Chapter 25 Chapter 25
ZAMANINMU!!!!!
(Hattara ƴan'mata)
*HAPPY JUMA'AT* *KAREEM TO ALL MUSLIM* *UMMATI* 🌹🌹🌹.
*Ina miko gaisuwa aunty* *safiya* *Muhammad*
*I* *love you lodi lodi* 🥀🌷🌷🌹🌹🤣🤣
Bismallahi Rahamir Rahim.
🅿️25
📝Yana gaf da karasa cin abinci Momy ta fito ganin jakarshi akan kujera yasa tayi turus a wurin tana kallanshi.
"Momy Ina kwana "ya mike da teshu a hannun shi.
"Lafiya Lau badai har tafiya zakayi ba"
"Wallahi ko Momy gobe Ina da aiki a office dukda ansanar masu,To sai nake ganin tunda da sauki gwamma kawai na tafi" Daidai ya rataya jakar sa a kafada.
"To ni Magaji sai dai na ce Allah ya kiyaye,sannan ka tafi da magungunan ka"?
"Na dauko su insha Allah zan rinka sha"Yana kokarin daura agogo a tsintsiyar hannunshi.
"Hmmm Ai bari kaji idan har bazaka rage wannan shegen tunanin ba to kullin kana hanyar ganin likita,Kuma ka dage da addu'a domin neman zabin Allah insha Allah komai zai wuce".tana Kai karshen maganar Farrah ta fito daga dakinta tana kokarin daura karamin dankwali a kanta.
Bata san da mutane a falon ba Dan haka ta wucewarta kiching.
Da manyan eyes din shi ya bita da kallo harta shige.
Sosai yaba Momy Tausayi,Duk da bata San asalin abinda ya hadasu ba Amma tana tabbatar kanta ba karamin so yake yiwa Farrah ba.
Kallanta ta maido gareshi ganin har yanzu hankalinshi baya wurin yasa tayi gyaran murya.Amma da yake Yasir namijin duniya ne sai yayi saurin wayancewa Yana sosa keya alamar jin kunya.
Momy murmushi tayi tana cewa "Wallahi kada ka bari wannan tinanin ya hanaka yin aikinka idan ba haka ba zan yima Jabir campen"ta karasa fada tana yimashi dariyar zolaya.
Murmushi yayi Yana Kara shafa Dan madaidaicin gemunshi"A a Momyna ai nasan bazaki yiman haka ba idan ko hakane to daga Abuja sai dai acemaku na mutu kawai.
Har a lokwcin Farrah Bata fito ba.
Ita kuwa sai da ta zo fitowa bayan ta dauko kanifarin da zatayi amfani da shi ta ji maganar shi Hakan yasa tayi saurin komawa saboda yadda taji gabanta ya fadi, a ciki ranta tana addu'ar Allah yasa gidan zai bari gaba daya ita kam yau da taji dadinta.
Har suka fita waje da Momy duk tana jin su irin hirar da suke yi a ranta ta ce "Ji shi Dan lambo kamar jiya ba shi ne aka kwantar a asibiti ba?Amma a fuska idan ka ganshi simi-simi kamar baya magana nan ko tsabar miskilanci ne cikin ranshi.Buntsiro Baki ta fice daga kiching din.
Momy har bakin mota ta raka Yasir tana kara yimashi nasiha tare da nunamashi mahimmancin addu'a da hakuri,Kafin tayi mai sallama.
Har ya tayar da motar Yana daga mata hannu.
Bayan yayima Baba Auwal alheri na kudi ya doshi fita daga estate din bakin shi dauke da addu'a Yana jin wani saban kuzari Yana kara sauko mai saboda irin shawararin da Momy ta Kara ba shi.shiyasa har gobe yake jin dadin zama da ita sabanin Ummahn su da take da fada,Ga shi Bata Basu lokacin ta ballantana ta fahimci damuwar shi.
Da wannan tinanin ya fara fita daga garin katsina ya Kara gudun motar shi dan so yake ya taras da su Dady a can kafin su juyo.
A bangaran Farrah kuwa tana jin fitar motar shi ta hau tsalle saboda tsabar farincikin daya lullubeta.
Tana cikin murna har bata san Momy ta shigo ba.
Hannuwanta ta harde a kirji tana kallan ikon Allah a ranta tana saka yadda Yasir zai sha dabir da wannan yarinyar dan ta fahimci rashin jituwar dake tsakanin su ita ta hana Farrah fahimtar irin San da yake yimata.
Tana cikin tsallanta kamar ance ta kalli bakin kofar taga Momy a tsaye tana kallanta.
Sosai taji kunya ta kamata Dan tasan Momy ta fahimci abinda take yiwa murna.
Cikin daure fuska Momy tace mata "Wallahi kinji kunya Farrah saboda dan'uwan ki ya tafi shiyasa kike wannan murnan ko?ke ko kunya bakya ji?shiko bawan Allah duk abinda kika ce kina so Yana rawar jiki yake siyamaki,Amma saboda Baki tsoran Allah baki da wanda kika tsana nan duniyar irin shi,to wallahi kibi a hankali dan akwai ranar kin dillanci.ke sakarai har yanzu baki San ciwon kanki ba hmmm Allah dai ya shirya ki.Tana kaiwa karshen nan ta wuce site dinta tabar Farrah anan da duk kunyar duniya ta gama rufeta.
Tana ganin ta shige ta ce "Ai kema dan bakisan irin cutar da yayiman ba shiyasa,Ai mugun nasan alhakina ne yake bibiyar sa shiyasa duk ya zama abin tausayi,Niko hankali na kwance Allah yasa daga can ya wuce zan"tana Kara murguda Baki kamar Yana gabanta.(ihu bayan hari kenan tunda Baki iya yi a gaban shi 🤣🤣) .Ta shige bedroom dinta zuciyarta cike da farinciki.
_____________________
Su Dady Karfe 12:20am daidai ta kawosu birnin tarayya Abuja daret unguwa su Aunty Safiyya suka nufa kasancewar unguwar masu kudi ce hakan yasa ba wata hayaniya kowa yana cikin gidan shi.
Daidai wani tamfatsetsen Ash din gate naga sunyi horn mai gadi ne ya bude masu daman Hajiya Safiyya ta sanar da shi zuwan yan'uwan nata,bayan sun gaisa Yana yimasu barka da zuwa ,dan haka ba tare da bata lokaci ba suka kutsa Kan motar su harabar gidan.
Akwai ta zara daga bakin gate din zuwa cikin gidan dan haka inda aka tana dan ajiye motoci anan suka yiwa tasu masauki.
Suna firfitowa kanwar tasu ta karaso cikin murna dan ganin isowar Yan uwan nata.
"Alhamdlillah Allah na godema daka kawomin Yan"uwana lafiya"cewar Hajiya Safiyya tana karasowa gare su.
Farin cikin fuskarsu ya karu ganin yar kanwar tasu cikin kwanciyar hankali.
"Sannunku da zuwa Yaya"
"Yauwa kanwarmu kinganmu sai yanzu ko"
"Wallahi yaya kunyi sauri ma,ku taho mu shiga ciki"
Suna kokarin juyawa suka hango mai gadi ya bude gate alamar akwai Wanda zai shigo,a tare suka juya dan ganin waye.
Motar Yasir sukaga ta shigo,Dan haka basuyi mamaki ba dan sunsan shi Idan ya kama sitiyarin ba wasa.
Jiranshi sukayi ya Kara so aunty tana cewa"yanzu soon saida ka taho saboda rigima ko?
Shidai baice komai ba saboda gajiyar da yayi ga shi Yana so ya watsa ruwa a jikinshi ya sauke faralin dake kanshi.
Gaba dayansu suka dunguma zuwa cikin gidan,shi Kuma Yasir ya wuce site din da yake sauka.
By
AUTAR AREWA.
✍️✍️✍️✍️✍️✍️