5
by @mamuhgee
*_MIN QALB 5_*
_Mamuhgee_
##Zafafa biyar#pay@ *** or ***
Usi ne yafara ankarewa dashi yaga yanda qarara idanuwansa da fuskarsa suka nuna tsananin qyama da takaicin Abinda idanuwansa suka gane Masa Nan ya fahimci cewar yarigada ya ganta yayi saurin dauke idanuwansa dga kallonsa yayi sbd tsananin kwarjini da cika masa ido da yayi yai saurin yin qasa da murya Yana cewa'"
Amah kiyi saurin barin Nan kokuma ki maida kudin.
Batareda ta fahimci Abinda yafadaba ta kallesa tana cewa'' oya yi sauri mutafi nagama ramawa kura aniyarta anan,
Insfector Garba Kuma zaizo yasameni a gida nasani acan zan fanshe wannan tozarcin dayamin agaban baqonsu da ko kallo bai isheniba bare na tsaya harsu gama kulasaba kafin su dawo kanmu.
Gaba tayi tana zuge zip din Jakarta data saka kudin usi na biyeda ita Yana satar waiwayen baqon dake bayansu fuskarsa a hade ko inda suke bai kallaba ua nufi motarsa Yana duba agogonsa dake nuna Masa lokacin ganawarsa da mahaifinsu yayi gashi shi mutum ne dayake aiki da lokaci komai lokacinsa yake ware Masa sbd tsari dayayiwa rayuwarsa.
Amah ko takan babbar motarsa batabi ba sbd gama quluwa datayi da Abinda Garba yayi Mata.
Usman kuwa suna fitowa tafiya kadan sukayi yaja ya tsaya jikin wata bishiya Yana sauke ajiyar zuciya ya zauna Yana jingina kansa jikin icen ya sake sauke numfashi ya kalleta yana sakin 'yar dariya kamar Babu rauni da tsamin duka a jikinsa yace"
Amah kina ganin akwai ranarda zamuyi rayuwa kamar sauran mutane masu daraja???
murmushi itama ta saki tana kallonsa cikin kulawa da rashin nuna damuwa kafin ta bude Jakarta ta shafo kudin dake ciki tana kallonsu tace"
Bama buqatar wani rayuwa ko gatan daya wuce muyi rayuwarmu ayanda take,
Karka saka wani Rai a wani rayuwan bayan kasan mu din asalin 'yayan bola ne,
Bamuda wani rayuwa bayan Wanda muke ciki a yanxu.
dariya Usi yayi hadi da miqewa tsaye yafara tafiya yana Dan dingyashi saboda raunin da akai masa a kafa sosai yake masa zugi
cikin sake quluwa Amah tabi shi da idanuwa tana tunano irin kalar rashin arzikinda zatayiwa Garba.
Tafiya sukeyi suna firarsu cikin nishadi sbd su Sam Babu Abinda suke ajiyewa arai ya damesu.
Suna shiga gidan da Aunty Salamatu suka fara cin karo aikuwa ta soma sakin numfarfashin masifa dan Sam bata manta dibar albarkan da Aman tayi Mata ba kafin fitarta,
Amah na ganin hakan ta fuske ko kallonta batayi ba ma tai wucewarta zuwa dakinsu jakarta ta ajiye hadi da cire karamin hijab dinta ta fito ta nufi qofar dakinsu kawu ta tararda
Usi zaune tare da Kawu wanda ke tambayar Usin" wane shegen kurtun Dan sandan ne yayi maka wannan ta'asar???
Qwafa yayi Yana taba qafarsa dake Masa zogi yace"
Ai kawu idona idon Sargent salisu saina saka anyi Masa zanen yarbawa har a goshi da qeya,
Shikuma insfector Garba duk Yakuma zuwa gidan Nan gurin amah saina Masa askin kwalba.
Cikin takaici kawu yace"
Shi garban me kama da an sulala naman Kai shine yasa aka maka wannan dukan? Kokuwa shi Sargent salisu din dayafi kama da danyar alala yayi gaban kansa yayima wannan dukan kamar wanda yayi kisa¿
Maman basiru dake kusa dasu tana aikin wanke rishonta ta tabe baki tana cewa'"
To meya raba dambe da fada¿
Tsuke fuska kawu yayi Yana kallon iyami dake fitowa daki daukeda robar garin tuwo dazata gyara yace"
Iyami kinajin matar nan nafadamin mgn bazakiyi Mata dukanda mijinta ba mijintaba ko yayanta bazasu ganetaba,
Waini iyami kodai auren dole ne mukayi?da kike wulaqantani ne kokuwa talauci haukane?
Dariya usi yasaki Yana cewa'"
Wlh kawu talauci haukane tunda gashinan duk bamuda hankali....
Butarda dake gefenda ya dauka a hasale
Usin na ganin hakan ya tashi da sauri
Kawun ya jefasa Masa Bata tsaya koina ba butar sai kan galan din kalanxir din maman basiru Wanda zata zubawa rishon take ya kwanta tana tsiyayewa dama kawun can yayi niyar jefawar ya tsuke fuska yahau masifar usi ya rainasa.
Usu kuwa dariya yake Yana kallon maman basiru dake kallon kalanxir dinta cikin tuquqin zuciya Tama rasa Abinda zata ce musamman ganin fuskar kawun tasan yanxu tana mgn zai Kira mijinta yace suje police ayi musu iyaka Dan aikinsa kenan cewa aje police ayi Masa iyaka da mutum.
Allah ya isana tace cikin ranta tana cewa bakinta yaja Mata saka baki cikin maganar Wanda Basu barin kowa da Allah.
Amah dake kawowa ta kalli maman basiru da idanuwanta sukai rau kamar ta saki ihu sbd takaici ta saki dariya tana cewa'
Iyami wlh karki Bari usi ya rainaki kaman yanda ya Rena kawu.
Kallon Usin iyami tayi tace'"
Kaje ka kimtsa idan kungama Abinda kukeyi kaida kawun,
Wlh usman ka daina biyewa wata fitinar.....
Iyami ki fito fili kice ni basai kin tsaya layi ba.
Nidai yanxu bance kaiba..
Iyami Anya kinason shiga aljanna kuwa?
Amah na ganin haka tasan fadan zasu Fara tayi saurin fiddo da kudin Jakarta take kalmar dake bakin kawu ta katse Yana qoqarin hadata.
Iyami ma aje robar hannunta tayi tana matsowa
Kawu ya bita da harara da qananun idanuwansa masu kama Dana 'yan Korea yace"
Ke amatu maida kudin Nan jaka sai anjima zansan me zaayi dasu tashi tafi daki dasu ki aje.
Kawu albashina ne na karba gurin aiki da niyar belin usi saigashi Basu karba ba sbd rawar jikin sunga wani baqonsu.
Nasani ai dama kedai tashi dasu daga Nan kafin wani ya wafce su.
Fizge jakar iyami tayi tareda cire kudin tana cewa'"
Wlh Babu dakinda zata kaisu Dan nasan ba albashinta bane,
Amatu kifadamin gskia inda Kika samo kudin Nan??
Kallon kawu tayi daya qura Mata ido Yana jiran jin Abinda zata fada saidai yanda tayi da fuska yasa ya fahimci inda kudin suka fito ya gyara zama tareda murzawa idonsa toka ya matse fuska yace"
Iyami so nawa nake fada Miki kidainawa yarinyar Nan haka?
Addua akeyi Allah ya shiryamanasu yabasu abinyi,
Kinga banason kina irin haka saiki tozarta gaban maqiya ga gida cikeda da maqiya komai muke ciki kunnuwan munafukai akanmu.
Kallon takaici tamasa tareda tura kudin cikin zaninta tana cewa'"
Allah yasa kugane yakuma shiryaku ku duka.
Ganin maman junior shugaban munafukan gidan ta shigo yasa ya hadiye maganar dayayi niyyar yi tareda cewa amatu "jeki.
Tana juyowa Ido biyu tayi da maman Junior wacce da alama daga kasuwa take ko dan jakar dake jikinta da uban mayafin data yafo daya gama miqewa da zufa ta dauke Kai ta wuce tana tsokanar junior dake gefen maman daukeda leda dayake yaron mutumintane suna dasawa sosai
Ko kallon maman taqiyi sbd ganin irin kallon masifar datake binta dashi tareda harara.
***
Bakin Babban gate din ZABEERA motarsa ta tsaya batareda yayi horn masu gadin suka bude Masa da sauri tsananin girmansa dasuke gani fiyeda kowa a gidan idan aka cire iyayen familyn.
Da kansa ya tuqo motar sbd yabar malam take gida da yaronsa suyi sorting matsalar data kaisa hannun 'yansanda harya kwana station.
Sake kallon agogonsa yayi bayan ya kashe motar kafin yafito a nitse ya rufe motar ya nufi doguwar hanyar dazata sadashi da sashen Modibbo wato mahaifinsu.
Tafiyar mintuna hudu ce takaisa shashen Yana tura babbar qofar palon ummi na fitowa babbar 'yar gaban goshinta nuratu na gefenta kowannensu fuskarsa Babu alamar farin ciki Wanda daga gani ummin ce ke cikin baqin cikin nuratu ke tayata damuwa.
Dattijuwace saidai hutu da tsananin jin Dadi da ilimi tareda gayu yasa shekarun nata sun dai 6oye sbd jikinta dayakeda kyau sosai.
Kallon daya zakayi Mata kasan itace matar gaban goshin me mallakar gidan sbd tsananin Isa da ikon datake nunawa.
Cak ta tsaya bayan ganinsa zuciyarta na qara tafasa da takaici saidai tayi controlling fitowar fushin nata ta kallesa da fararen idanuwanta
Batareda ya kalli fuskartaba Yana kallon qofa cikin nutsuwar muryarsa data sanya nuratu Dan matsawa gefe tana kama kanta sbd tsananin kwarjininsa yace"
Umme barka da yamma,
Kina lafiya??
Kamalalliyar fuskarsa dake daukeda wani sirrin kyau ta kalla tana danne bacon ranta tace"
KHALIL baya daukan maganata ka fahimtar dashi inason yayi aurene sbd lafiyarsa sbd mganarka kawai zai saurara sbd Kaine ubansa.
Tana fadar hakan ta wuce Bata tsaya jiran Abinda zaice ba sbd tasan ba maganar zaiyiba ko zasu shekara ahaka tasan dai yaji Kuma ya fahimta.
Wannan shine daya daga cikin Abinda ta tsana gamedashi shine tsabar miskilancinsa datake kallo amatsayin ji da Kai ganin yafi dukkanin 'yayan ZABEERA zama successful business tycoon Wanda yake muamala da manyan gwamnati da sarakuna.
Kai tsaye yashiga cikin palon na Modibbo bakinsa na fitarda sallamarda modibbon ne kawai yaji ya amsa sbd sanin yanda mgn ke fitowa abakin 'dan nasa.
Gaban Modibbo din ya zauna tareda dagowa cikin girmamawa yace"
Barka da yamma modibbo,
Ka yini lfy?
Alhmdlh MAHMOUD
Ya iyalin naka??
Alhmdlh"kawai yace tareda kallon 'dan uwansa dake gefensa zaune ya sakar Masa wani qayataccen murmushi Wanda duniya dashi kadaine zakaji yayi doguwar magana ta fira a kaf family haryayimasa murmushi Wanda ko mahaifinsu iyakacinsa dasu bin umarni da biyayya Amma Khalil ne kadai Wanda ke ganin sakewar Mahmud din ciki kuwa harda matarsa wadda iyakacinsa da ita zaman biyayyar aure da bin umarni tareda mutunta juna.
Cikin murmushi Khalil ya kallesa Yana cewa'"
Allah ya taimaki ZABEERA na hudu.
Batareda ya kallesa ba ya murmusa har fararen haqoransa suka bayyana sbd wannan wata zolayace da Khalil din yake Masa tun suna Yara sbd ya tsokanesa musamman yanxu dayasan karban wata sarauta shine Abu na qarshe dazaiyi arayuwarsa sbd ya tsaneta indai akansa ce.
Gyaran murya Modibbo yayi tareda kallonsu suka nutsu tareda maida hankalinsu akansa yasake gyara murya cikin bada umarni da hukuntarwa yace"
Mahmud safiyar yau ZABEERA ya aiko da saqon a sanar dakai waadin mallakar kujerarka ta ZABEERA na hudu Dana bayarda sunanka yacika
Zaka shirya komawa masarauta tareda iyalinka.
A matsayin mummanan sako ya dauki zancen sbd zuciyarsa da Bata karbi abinba ko da a mafarki saidai Kuma Sam fuskarsa Bata nuna alamar gamsuwa ki rashinta Khalil kawai ne zai qarar da cewa wannan ba Abu bane me yiyuwa a rayuwar md zabeera din.
Cikin girmamawa yace"
Modibbo idan naje Naga ZABEERA akan wannan alamarin Ina fatan bazan 6ata maka ba???
Kallonsa Modibbo yayi na tsawon sakanni kafin yace"
Idan har kana tunanin sanarda mahaifina ne cewa baka karba saqonsa ba tabbas zaka Sa6a ne.
Cikin sake nuna biyayyarsa yace"
Inshallah ba hakan bane.
Karka damu zakaje Amma sai ranar tafiyarka gaba daya.
Shiru yayi na Dan lokaci kafin ya miqe tareda cewa'"
A yini lfy Modibbo.
Ficewa yayi Khalil na biye dashi suna fitowa ganin yanayinsa yasa Khalil barinsa yaje yasamu nutsuwa tukuna duk da Babu Abinda ya nuna na damuwa ataredashi.
Motarsa yaja ya qarasa sashen dayake can kusan qarshen babban gidan Wanda yake nasa yanayin parking yafito yashige.
ZARAH dake zaune palon tareda me aikinta ta dago Kai tana ganinsa ta ajiye wuqar datake yanka gwaiba da ita ta miqe tareda qarasowa gabansa tana Masa sannu da zuwa cikin nutsuwa daidai shigewarsa hanyar dazata sadashi da zuwa sama inda dakinda yake ya amsa Mata da madaidaicin sauti sbd Bata iya wulaqanta ta sbd darajar sure dakuma biyayyarta tareda darajar Modibbo daya aura Masa ita.
Ganin yanda ta taso din Dan kulawa yasa yadan tsaya tareda kallonta cikin Ido sosai Yana qoqarin Bata mahimmanci yace"
Ina buqatan light abinci Mara nauyi.
Murmushin qara ganin girmansa tasaki sbd yanda akoyaushe yake mutunta zamanta matarsa har kaqoranta suka bayyana ta matsosa sosai tareda kama hannun damansa ahankali ta riqe cikin nata ta dago ta kalli fuskarsa da ya juyo ya kalleta tace'"
Thank you MD ZABEERA.
Kallonta yayi yace"
Ina jira""ya haye saman tana binsa da kallon kauna fuskarta cikeda murmushi kafin tajuya ta nufi hanyar kicin tana cewa'"
Hafsat zo ki niqamun kayan Miya a blender.
**
Umme tunda Takoma palonta ta zauna tana sauke numfashi tanason saukar da zuciyarta ga wannan al'amarinda yake faruwa da ita ako yaushe.,
'yayanta kusan sune koma baya a cikin familyn ZABEERA,
Dukkanin 'yayan Modibbo matane su goma sha shida Khalil da Mahmud ne kawai maza Kuma sune dukkanin wani burin Modibbo ya Dora akansu sai gashi ita nata 'dan shine wani iri Sam ko kyashin 'dan uwansa bayayi duk da Shima Barr ne babba me zaman kansa Kuma yanada nasa arzikin daya Tara bana mahaifinsu ba Amma Sam bai kamo MAHMOUD ba Wanda duniya shi kowa yafi sani a familyn ZABEERA yanzu.
Burinta idan har MAHMOUD yafi Khalil ta wani bangaren to shi zai karbi zabeera na hudu ta yanda zai take MAHMOUD din ta fagen suna,arziki,mulki,dakuma martaba a idanun mutane saigashi Rana tsaka su Modibbo da zabeera sun zaba MAHMOUD Wanda Sam bazata yardaba.
Kamar daga sama taji daga bayanta ance"
Aisha wannan karon damar kice ta qarshe kisa Khalil yayi aure ko su Modibbo zasu sauya shawara su zabesa sbd shi wancan miskilin baya buqatar kujerar zabeera,
Duk wani suna ko arziki ko girmanda ake buqata ya samu abinsa da kansa amatsayinsa na Architecture MD ZABEERA so yanzu zabi ya rage naki na kisan yanda zakiyi.
MD bayada uwa a duniya bayada dangin uwa a duniya to kina tunanin idan yazamo zabeera na hudu waye zai nuna Miki iyakarki idanba zainab uwar matarsa ba wadda ko kadan kinsan Bata qaunarki.
Rintse ido ummen tayi tana jinjina 'dacin da zuciyarta keyi da zafi tace'"
Babu Abinda yakai ciwon hassada zafi a zuciya wlh Maryam,
Tun kafin MAHMOUD yazo duniya bandamu da uwarsa ba harta haifesa ga bar duniya bantaba kulawa dashiba duk da tsananin biyayyar dayakemin Amma tunda yafara zama wani abu a rayuwa Abu yazo ya dameni wannan masifa dame tayi Kama wlh zuciyata takasa samun nutsuwa shawon shekarun cigabansa
Amma wannan karon zanyi Abinda bantaba yiba.
Dawowa gabanta haj Maryam tayi tareda zama kusada kejerar dake kallonta tace'"
Me kenan???
Miqewa tayi tsaye tana takawa ahankali tace'"
A duniya Babu Abinda Modibbo da zabeera suka tsana irin cin Amana da zubarda mutunci,
Zansa su tsanesa tsana mafi Muni wadda zatasa sunansa yafita daga cikin zabeera bama zabeera kawaiba duk duniya ma saisunji yafita ransu sundaina ganin mutuncinsa.
Murmushin mamaki haj Maryam tasaki tana cewa'"
Wane laifi?
Wane cin Amana Kuma???
Laifin ciki
Da laifin zubarda mutunci ta hanyar aikata 6anna.
Wani murmushin haj Maryam tasaki tana cewa'"
To waye yayiwa cikin ni ki fahimtar Dani yanda zangane.
Baiyiwa kowa cikiba Amma kudi zasusa ace yayi cikin.
Aisha kina tunanin akwai Wanda kudi zasusa tace MD yamata ciki karki manta MD mutuminda kowa ke mutuntawane wannan maganar bamai karbuwa bace mu canza shawara.
Maryam kudi duk inda kike tunanin su sun wuce Nan,
Akwai mutane birjik a duniyar Nan dazasuyi aikin komai sbd kudi musamman kudi irin wainda zan zubar akan wannan aikin.
##Mamuh##
#ZAFAFABIYAR##