ZAMANINMU (Hattara ƴan'mata)

Chapter 3 chapter 3

by @autararewa101

🤦🏽‍♀️ZAMANINMU🤦🏽‍♀️.*

_(HATTARA YAMMATA)_




*NA*

*RUKAYYA IDRIS BALAH*

*(AUTAH)*




*Wannan littafi kirkirarran labari ne, Banyishi dan cin zarafin wani ko wata ba.Nayi ne dan fadakarwa, ilimintarwa tare da nishadantarwa.idan yayi daidai da rayuwarka/ki to arashi ne.*


__*GODIYA*__

INA GODIYA GA ALLAH (S W A) DAYA BANI IKON RUBUTA WANNAN LITTATI,ALLAH KARA DADIN TSIRA GA SHUGABANMU ANNABI MUHAMMAD (S A W),DA ALAYENSA DA SAHABBAN AMEEN.



__~GARGADI~__

~BANYARDA~ ~WANI~ ~KO~ ~WATA~ ~YA~ ~JUYAMAN~ ~LITTAFI~ ~BA~ ~TARE~ ~DA~ ~AMINCEWA~ ~TA~ ~BA~, ~A~ ~KIYAYE.~


*SADAUKARWA*__

NA SADAUKAR DA WANNAN LITTAFI GA MAHAIFANA,

*MALAMA* *AMINA* *IDRIS*

*MALAM* *IDRIS* *BALAH* *MAI* *GORO*

ALLAH YAYIMAKA RAHAMA AMEEN.


*Ina Mika godiyata gareki* *uwar room KHADIJAH ADAM IDRIS* *(shalelen kainuwa)Allah yabar zuminci ameen.*

*God bless you my Aunty.*



*INA* *JINJINAR* *BANGIRMA*

*AUNTY* *HAUWA* *TARE* *DA* *DOCTOR* *MARYAMA* *ALLAH* *YABAR* *ZUMINCI* 💋💋


*NOT* *EDITING* 🤗


بسم الله الرحمن الرحيم



🅿️3

📝 YASIR Yana isa G R A ya tadda su JABIR a falo suna kallo a system.


Yayi sallama

Bayan sun amsa,ya zauna suka gaisheshi.


Ya ce "Ina UMMAH"?


UMAR ya amsa da tana off-site dakin ABBA.


Saman ya haura Naga yabiyo ta wani hadaddan falo komai na falon kalar brown ne da milk.


Yayi sallama dai-dai UMMAH ta fito da ga dakin ABBA.


Kaman daman jiranshi takeyi ya ta fara fada,baka sati 2 baka zo garinnan ba Kai ba mata ka aje a garin ba,Amma baka iya zama kayi aikinka.


Kamo hannunta yayi ya ce "Haba UMMANA kiyi hakuri mu gaisa Mana"


Bayan ta zauna kan daya daga cikin kujerun dake falo,kannan ya samu damar zama kasan kafet din ya tankwashe kafafunshi Yana kallanta .


Ya ce" afuwan UMMANA"Yana hade hannuwanshi wuri daya alamar ban hakuri .


Shafa kanshi tayi ta ce"Allah ya albarkaci rayuwarka da sauran yan'uwanka.


Ameen UMMAN MU Allah ya karamaku nisan kwana.


Amen Amma kasan me zakayi dan kaga farincikina .


Tau UMMAH kuyi hakuri adan karaman lokaci insha Allah komai zai daidata.


Tau Allah yarda ka jira ABBANKU ya fito ku gaisa .


Dai dai ta fita da ga falon ya amsa da "To".



Jima kadan ABBAH ya fito ya gaisheshi cikin girmamawa.


Ya amsa cikin sakin fuska.


Ya Kara da ce wa duk naji irin maganar da kukayi da UMMANKU,karka damu MAGAJI na gano matsalarka Amma Insha Allahu komai ya zo karshe.tashi ka tafi ni zan fita cikin gari.


Haka ya tashi sororo kamar Wanda kwai ya fashewa a ciki.


Yayima su UMMAH da kannanshi jabir da umar sallama ya nufi BARHIM.



______________


__ASALINSU_


Asalin iyayensu haifaffun garin DUTSIMMA ne daya da cikin local government din jahar KATSINA STATE. Sunan mahaifinsu Alhaji UMAR HASHIM UMAR.


A wannan lokacin Alhaji UMAR HASHIM UMAR duka iyayenshi sun rasu Yana zaunene a hannun Kanan mahaifinshi wato Alhaji YUSUF UMAR matar shi ta rike Alhaji UMAR HASHIM UMAR,Anan yayi dukkanin karatunshi tunda ga matsayin primary School aka kaishi bording school BINDAWA. Bayan ya gama Alhaji YUSUF HASHIM ya hadashi da Yan uwanshi guda biyu ya kaisu B U K KANO anan kowanne ya kammala digreen shi na farko.bayan sun dawo gida kowanne aka bashi kasuwancinshi a hannu shi Alhaji UMAR HASHIM UMAR aka budemashi shago a cikin centeral market cikin garin katsinan dukko shida Dan Alhaji YUSUF din ya kamamasu gida a katsina a cikin unguwar kofar dirbi sukaci gaba da harkokin kasuwancinsu.


Daman shi Alhaji UMAR HASHIM UMAR shi kadai iyayenshi suka haifa a wannan lokacin.


Cikin ikon Allah business dinsu ya bunkasa musamman shi Alhaji UMAR HASHIM UMAR saboda an hadamashi da dukiyar da iyayenshi suka barmashi bayan sun rasu.


A bangare daya Kuma Yana soyayya da masoyiyarshi wato HINDATU itama haifafiyar garin DUTSIMMA ce babanta Yana koyarwa a G. D .S.S DUTSIMMA .


_BAYAN_ _SHEKARA_ _DAYA_


Saida Alhaji umar ya tabbatar sun mayar da hankalinsu akan business dinsu kafin ya fara yimasu maganar aure.inda Alhaji UMAR HASHIM UMAR ya gabatar da HINDATU shi Kuma Dan uwanshi Abdullahi ya yadu da wata nutsasiyar yarinya HAUWA'U a anan unguwar filin samji.


Cikin ikon Allah ba'a dauki lokaci ba akayi aurensu inda aka siyanmasu gidaje anan cikin KASTINA .


_BAYAN_ _AURANSU_ _DA_ _SHEKARA_ _26__


A lokacin Alhaji UMAR HASHIM UMAR ya Kara zama babban mutum Yana da yara guda 3 USMAN, BISHIR, sai auta SAFIYYA.


Daga su haihuwa ta tsayamasu.



Hajiya HINDATU ta Kara zama babbar mace tana rayuwa da yaranta guda uku cikin jindadi da annashuwa.



Alhaji ABDULLAHI shima Yana zaune da matar shi HAUWA'U lafiya da yaransu biyar IBRAHIM shi ne babba sai mai bimasa YUSUF wato sunan mahifin Alhaji ABDULLAHI kenan.sai UBAIDULLAH,FATIMA da karamarsu BILKISU.



A lokacin USMAN Yana da shekara 25, BISHIR nada 22,sau autarsu SAFIYYA tana da 18 years.



Inda USMAN yake Aji karshe A B U ZARIYA Yana karanta LAWYER saboda ya ce gwmma ya sauya course saboda Babanshi BUSINESS ADMINISTRATION ya karanta.

Shiko BISHIR Yana aji 2 inda shi ya gaji mahaifinshi yake karantar business administration.


Itakuwa Autah little

SAFIYYA a wannan lokacin tana S S THREE bording school din AJIWA local government


~BAYAN~ ~SHEKARA~ 22

_22_ _YEARS_ _LETTERS_

Garin ABUJA QUATTERS wani kyakkyawan sairayi ne durkushe a gaban wata mata mai kwarjini da cikar haiba,kamaninta zai nunama Bata tsufaba domin bazata gaza 36 years ba,HAJIYA SAFIYYA KENAN mata ga Alhaji UBA KWANGILA.

Saurayin da yake durkushe gabanta ya ce "AUNTY Dan Allah ki barni gobe naje KATSINA nan"

Ta nisa a hankali tare da maida hankalinta wurinshi ta ce "banaso kana nisa da ni YASIR saboda kaga FARRAH ta koma can shi ne kaima zaka gudu"?

A a AUNTY kinsan bana wuce 2 days saboda aikina.


Tau Allah ya kiyaye hanya Kai gaisheman da su Yaya.tana nifin (ALHAJI USMAN UMAR YAYANTA DA ALHAJI BISHIR UMAR).


tau AUNTY insha Allah zasu ji.


Wannan shi ne asalin tahowar YASIR da ga ABUJA zuwa KATSINA.


Bayan auran Alhaji USMAN UMAR da hajiya MARYAMA,ALLAH ya azurtasu da yara guda 5 AUNTY ZEENAT it's ce babab tana aure a KADUNA unguwar sarki sai mai bimata tana HALIMATUS SA'ADIYYA tana auren wani DOCTOR suna zaune anan cikin G R A wurin gidan babansu.sai YASIR Wanda a yanzu yake aiki a CBN BANK na ABUJA yana zaune wurin AUNTY SAFIYYA maman FARRAH kenan JABIR yake bimashi sai karaminsu UMAR suna kiranshi da ABBA saboda sunan baban su ALHAJI USMAN aka sanyamashi.


Alhaji BISHIR UMAR yaranshi biyu da ga HUSNAH da take aure a ABUJA sai auta NUSAIBA da take da 10 years.


HAJIYA SAFIYYA diyar ta daya wato FARRAH.

saboda ta dade Bata samu haihuwa ba bayan auranta da Alhaji UBAH,sai bayan shekara 10 da ga ita Basu Kara samuba.


Wannan shi ne takaitaccen tarihin familyn su ALHAJI BISHIR UMAR Wanda yake zaune a BARHIM cikin garin KATSINA.


____________


YASIR ingarman namiji ne kyakkyawan gaske dukda ba fari bane sosai Amma Yana da diri tafiyarshi ma abin kallo ce Kuma Broad minded ne.uwa uba Kuma idanunshi masu kaman na Yan chaina 🤣🤣 hakan yasa FARRAH Bata San hada ido da shi saboda Yana sanyata faduwar gaba jijiyoyin jikinta duk suyi sanyi,shi Kuma hakan yasa ya ke cemata MUNAFIKA saboda duk abinda zai mata Bata kallan idanunshi saboda ta ce Yana da ido irin na UMMAHN shi saboda ita UMMAH MARYAMA haifafiyar fulanin BAUCHI ce.


FARRAH ta gudo KATSINA ne saboda Bata San zamanta da YAYA YASIR wuri daya .domin shi a lokacin bai Dade da fara aiki a CBN BANK na ABUJA ba,Yana takurata sosai dan inhar yananan to baya barinta zuwa ko ina.hakan yasa da taga Bata komai saboda lokacin ta gama secondary School ta hada kayanta ta ce ma AUNTY SAFIYYA a kaita KASTINA hutu dakyar ABBANTA ya amince saboda Yana kaunarta baya so tayi nesa da shi ..


To shi ne asalin tahowar ta Bata Kara komawa ba har DADY BISHIR ya sanyata a ALKALAM UNIVERSITY yanzu tana second semester a shekarta ta farko.da farko direver yake kaita Amma ta tada balli saida aka Bata key din motar take zuwa da kanta.


YASIR baya cikakken sati 2 ba tare da yazo KATSINA ba hakan yasa UMMAN shi takeyimashi fada kullun Yana faman yawo kaman Wanda ya aje mata🤣😜.



HAkan yasa FARRAH take Kara jin ta tsaneshi saboda yawan zuwa da yakeyi,Kuma dan gulma idan ya zo baya zama a gidansu sai gidan dady BISHIR.( 🤔 Ka ji su FARRAH harda su gori sai ka ce itama gidansu ne.


_BACK TO STORY_


MUN DAWO LABARI ✍️.






By


AUTAR AREWA


✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️