12
by @shooly84
🤳🏻
💘 нalιn dana ѕнιga...💘
~Labarin gaske ne~
© ᴬYˢᴴᴬ ᴹᴬᶜᴴᴵᴷᴬ
*Arewabooks@shooly84*
*_Not edited_*
💘 *12* 💘
Mun kusa mintina goma tsaye muna kallon juna, a zuciyata ina raya abubuwa da dama, ji nake kamar naje na rufeshi da duka naita ƙudunduma mashi ashar, zagi na rashin mutunci irin wanda shi da kanshi sai yaji ya tsaneni ( To amma ko nayi hakan ribar me zanci, illa ce dai sun riga sunyi mani).
A hankali na ɗauke ido kanshi na samu waje na zauna nai ƙasa da kai, ya samu waje ya zauna kusa dani, ban kalleshi ba shima bai tankani ba, shiru na ɗan tsayin lokaci, daga bisani naji fitar numfashinshi tare da tashin muryarshi...
Kiyi haƙuri Asiyah, na tada kai na kalleshi na ce haƙuri?
Akan me Muhammad, na san mun zalunceki mun shiga haƙƙinki mun haifar maki da damuwa da tashin hankali, amma ina son ki yarda a kan wallahi ba laifina bane...
Ƴar dariya nayi na ce na tambayeka mana Muhammad, ya ɗaga kai da faɗin ina jinki, na ce dan Allah taya kake sarrafa muryarka wajen magana dani as Ibraheem?
Yai ɗan shiru yana kallon ƙasa daga bisani ya ɗago ya ce natsuwa nake na cire wasa a raina sai na tausasa muryata nayi ƙasa da ita sosai.
Na runtse ido da ƙarfi cikin takaici da yarda da abinda yace na ce daure ka gwada min yanda kakeyi, kamar ba zaiyi ba sai kuma can ya ɗauko waya daga aljihu ya kai kunnenshi...
Nan naga ya natsu ya maida hankalinshi gaba ɗaya kan wayar bayan ya ɗora yatsunshi biyu akai sannan ya fara magana ahankali cikin tausa murya...
Ina sonki Asi, irin son da ban taɓa tsammanin anaiwa wani rai ba, na zamo wawa sakarai akan ƙaunarki,. *halin dana shiga* mai girmane adalilin sonki, na kan jini a takure a ƙuntace hankalina baya kwanciya har sai na furta maki ina sonki ina ƙaunarki ina muraɗin kasancewa tare dake.
Da zaki taimakeni Asi da na roƙi arzikin ki dawo da alaƙar soyayyarki gareni karki duba girman laifina agareki...ina sonki da yawa ni Muhammad ki taimaka kar ƙaunarki taimin illah...
Na bishi da kallon tsana inda na ƙara gasganta lallai shi ne dai, ba tare dana tankashi ba na tsallakeshi na shige gida zuciyata ta ƙara cika da tsanarshi, a yanzu kam na ƙara yarda Muhammad shi ne Ibraheem, haƙiƙa ayanzu na tabbata son da nai gaibu naiwa, na so iska na so babu kai anzalunceni da yawa an taɓa zuciyata.
<<<<<<<<<<<<<<<<<<
Duk yarda na so na cire son Ibraheem a zuciyata na kasa, duk yanda naso na yarda babu shi ɗin nakan so na yarda a duk lokacin da nai ƙoƙarin na amince babushi sai zuciyata ta bijiro min da batun mutumin nan mai baƙaƙen kaya sai gaba ɗaya nabi na sukurkuce.
Wata matsifa shi kanshi mai baƙaƙen kayan na yarda bashi bane Ibraheem amma zuciyata ta afu akan matsanincin ƙaunarshi domin ni shi aka dangantamin da cewar shi ne, dan haka ne dai nasakankance akan koshi waye shi na baiwa soyayyata da zuciyata kai dama kaina gaba ɗaya.
Cikin tsakankanin ne akai bikin Faridah wanda agareni gaba ɗaya bikin yazo min ba cikin daɗin rai ba, saboda bana cikin sukuni bana iya aiwatar da komi daga zama waje ɗaya sai kuma na tashi na kama aiki, na kasa sakewa cikin mutane ai harka..
Har aka gama bikin nan amarya ta tare abinta ni dai ina nanne har zuciyata bata tafiya dai-dai, abin takaici ma awajen bikin daga naga namiji kyakkyawa yai shigar kwatankwacin saurayin da muka haɗu a Business center saina rinƙa aiyanawa araina shi ne Ibraheem.
La'asar sakaliya nai wanka na shirya cikin ƙaramar T-shet da dogon siket na kawo ƙaramin hijabi nasa ƙafata da silifas ɗan madina, na fito falo na iske Mami na ce zanje gidan Anti Lubah yanzu zan dawo, tace to ki gaisheta.
Ina fitowa na hango Abdul ya dawo aiki, yai saurin yin parking ya fito yayo inda nake yana faɗin magana nake sonyi da ke Asiyah.
Na kalleshi da ido ɗaya na ce dan mi? Dan Allah, ya faɗa na juya kai ina tafiya na ce kajirani na dawo, yai tsaye zai sake magana na galla mishi harara nabi gefenshi na wuce ina cewa inhar ba zaka jira dawowar tawa ba to maganar takma bana son jinta, har nayi nisa najiyo muryarshi yana cewa ba zan daina baki haƙuri ba Asiyah, ban dai tankaba nasa kai na wuce ina ƙara tsanarshi da tsine mishi araina...
A gidan Anti Lubah mun daɗe muna maida magana kan wannan al'amari, tace nifa Asiyah na rasa yadda zan fassara wannan al'amari, har zuwa yau na rasa dalilin daya sa Abdul ya shirya irin wannan abu akanki.
Nai tsaki tare da girgiza kai na ce ki barni kawai Anti Lubah wallahi na rasa yanda zanyi akan abinnan, ni abinda yafi damuna illar da sukaiwa zuciyata na rasa yanda za'ayi na tirsasata akan ta yadda babu Ibraheem.
Anti Lubah tace na daɗe Asiyah abinnan na damuna sai nake ganin kamar abin ya faru ne ashirin fim koko irin na karanto a labarun Hikaya, nai dariya na ce fim ko sosai Anti Lubah...tace amma fa ni ina ganin kamar Abdul sonki yake, Allah inhar ba sonki yake ba me zai sa ya damu da al'amuranki.
Na kalleta da kyau na na ce abinda ke kike gani kenan?.
Ta ɗaga kai, na ɗanyi murmushi na ce dako yaci....Anti Lubah ta hana ashar ɗin fitowa ta hanyar rufemin baki da tayi, na kalleta na ce Abdul ko? Uhm , na sake girgiza kai idanuwana kuma sun ciko da kwalla.
A ɗakina Abdul ya sameni ina shirin kwanciya, ya zauna gefen gadona yace dan Allah Asiyah ki saurareni muyi magana ta fahimta, na kalleshi awulaƙance na ce tuni na faɗa maka magana ɗaya ce zan iya yi da kai ayanzu shi ne ka faɗamin dalilinka na kullamin wannan sharri amma kaƙi, kaga ko lakacin tsayawa nai magana da kai ba zai samu ba awajena.
Ya musƙuta yace ba zaki gane bane Asiyah, nifa...ba abinda ba zan gane ba Abdul, na katseshi da faɗin haka cikin buɗe murya, na ɗora da cewa inhar ba waccan maganar bace ta kawoka to katashi kafita ka kyaleni kaji ko?
Yai zaune anan shi bai fitanba bai kuma cemin komai ba, cikin irin kallon da nake mashi na tsana na fahimci mai yiwuwa abinda yake son cemin yake tsarawa a zuciyan shi.
Abdul, na kira sunanshi ya tada kai ya kalleni na ce kana shirya ƙaryar da zaka faɗamin ne? Ya juya kai da faɗin ayanzu nasan komai da zakiji abakina ƙarya zaki ɗaukeshi, amma ba yanda zanyi koma menene ni najawo wa kaina, yanzu dai ki saurara muyi magana, wacce a ciki? Wadda kike so, na gyara zama na ce to ina jinka.
Shima ya gyara zama yace me ki ke so na fara ce miki, ka faɗmain tsakaninka da Allah waye mutumin daya sameni a business center, kasan dashi ka rinjayeni dan kacemin shi ne Ibraheem kuma kai da kanka kasan basuyi ko kama da Muhammad ba balle kace min shi ne.
Yace ƙwarai wannan ba Muhammad bane, to waye? Na tambayeshi.
Yai ɗan shiru yana kallon ƙasa can yace maganar gaskiya bansan ko waye ba shiba, na ware ido kanshi na ce kana nufin me anan?
Abinda nake son sanar dake nima a randa kika ganshi nima aranar na fara ganinshi, banda wannan ranar bancewa ga inda na sake ganinshi, ban kuma san komai game dashi ba, na daɗe ina kallonshi daga bisani nai ajiyar zuciya, na ce taya za'ayi na yarda baka sanshi ba baka san komai game dashi ba alhalin ranar da aka fara yomin waya sunan dana faɗa mishi ne na ce sunana kenan dashi ya kirani.
Ya daga kai yace kin gane ko Asiyah nifa hangoku nayi dashi atsaye alokacinne na raya yin wani abu game dake da wancan maganar, sunan ko da kikaji ya kiraki dashi aranar nina baiwa Muhammad labarin yanda kukayi da mai baƙaƙen kaya, na ce inya kiraki ya kiraki da sunan Talatuwa kamar yanda kukayi da wancan.
Kallonshi nake cikin matsinaciyar tsana, shi kanshi ya karanci tarin tsanarshi dake cikin zuciyata dan haka ya sunkuyar kai ya soma magana ƙasa-ƙasa, kiyi haƙuri Asiyah, nasan anshiga haƙƙinki munyi miki abinda sam bai kamata ba, to amma ni...
Tsaya Abdul, na katseshi da faɗin haka, ya kalloni na ce kasan abinda nake sonji?
Ya girgiza kai na ce yau ina so ka tabbatar min magana ɗaya akan Ibraheem, tsakaninka da zatin Ubangiji ka faɗamin gaskiya akwai Ibraheem ko babu shi?
Ya daɗe yana kallona kamin daga bisani ya nisa yace, zahirin magana Asiyah Ibraheem akwaishi to amma...yai shiru yana kallona, na ce to amma me kaci gaba da maganarka man.
Yace ai maganar ce bansan ta inda zan ɗauko miki ita ba ki fahimceta, na ce duk ta inda ka ɗaukota zan fahimceka ni dai ka warware min ƙullin dakukamin, ya juya kai tare da gyara zama ya soma magana da cewa...
Machikanovels