Halin Dana Shiga...

8

by @shooly84

🐽𶀠нalιn dana ѕнιga...💘



~Labarin gaske ne~




© ᴬYˢᴴᴬ ᴹᴬᶜᴴᴵᴷᴬ




*Arewabooks@Shooly84*




💘 8 💘







  Ina nan ina lisssfin zuwan Ibraheem kaduna tare da lissafin ranakun da suka rage na bikin ƴar uwata Farida, abin haushi Muhammad ke faɗa mun wai Ibraheem ya fasa zuwa, hankalina ya tashi na shiga damuwa nace to akan me ya fasa Muhammad?


Ba wai ya fasa bane gaba ɗaya, ya dai ɗaga tafiyar ne sabosa Abdul ya faɗa mishi bikin Farida 21 May shine yace zai bari sai lokacin yazo danya samu ya halacci bikin, yace dai wuraran 15 May ko 18 zai iso, kinga alissafi yau saura wajan kwana ashirin da huɗu kenan.


Ni dai kam jikina ya mutu dan naji ba daɗi nariga na gama sa rai da zuwanshi yanzu kuma ace an fasa, Muhammad yace "haƙuri zakiyi ki kwantar da hankalinki kamar yau ne zakiga lokacin yayi har kunga juna..."


Aini damuwata ɗaya Muhammad kar lokacin yazo yace ya kuma fasawa, yace ina insha Allah haka ba zai faru ba kisa rai ma kinga Ibro ɗinki kin gama.



Muna nan tsaye tare da Muhammad Abdul-Jabbar yazo ya faka motarshi kusa data Muhammad, inda muka bishi da kallo.


Inda Muhammad yace kai wannan rai da naci yake, shiko fushi ba yayi, jiya yazo an wulaƙantashi yau ba zai hamashi zuwa ba, amuzantashi amma ba zaisa yaƙi dawowa gobe ba, kaini ban taɓa ganin jarababben mutum irin wannan ba.


Nayi dariya nace na yadda lallai da gaske kana taya Ibraheem kishi, tunda agabana kake zagar min saurayi, ya ɓata fuska yace "Asiyah tunda Ibraheem ya soma sonki bai ƙara kula wata mace da sunan so ba, amma ke kullum cikin tara samari kike saboda Allah kinyi mishi adalci"?


Toh ya zanyi Muhammad, cewa fa ake ana sona bani ke cewa ina so ba, amma dai ya kamata kisan irin takun da zaki rinƙayi masu ko?  


Na rinƙa wulaƙantasu ko?


Bance ba, amma ya kamata ki guji fushin Ibraheem dan yana kishinki da yawa, duk randa ya ganki da irin waɗancan akwai fitina, nace to shikenan zanyi ƙoƙari na kiyaye, bai bari Abdul-Jabbar ya ƙaraso inda muke ba yai min sallama ya shige motarshi yai gaba ya barni da dariyar yanda yai kicin-kicin da fuskarshi kamar shine Ibraheem ɗin, shi bai yadda ba yana taya ɗan'uwanshi kishi.


*****************


Ina zaune kan dardumar dana idar da sallar magriba ban tashi ba inaso akira isha nayi saina fito falo, daganan cikin ɗakin naji muryar Bashar da Abdul a falon Mami.


Bashar ke faɗima Abdul wai Isa yai mai waya ɗazu yace afaɗa mishi Ibraheen yayi Accident, ya nemi layinshi bai samu ba shiyasa ya kirashi ya faɗa mishi, itama Asiyar bai sameta alayinta ba...


Ni da nake sauraro daga ɗaki nafi wanda ake gayama saƙon fahimtar abinda akace, Ibraheem yayi Accident kalmar dana rinƙa nanatawa akan harshena kenan, yayin da gaba ɗaya jikina ya ɗauki rawa saboda tsoro da firgita dajin abinda ya faru ga Ibraheem.


Na tashi da kyar jikina ba ƙarfi na isa inda su Abdul suke na jinkina da ƙofa wadda taimin makari daga faɗuwa naci gaba da sauraren abinda Bashar ke cewa.


Wai jiya sukai hatsarin su huɗune acikin motar ɗaya ya mutu shi kuma Ibraheem ɗin yai muguwar buguwa wanda har yanzu baisan inda kanshi yake ba...


Jiri gaba ɗaya ya taso min na tashin hankali nai taga-taga zan faɗi Mami tai saurin taroni ta zaunar dani kan kujera, nan na sami damar rintse idanuwana da ƙarfi kalmomin da naji abakin Bashar su suke yawo atsakiyar kaina suna haddasamin tashin hankali.


Abinda zuciyata tafi rayamin shine mutuwa Ibraheem yayi, inba haka ba ya za'ace tun jiya har yau baisan inda kanshi yake ba, hawaye masu zafi suka soma zuba daga idanuwa zuwa kuncina, naji wasu hannaye masu taushi suna goge mun, na buɗa ido Mami ce itama cike da tausayi, na kifa kai acinyarta na soma rera kuka irin mai tsayawa arai cike da tausayi.



Ina nan zaune cikin tashin hankali aka aiko kiran Abdul ya fita bada daɗewa ba ya dawo yace zo nan Asiyah, na tashi da hanzari jiri na ɗibata nabi bayanshi, na iskeshi tare da Muhammad awaje gaba ɗayansu cikin damuwa suke, nai saurin ƙarasawa wajensu na tsugunna gaban Muhammad ina kuka mai tsima zuciya.


Shima ya tsugunna gabana yace "ba kuka bane abinyi Asiyah, ki miƙa duka lamarinki ga Allah", na ɗago fuskata data lalace da hawaye nace Muhammad wane hali Ibraheem yake ciki?


Ya yarfar da hannaye tare da ɗauke ido akaina, nai saurin riƙo hannayenshi nace ka taimaka min Muhammad nasan halin da yake ciki, yace "bansan halin da yake ciki ba yanzu Asiyah".



Na maida kai cikin cinyoyina na tsananta kuka ina faɗin kantaimaka min Ya Allah! Ka tada kafaɗar bawan nan naka Allah, karkasa halin nan da yake ciki yai sanadin rabuwarmu ta hanyar ɗaukeshi aduniya, ka agaza min Ya rabbi.



A cikin gida na kasa tsaida hankaina waje ɗaya, na kasa tsayawa na fahimci inda kaina yake, na dai tsinci kaina na ɗauro alwala nazo na tada sallar isha'i cikin rashin fahimtar me nake karantawa, atunani na idar na zauna na dunga rabka roƙo ga Lillahi ina fatan ya baiwa Ibraheem lafiya.


Na daɗe awajan kafin na sami ƴar natsuwa araina har na ɗauko waya na soma neman layin Ibraheem, cikin rashin sa'a layin akashe yake, nan na soma wani sabon hawaye haƙiƙa Ibraheem inma yana raye toh yana cikin mawuyacin hali.


Tunanin Yusuf ya faɗomin aminin Ibraheem da suke tare a lagos ta hanyarshi kawai zan san awanne hali Ibraheem yake ciki yanzu, dan haka nai hanzarin nemo lambarshi cikin sa'a bugu ɗaya ya ɗaga da faɗin Asiyah ya kike?


Cikin muryar kuka nace Yusuf awane hali Ibraheem yake ciki?


Yai ɗan shiru can ya nisa yace Asiyah Ibraheem kam yana cikin mawuyacin hali, na damƙe bakina da hannu sakamakon kuka mai ƙarfi daya suɓuce min, yaci gaba da cewa "har yanzu wallahi baya cikin hayyacinshi, tunda aka kaishi asibiti har zuwa yau ko yatsa bai motsa ba, wallahi Asiyah addu'ace kawai ya kamata mutashi da ita akan Ibraheem domin rayuwanshi yana cikin wani irin hali....


Duk yanda naso ɓoye mishi halin damuwar dana shiga hakan ya faskara domin gaba ɗaya na sakar mishi kuka matsinanci, ba na iya ce mishi komai sai kunji nake ina salati yana rarrashina daban haƙuri amma bana iya sauraron me yake cewa, aƙarshe ma kashe wayar nayi nai kwance kan kafet ina rusa kuka.


Tun daga ranar ban ƙarajin komai dangane da Ibraheem ba, duk wata hanya da zanji halin da yake ciki toshe suke, na daina ganin Muhammad na daina ji daga Abdul, Yusuf ko yaushe wayarshi akashe take, Isa baya ɗaukar wayata su Nafisa ma gaba ɗaya na daina jin ɗuriyarsu.




Tsayin kwana shidda ina cikin mawuyacin hali na rashin sanin halin da rayuwata ta shiga, kwatsam da yamma ranar saiga waya daga Aunty Amina, da fari ban ganeta ba saboda muryarta ta canza min ainun saida tace nice Aunty Amina, nai saurin tashi zaune, tana tambayata ya nake ina tambayarta halin da Ibraheem ke ciki.


Tace ki kwantar da hankalinki Asiyah na juya kai ina faɗin ba zan iya ba Aunty, na kasa samun natsuwa bana cikin hayyacina duk akan rashin sanin halin da yake ciki, hankalina ba zai taɓa kwanciya ba sai naji yanda yake dan Allah Aunty ki taimakeni nasan halin da yake ciki, (Duk cikin kuka nake maganar).


Tace to ya isa kibar kukan haka, shi kuma jikinshi da sauƙi gaya nan yana jinmu, kukana ya daɗu wanda zan iya cewa ƙila na murnar jin cewa ya soma samun sauƙi ne, ina kukan nace dan Allah ki taimakeni ki haɗani dashi Aunty.


Tace ƙoƙarin da nikeson yi maku kenan, sai dai ina son ki bashi baki akan ya daina magana saboda dokar da aka samashi kenan sakamakon buguwa da yayi ahabarshi harya taɓo wuyanshi wanda ayanzuma matsalar wuyan tafi tayar da hankalinmu.


To tun farfaɗowarshi yake faman kiranki yana son magana dake, an hanashi magana amma yaƙiyin shiru shi lallai sai anhaɗashi dake yaji lafiyarki, dan asamu ya daina maganar ne yasa Daddy yace ahaɗaku kuyi maganar, to dan Allah Asiyah ki tirsashi akan ya daina maganar tunda munkula ke kaɗaice zaki iya sashi ya bari.


Cikin kuka nace to Aunty zan mishi magana tace na gode gashi ɗin.


Yanda naji muryarshi ita kanta ta canza ya ƙara tayarda hankalina, nama kasa cemishi komai sai kawai nasa kuka, cikin muryarshi mara daɗin sauraro dake cike da alamar zafin ciwo atare dashi yace " daina kuka Asi insha Allah zan samu lafiya, abinda nake so dake ki dageyi min addu'a ba kuka ba kinji"? 


Na sassauta nace toh zanma addu'a amma hankalina ya kasa kwanciya, kin damu dani da yawa Asiyah, ina so ki kularmin da kanki, karki bari damuwar ciwona ta haifar maki wata cuta kinga zaki ƙaramin wata damuwar dan Allah ki rinƙa dauriya kinji Asi?


Na ɗaga kaina kamar ina gabanshi jin banyi magana yasa yace kukan ne ko? 


Muryata na rawa nace a'a inayima addu'a ne azuciyata, na gode Asiyah kin damu dani da yawa...tari ya somayi ahankali ya fara ƙarfi har takaishi ga yin wani irin kakari yana fidda wani irin wahalallen nishi, anan na ruɗe hankalina ya ƙara tashi na birkice ina ihun kiran sunanshi amma bai kula ba aƙarshema dai wayar tsinkewa tayi ta barni nan cikin matsinaciyar damuwa da tashin hankali...




(Wayyo Allah Asiyah, wayyo Ibro😭😭😭 rayuwa kenan mai zuwa maka salo-salo da canji tamkar canjin launi Hawainiya)






Machika novels🤳🏻