DARASI

18/19

by @rabiattu0444

*✨🌈DARASI!!!🌈✨*

(Topic)

 *` _``a love&```_ destiny story*



 By

Ummu Maher(Miss green)🍀💚



*Littafin na kuɗi ne ban yarda ki karanta mun baki biyani ba,Gamai buƙata n cigaban labarin zai biya ₦300 normal* group...Vip group

 ₦500... Special₦1k....zaku iya Turo da katin MTN ta wannan number ***

 ko kuma ku tura ta wannan account number 2212328303

RABIATU BASHIR

Zenith Bank.



  *Free page*


18/19



Maganar ƙarshe da mahaifin Ammar ya faɗa shine"Ammar kada ka wulaƙanta wannan yarinyar kada ka juya mata baya,don kaga bani da rai,kada ka taɓa rabuwa da ita ma'ana ka saketa matuƙar ka saketa to ka saka a ranka babu ni babu kai."



wannan maganar ita ce ta ƙarshe da ya faɗa ya fara wani irin tari mai sarƙe maƙoshi daga nan rai ya yi halinsa,babu irin kukan da Ammar bai yi ba na rashin mahaifinsa ga abu goma da ashirin wai kada ya yarda ya saki Sakinat,shi ya rasa me yasa ma ƙwata2 ko kallonta ba yasan ya yi,yadda kasan wata mujiya haka take a wajen Ammar amman ya zamar masa dole ya fara sakin jiki da ita ko don nasihar mahaifinsa.




Bayan wata biyu rannan Sakinat tana zaune suna hira da Ammi,aka yi sallama da gudu Sakinat ta rungume Falmata ƙawarta ta yarinya ta,sosai taji daɗin zuwan Falmata don tunda ta yi aure ko dangin mahaifiyarta basu zo ba,don basu san ma ta yi auren ba.



Kalle2 Falmata ta shiga yi sosai irin kallon tsaf ɗinnan,Ammi sai kallonta take tana mamakin hali irin na wannan baiwar Allah.



Sai da Sakinay ta ɗan dunguri Falmata sannan ta dawo cikin hayyacinta,tana harar bayan Sakinat don gani take Sakinat bata dace da wannan gidan ba ita ce ta dace dashi,don haka ko ta halin ƙaƙa sai ta zauna itama a wannan gidan kuma ta fitar da ƙawarta Sakinat.



Tunda Falmata tazo gidan babu abinda take sai zuga Sakinat akan cewa wai tsabar baya sonta har yanzu yaƙi ya kaita gidanta ya barta a gidan iyayensa,wani lokacin kuma ta ce kinga gidansu kamar aljannar duniya ko ina gwanin sha'awa,duk yadda akayi komai shi yake a gidan kuma yana jin maganar mahaifiyarsa.



Da ya ke Sakinat sokuwa ce sai maganganun Falmata suka fara tasiri aranta har ta fara ganin ayanzu za ta iya fito na fito da Ammi don tun ba yau ba tana ganin irin abubuwan da Ammar ya ke wa Ammi,yana matuƙar girmama maganarta don har yafi jin maganar mahaifiyarsa da ta mahaifinsa.



Acikin satin Ammi babu irin rashin kunyar da ba ta gani ba awajen Sakinat kuma ta lura Falmata ce ke ƙara zugata,don haka duk sai ta watsar da su ta cigaba da sabgoginta,don dama Khalisat tana boarding Ammar kuwa ya yi tafiya zuwa ƙasar England wani aiki.




Ƙwanan Falmata biyar ta haɗa kayanta don tafiya gida,ta tambayi Sakinat ina ne ɗakin Hajiya,babu musu Sakinat ta nuna mata ta ƙwanƙwasa alokacin Ammi tana azkhar.

Ammi ta buɗe mata ta shigo tana gaida Ammi,ta amsa tana mamakin ganinta bata gama mamakin ba ta jiyo Falmata tana ce wa.



"Da man gida zan tafi shine na ce bari inyi miki sallama sannan in faɗa miki wata magana don nasan baki sani ba,lulluɓin biri aka yi muku.



Da mamaki Ammi ta ke kallonta tana mamakin hali irin na Falmata na munafurci,wato don taga ƙawarta ba ta nan shikkenan sai kuma ta yi gulmarta.



"Hajiya Sakinat fa kafin ta auri ɗanku sai da aka cire mata ciki har sau biyu,kuma wallahi har yanzu bata daina bin maza ba".



da sauri Ammi ta ɗaga mata hannu sannan ta ce cikin tsawa"get out in my room".



da sauri Falmata ta fito har tana haɗa hanya tana da na sanin zuwa wajen Ammi don yadda kasan zaki haka ta juye mata.



Akan hanya suka haɗu da Sakinat sannan ta rakata har bakin gate,tana mamakin sauyin Falmata lokaci ɗaya.





Ammar yana dawowa Ammi ta sakashi a gaba da ya tafi da Sakinat sabon gidansa na Abuja,babu yadda ya iya haka ya tafi da ita ransa baiso ba.




Wannan tafiya itace ta zamewa Ammi wannan mummunan tabo a rayuwarta don tun daga ranar Ammar bai sake zuwa wajen mahaifiyarsa ba,don tun bayan komawarsu da Sakinat ta ga Ammar ba ya ko kallonta ballan tana ta saka ya yi mata magana.


Da kanta ta nemi Falmata suka haɗa kai aka raba tsakanin ɗa da uwa Ammar da Ammi.








*Cigaban Labari*


  *Fahima*

-------------------


A yanzu Amma ta matsamin wai acikin mane ma na wai in fito da mutum ɗaya don ita ta gaji da kallona babu aure,abin har mamaki ya ke bani don har yanzu ko shekara sha biyar ba amman ake min zancen aure.



A cikin masu sona aƙwai wani Alhaji Tasi'u mai nera,shine wanda Amma tafi don yana matuƙar jiƙata da kuɗi.



Ita kuwa Fahima ta yi mugun tsanarsa don mutumin mugun ɗan iska ne duk ranar da yazo sai ya nemi daya taɓa jikina ni kuma in ƙi yarda.


Kuma kamar maye gobe ma sai ya dawo,kuma a ƙalla ko da baiyi shekara hamsin ba to kaɗanne.





*miss green ce*