JALALA

Part 4

by @ummunasmah

💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫



      💑 *_JALALA_* 💑



💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫





  *_New story from Rasheedat Usman (Ummu Nasmah)_*




  *_The writer of_*



-Sauyin Rayuwa.

-Nasmah ko Nasirah.

-Sara da Sassaqa.

-Indo a Birni.

-So Bai San Jini Ba.

-Ruɗanin Zuciya Biyu.

-Akan Ƴar Uwata.

-Doctor Hassan.

-Gelle Ɓingel.

-Ƙauyenmu.

-Hatsabibiya Saude.

-Aminaina ko Ita?.

-Ƙullalliya.





*_Special tnx to my people masoya masu ƙaunata masu bibiyata ako da yaushe, yanzu ma gani tafe muku da sabon salo sabon labari mai tafiya da zamani labarin daya ƙunshi abubuwan ban al'ajabi a cikin sa ku kasance dani domin jin yacce cakwakiyar zata ƙarke, idan kinsan kina da ra'ayi akan wannan labarin to ki fara bibiya tun daga farko kar sai nayi nisa kice min daga farko please._*





   *_FREE BOOK ONE_*





*_WRITING ON 01/03/2022_* ✍🏻




*_Page 7 to 8_*





Murmushi Jidda tayi tare da harɗe hannunta a ƙirji tana yiwa Hisham kallon mahaukaci Nameer ne yace.

  "Ya isa haka Hisham, meye haka meya kawo iyaye cikin wannan maganar, iyaye suna da mahimmancin da taka su mungun haɗari ne a rayuwa, koda basu haifeka idan sun kai girman haifar kamarka to iyayenmu zamu kirasu, karna kuma jin ka zagi iyayenta, please Hisham ka dinga dannar zuciyar ka."

  "Da ka barsa ya cigaba da zagin domin kuwa mahaukacin kare shike haushi, Malam Hisham dan Allah karka fasa tozarta ni, idan kuma ka fasa to baka amsa sunan gidan ku ba, idan kai mahaukaci ne ni kuma likitar mahaukata ne zanyi maganin haukarka, karka fasa."

  Jidda tayi maganar tana jan doguwar tsuka tare da juyawa ga Sargent Bala ta cigaba da cewa.

  "Idan kunga dama ku kamasa idan kunso ku ƙyalesa, ni kuma bazan fasa ƙudiri na a kanku ba ku tuna da wacece ni."

 Tayi Maganar tana juyawa tabar wajen ba tare da ta tsaya taji me Sargent Bala zai ce ba.

  Wani irin hura zuciyar Hisham yake tunda yake a tarihin rayuwarsa babu wanda ya taɓa tsayawa a gabansa ya faɗa masa magana yadda ta masa cikin tsawa mai rikitarwa Hisham ya jawo kwalar Sargent Bala yace.

   "Waye ita! Dame ta dogara waye ya ɗaure mata gindi ƴar uban waye Minister ne ko shugaban ƙasa ko gomna ka faɗa min na rantse da Allah sai na tozarta ta sai na bambance mata tsakanin aya da tsakuwa, sai na zamo sanadiyyar lalacewar rayuwarta idan ban aikata hakan ba ni ba jinin Iyab..............

  Saurin toshewa Hisham baki NAMEER yayi yana janye hannunsa daga rigar Sargent Bala, cikin taushin murya NAMEER yace.

   "Cool down Hisham ba komai ake ɗagawa hankali ba, kar ƙaramin abu ya tayar maka da hankali ma, kayi haƙuri ka koma ciki ni zanje station ɗin rago shike tsorata marar gaskiya kuwa gumi yake bana da matsala ko jin zafin akan Sargent Bala yazo tafiya dani aikinsa yake ka barsa yayi aikinsa kaje ka sanar da Abba abinda yake faruwa, muje Sargent Bala."

  "Bazai yiwu ba Nameer mutuncika ya wuce ka shiga cikin motar Police, bazai yiwu ba hakan ba mai yiwuwa bane, Sargent Bala kaje ka cewa Dpo ni Hisham nace NAMEER bazai zoba, ku fice ku bar gidan nan ko na sunce muku karnuka suyi maganinku."

  A ɗan tsorace Sargent Bala ya ɗago ya kalli Hisham domin kuwa yasan zai aikata duk abinda ya furta NAMEER ne yace.

  "Sargent Bala kuje zanzo a motar gida ɗan uwana baya son na shiga motarku bazan shiga ba amma zanzo karka sanar da Dpo sakonsa domin kuwa baku da laifi aikinku kuke kuje."

 Kansa Sargent Bala ya ɗaga tare da bawa sauran Police ɗin umarnin su tafi, NAMEER kallon Hisham yayi tare da cewa.

  "Baka cika bibiyar jarida bane shiyasa baka santa ba, tabbas zata iya ɓatawa station ɗin su suna muddun basuyi abinda tace ba, ba ƴar kowa bace face ƴar Jaridar Aminci mataimakiyar shugaban Aminci na santa domin kuwa na juma ina son na kai mata ziyara sai dai kuma gashi ita ta riga kawo min, naji daɗin hakan sosai."

 Cike da rashin fahimta Hisham yace.

  "So whatt! Idan ƴar Jaridar ce, tukunna ma ya akayi kasan wani abu a kanta kana da alaƙa da ita ne.?"

  "Hmmm! Yanzu ba lokacin tambaya bane Hisham, ka koma ciki ka sanar da Abba abinda ke faruwa ni zanje station ɗin sannan karka fasa zuwa gidan Mamabisola kamar yadda muka shirya dan Allah kaje."

  "Ta yaya zan Barka ka shiga cikin station kai ɗaya sam bazan iya barinka ba tunda ka dage sai kaje sai dai mu tafi tare babu gidan Mamabisolan da zanje muje kawai."

  "Bazamu tafi ba tare da ummi tasan abinda ke faruwa ba, kaje ka sanar da ita ta yadda zata fahimta ka tabbatar hankalinta bai tashi ba."

 Kansa Hisham ya girgiza tare da juyawa cikin gidan cikin wani irin mungun yanayi, yana shigewa NAMEER ya buɗe mota da sauri sauri ya shiga tare da jan motar ya fice.



 Falon ya koma cikin sanyin jiki tare da zama gefen Ummi, Ummi cike da mamaki take dubansa tare da cewa.

  "Lafiya Hisham ka shigo haka cikin wani irin yanayi, ina shi NAMEER ɗin yake, kun fasa zuwa gidan Mamabisolan ne.?"

  Ummi ta jefa masa tambayar daidai Tutu na shigowa falon ta zauna gefen su.

  "Tambaya uku Ummi kika min ajere sai dai kafin na baki amsar ki, ina da bukatar wata amsa daga gareki, Ummi meyasa ya sanda basu da amana meyasa basu san mai basu ba, Ummi shin dama muna da maƙiya ne wadanda zasu iya mana mungun ƙazafi, ana niyyar tozarta min ɗan uwana! Kuma wallahi bazan bar hakan ba sai na sanya duk mai hannu cikin wulaƙanta min ɗan uwana cikin JALALAR da bazasu taɓa iya fita ba, wannan yarinyar da ta samu zarrar kai ƙarar ɗan uwana Police station da mungun ƙazafi harma ta tako cikin gidan nan take faɗa min Magana son ranta Hmm Ummi! Sai na hana rayuwarta bacci a yayin da ni zanyi bacci a cikin zuciyarta, na rantse da Allah sai tayi danasanin taɓo ni, ta tsokono rigimar da bazata iya ba, wuta ce wacce zata babbakata ta ɗauko bazan taɓa ƙyaleta ba."

  Tunda ya fara Maganar Ummi take kallonsa cikin rashin fahimta da tashin hankali, tafi kowa sanin ɗanta mutum ne mai zafin zuciya da saurin fushi, bai cika yafiya ba, ba kuma a dannarsa ya dannu numfashi Ummi ta saki cikin yanayin damuwa tace.

   "Hisham yanayin maganganun ka da yadda ka hasala ya ɗaga min hankali domin kuwa hakan na gwada min cewa ƴan sandan da sukazo sun tafi da NAMEER, hmmm! Wani laifi NAMEER ya aikata wanda har zai kai Police su zo su tafi dashi, NAMEER ɗane mafi soyuwa a cikin zuciyata bazan taɓa bari wani mummunan abu ya samesa ba, rayuwata ne shi, bazan bar wani abu ya samesa ba, dan haka sanar dani wani laifi ake zarginsa dashi, nasan sharrin magauta ne domin kuwa kaf ƴaƴana babu mai jawo rigimar da zata tada hankalin mu."

  "Yaya Hisham meya faru da Yaya Nameer dama ni hankalina bai kwanta da zuwan wadannan Police ɗin ba, yanzu ina yaya Nameer ɗin."

  "Me yake faruwa ina daga sama ina jiyo hayaniyar ku, Hisham me nace maka ɗazu ba cewa nayi ka shirya kaje ka gaishe da Mamabisola ba ina shi NAMEER ɗin yake."?

  Suka jiyo Muryar Abba daga saman step yana tsaye, numfashi Hisham ya sauƙe tare da ɗaga kansa yace.

  "Abba ƴan sanda sun kama NAMEER wai suna zarginsa da Case ɗin fyaɗe."

  "Whattttttt!"

 Abba ya furta da ƙarfi Ummi wani irin sarawa kanta yayi itama tace.

  "Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, Nameer ɗin nawa shine aka yiwa wannan ƙazafin innalillahi wa'inna ilaihirraji'un na shiga Uku, Abban Hisham Case ɗin fyaɗe fa babban Case ne."

  "Ƙwarai kuwa babban Case ne, hmm! Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un! Bana tunanin cewa NAMEER zai aikata wannan laifin, Case ɗin fyaɗe."

  Abba yayi Maganar cikin tashin hankali, yana sauƙowa tsakiyar falon, Hisham runtse idanunsa yayi kafin yace.

  "Abba ka kira a sakar min ɗan uwana, wannan yarinyar da ta masa ƙazafi wallahi Abba bazan ƙyaleta ba."

 Zama Abba yayi yana kallon Ummi da hankalinta yayi mungun tashi har gumi take haɗawa ya cewa Hisham.

  "Wacce yarinya ce takai Case ɗin.?"

  "Abba wata ce naji ma suna cewa ƴar Jarida ce, har ikirari take cewa muddun Police ɗin basu amshi Case ɗin ba sai ta yi sanadiyar aikinsu, na rasa gane wacece ita da me take taƙama ƴar uban waye, kuma kamar tsoronta Police ɗin sukeji, ni dai Abba ka sanya a sako min ɗan uwana."

 Numfashi Abba ya saki yace.

  "Bazai yiwu ba Hisham, a yanzu bani da ikon sanyawa a saki Nameer Case ɗin fyaɗe babban Case ne da duk gatanka baza'a iya fitar da kai ba, idan naje na ce a saki NAMEER tamkar na zubar da mutuncin gidan nan ne domin kuwa duniya ɗauka zatayi ɗana yayi laifi nayi amfani da ƙarfi da dukiyata na sanya an sakesa bare kuma Case da ƴan jarida aciki dan haka mu ƙyale Nameer gaskiyar sa ta fitar dashi."

  A wani irin zabure Ummi ta miƙe tare da cewa.

  "Me kake nufi Abban Hisham! Kana nufin mu bar Nameer ya tozarta a ɓata masa suna ƙarshe ya ƙare rayuwarsa a gidan yari bayan kana da hanyoyin da zaka saka a sakesa, meyasa zamu barsa a wulaƙance, ko dan saboda ba ɗanka na cikinka HISHAM aka kama ba, ina ƙaunar Nameer fiye da yadda nake jin Hisham a cikin raina ji nake tamkar ni na shayar dashi nono bazan taɓa bari ya tozarta ba, Abban Hisham ya zamo wajibi a kanka ka sanya a sako min ɗana."

  Abba kallonta kawai yake tare da miƙewa shima yace.

  "Hmmm! Mata kenan duk girman ku, hankalin ku kaɗan sam baku da dogon lissafi a tunaninki kin fini son Nameer ne, ko da kaso ɗaya a cikin goma na Soyayyar Nameer da nakeji a raina baki ɗauki ɗaya ba, domin kuwa Soyayyar da nake masa yasa na sanya wasiyyar koda bayan raina ne a raba dukiyata biyu a bawa NAMEER kaso ɗaya sauran kaso ɗaya kuma iyalina suyi tarayya a kai ki faɗa min idan ba Soyayya ba me zaisa nayi haka, shin yanzu kina jin kin fini sonsa ne, ki faɗa min."?

   Bakinta Ummi ta toshe tare da silalewa ƙasa ta zauna tana sakin wani irin kuka mai cin rai Hisham kuwa zuciyarsa tafasa take, cikin wani irin yanayi na damuwa ya dubi Abba.

  "Abba kana nufin bazaka sanya a saki ɗan uwana ba, ina bazai yiwu ba Abba ka sake tunani ya zamo dole ɗan uwana ya kwana a gida yau zanje Police station ɗin kafin fito ya zamo wajibi a kanka mu dawo tare da Nameer, ki daina kuka Ummi bazan taɓa bari NAMEER ya wulaƙanta ba zanyi duk yadda zanyi ya fito ko da kuwa babu ƙarfin Abba."

  Yayi Maganar yana saka kai zai bar wajen Abba ne ya kira Sunansa.

  "Kai Hisham ka dakata karkaje ka aikata wani kuskuren."

 Juyowa HISHAM yayi a fusace tare da cewa.

  "Kuskure! Hmmm! Domin gyara wani kuskuren dole sai an tafka wani kuskuren, tunda baka da karfin dawo da Nameer ni zan nemo wannan ƙarfin."

  Yayi Maganar tare da ficewa Abba na kiransa ko sake waiwayowa baiyi ba, Tutu share hawayen fuskarta tayi tare da miƙewa ta haura sama.



 Hisham yana fita Police station ɗin ya nufa abun baƙin ciki da takaici Nameer ya iske a cell yana zaune tamkar wani marar galihu idanunsa ya runtse cike da baƙin ciki, wajen Sargent Bala ya nufa tare da tsayawa a gabansa yace.

  "Sargent Bala waye ita meye sunanta ka bani bayani akanta har adress ɗin ta ina bukata."

  Yayi Maganar yana watsawa Sargent Bala kuɗi, kuɗin Sargent Bala ya ɗauka tare da ɗago kai ya dubi Hisham.

   "Jidda Muhammad Bello, cikakkiyar ƴar Jarida, ƴar unguwar ORA layin igbaja gida mai number 234."

  Numfashi Hisham ya saki tare da kuma cewa.

  "Ina Dpo ina son magana dashi."

  "Dpo yana ciki zaka iya shiga."

 Kansa Hisham ya kaɗa tare da shigewa nocking yayi kafin Dpo ya basa izinin shigowa.

  Shiga Hisham yayi tare da tsayuwa ya harɗe hannunsa a ƙirjinsa Dpo dubansa yayi cike da mutuntawa yace.

  "Hisham Barka da zuwa Bismillah ka zauna mana."

 Kujerar Hisham ya duba tare da takowa ya zauna yana cewa.

  "Barka Dpo kayi mamakin ganina ba."

  "A'a banyi mamaki ba duba da ɗan uwanka yana station ɗin nan, nasan dole zakazo sai dai bansan da wata bukatar ka shigo office ɗina ba.?"

  "Ka san bukatar da ta shigo dani, belin NAMEER nake bukatar ka bani, duk da kunyi kuskuren ijiyesa a inda yafi ƙarfin zama."

  "Sorry Hisham da ace zamu iya bada belin NAMEER to da bazamu je mu kamasa ba, kayi haƙuri bamu da damar sakin NAMEER har sai bincike ya tabbatar cewa bashi da laifin da ake zargin sa, saboda Case ɗin sa mai girma ne."

 Cike da mamaki Hisham ke kallon Dpo tare da cewa.

  "Whatt! Dpo kasan abinda kake faɗa min kuwa, Dpo wannan itace kawai alfarmar da zaka mana a rayuwa karka manta Matsayin da kake kai yanzu silar arzikin mu ne, sannan ka saka a ranka muddun NAMEER ya fito zaka haura wannan matsayin, well idan ma bazaka iya kyauta ba, ka faɗi farashin ni zan biya ko nawa kake bukata, koma ya za'ayi NAMEER ya fita daga wannan kurkukun da kuka jefasa."

  Murmushi Dpo yayi yace.

  "Ka kasa fahimta ta Hisham, tabbas kun min rana domin kuwa ko wani irin matsayi na kai kune sila sai sakin NAMEER kan iya jawowa na rasa aikina gabaki ɗaya, karka manta Case ɗin fyaɗe ake tuhumar sa dashi wanda gata da faɗa aji gami da dukiyarka bazasu taɓa ƙwatarka ba, da fito da NAMEER zai yiwu to da mahaifinku shine mutumin da zai fara kirana, naso ace ina da halin taimakawa NAMEER da sai na fi kowa farin ciki.''

  "Hmm! Okay na fahimta idan kai bazaka iya ba akwai na gaba da kai, sai dai ka sani ka yiwa kanka babbar asara."

 Hisham yayi Maganar yana tashi tare da ɗaukar wayarsa ya fice numfashi Dpo ya saki tare da bin ƙofar da kallo ya furta.

  "Ikonku da kuɗinku bazai taɓa fitar da NAMEER ba sai dai gaskiya da tsantsar bincike ya fitarsa, kana da matsala Hisham zafin rai gami da izza sun maka yawa uwa ba ƙasƙantar da Mutum."

 Dpo yayi Maganar yana mai da kansa ga aikin sa.



 Ko da Hisham ya fito bakin cell ɗin ya tsaya cikin ɓacin rai murmushi Nameer ya saki tare da cewa.

  "Wai damuwar me kake ne Hisham, akan wannan ƙaramin lamarin kake damuwa.?"

  "Ƙaramin lamari wannan kake ƙaramin lamari, wankin hula na shirin kaimu ga dare amma kana kiransa ƙaramin lamari, Hmm! Gaskiya ko waye ya shirya wannan tarkon yayi dogon lissafi akanmu, ina zuwa."

 Hisham yayi Maganar yana juyawa zai bar wajen, yaji muryar NAMEER.

  "Ina Ummi da Abba ina fatan hankalin su bai tashi ba."

  "Hmmm! Kaima kasan dole hankalinsu zai tashi."

 Yayi Maganar yana saka kai ya fice daga Police station ɗin motarsa ya shiga yaja karfi babu inda ya nufi sara Ora cikin mintuna kaɗan ya samu damar shiga unguwar baisha wahala ba wajen gane layin igbaja, kasancewar yasan wajen, parking yayi a ƙofar gida mai 234 tare da harɗe hannunwansa.




 *********



 A tsugunne taga Basmah gaban Umma cikin sanyin jiki ta ƙarisa domin kuwa tasan duk yadda akayi Basmah ƙarar ta ta kawo, ƙarisawa tayi tare da zama gefe tana cewa.

   "Umma sannu da hutawa."

  A hasale Umma tace.

   "Sannun gidan ubanki, nace sannun gidan ubanki, Jidda ashe dama mahaukaciya ce ke ban sani ba, so kike ni ki kasheni ki raya iyayen wasu, ina kiranki da sunan Alkairi kullum sai kuma gashi kina niyyar Kawo min masifa ina ke ina faɗa da ahalin Abdulzahir Hmm! Tabbas cikakkiyar mahaukaciya ce ke Jidda."

  Idanunta Jidda ta runtse tare da jin haushin Basmah cikin sanyin murya tace.

  "Umma mahaukaciya kuma, kenan Umma saboda su masu kuɗi ne shine sai mu bari su zalunci talakawa muyi shuru Umma kefa kikace na taimaki duk wanda na gani yana bukatar taimako, muddun ina da halin taimaka masa meyasa zan gani nayi shuru bayan zan iya bata gudunmawa Umm........

  "Ki rufe min baki dan ubanki! Da nace ki taimaki al'umma cewa nayi kisa Rayuwarki a cikin haɗari, ita yarinyar bata da iyayene da zasu kai ƙara sai ke gwali, duk masifar da muka shiga a baya bai isa haka ba Jidda har sai kin ƙara ɗauko min wata masifar so kike bakin ciki ya kasheni da badan wannan Yarinyar Yar albarka Basmah tazo ta sanar dani ba da shikenan sai ki jawo mana masifa, to muddun ni ce uwarki, ki cire hannunki a cikin wannan Case ɗin."

  Kanta ta sunkuyar ƙasa tana sauraren faɗan mahaifiyarta kafin ta ɗago tace.

  "Kiyi haƙuri Umma."

"Ba haƙurinki nake son ji ba, ki fita daga cikin wannan faɗan da babu ruwanki tashi ki bani waje."

  Umma tayi Maganar tana tashi ta shige ciki, ɗago idanunta tayi ta kalli Basmah tare da girgiza kai zatayi Magana sukaji muryar yaro.

  "Assalamu alaikum wai inji wani a waje Jidda ƴar tasha tazo ko shi ya shigo da kansa."

  "Jidda ƴar tasha! To fa a gidan nan kuwa.?"

  Jidda tayi maganar cike da mamaki, Basmah ce ta taɓe bakinta tare da cewa yaron.

   "Jeka tana zuwa."

 "Yaje ina zuwa zakice bakiji sunan daya ambata ba Jidda ƴar tasha, gani nayi gidan nan babu ƴar tasha."

 Shidai yaron bai tsaya ba yayi ficewar sa, Basmah cewa tayi.

  "Idan har lissafina dai-dai ne kinje gidan Iyabo idan har kinje Kuma an kama NAMEER to babu shakka Hisham ne yazo ƙofar gidan nan kuma ya aiko a kiraki da Jidda ƴar tasha."

  Zaro idanunta Jidda tayi tare da furta.

   "Hisham! Kuma a gidan mu.?"






Share and comment my fan's🥰






  *_For more information ***_*