episod 5
by @mrsfh
wasila omar (mr's f.h)
🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
***
*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~
Ai su na ƙarasawa cikin ɗakin ba su yi wata-wata ba sukae ɗauko ɗan k'ullin kayanta su ka wurgo su tsakar gida. Jasra da ke zaune take gaban ta ya fadi dan tunda ta ga sun yi wurgi da kayanta ta san saura ita, dan haka ta yi saurin ɗaukar Aryan da ke kwance ta rungume shi k'am, "yanzu dai na san kin san manufar mu dan haka ki yi gaggawar fita kafin mu fitar da ke da kan mu" ,Hanne ta faɗa tana karkad'a jiki, share hawayen da su ka gangaro mata tayi ta fara takawa kamar wadda ƙwai ya fashe mata ta nufi fita, har ta d'aga zanin labilen da ke ƙofar ta juyo ta kalle su suma ita su ke kallo, da ƙyar ta iya tattaro sauran yawun bakinta ta iya haɗa kalmar"na gode da taimakon ku a gare ni na san tabbas watarana za ku yi alfahari da taimakona, sam ba zan ga laifinku ba, domin ba kowa zai iya zama da wanda be sani ba amma na tsawon wata biyu kun riƙe ni ina muku godiya akan hakan", tana kaiwa nan ta yi hanyar waje da sauri ba tare da ta dau k'ullin kayan da ke yashe tsakar gida ,ai tuni jikin Hanne yai sanyi amma da ta tuna gorin k'awaye ai tuni ta ji farin ciki ya mamaye mata zuciya haka suka koma daki ba tare da tunanin ko ina zata nufa ba. . Tafiya kawai ta ke yi ba tare da ta san inda ta nufa ba sai da ta yi tafiya me ɗan nisa har ta ji ta gaji ga duhun dare, sannan ta durk'usa a inda ta ke ba tare da ta lura da inda ta ke ba ta fashe da kukan tausayin kanta da kuma Aryan da sanyin farin wata ya sa shi buɗe ido,ita ma idon ta zuba masa tana matsar kwalla "ya za mu yi Aryan haka Allah ya rubuta mana dole haka rayuwarmu zata kasance" ta kai ƙarshen maganar ta na rushewa da kuka me taɓa zuciyar me saurare, kukan da ta ke ne ya sa ba ta ji tsayawar mota kusa da ita ba tadai ji an dafa bayan ta, a firgice ta waigo dan sai yanzu tsoro sosai ya shige ta ido biyu su ka yi da wata farar mata kyakykyawa nan take ta sauke ajiyar zuciya tana kallon matar "yarinya me ya same ki da wannan tsohon daren ki ka fito titi ina iyayenki, ina ne gidan ku?"gaba ɗaya matar ta jero mata tambayoyin a lokaci ɗaya ,ƙara sautin kukanta ta yi haɗe da yiwa matar bayani,"dan allah ku taimake mu iyayen mu sun rasu sanadiyar hadari, mu kadai muka tsira ga shi kuma ban san kowa namu ba", ta kai ƙarshen maganar da sharb'ar majina,kallonta kawai matar takeyi cikin.tausayawa ta sunkuyo dai-dai tsayinta ta dafa ta"kiyi shiru kinji ki daina kuka Allah yaji k'ansu wannan kanin ki ne" ta faɗa tana kai hannu ta karɓi Aryan "ehh kanina ne", "meye sunan sa", “Aryan "ta bata amsa,"to masha Allah yanzu za ki biyo ni mu je gidana kinji kin ga dare yayi sosai"gyad'a mata kai kawai tayi had'e da bin bayan matar su ka shiga motarta suka yi gaba,
"Wai nikam aboki yau banji kayi maganar mutuniyarka ba, ko yau an manta da ita ne " me maganar ya faɗa ya na kallon Fahad domin ya ga ko aikin na su ya yi aiki","akan wa kake magana kenan?"ya faɗa cikin halin ko in kula ,take naga yayi wani shu'umin murmushi wanda ni kaina ban san ma'anarsa ba dan ya fahimci tarkonsu ya kama k'urciya" ,"ohh am sorry ashe na bar bak'i a office d'ina bari na je "ya faɗa yana mai mik'ewa da sauri ya fice daga office ɗin cikin farin ciki.
A ɓangaren Jasra kuwa wani katafaren gida su ka yi horn wanda iya get din gidan ya isa tabbatar maka ko waye me gidan ya tara arziki, faɗar tsaruwa da yanayin gidan ma ɓata lokaci ne gidan ya gama tsaruwa, sai da tai parking kafin ta kalli Jasra ,"ki saki jikinki kin ji y'ata nan ma ki ɗauke shi a matsayin gidanku kin ji ,", ta faɗa murmushi kwance a kan fuskarta, kai kawai Jasra ta daga alamar to ita ma tana nata murmushin ,a tare su ka nufi cikin gidan da ya gaji da haɗuwa ,mukulli ta sa ta buɗe kofar falon su ka kutsa kai ciki ba kowa a falon sai k'arar Ac Ka ke ji, jan hannun Jasra matar ta yi zuwa wani ɗaki dake gefe guda takai ta har ciki ɗakin ya yi kyau sosai komai na dakin pink ne masu kyau ta ce " ki kwanta ki huta da safe in Allah ya kai mu zan turo miki wanda zata nuna miki yadda komai ya ke ,kuma za a samo me kula da Aryan kinji,"na gode allah ya ƙara bud'i,"abinda kawai ta iya faɗa kenan ,murmushi matar tayi tana jin Jasra har cikin ranta, tai mata sai da safe ta fita ta ja mata ƙofar
to nima a nan zance sai da safenku fans. ku biyo alƙalamin 📝
mr's f.h📝📝