IDON DUNIYA

episod 7

by @mrsfh

wasila omar (mr's f.h)



โญ๐ŸŒ™๐ŸŒ™๐ŸŒ™๐ŸŒ™๐ŸŒ™๐ŸŒ™โญ

 ๐ŸŒ™โœจMOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION๐ŸŒ™โœจ

***


""we are the moonlight writer's we shine all over the world."๐ŸŒŽ'โœ๏ธโœ๏ธ


Bismillahirrahmanurrahim

~~~~~~๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž~~~~~~



   page 11&12


Washe gari kuwa jasra kasa tashi tayi dukda tana jin kiran sallah amma taji dadi baccin,sai da taji an shiga masallaci sannan ta iya mike wa ta nufi toilet ta dauro alwala anan kan carpet din tayi sallah tayi azkar gami d yan addu'o'in ta sannan ta jin gina da gado tana lazimi,sai sauke aziyar zuciya take tana jin wata nutsuwa na saukar mata,tana haka taji an bude kofar dakin ido biyu sukayi da ita ta saki murmushi JASRA tayi sauri sadda kanta kasa tana gaishe ta"ina kwana anty"sosai taji dadin yadda ta kira ta domin haka ake kiranta dashi tana murmushi ta amsa "lafiya kalau diyar kirki ya kwanan bakunta harkin tashi ashe"?gyada kai tayi alamar ehh murmushi kwance a fuskar ta tana me jin dadi

kai tsaye anty gadon tayi ta dauki Aryan da yake bacci sannan ta kalli jasra tace "idan kin idar ki kwanta ki huta kafin na tura asamo muku kaya anjima sai kiyi wanka kinji," "to anty na gode" "ba komai shi aryan yanzu zan masa wanka akwai wasu kaya da na siya zani barka bazan barshi ya zauna haka ba"t karashe maganar da kallon yaron dake hannun ta,murmushi jasra tayi ranta fari ana nunawa Aryan dinta kulawa "to anty aikuwa yana son wanka"ta karasa maganar tana rausayar da kai,murmushi Anty tayi tace "aikuwa ya samu bari muje ki huta kinji d'iya ta"ta kara sa tana fita daga dakin murmushi kawai Jasra ke saki ita daya kafin daga bisani ta mike da koma gadon ta kwanta aikuwa bacci me dadi yayi awon gaba da ita,sai wajen karfe goma ta farka sanadin bod'e kofar da akayi ta kalli kofar da fuskar masu bacci anty ce rike da manyan ledoji guda biyu ta karaso ta ajiye kana ta kalli jasra"d'iya ta ki tashi ki shirya ga kayan ki nan sai ki fito kiyi break koh"ta karasa tana duban jasra"to anty na gode allah kara budi" "karki damu maza ki tashi dan nasan kina jin yunwa" ta sakko daga kan gadon tana ji kamar ta tambayi anty ina aryan amma sai ta kasa ta nufi toilet dan yin abinda anty tace,


  Duk suna falon azaune ta fito sanye da wata doguwar riga ashh me stones kamar an auna da jikin ta ta zauna das da ita ta daura dan kwalin rigar duk da akwai rama a jikin ta tayi kyau sosai,kanta akasa ta karasa katafaren falon dake cikin gidan ta zauna a k'asa kusa da anty ta gaida wanda ta gani a zaune"ina kwana"ta furta a sannu sosai mutumin yake kallon ta yana gani kamar yasan fuskar ta amma ya kasa tuna inda yasan fuskar"lafiya kalau diya ta ya kwanan bakun ta"?"lafiya kalau alhamdulillah"sosai yaji yarinyar ta kwanta masa yanda yaga nutsuwar ta tafi yanda Maryam(anty)ta fada masa,maida kallonsa gun anty yayi da take ta murmushi yace"yau dai maryam anyi ya'ya hankali ya kwanta"ya fada da murmushi kafin ya kalli jasra ya ce "ya'ta zaku zauna anan tare damu ki dauke mu amatsayin iyaye kinji,ni sunana alhaji abbas amma abbu d'ana ke fada min sai kuma matata gata nan kin ganta ita kasan cewar kowa na gidan su anty kece mata yasa shima danta ke ce mata anty,sai kuma yayan ki wanda yake kasar waje karatu sunan sa habib amma nanda yan watanni zai dawo,to yanzu ke da aryan kun shigo cikin mu ina fata zaku iya zama a cikin da wannan familyn".ya fada yana duban ta Jasra rasa abin fada tai tsabar dadi kawai ta fashe da kuka me sauti cike da tausayi anty ta jawo ta jikinta tana dan dukan bayan ta,har ta tsagaita da kuka antyn tace ku tashi muyi break.


WAYE ALHAJI ABBAS 

 

ku biyo alkalamin mr's f.h domin jin asalin sa

 



mr's f.hโœ๏ธโœ๏ธ