6
by @shooly84
💘 нalιn dana ѕнιga...💘
~Labarin gaske ne~
© ᴬYˢᴴᴬ ᴹᴬᶜᴴᴵᴷᴬ
*Arewabooks@Shooly84*
*S͢A͢D͢A͢U͢K͢A͢R͢ WA G͢A͢R͢E͢K͢U*...
*ᴷᴴᴬᴰᴵᶻᴬ ᵁˢᴹᴬᴺ*
*ᴺᴬᴮᴵᴸᴬ ˢᵁᴸᴬᴵᴹᴬᴺ*
*Ɗᴬᴵᵞᵞᴵᴮᴬ ᴵᴰᴿᴵˢ*
*ᴴᴬᵁᵂᴬ ᴬᴸᴵᵞᵁ ᴿᴬᴮᴬᴴ*
*ᶠᴬᵁᶻᴵᵞᵞᴬ ᴰᴬᵁᴰᴬ*
💘 6 💘
Kwana da yini banji daga Ibraheem ba, ba waya ba saƙo innice na kira layinshi nakan jishi akashe, hankalina ya tashi nasan ba lafiya ba, haka kawai Ibro na ba zai shareni ba baiji yanda nake ba.
Muhammad ma rabona dashi tun jiya da rana, dana ganshi ne ma dana ji yaya Ibraheem yake...
Abdul kuwa kwana uku kenan baya nan yaje gaida iyayenshi.
Har cikin dare bacci ya gagareni ina ta zullumin yaya Ibraheem yake ciki, waya a hannuna inata juyawa waini ina jira naji kiranshi ne.
Bansan yanda akayi ba na dai tsinci hannuna na danna lambarshi lokaci kaɗan ko layin ya haɗu harta fara ringing hakan ya sani saurin tashi zaune.
Amma harta ƙaraci kukanta ta tsinke ba'a ɗaga ba, na sake kira wannan karon sai da ta kusa katsewa aka ɗauka, muryar mace naji tana faɗin hello wake magana?
Faɗuwar gaba tare da matsinacin tsoro suka bigi zuciyata, atake na shige wani irin yanayi na tashin hankali.
Wa yake magana ne?
Aka sake faɗa cikin rawar murya nace ke wacece meya haɗaki da wannan wayar?
Asiyah ce ko? Aka sake tambaya, na buɗe ido sosai nace ke wacece?
Tayi dariya tace Anty Amina ce, nan wata bala'in kunya ta rufeni na fara inda-inda...na rasa ma ne zance da ita, can dai na daure nace kiyi haƙuri Anty bansan ke bace, ta sake yin dariya kada ki damu na sanyaki fargaba ko?
Uhm kawai nace, tace kinji mutumin naki shiru ne ko?
Ban bata amsa ba taci gaba da cewa, bai da lafiya ne yanzu haka ma a asibiti muke, kaina naji ya sara da faɗuwar gaba naji bakina ya furta Innalillahi wa'inna'ilaihir raji'un!
Tuni muryata ta hau rawar kuka ina son tambayarta ciwon me yake na kasa sai kuka, ki kwantar da hankalinki Asiya tace dani, ba wani ciwo bane serious ya yanke jiki ya faɗi ne.
Amma likitoci sunce babu damuwa yawan tunani da damuwa da kuma rashin ishasshen lokacin hutu da bacci ke damunshi, shine sukayi mashi allurar bacci dan ya samu hutu, amma sunce da zarar ya tashi shikenan zai koma normal.
Bance mata komai ba illa wayar dana kashe na faɗa gado na soma rera kuka ina tunanin inna rasa Ibraheem ya rayuwata zata kasance, na tabbata yadda Anty tace mani ba iya abinda ke damunshi bane ta dai ɓoye mani ne kawai.
Tunda kwanakin baya mutumin da har Accident yayi ya karye ahannu amma wannan bai hana mishi dare da rana yana tare dani awaya ba, yanzu ace wai ɗan ciwo zai hanashi nemana.
Ni dai bansan lokacin da bacci ya ɗaukeni ba, kiran sallar asuba ta farkar dani naso makara dan har anshiga sallar nai saurin tashi, sai dana ɗauro alwala kana na fito na leƙa sassan Mami na taddata ta tada sallar dan haka na koma ɗakina nima na tayar.
Ina idarwa ko doguwar addu'a ban tsaya yiba naja waya na nemo layin Ibraheem.
Bugun farko aka ɗaga nayi mamakin jin muryarshi garau tamkar ba mai ciwo ba, da zumuɗi na kira sunanshi Ibraheem ya jikinka?
Yai dariya na samu lafiya Asi, dama fa ba wani ciwo bane mai zafi, nace to na gode Allah dan har ina tunanin Anty Amina ta ɓoye min halin da kake ciki ne, yace gata can ko tana miki dariya yanzu ma ta gama bani labarin wai kuka kika sanya mata jiya, yanzu sai hankalinki ya kwanta ki samu ki koma bacci danna san jiya dai ba'a samu rintsawa ba ko?
Banyi magana ba yace, ki kwanta kinji Asi zan tasheki anjima innaga lokacin daya kamata ki tashin.
************
Kwana biyu komai ya dawo dai-dai Ibraheem lafiya ta samu harya koma bakin aikinshi, tsakaninmu kuma sai abinda yai gaba fatanmu koda yaushe mu faranta ran junanmu...
Yau na dawo daga makaranta da wuri ban wuce gida ba gidan Anty Lubah na tsaya muka sha hira sai yamma lis na koma gida.
Na samu nai wanka na kwanta danna huta, ban jima da kwanciya ba aka aiko kirana, Mami ake gaya ma saƙon dan haka ta leƙo tana shaida mani, haka nan ba dan ina soba na miƙe na fita.
Jingine da get ɗin gidanmu na sami baƙon muka kalli juna yai dariya mai nuna sanayya niko na ƙara gyara fuskata dan ban ganeshi ba, ta wajan gaisuwarshi na gane wanene shima ta hanyar yanda yake gaidani awaya da yanayin maganarshi...
Abdul-malik ko?
Na faɗa nima ta hanyar wadata fuskata da murmushi da nuna sanayya, shima ya sake dariya yace na yadda kinada saurin fahimta Antinmu, nace ko?
Ya zare ido, kin koyi halin yayanmu nacewa ko ɗin nan ko?
In an mashi magana yace wani ko, kamar bai yadda da abinda mutum yace ba, nai dariya nace ya Momi, Daddy dasu Nafisa?
Duk suna gaisheki amma fa banda Daddy shi baya ƙasar ma wajen sati biyu kenan, nace Allah ya dawo dashi lafiya ya amsa da Amin.
Nan na jashi cikin gida na gabatar mishi da abubuwan motsa baki, Mami ma ta fito sun gaisa, da zai tafi yaima su Ruƙayya da Rabi'a kyautar kuɗi mukayi sallama.
Da daddare muna waya nake ce ma Ibraheem yau dai naga Abdul-malik, yace ko?
Nace wallahi kuwa, kuma nina ganeshi ba tare daya gabatar min da kanshi ba, yace shima haka ya faɗa min yai murnar ganinki, ko?
Haka mana ai kina da kirki Asina, ko?
Sosai ma ai nayi dacen matar kirki, nima nayi dacen samun mijin ƙwarai duk mukai dariya.
Abdul da Muhammad sukaje ɗaukata makaranta, Abdul ɗinne ya ajeni da safe ya tafi da motar tawa, ahanyarmu ta dawowa suke bani wani labarin daya sanyani dariya sosai...
Wai Ibraheem ne yaga wata yarinya cikin Shopright a Lagos, haka kawai idonshi yayi mashi gizo da kece yako kama bin yarinya na wajen awa uku shi a dole sai yaga inda zaki.
Nayi dariya sosai nace, yaushe akayi hakan Muhammad, jiya da daddare yake bamu labari, nace amma ni sam bai gayamun ba, sukai dariya, Abdul yace amma fa ya kusan shan duka dan yarinyar mutane ta tara mishi tayi zaton ɓarawo ne ke binta.
Ina dariya nace kace dai da yanzu an taɓa lafiyarmu, lallai kam Allah ya taƙaita maku wahala.
Da daddare kamar yanda ya saba yayo wayar tashi ta ƙa'ida, mun gaisa cikin barkwanci da nunawa juna so ta hanyar musayar kalamai masu daɗi, nace ashe kuma malam Ibro sabuwar Asiyah akayi a Lagos abin ko labari babu...
Ya kyakkyale da dariya, mugayen mutanen nan sai da suka baki labari ko?
Da gaske bakaso naji ba, eh to tsoron tsiyarki nake, nace ba zanyi maka tsiya ba sai dai nace arinƙa kula kar wataran ka janyo jangwam dan matasan Lagos ɗin nan in suka ɗamƙeƙa sai Allah..
Yace haka ne Asi, to amma fa abunne kamar sihiri na shigo shopright ɗin zuciyata cike da tunaninki kawai take wallahi, ina ɗago ido naga gittawarta, abinda idona ya bani kawai kece, abinda ya ƙara jan hankalina irin shigar dana ganki da ita rannan a Business center tsaf ke.
Wannan yasa nabi bayanta ba muyi nisa ba ta farga, nace amma ni ance nin wajen awa uku kana binta ka kusa shan duka ma, la, la, la sharrin su Muhammad ne wallahi.
Bamuyi nisa ba ta farga ta tsaya tana kallona, ina ganin bake bace raina ya ɓaci na juya ko sake kallonta banyi ba, na sauke numfashi nace adai sake kula Ibro, yace zan kiyaye kwarai Asi.
Kinsan abinda nake so dake?
Na juya kai da faɗin a'a, wani abu nakeso awajenki ko zaki iya bani...faɗi ko menene Ibro ko bani dashi zan nemo maka ako ina ne, hotonki nake so Asiyah shi nake buƙata.
Hoto kawai, shi kawai Asi, Isa zai zo Lagos nan da kwana uku, sai kiyi ƙoƙari ki bashi ya taho min dasu, nace to ka kwantar da hankalinka ka fara tunanin ga Asiyanka can zane cikin hoto maƙale ajikin bango saitin da kake kwanciya.
Yayi dariya yana faɗin godiya mai tarin yawa agareki *MY LOVE*.
Banma tsaya duba tsofoffin hotuna ba washe gari da yamma na gayyaci Abdul ya rakani *Studio 24* sai da nayi hotuna kala goma kowanne cikin kyakkyawar shiga.
Abdul ya karɓo mani washe gari, kamar hotunan sunsan gun gwarzon masoyi zasu babu na yarwa aciki, sunyi kyau na ban mamaki, Abbanmu kanshi sai daya yaba da kyawunsu har ya ware kala huɗu aciki yace waɗannan sai ayi manyan katinansu ku ƙawata falonku dasu, kunya ta kamani na laɓe bayan Mami ina dariya.
Bayan sallar magriba Isa ya zo mukasha hira da zai wuce na ɗauko saƙon Ibraheem na hotuna nace gashi hannunka hannun mijina, yai doguwar dariya da faɗin Madam Asiyah za'a isar da saƙonki...
Randa saƙon ya isa wajanshi ranar bai barni nayi sukuni ba, duk bayan mintuna goma yake kirana ya isheni da kuranta kyauna da yaba tsarin halittata ni dai dariya nake mishi ina ƙarajin daɗin yanda ya damu dani.
Da daddare lokacin wayarmu ya kirani yace "Asi na samu abin kallo tun safe na kasa ɗauke ido akan hotunanki, nai dariya da faɗin da dai ka ajesu ka huta gashi hotunan ma ba wani kyau sukayi ba, kai Asi kinfiye neman zance yanzu kice hotunan nan ba suyi kyau ba to wanne ne zaiyi?
Nayi shiru kawai yaci gaba cewa, kin ƙeru da yawa Asiyah, duk da a cikin hotone babu abinda ya ragu na daga kyawon fuskarki har zuwa ƙirar jiki, kinga wannan da kikayi da dogon wandon nan yafi ko wanne ɗaukar hankalina, yafi bayyanar da sirrin halittarki a fuskarki ma komai cas-cas...
Gaskiya da gani kinada sirrika kala-kala Asiyah, ni kam duk randa na mallakeki Asi...wayyo Allah ki dai jirani zan zo na ganki kwanannan akwai maganganu da yawa da zamu tattauna aciki harda babban burina na son kasancewarki kusa dani....
Kwanan Isa tara a Lagos ranar da zai taho da safe Ibraheem ya kirani yace "Isa ya taho akwai saƙo da zai kawo miki, nace amma kafi son kullum muyita rigima akan wahalar da kake yi akaina ko?
A'a ai naji maganarki na daina turo miki komai yanzu ma nima hotunane na bayar akawo miki kosuma ba kyaso...wani ihun murna nayi, nai tsalle na dire ƙasa nace da gaske Ibro hotunka za'a kawo min? Yace kina mamaki ko?
Nasa dariya ina ɗokine zanga fuskarka Ibraheem, ni yau wane irin farin ciki zanyi? Nace dan Allah hotunan masu kyaune?
Kamar naki ba, sai dai suna ɗauke da abin mamaki, nace aini ka gama min komai tunda kaimin iznin ganin fuskarka yai dariya mukai sallama.
Kafin Isa ya ƙaraso duk na ƙagara, Mami ko harta gaji dajin labarin yau zanga Ibraheem ahoto, hatta Abbanmu da baya ƙasar sai da nai mai waya na shaida mashi yau za'a kawo min hotunan Ibraheem, yai dariya cikin zolaya yace to inkin gani nima a adana min inna dawo na gani.
Anty Lubah ma waya nai mata nace in ankawo zan zo na kawo mata ta gani, Abdul yaje aiki Benin shima sai da nai waya na shaida mishi, hatta Muhammad na labarta mawa.
Isa ya kirani awaya wajan ƙarfe tara na dare yace gashi aƙofar gidan...baima rufe baki ba na fito ko gaisawa bamuyi ba nace bani saƙona Isa, yace a'a ha Madam ko gaisuwa ba za'ayi ba?
Na ɗanji kunya nace ina yini?
Yaƙi amsawa yace ai saida na nema, na lura saƙonki yafi komai muhimanci awajanki dan haka bari na ɗauko miki, ya buɗe motar ya fiddo da ƙatuwar leda ya miƙo min, nai mishi galala nace hotuna yace ya baka ka kawo min, yace oh haka ne fa bari na duba Allah yasa ban mantosu a Lagos ɗinba.
Gabana ya faɗi na sanya mishi ido kawai, ya hau dube-dube acikin motar, ya fito da wata ƙatuwar ambulan, na saki dogon numfashi tare da hamma, yace "lallai Allah ya soki dana mance su acan wallahi", ni dai tunda naji saƙon ahannuna na juya ina faɗin mu kwana lafiya Isa, ina jinshi yana faɗin gafa sauran saƙon kayanki, banko waigoba na shige ciki...
Tun daga falo na fara yage ambulan ɗin, na isa ɗaki na zazzago hotunan gaba ɗaya suka zubo kan cinyata, nasa hannu na ɗauki ɗaya cikin matsinacin farin ciki tare da zumuɗin son ganin surar dana daɗe ina son gani...
Gabana ya faɗi raina ya ɓaci, zuciyata ta tsinke hankalina kuma ya tashi da ganin abinda ban taɓa zato ba....
Opps...🙄😃 bacci nake ji wallah😉
Machika novels🤳🏻