Halin Dana Shiga...

1

by @shooly84

🤳🏻


💘 нalιn dana ѕнιga...💘


*~Labarin gaske ne~*



© ᴬYˢᴴᴬ ᴹᴬᶜᴴᴵᴷᴬ



*Arewabooks@Shooly84*





*S͢A͢D͢A͢U͢K͢A͢R͢ WA G͢A͢R͢E͢K͢U*...


*ᴷᴴᴬᴰᴵᶻᴬ ᵁˢᴹᴬᴺ*

*ᴺᴬᴮᴵᴸᴬ ˢᵁᴸᴬᴵᴹᴬᴺ*

*Ɗᴬᴵᵞᵞᴵᴮᴬ ᴵᴰᴿᴵˢ*

*ᴴᴬᵁᵂᴬ ᴬᴸᴵᵞᵁ ᴿᴬᴮᴬᴴ*

*ᶠᴬᵁᶻᴵᵞᵞᴬ ᴰᴬᵁᴰᴬ*



*DAGA MARUBUCIYAR:*


*MUNAH*


*MUSO JUNANMU*


*ZARAH HAYAT*



*Gani Allah ya nufeni da sake dawo maku da wani sabon salo, Allah ya bani ikon rubuta abinda zai amfanar ga al'ummar duniya, yadda na farashi Allah ya bani ikon gamawa lafiya Ameen*




💘 1 💘




*Da sunan Allah mai rahama mai jin ƙai!*






*Halin dana shiga* arayuwata, haline mawuyaci mai rikitarwa sa'an nan mai ban al'ajabi.


In'an juya ta wani ɓangaren kuma zai zamo abin ban haushi mai ban takaici, wasu da yawa kuwa na tabbata zasu zamo ne masu yin dariya agareni...


wanda ba zan so mai karatu ya zamo maiyi mani dariya ba akan *halin dana shiga* ba...


Abinda zan so da kai, ka zamo mai tausayawa a gareni da kuma bani shawarar abin daya dace nayi game da wannan *halin dana shiga*.


Abinda nake son fara sanar da kai shine ni ɗin nan anjefani cikin damuwa wadda ba zata taɓa barina ba har illah masha Allahu, domin haƙiƙa anyi min illah babba cikin rayuwata....


Mai karatu bari kaji irin mawuyacin *halin dana shiga* cikin rayuwata.



*_Halin dana shiga_*



Ni na zamo ƴa ta hudu daga cikin jerin ƴaƴa shidda da iyayenmu suka haifa, mahaifinmu Alhaji Bello Jalingo ɗaɓ kasuwa ne wanda Allah ya azurtashi da arziki na ban mamaki...


Sai dai gaba ɗaya harkokinshi yana yinsu ne a ƙasashen ƙetare, dan haka ne bai fiye zama tare damu ba, cikin wata biyu ba yayin cikakken sati biyu a gida Najeriya.


Amma fa akwai kulawa irinta Uba da ƴaƴanshi, duk wasu harkokinmu dake kanshi yana biya mana su, yana kula da duk wasu al'amuranmu na rayiwa...


Kulawa da tarbiyarmu yana hannun mahaifiyarmu Hajiya Karimatu, wadda mu mukan kirata da Mami, ita kuma ta zamo mace mai tsananin haƙuri da kawar da kai da rashin nuna damuwarta akan al'amura da dama.


Babban burin rayuwarta shine kwanciyar hankalinmu, ta tsani abinda zai taɓa mana hankali, sau tari akan gane damuwarta ne idan ɗanta yana cikin mayuwacin hali...


Wannan yasa mutane da yawa kan ce wai ita mai ƙulafucin ƴaƴa ce...




Ita da mahaifinmu tushensu ɗaya, fulanin Jalingo ne ta cikin jihar Taraba, haka kuma sun zamo ƴan uwa dan sun haɗa kakanni ta ɓangaren iyayensu maza.


Tun kafin mahaifinmu yayi aure yake harkokin kasuwancin shi a Kaduna, bayan auran Mami ma ya taho da ita Kaduna sukaci gaba da zama yana gudanar da harkokinshi har Allah ya azurtashi da dukiya da ya'ya.




Babban wanmu Hashim shike tsaye akan harkokin Babanmu dake nan gida Najeriya, sai Abbas wanda shi kuma "Personal Manager ne a A. B. J motors shima mallakin mahaifinmu ne.


Bashar a yanzu yake shekarar ƙarshe a University dake jihar Delta, sai ni Asiyah sannan ƙannaina biyu Ruƙayya da Rabi'atu.


Sannan akwai yara biyu da ake riƙo gidanmu, Farida ɗiyar ƙanwar Mami sai Abdul shi kuma ɗan maƙotanmu ne.


Baban Abdul ma'aikacin gwamnati ne, yawan canje-canjen wajen aiki da ake mashi ne yasa ya bar ma Babanmu riƙon Abdul tun yana secondary har gashi yanzu suna karatu da Bashar a Delta, bayama maganar komawa wajen iyayenshi ko kaɗan, muma gidanmu babu mai damuwa da zamanshi, tunda ya nuna son zama damu shiyasa aka maidashi ɗan gida...


Sam ba mai nuna mashi banbanci inba gaya maka akayi ba baka cewa ba'a gidan aka haifeshi ba, abinda ɗan gidan zaiyi shima haka yakeyi, bai taɓa ware kanshi ba ajerin yaran gidan, muma ko lissafi za'ayi da Abdul a ciki.




*June 2000*



Cikin waɗannan shekarun na kammala karatuna na secondary, lokacin ban ida cika shekara sha takwas cif ba.


Gashi na kasance yarinya mai ɗan jiki, bani da tsayi dan in an kirani da gajera ba zanyi gardama ba, sai dai gajartar tawa bata janwo mani muni ba, musamman ma da bani da ƙiɓa...


Ƴar shafal-shafal nake sai dai jikina irin mai cikar jin daɗi ne, bani da rama ko awuya acik nake bani da ƙashi.


Inada cika a ƙugu da zaunannan kwankwaso, na kuma wadatu da mazaunai da suka dace da yanayin jikina.


Marata ashafe take tsam bani da tumbi ko kaɗan, wannan yasa inna sanya kaya ko wane iri ne suke bala'in karɓata suyi mani mugun kyau, ya zamto duk inda na gibta sai an kalleni an yaba an kyasa..


Wannan yasa duk yawancin kayana matsattsune, bana kyashin komin tsadar zani aimin ƴar matsattsiyar riga, nidai burina na sanya kayan da suka karɓeni suyi mani mugun kyau ta yanda duk inda na wuce za'abini da kallo, inda hali ma abiyoni anaimin ƴar murya, niko ina tafiya ina yatsina da juya halittar da Allah yai min...


Fuskata ina mugun alfari da ita, dan Allah ya ƙawata min ita yayota kyakkyawar fuska data zamo aba3 rububi da son gani awajan samari harma da dattijan..


Ina alfari da kyan da Allah ya bani, sai dai kuma bawai alfahari na wulaƙanci ko na zamo mai izgilanci da ire-iren haka ba, ina dai alfahari dani mai kyau ce, akulluyomin ina gode ma Allah daya yoni kyakkyawa ya kuma fifitani cikin kyawawa dan a gaskiya kyawuna irin mai wuyar samu ne.



A halayna ina da miskilanci naƙin ƙarawa, tun ina yarinya na zamanto maras son kwaramniya da yawan magana, kawowa yau ba abinda ya canja na halina musamman miskilancina yana da matuƙar wuya nayi dabo da mutum.


In har kaga nayi sabo da mutum harya zamo abokin hirata to ƙaddara wannan mutumin mai matsinancin haƙuri ne, mai kuma iya zama da mutane danni da kaina ina yabawa mutumin da zai jure halina har yaso mu'amula dani.


Ga mutanen unguwa sukan ɗaukeni mai wulaƙanci wasu suce mai girman kai yayinda wasu kuma suke ganin miskilancina ne da wai yanga.



Anty Lubah amiyata ce duk da cewa ba tsarata bace wannan bai hana aminci tsakaninmu ba, ta girmeni da shekaru masu yawa, dan ita matar aure ce alokacin ɗanta ɗaya Aliyu.


Ta fahimce ni fahimta mai kyau, ta laƙanci halayena tasan koni wace irin jinsi ce acikin mutane dan hakane miskilanci bai taɓa damunta ko kaɗan duk yanda na murɗe tasan yanda zata juyani muyi magana ta fahimta...


Ina ƙaunar Anty Lubah dan da ita ɗaya ne nake iya zama mu kwashe Awoni muna hira, gidanta nanne wajen zuwa na agaba ɗaya unguwarmu, inka ganni awaje na ɗauki hanya tabbata gidan Anty Lubah zani...



Hashim ya samo mani Adimission bayan fitowar result ɗina kenan a Poly Tudun Wada inda zan karanci *Mass Communication*.


Sstin da zan fara zuwa ɗaukar lecture Abbanmu yai min kyautar mota Honda Errocdic ta zuwa makaranta, daɗi ya kamani dan gaskiya Abbah ya taimaka min, dan ba ƙaramin nisa ke tsakanin Unguwar Rimi da Tudun Wada ba.


Bani motar kuwa zai kawo mani sauƙi wajen tafiya, dama tuni na koyi tuƙi awajan Abdul.




Ban samu wasu matsaloli ba wajen karatuna saboda samarin gidanmu duk ƴan boko ne, duk abinda ya shige mani duhu su nake samu su warware mun musamman Abdul wanda in dai yana gida to rabin lokacinshi yana cinyesu tare dani wajan ƙara fahimtar dani wasu al'amuran game da course ɗin da nake...


Matsalata ɗaya samarin Poly da suka samin ido, bani da sukunin watayawa acikin makaranta, duk inda nabi sai an bini da ɗan kira...


Gashi ni kuma ba abinda na tsana irin samarin rainin hankali, wanda su burinsu agansu da kyakkyawar budurwa suna ratsa cikin makaranta.



Gaba ɗaya bana bi ta kansu bana kula al'amarinsu shiyasa da yawansu muke ƴar tsama suna ɗaukata mai wulaƙanci da izgilanci...




Yau dana taso makaranta kafin na wuce gida sai da na biya gidan Anty Lubah, nayi sallar azahar tare da bata saƙon data bani na siyo mata littafi, har zan fita bayan munyi sallama tace "af Asiyah baki faɗa min yanda kuka yi da Ahmad ba".


Na ɗan taɓe baki, raina yana baci akan Ahmad Anty Lubah, na rasa abinda zan mashi ya rabuda ni, tace" ni kuma na rasa dalilin daya sa kika tsaneshi", aganinki kenan Anty, amma a gaskiya ban tsani Ahmad ba, koba komai ɗan'uwana ne, kalmar da yake bina da ita ne kawai na tsana.


Anty Lubah tayi murmushi tana kallona tace " kinada matsala Asiyah", na juya kai maye matsalata Anty Lubah?


Kowa bakya so, nayi ɗan murmushi ba kowa bane bana so, kawai dai wanda ya dace na so ɗinne har yanzu bai baiyana ba, ta zuba mun ido amma meye aibun Ahmad?


Yaro ne na bata amsa kai tsaye, ni da ita mukayi dariya, zata sake magana na katseta, dan Allah Anty mubar maganar Ahmad mu daina tadata, kin riga kinsan ra'ayina akan irin mijin da nake son aure babban mutum ba yaro ba irin Ahamd, kinga tada maganarshi tamkar ɓatawa kanmu lokaci ne.


Batace mun komai Ba illa ido data bini dashi, nayi mata sallama naja hannun yaronta Aliyu muka fice, ahanya na rinƙa tunanin al'amarin Ahmad, shida gaske yake ya dage ni yake son aure, banda rigima ko ina zai kaini duka fa shekara biyu ya bani, daɗin daɗawa ba wani tsawo gareshi ba da ɗan mitsitsi ya ɗarani.


Kuma alokacin yake tsakiyar karatunshi a Bayero kano amma dan rigima ya dage nice tsarar auranshi, kaini wani lokacin ma bala'in dariya yake bani, ɗan wan babanmu ne da suke uba ɗaya.



Na isa gida na iske Abdul yazo, banyi mamakin zuwan nashi ba dan sati biyu kenan da komawar Bashar ya kuma sanar dani zuwan Abdul ɗin adai-dai wannan lokacin, ya taroni da murmushi nima nai murminshi dan naji daɗin ganinshi, dan dama an bamu Asdignment mai wahala.


Muka shige falo a tare yana cemun tun ɗazu nake neman layinki ban samu ba, nace "uhmmm" na kashe wayarne tun a makaranta ban kunnata ba har yanzu, na barshi a falo na wuce ɗakin Mami na gaisheta na wuce ɗakina na cire kayan jikina na watsa ruwa,nasa ƙananan riga da siket na English wears na dawo wajan Abdul muka dasa hira.



Washe gari banje makaranta ba, bani da lecture dan haka gidan Anty Lubah na yini, yamma lis wani yaro ya shigo yana faɗin ana nemana awaje, na fita naga Abdul ne, yace "nazo na tafi dake ne" na tambaya danme?.


Gidanne shiru ba daɗi baki, mts nayi ɗan tsaki kai ka faye jan magana Abdul, naji dai mu tafi hira nake so muyi kinsan gobe zan koma school, nace to jirani naiwa Anty sallama, ki miƙa gaisuwata nace toh na shige ciki.


Muna tafiya muna hira har muka isa gida, aƙofar gidan muka tarar da Hashim da abokinshi muka gaisa da abokin na barsu tare da Abdul na wuce ciki.






Machika novels🤳🏻