SILAR FYAĆŠE

19/20

by @rabiattu0444

*🍀SILAR FYAƊE🍀*




NAđź’‹

*UMMU MAHER(MISS GREENđź’š)*


Wattpad user name

  Rabiatu333


Arewabooks

rabiattu0444




 19⬜20



Kai tsaye ɓangarensa ya nufa bai nemi kowaccensu ba,Rasheeda kuwa ta kafa ta tsare tana jikin windon ɗakinta ta saman bene tana hango Admiral A.sanda ya shigo don haka har komawa ɗaki ta yi ta ƙara shafa hoda da janbaki tare da ɗakko wani turarenta mai mugun ƙarfi ta shafa.



Ita kuwa Gimbiya Salimat tana kan sallaya ta ɗaga hannuwanta biyu tana roƙon Allah akan Allah ya mallaka mata ziciyar Sojanta.



Tana cikin wannan addu'ar jakadiyarta ta shigo tana neman iso,tana shigowa ta ce"uwar É—aki na kuma uwar gida a wajen angonta Admiral A.Yanzu naga motocin Admiral sun shigo gidannan, don haka na garzayo don inzo in gaya miki wannan albishir.

Ɗan murmushi Salimat ta yi sannan ta ce"nima ina yi mishi barka da dawowa Allah ya tsare mana shi a duk inda ya saka ƙafafunsa,amman bazan je ɓangarensa ba don a yanzu hutu ya ke buƙata don haka nasan da kansa zaizo".


kallonta Jakadiyarta ta yi sannan ta ce"haba uwar gijiyata kin fa san ba ke kaÉ—ai ce matarsa ba yana da wata,ba kya tsoron ita yanzu taje ke baki je ba."



"Hmm Yaya na fuskanci abinda ki ke nufi amman nasan kinfi kowa sanin Ć´aĆ´an sarauta da kuma yadda suke gudanar da sha'aninsu na sarauta,don haka ba zan iya zuwa wajensa ba saboda kada ajina ya zube".



Jakadiyarta dariya ta yi tana ganin wauta da kuma ƙuruciya ce ta ke damun Salimat don haka bata ƙara cewa komai ba ta fita daga ɗakin don tasan halin ƴaƴan sarauta akwaisu da kafiya.



Tun rana Aliyu ya dawo amman ko nan da cen baije ba,don yana shiga ɗakinsa da ya yi wanka yabi lafiyar gado ya ƙwanta don baya son hayaniya.




Rasheeda kuwa tana cen hankalinta a tashe don tana saka ran dawowar miji amman kuma taji shiru,don haka da kanta da daddare ta shirya cikin wasu arnan kayan bacci wanda sunansu sabon salon fanÉ—arinka a waje.



Sannan ta ɗakko wani turarenta wanda Hajiyar Aliyu tayo mata oder ɗinsa tun daga Sudan,matuƙar namiji ya shaƙesa to fa ya gama aiki.




A hankali ta fara ƙwanƙwasa ƙofar ɗakin,shi kuwa Aliyu ya zata mai kawo mishi abinci ne ya ce"come in".



Babu wani jan aji Rasheeda ta shigo tana wani takunta kamar wata munafuka,tana shigowa ta cire hijabinta kai tsaye ta yi wajen Aliyu.








*Miss green ce*


Kuyi min afuwa rashin charge ne👏🏻



Na gama littafin darasi free page,don haka idan mutum yana da buƙata ya tintibeni ta wannan no ɗin.




Ga É—anÉ—ano da ga littafin darasi na payments.



DARASI!DARASI!!DARASI!!!




Alokacin General A.ya shigo da muƙarabansa waɗanda suka rakosa motoci sunfi goma sha,tun daga nesa ya ke kallon kyakkyawar halittar Fahima ga gashinta sai ɗagawa ya ke kamar wara ba indiya ko balarabiya,ya yi tsaye yana kallonta yana mamakin a ina aka samo wannan kyakkyawar yarinyar?.



Dai dai lokacin aka tsuge da ruwan sama mai tattare da ni'ima da ƙanshin ƙasa haɗi dana flowers ɗin gidan,ga wata iska mai daɗi.




Tsalle Fahima ta ke tana wasa da ruwan kana ganinta ka ga yarinya,a hankali Ammar ya biyo ta bayanta ya cire rigar sanyin da ya saka ta sojoji ya lulluɓawa Fahima,da sauri ta juyo cikin tsoro,aka yi rashin sa a ta zame ta faɗo ƙirjin Ammar yadda kasan awani indian film haka abin ya faru,daga shi sai singlet,gashin ƙirjinsa ya ƙwanta kamar wani gashin jariri.



Kallon ƙuda suka shiga yi babu ko ƙiftawa zuciyoyinsu sai bugawa suke kowannensu zai iya juyo ta ɗan uwansa.




A dai dai wannan lokacin kuma hancin motar Hajiya Sakinat ta shigo,bata kula da abin da ke faruwa ba sai da ta fito sai da ta da fa murfin motarta sannan ta iya tsayawa da ƙafafunta,idanunta sunyi jawur kamar gauta wata wutar jaraba da wutar kishi Sakinat taji a ƙirjinta,cikin wani irin mahaukacin sauri ta tunkaro inda su Ammar da Fahima suke.