4
by @shooly84
🤳🏻
💘 нalιn dana ѕнιga...💘
~Labarin gaske ne~
© ᴬYˢᴴᴬ ᴹᴬᶜᴴᴵᴷᴬ
*Arewabooks@Shooly84*
*S͢A͢D͢A͢U͢K͢A͢R͢ WA G͢A͢R͢E͢K͢U*...
*ᴷᴴᴬᴰᴵᶻᴬ ᵁˢᴹᴬᴺ*
*ᴺᴬᴮᴵᴸᴬ ˢᵁᴸᴬᴵᴹᴬᴺ*
*Ɗᴬᴵᵞᵞᴵᴮᴬ ᴵᴰᴿᴵˢ*
*ᴴᴬᵁᵂᴬ ᴬᴸᴵᵞᵁ ᴿᴬᴮᴬᴴ*
*ᶠᴬᵁᶻᴵᵞᵞᴬ ᴰᴬᵁᴰᴬ*
*Gaskiya fans ɗina bana jin daɗin rashin yin comment ɗinku yarda ya kamata, in littafin baiyi maku bane na daina typing ɗinshi tun kafin nayi nisa, musamman ƴan Wattpad kunba Muso Junanmu haɗin kai amma wannan kuna neman yin eh yane*...😃
💘 4 💘
Nai ɗan dum sakamakon canjin yanayin da muryar mai maganar ya saukar min a jiki, saboda yanda aka karya harshe wajan yin maganar...
Kinyi shiru ko, aka sake faɗi cikin irin muryar farko, uhm na aje numfashi tare da faɗin *Ibraheem* ko?
Naji fitar sassanyar dariyarshi kana yace"a ina kika sanni?
Nace amma dai ni ya dace nai wannan tambayar ko?
Kice a ina na sanki? Kwarai, ya yi dariya, ba zan so kiyi min wannan tambayar ba Asiyah, danni tuni kina zuciyata, ako yaushe ina nan tare dake cikin rayuwata..
Ya akayi bansan da hakan ba?
Dalilai masu yawa Asiyah, da kuma lokacin ki sannin ne baiyi ba sai yanzu, ko ba haka ba Asiyah?
Haka ne na faɗa asanyaye, to ina fatan kin gamsu da saƙona kin kuma amincewa buƙatata?
Ina ka taɓa ganin anyi haka ka amincewa wanda baka sani ba?
Ya zakice dani haka Asiya, alhalin na kawo kaina gareki? Amma ai baka zo min da suffar inna sake ganinka zan ganeka ba.
Ban gane nufinki ba fa, kasan ka ɓoyemin fahimtar kamanninka, kina nufin ba zaki iya bada labari game da suffata ba?
Abinda nake nufi kenan, yai ɗan shiru daga baya ya nisa yace "kwarai nai ba dai-dai ba, amma ban taɓa tsammanin zaki kasa gane siffata ba amman yanzu ya za'ayi?
kai zanma wannan tambayar, yai shiru alamar nazari ɗan tsayin lokaci ina saurarenshi, yace "kinsan yanda za'ayi?
Sai naji daga bakinka, kamata ya yi ki kwatanta kamannina azuciyarki, kamar ya? Na tambayeshu, kota ya ma Asiyah...
Dariya nai nace to ka bani lokaci zuwa gobe zanyi ƙoƙarin yin abinda kacen, hakan yayi amma abinda nake so dake ayanzu kiyi ƙoƙari kiga nazo miki cikin barcinki da kamannina na zahiri ba na canka ba.
Taya kenan Ibraheem?
Ki sani a zuciyarki, ki kwanta dani aranki ya zamana tunanina shine abu na ƙarshe da zaki yi kafin bacci ya ɗaukeki, in kinyi hakan babu makawa zaki ganni ni Ibraheem cikin barcinki, nayi ƴar dariya kawai...
Kinyi shiru, nace to zanyi hakan, yace da kyau Asina bari na barki ki sami ishasshen bacci dan haka mu kwana lafiya.
Bai jira daga gareni ba ya kashe layin ya barni cike da ƙaunarshi.
Da matsinacin tunaninshi na kwanta yayinda ƙaunarshi mai zafi ke ratsa ɓargo da jinina.
Wannan ya kaini gayin mafarkai barkatai wanda dukkansu akanshi sai dai dukansu basumin daɗi ba domin harna farka banyi dacen ganin abinda nake son gani ba, wato zahirin fuskar nan tashi dana ƙwallafa rai akan son ganin nata.
Kamar jiya yau ma sha ɗaya da rabi wayarshi ta shigo, saida na natsu kwarai na maida dukkan hankalina gareshi sannan na amsa kiran da sallama...
Ya amsa min cikin daddaɗan lafazi mai cike da nagarta ya ɗora da cewa mai ya hanaminke bacci har zuwa yanzu Asina?
Na lumshe ido kamar ina gabanshi tare da lanƙwasa murya nace abinda ya hanaka Ibraheem...
Ya kyakkyale da dariya, begenki ya hana Ibraheem bacci Asiyah, shiya hanani sukuni kina nufin kice min kema abinda ya hanaki bacci kenan?
Nai murmushi da canza maganar da faɗin ya mutanen Lagos?
Suna nan suna fama da ciwon sonki Asiyah, burinsu su sanyaki cikin idanuwa haka zai kawo masu kwanciyar hankali, nace ko? Kinfa zarta duk inda kike zato Asiyah.
Nai murmushi nace, daga jiya zuwa yau naji haka yafi ƙarfin ƙirgawa yace " ina fatan kin yarda da abinda kika jin?
Na sassauta murya nace kalamanka Ibraheem sunfi ƙarfin aji aƙi yarda dasu, naji ajiyar zuciyanshi yace " burina na farko ya cika Asiyah kin yarda ina sonki, toni ya za'ai nasan matsayina cikin zuciyarki"?
Nai shiru ina fitar da murmushi mai sauti, azuciyata ina tunanin me zance da Ibraheem ya yarda ina cikin zazzafar ƙaunarshi...kinyi shiru Asiyah kin barni cikin zulumi da tunanin ba...amma bai kamata ace ka shiga damuwa game dani ba Ibraheem, ko Asiyah?
Na ɗaga kai da faɗin kana iya faɗa ako ina ni Asiyah bani abin so daya wuceka Ibraheem, yai sansanyar dariya yace " kuma fa na fahimci haka dama naso ne naji fitar kalmar daga bakinki, nace toh da kaji kuma sai yaya?
Sai hankalina ya kwanta Asi, yai maganar ne cikin kwantar da murya wanda ya sani nai dariya shima ya dara, af na mance na sanar dake Asiyah dake nai bacci na na jiya, kefa kin ganni ko yaya?
Nace uhm nima na ganka sai dai baka yarje min ganin fuskarka ba, kamar ya Asi?
Ɓoyan fuskarka kake Ibraheem, duk yarda naso gani sai ka kauce, daga ƙarshe ma guduwa kayi ka barni ina magiyar ka tsaya amma bakayi hakan ba.
Yai dariya sosai kamin yace "da gaske Asina bakiga fuskata ba?
Allah kuwa bayanka kawai na gani daga kai zuwa ƙafafu ka juya min baya kenan, kana sanye da korayen kaya dogaye, yace "da kyau Asina, toh zaki iya kwatantani, na sassauta murya nace, na ganka ingarman namiji mai kyan siga da kyawon ado.
Yai dariya amma fa kamar kin kurantani da yawa Asiyah, nace ai dan an kuranta masoya ba aibu bane muddin wanda akayi mawa saiji daɗi ya yaba.
Na yadda da maganarki Asiyah, abinda zance akullum shine Allah ya ƙara wanzar da ƙauna atsakaninmu yayi gaggawar kawo ranar haɗuwarmu...
Na amsa da Amin da saurina dan daga jiya zuwa yau jina nake akamar nayi tsuntsuwa na bishi zuwa Lagos.
Bari na barki ki kwanta Asi karna ɗauki alhakinki da yawa, ban musa ba nace sai yaushe kuma zan sake jinka?
Yace "karki damu nai maki alƙawarin ni zan tasheki sallar asuba, yanzu dai ki kwanta ki sami ishasshen bacci.
Da asuban ko kiran farko wayarshi ta tasheni, ina ɗauka yace "kije kiyi sallah nace na gode ya kashe nashi layin.
Na idar da sallar kenan test ya shigo, ina ji zuciyata ta bani saƙon daga gareshi ne, nai saurin janyo wayar na duba.
*Asi my love*
*_Zuciyata na azabar ciwo, takanyi min nauyi kwarai wani lokacin ta ɗau zafi da ƙuna duk akan ƙaunarki, ba komai ke kawo min haka ba illah so da ƙaunarki dake wahalar da ita, ki sani Asiyah ina sonki son da baki ba zai iya fayyace shi ba sai dai akullum ina addu'ar kasancewa tare dake_*
*Mai sonki Ibraheem*
Na karanta na sake karantawa, naita karantashi kai na karanta wannan test ɗin sau ba adadi, wani irin farin cikine maras musaltuwa ya rufeni, zuciyata tai fari tas haƙiƙa na yarda Ibraheem masoyine na gaskiya agareni.
Bayan na gama mayatar karantawa na natsu wajan mayar mashi da amsa.
*Mosoyin Gaskiya*
Babu tababa kai abin sona ne Ibraheem, dan haka nai maka alƙawarin mallakamaka kaina tako wanne irin hali, buƙatata kaci gaba da faranta raina da daɗaɗan kalamanka haka shi zai ƙara tinzira wutar ƙaunarka agareni...
*Your love Asi*
Na gama karantawa na tura mashi minti biyu tsakani ya dawomin da amsar godiya.
****************
Yau agidan Anty Lubah mun yini hirar Ibraheem, ita kam mamakina take wai ashe akwai ranar da zan mace kan son wani ɗa namiji haka, nai dariya nace Anty Lubah Ibraheem da banne, sonshi wani irin halitta ce da nake ji tamkar dashi aka halicceni.
Ta kama haɓa tana dariya tace " Ibraheem mai sa'a akan Asiya, zanso ganinshi naga wai da meye ya siye zuciyar nan mai...shigowar wayarshi ta katse maganarta, nai saurin ɗauka cikin farin ciki ina ce mata ga ɗan halak.
Muka gaisa cikin so da aminci bayan ƴan hirarraki na ƙauna wanda Anty Lubah na gefena tana jina, na kalleta naiwa Ibraheem magana...
Ga Anty na ku gaisa, yace "Anty Lubah ko? Ita na bashi amsa, yace "zan ko so magana da ita danna bata amanar kula sa soyayyata ahannunta, nace to ai gata sai ka bata dama itama ƴar bayanka ce.
Na bata wayar ta karɓa suka gaisa naji yana ce mata Anty Lubah dafake na dogara, arinƙa kulamin da rayuwata dake kusa dake, ataƙaice dai amanar soyayyata harda ke na damƙawa, abin nufi ki zamo mai taimakona da bawa soyayyata kariya ta hanyar sa ido da tsawatarwa karki bari arusani ta ko wace hanya Anty Lubah...
Tayi dariya karka damu Ibraheem kasa aranka Asiyah taka ce kai kaɗai, zaɓinta kaine burinta na duniya dama lahira abin da nakeso dakai ka kwantar da hankalinka Asiyah taka ce.
Ina jin doguwar dariyarshi yace " na yarda dake Anty Lubah, amma duk da haka ina buƙatar kulawarki akanta, tayi dariya tace za'a kula maka, sukayi sallama tabani nima mukayi sallama bayan gama wayar tamune na dubeta nace Ibraheem ya damu dani sosai Anty Lubah kinga nima ba laifina bane inna damu da al'amarinshi ko?
Sam ba wani laifi Asiyah ai dama ance kaso mai sonka...
A gida cikin dare wayarshi ta sake shigowa, bugu ɗaya na ɗauka shiya fara magana da cewa barkanki da dare sanyin zuciyata na amsa da cewa barkanka dai farin cikin rayuwata, dukkanmu mukai dariya yace "kin ganni cikin barcinki dai ko?
Na ɗaga kai da faɗin sai dai har yau kaƙi yarje min ganin fuskarka, irin mafarki ɗaya mukai kenan sai dai ni naga ankawo minke ne amatsayin amaryata kina ɓoyemin fuskarki cikin wani kyakkyawan farin mayafi, anyi miki ado da kyakkyawan tufafi masu matuƙar ɗaukar hankali.
Haka nan hannayenki an lulluɓe da fulawowi na alfarma irin wanda akewa isassun amare, ga wani irin ni'imtaccen ƙamshi mai daɗi dake tashi ajikinki wanda shine ya rinƙa fizgata zuwa gareki harna rinƙa ƙoƙarin yaye mayafin da yai min tsakani da kyakkyawar fuskarki, ke kuma kika rinƙa nuƙu-nuƙu da ƙoƙarin ɓoye fuskar tsakanin cinyoyinki.
A ƙarshe dai banyi dacen ganin fuskarki ba Asina kiran sallar asubahi ya katsemin daddaɗan mafarkina, na farka cike da takaici ga rashin ganin ƙarshen shi gashi kuma bada gaske bane.
Amma daga bisani sai nai farin ciki dan mafarkin nawa na fassarashi da abubuwa masu yawa a ciki harda tsammanin zuwanki gareni nan da ɗan ƙanƙanin lokaci.
Na kwantar da kai akafaɗata tare da runtse ido na sassauta murya nace Allah ya cika mana burinmu na ganin mun mallaki juna, ya amsa da Amin da sauri.
Nace amma kai min rai ka taimakeni Ibraheem na ganka mana, wallahi na fara shiga damuwa zuciyata da jikina, yai shiru na ɗan lokaci can ya nisa yace " ki ƙara haƙuri Asiyah nasan dole ki damu amma nai miki alƙaqarin kawo kaina gareki cikin gajeran lokaci, bari ayyuka suyimin sauƙi zan baki mamaki Asi...
Nace nima anan zan baka mamaki Ibro dan zanmaka tarbane irin wadda masoyi kaɗai ke samun irinta, yace ko Asina, nace sai dai kazo ɗin *zaka sha mamaki*.
( *Cikin shi da ita ɗin kowa zai sha mamakin* 🤔)
Machika novels🤳🏻