gurin cire mata cikin..."
"Innalillahi wa inna ilaihirraji'un!" Kowa ya dauki salati cikin tashin hankali, Mamanmu kuwa kuka ta sanya tana fadin "Na shiga uku ni Larai, kisan kai? Fatuhu kai ne da kisan kai? Irin tarbiyyar da na baku kenan? wayyo Allah na, Fatuhu Allah ya isa tsakanina da kai kuma na yi nadamar haihuwar makashin rayukan bayin Allah, wallahi da na san abin da zaka tashi ka aikata kenan a rayuwarka da ni zan fara kashe ka da kaina..."
Yayana ne ya yi saurin rufe mata baki, yayin da ni kuma na cigaba da zabga kuka mai cike da nadama, na shiga rokon Mamanmu kan ta yafe min amma ina! Tashi ma ta yi tace ita ba zata kara koda minti daya cikin gidana ba, kuma babu ni babu ita har abada ta yafewa duniya ni.
Da kyar da saka bakin Aljanar Nuratu Mamanmu ta hakura ta zauna dan jin cigaban abubuwan da su ka biyo baya.
Aljana Zinat ta ba su labarin Bilkisu tun daga farko har zuwa lokacin da ta samu ciki daga Magaji da irin tashin hankalin da mahaifiyarsa Hajiya A'i ta shiga da yadda suka dage sai sun zubar mata da cikin.
Babban abin da ya tsorata Bilkisu shine ganin an fito da mace daga dakin aikin kwance akan gadan Asibitin tamkar gawa, babu abinda ke motsi a jikinta, nan fa Bilkisu ta shiga tashin hankali tare da rokonsu a kan kar su kasheta su barta da cikinta su maida ta kauye a haka, amma ina saboda gudun lalacewar kasuwar Tabawa yasa ta nace sai da aka shiga da ita dakin zubar da cikin inda a gurin aikin ta rasa ranta.
Mun shiga tashin hankali matuka! Mun yi kuka har sai da hawayenmu suka kare, daga nan mu ka ci alwashin daukar fansar ran Bilkisu.
Nan mu ka dinga bin duk wanda ya ke da hannu cikin lalacewar rayuwar Bilkisu daya bayan daya tun daga kan kanin mahaifinta na kauye har zuwa kan Fatuhu wanda mu ka bibiyi irin ayyukansa na baya da yadda ya salwantar da rayukan Jarirai babu adadi, wanda hakan ke bawa lalatattun mata karfin gwiwar su je su dauko ciki su zo ya cire musu, har wata inkiya gare su dan sakaye aikinsu a idanun wadanda ba su san dawan garin ba, wato suna kiran cikin da suna MUSHE, ita kuma mai cikin sunanta GAFIYA."
Jikin kowa ya gama yin sanyi, na tabbatar kowa Alla-wadarai da halina ya ke, to ya na iya! Ni na jawa kai na.
Aljana Zinat ta cigaba da cewa, "Na san zuwa yanzu babu wanda ya kai Fatuhu yin nadama, ko iya nan muka barshi tabbas ya hukuntu yadda ya kamata, saboda haka Malam ka shaida za mu bar rayuwarsa har abada, sannan za mu dawo masa da Nuratunsa, saboda haka za ku tsinci Nuratu a kan gadonta tana barci, kar ku tashe ta dan bata san duk abin da ya faru ba, idan ta tashi za ta cigaba da rayuwarta yadda ta saba, a nan nake muku sallama, Allah ya shiryi bayinsa amin, kai kuma Fatuhu ina fatan ka tuba ga Allah ka nemi yafiyarsa sannan ka cigaba da yiwa ruhikan Jariran da ka salwantar addu'a, hakan shi zai rage maka bibiyar hakkin rayukansu a gare ka.!
Daga haka ta tashi ta shige dakinmu, shikenan kuma komai ya zo karshe.
Abubuwan da suka biyo bayan hakan ba masu dadi ba ne gare ni, domin kuwa sosai Mahaifiyar mu ta ke fushi da ni, na sha wahala matuka kafin ta yafe min, a gefe guda kuma na yi tsarkakken tuba tare da cigaba da neman fatawa kan rayukan da na salwantar sanadin zubar da ciki.
Nuratu kuwa daga baya ta san duk abin da ya faru kasancewar halin damuwa da na shiga...
To wannan shi ne labarina, a kansa kuma na ke so in tabbatar muku da cewa na tuba na daina aikin zubar da ciki yanzu, ku ma kuma ina mai baku shawara da ku guji aikata wannan ta'addancin ku koma gida ku rungumi kaddarar da Allah ya dora muku, Allah yasa mu dace."
Doctor Fatuhu ya yi shiru bayan ya gama ba su labarinsa, wata macece tare da diyarta wacce saurayinta ya yaudareta ya yi mata ciki shine su ka samu labarin Fatuhu da yadda ya kware wajen aikin cire ciki, sai kuma su ka yi sa'a ya tuba ya daina, har kuma ya basu labarin abin da ya faru da shi a rayuwarsa.
Cikin sanyin jiki su ka tashi su ka koma gida tare da godewa Allah da baisa sun kai ga tafka babban kuskure ba, sun yi amfani da shawarar Fatuhu na rungumar kaddarar da Allah ya aiko musu.
Ma sha Allah! Nan na kawo ƙarshen wannan gajeren labarin, da fatan an fadakantu, da fatan kuma sakon da ke ciki ya isa.
Jinjna ta musamman gare ku makaranta da yadda ku ka nuna soyayyarku kan labarin, hakan ya gamsar da ni cewar sakkonin da mu ke son isarwa cikin labaranmu su na isa, madalla Allah ya bar zumunci.