MIN QALB

2

by @mamuhgee

_*MIN QALB*_

_Mamuhgee_


2


Bazai iya ganiba 

sunaji suna gani qaton saurayin yake kokarin keta rayuwarta dabata gama sanin ciwon kantaba,

Ita kukan datakeyi dannewar dayayi Mata akan duwatsu suna cin jikinta

Shikuma Usman kukan zabar dayasha yake tunowa itace zaayiwa amatu Wanda sanadin hakan sunzama 6arayi dole da qarfi da yaji.


Qoqrin bude qafafuwanta qaton keyi 

Usman yayi wani yunkuri tareda kama hannun Wanda ke maqure dashi ya sakar Masa mugun cizo Mai qarfi da haqoransa dasuka gama bushewa da dau'da.


A gigice yasakesa Yana yarfe hannu sbd azabar cizon.


Wani qaton dustsi Usman din yadauka baiyi wata wata ba ya buga akan qaton dake kan amatu 

Take ya sulale gefe kansa na tartsin jini sosai ko ihu daya beyiba ya zube agurin Yana wani irin Shure Shure.


Suna ganin hakan wani irin tsoro yashigesu da gudu ya kamo hannun amatu Yana cewa'"


Zo mu gudu amatu.


A firgice dayan ya riqesu Yana cewa'"


Kun kasheshi....a kidime yake fadar hakan cikin tsananin tsoron ganin abokinsa na Shure shuren mutuwa.


Qoqarin jansu yakeyi Yana cewa'"


Wlh police zan kaiku Kun kashesa,

Bazaki guduba ku barni cikin masifa akamani.


Jansu yakeyi da qarfi cikin firgici da tashin hankali suna kuka sosai suna rokonsa ya sakesu Amma Shima a rude yake kansa zai wanke kota halin Yaya.


Irin kukan dasukeyi Basu taba yinsaba arayuwarsu sbd jin wani ya mutu sbd su Kuma Suma kashesu dayan sukaji yanacewa zaayi.


Sosai suke kuka suna rokonsa ya sakesu Amma ko jinsu bayayi Dan Shima kusan kukan yakeyi na tsoro da firgici.


Wata qatuwar gora daga bayansu aka kwadawa qaton a tsakiyar Kai 

Ya tsaya cak tareda sakin hannuwansu Yana qoqarin juyawa yaga ko waye ya yanke jiki yafadi jini nafita a qeyar kansa.


Jikinsu na rawa cikin tsananin tsoro da firgici suka juyo suna qanqame hannuwan junansu tareda ja baya suna kallon qaton dashima yake Shure Shure.


Cikin sauri megadin makarantar ya matso gabansu tareda riqo hannuwansu yasaka musu kudi Yana waige waige Yace"


Kuyi gudu sosai kuje can qasan layin gaban kasuwar baya akwai makarantar almajirai ku shige cikinsu ku kwanta ku boye zanzo idan ankwana biyu

Kuyi sauri karku taba dawowa tanan 

Kuyi sauri kuje..


Kallonsa sukeyi suna sake sakin sabon kuka sbd sunqara firgicewa da Abinda yake fada,


Yaturasu Yana cewa'"


Kuje kuje kuyi sauri karku dawo.


Gudu suka Fara suna waiwayensa sbd akaro na farko da wani ya taimakesu arayuwarsu.


Tun suna waiwayensa harsuka bace suna gudu cikin Daren gashi yace karsu hau titi subi kwana kwana.


Koda suka Kai makarantar almajiran dare yayi sosai gashi karnika sai haushi suke musu duk inda sukabi.


Suna kaiwa bakin makarantar suka tsaya suna rarraba idon Ina zasu boye sbd almajiran gasunan kwance birjik a fili kowa da matacciyar tabarmarsa wasu Kuma da kwalaye wasuma hakanan suke kwance a qasa ga cinnakai da qwari da komai Amma ba ruwansu kwance suke abinsu suna bacci.


Hanunta usman yakama suka qarasa can qarshe yacire matacciyar rigar jikinsa data gama yagewa ta mutu ya shimfida musu suka kwanta kowannensu jikinsa na rawa numfashinsu na fita da sauri sbd tsananin tsoron dasuke ciki.


Asubar fari dukkanin almajiran aka tadasu suyi sallah 

Wanda wannan shine karo na farko dasuka tabayin sallah Shima Suma dai sunyi yanda sukaga kowa nayi gurin bin Abinda malam yayi.


Ana gama sallah kowa yadauko allonsa Yana bita.


Gari yafara haske sai sukaga almajiran na kallon amatu cikin mamaki suna kallon kanta Wanda gashinta ke butu butu da dau'da da qazanta Wanda yake son nuna ita mace ce.


Daga dama sukaji wani almajiri yace"


Kai wallahi idan malam yazo yaga mace dukanku zaiyi wayace mace tana zuwa Nan?hmm

Korarki ma malam zaiyi yanzu Yana fitowa.


Usman najin kora ya kama hannunta suka miqe anabinsu da kallo suka fice a sanyaye.


Harsunyi nisa kadan yatuno da maganar kawu megadi na cewa karsu koma yayi saurin juyawa da ita Yana kalle kallen inda zasu fake Kuma.


Ganin har yamma tayi suna gararin gurin zuwa yasa ya lalubo kudinda kawun yabasu yaje shagon dake kallon inda suke yasiyo Rezar nera ashirin yadawo yajata suka zagaya bayan wani gida Yana cewa'"


Amatu zo muyi aski irin nasu almajiran malam saimu koma cikinsu tunda bamuda wani gurin.


Haka ta zauna yahau yimata aski

Saida ya aske kan tas Wanda duk kusan Rabin kan ya yayyakenta sai jini ke fita kadan kadan Amma Sam Basu damuba Shima sama sama yayi nasa askin rabi yayi rabi beyiba suka dunkule Rezar sbd gaba suka koma makarantar dama kayan jikinsu duk riga da wandone dasuka gama yayyagewa suka sauya kamanni.


Dayake makarantar ba qa'ida sukebi ba take malam ya kaebesu yaga sabbin alamjirai aka Basu tsoffin allon karatu take suka shiga sahun almajirai batareda kowa yasan cewa amatun mace ceba Koda malam ya tambayi sunayensu sukace Usman da amadu.


Ahankali suka Saba da rayuwar almajiranci duk da akwai wuya Amma tafi musu rayuwarsu ta baya dansu yanzu ganin sukeyi sunyi gata.


Akai akai Usman kemata aski sbd kar gashinta yafito musamman sbd tanada saurin tsirowar gashin,


Sunsaba idan sungama ayyukan gidan malam akayi karatu aka gama su fita yawon bara sai yamma sudawo karatun yamma sannan sufita barar dare daga Nan Kuma dare nayi zuzo su kwanta.


Yanzu suna samun yin wanka a sati ko so dayane shiyasa suka Dan Fara canzawa.


Tun suna qirgen kwanakin zuwan kawu megadi harsuka daina suka koma qirgen kwanakin zuwansu har lissafi ya batar musu.


Ko ayanxu dasuke cikin inuwar almajiranci abun dai 'dayane shine idan baka tsayawa kankaba Kaine a qasa ko yaushe,


Sunsha gwagwarmaya zamansu makarantar malam din,


Idan anyi sata su ake maqalawa,

Barna sune,

Laifi sune,

Hatta laifin cikin gidan malam su ake maqalawa shiyasa sunfi kowa azabtuwa sbd irin dukan da malam da ya manyan yaransa suke musu,


Shatin buloli ajikinsu yazama tamkar zanen fatarda aka haliccesu da itane,


Tun suna kuka a almari harsun qame sun daina sbd ganin rayuwar ahaka take koina na sama ya danne na qasan.


Duk hutunda akeyi sukam basa zuwa koina sbd basuda gurin zuwa shiyasa rashin tausayinsu yafi yawa sbd ansan ko an zalincesu basuda me tsaya musu.


Ahaka dai rayuwa taja tsananin rayuwa Yana qara musu yawa musamman yanxu da amatu take Fara nonuwa kullum cikin boye boye suke gashi yanxu abubuwan naqara tsanantar musu ne gashi amatu ko mgn batayi sosai da qarfi da yaji suke boyon mganarta kar agano mace ce.


Yanxu dasukayj wayo Usman shine me wahalar Abinda zasu ci duk da tare suke zuwa duk inda zasu gashi baqin jini tamkar a jininsu yake sbd duk inda sukaje tsanarsu da kyararsu akeyi shiyasa suka riqe aransu duniya kowa kansa kawai yasani basuda Abinda yafi musu junansu.


Wani hutu da akayi kamar daga sama saiga kawu megadi Wanda tuni suka Fara mantawa da kamanninsa,


Farin ciki da murnar dasukayi kamar shine danginsu da basuda musamman dasukaga yazo musu da gari kusan kwano buyi jikinsu har rawa yakeyi gurin yimasa godiya.


Amatu ya qurawa ido musamman kanta dake aske tas Yana qyalli ga wasu qananun quraje a jikinsu zuciyarsa na susa yaji dukkanin kuzarinsa ya karye sbd tabbas duk da baitaba haihuwaba ita 'ya mace ce bazaa jima ana boyeta ba amatsayin namiji.


Dazai tafi yasiya musu gwanjo kowannensu riga da wando masu Dan dama dama.


Tun daga lokacin yake Dan zuwa akai akai Yana dubasu sai rayuwar tadan Fara yimusu sauqi.


Awani zuwa da yayi

Baizo da niyar tafiya dasuba Amma atake tunaninsa ya sauya akan amatu sbd girma daya Fara zuwar Mata gadan gadan Yana tsoron amatsayinta na mace ta abalage acikin maza.


kallonsu yayi bayan sun zagayo bayan makarantar cikin karyewar zuciya Yana jinjina rabasun dazaiyi yace"


Usman kaga amatu tafara girma akwai hadari abarta cikinku anan..


Kallonsa sukayi atare cikin rashin fahimta.


Gyara tsayuwa yayi yace zantafi da ita zan kaita gurin me 'dakina idan yaso Kai saika riqa zuwa Mana hutu.


Atare suka girgiza Kai itada Usman din suna kallon juna idanuwansu na cikowa da hawaye.


Nasan zaa rina yafada cikin ransa Yana kallonsu zuciya a karye.


Kamo hanun Usman yayi yajasa gefe ya fahimtar dashi sosai ta yanda zai gane Abinda yake nufi 

Harya gane Yakuma amince sbd har abada bazaiso Abinda zai samu amatu ba.


Daga haka suka hakura sunaji suna gani suka rabu da juna kawu yatafi da su kafin daga baya Usman yadawo makarantar malam.


Tunda amatu tadawo gidan kawu Bata taba haduwa da tsangwama ba saidai Kuma babuwa wani janta ajiki da iyami tayi.


Basuda qarfi sai rufin asiri da haka malam yasakata primary school dinda yake gadi wadda tuni aka maidata 'yar maigadi.


Usman shekara daya yayi batareda itaba ya tattara karatun yadawo gidan kawu Yana kwana a soro komai tsananin sanyi da zafi kuwa.


A haka kawu yasamar Masa aikin tsaron gidan wanka da bahaya a Tasha har Shima yashiga primary 2 

Yana shiga primary 5 ya tattara karatun ya ajiye sbd gwagwarmayar rayuwa.


Kawu da iyami sune gatansu na farko,

Kawu da iyami sune wainda suka cirosu daga bola suka basu sunanda ake kallonsu da daraja ayanzu.


Shekakarda tashiga js 2 a shekarar suka shiga wata sabuwar masifar da akayiwa kawu sharrin satar cire winduna da qofofin makaranta ya siyar.


Duk inda ake zuwa roqo da Kai kuka sunkai akan alamarin Amma Abu ya agagara qarshe dpo nunawa yayi sai idan ita amatu kokuma matar kawun zasu kwana dashi tukuna zai taimakesu.


Akaro na farko da amatu ta tsani maza da taimakonsu.


Ranar dukkaninsu kwana sukayi kukan baqin ciki sunaji suna gani akayi gidan yari da kawu hukuncin shekara biyu dama Kuma abin hadda gayya sbd Shima alqali yaso amatun tabasa hadin Kai sbd irin wankewa da jikinta yayi gashi fatarta Ashe me irin hasken Nan ce ga jikinta daya gama fitowa ana mace tsaf yanzu iyakaci qarasa balagewa ne dabatayiba a cikakkiyar mace.


Tunda akayi gidan yari da kawu alamarin duniya yasakosu gaba ko abincinda zasuci ya gagaresu dole Usman ne yanaji Yana gani yake fita gwagwarmaya Amma sai ahankali.


Wata bakwai da zuwan kawu gidan yari aka koresu daga gidan dasuke suka rasa gurin zuwa ga iyami Dan cikinsa take dauke dashi wahala tasaka ya bare ko kudin asibiti basuda.


Akaro na farko da Usman yakoma sata kenan arayuwarsa ya kama musu daki buyi a wani gidan haya me dakuna goma reras a jere kamar shaguna,

Gidanda ya hada mutane dabam dabam masu halaye dabam dabam.

#mamuh#


MIN QALB❤️

Mamuhgee


ZAFAFA BIAYAR


SIRADIN RAYUWA

safiyya huguma


MIN QALB

mamuhgee


YANKAN BAYA

billyn Abdul


KIBIYAR AJALI

Miss xoxo 


ABINDAKE CIKIN ZUCIYATA

hafsat rano


Pay @***

Or ***