Rumanah (Zabin Iyaye)

6

by @shooly84

Rumanah🕊️

(Zabin Iyaye)




Arewabook@Shooly84





©️ Aisha Machika







Page~6






Tambayar a ba zata tazo mani, sai da na dai daita numfashi na sannan na ce, banji abinda kace ba sosai É—an maimaita, yayi murmushi oh! Baki ji da kyau ba ko? Cewa nayi ki aure ni, wani kallo nake mai nace wai wasa kake ko gaske dan Allah? 


Wane irin wasa Rumanah, dama ana maganar aure da wasa ne, da gaske nake, kada ka mance dai kai yayana, na sani amma ai akwai aure tsakanin mu, na kawai da kai, rufa man asiri gwanda kai Baba Sarki ya gama da naka babin, ka barni nima in auri *Zabin Iyaye* .


Saboda baki sona? Na kallai, kasan dai in Baba Sarki yaji wannan maganar korarmu zai yi, gara kai kana da gida nifa? Har yau baki bani amsar tambayata ba, shin kina so na? Na ɗauke kai ganin ya ƙura man ido, ni bana wani son ka, bana maka son aure sai na ƴan'uwanta ka, dariya ya yi kalli idona ki ce baki so na, nai mashi kallo ɗaya na ɗauke kai, na kalla kuma bana son ka, hmmmm kina zaton zan barki ki aure wani ne ba ni ba? Kinyi kuskure idan tunaninki kenan, na rasa Hairatu nayi haƙuri karo na biyu Allah ya sanya mani naki son ba zan yadda inyi sakaci ba.


Ni dai nace bana sonka kuma ba zan aure ka ba, saboda haka a buɗe man ƙofa na fita ga sallar magriba can ana kira, shin yaya ma zaka yi da matarka kake tunanin sake wani aure? Jamila wai uhm wannan ƴar tsaron gida ce, dan ban ɗauketa mace ba, look Rumanah ki tausaya mani mana yanzu fa am 36 yrs bani da matar da nake so...kaga Saraki idan bacci kake ka tashi ka buɗe man ƙofa dan Allah in fice, ya juya kai, sai kin amince zaki aure ni, na tsaya kurum ina kallon shi cikin mamakin shi, dan gaba ɗaya ya sauya mani kamar ba Yaya Sarakin dana sani ba, nace an taba aure ba'a so ne? Bana maka son aure...ni ina sonki ai, son nawa kuma ya ishemu rayuwa, zan maki komai da kike so, gobe ma zanje in faɗi ma Baba Sarki, na tabe baki kaje mana iyaka dai kai zaka soma shan bullet ba ruwana, kuma indan ina zama gidan ka yasa ka bullo da wannan tatsuniyar toh sha kiruminka gobe zan bar maka shi.


Bai sake cemun komai ba ya buɗe man ƙofar, na kusa shiga ɗakina naji muryarshi, kifa shirya gobe zan faɗima Baba Sarki, banko juyo ba dan ban ɗauki maganarshi da wani muhimmanci ba, toh idan ba wasa yake ba ai yasan yarda suka kwashe da Baban kan maganar Hairatu, dan haka zuciyata ta amince da wasa yake.


Bayan na idar da sallah kayana na haÉ—a tsab, ina gama abinda nake na mike na nufi É—akin Jamila, tana zaune bakin gado, nima zama nayi a kujerar madubi na fara magana, toh Jamila mu yafi juna danni gobe in sha Allah zan bar maku gidanku, tun kafin mijinki ya ce yana so na ki bani, dan Allah idan nayi maki wani abu ki yafe mani ni dai na yafe maki duniya da lahira.


Sannan dan Allah ki daina yi ma mijinki rashin kunya, hakan zai sa sonki a zuciyarshi shekarunku bakwai da aure fa amma har yanzu ba wani labari, ba wani jin daɗin ƙuricciya balle maganar ƴa'ƴa, ba wai wa'azi zanyi maki ba amma dole in gaya maki gaskiya saboda kina mace ƴar'uwata, kinga biyayya ita ce aure, wallahi in har ba biyayya da ladabi da ganin mutuncin juna tsakaninki da mijin ki toh dama ba wani daɗin zama zaku ji ba.


Mace kike fa, kina da kyau ga miji mai kyau kin samu wanda ko wace mace zata yi fatan samu, amma ke kin samu kina wulaƙantawa, Jamila mu mata Allah yayomu da wata irin baiwa ta sarrafa ɗa namiji, ko wace mace da tata hikima da baiwar da Allah ya bata, dan haka kibi duniya a hankali ba matabbata bace, tun kina tashe wataran tsufa zai zo da dana sani mara amfani.


Ni ka É—ai ke surutu na domin Jamila kanta na Ć™asa ba tace uffan ba, ta kalleni kin gama wa'azin naki? Nayi murmushi oh wa'azi ne ma Jamila? 

 

Inde kin gama dan Allah ki fice man a ɗaki, gida kuma Allah ya kiyaye hanya ki gaida mutanen gidan, na miƙe ina kallonta, Jamila daga ƙin gaskiya dai sai bata, na juaya na fice.


Washe gari naje makaranta yin wasu abubuwa, bayan na gama taxi guda na ɗauka saboda kayana da yawa, na baro makarantar duk da nasan Saraki na ciki, koda na shigo falo babu kowa kamar koda yaushe, na wuce ɗaki na hau fiddo kaya na ana sanyawa a boot, na gama na kullu masu ɗaki daga nan na fito, ina fotowa ba taxi ba dalilinta sai motar Saraki, na ce ina mai taxi ɗin Yaya, ni nace ya tafi kayanki na cikin boot shigo na maidaki gidan kamar yarda na ɗaukoki, na buɗe gaba na shige bance komai ba, muka miƙe titi sosai, yace yanzu kina tunanin in Baba Sarki yaga bani na maidaki ba ranshi ba zai baci ba? Nag kana makaranta ne shiyasa na ɗauko taxi, ok jiran nawa ne ba zaki iya ba, ba haka bane amma kayi haƙuri, yayi shiru tare da sauke ajiyar zuciya.


Yana gama fakin a cikin gidan Baba Sarki na buÉ—e motar zan fita yace Rumanah, maganar jiya fa da nayi maki wasa nake, nace nima nasan wasa kake Yaya, dama yaya za'ayi kace kana so na, na buÉ—e na fito motar.


Ina shiga gida idona da Iyalle ya fara gani, da gudu na isa inda take na rungumeta ta baya, ta saki dariya Ć´an makaranta har an gama jarabawar? Na gama Iyalle, yanzu saura inyi maku allura idan baku lafiya, muka yi dariya gaba É—aya, Iyalle khalipha na gari kuwa?

Jiya dai naji yana faɗin yaje Rano, wai suna da wata shari'a zai yi bincike, na saki Iyalle ina faɗin Allah sarki khalipha na so ganin shi, ɗakin mu na shiga na riƙe wist ina bin ɗakin da kallo ganin yarda duk ya yi ƙura, dole na cire gyale na hau aikin gyara, na gyara shi fes tare da shirya kayana sannan na shiga wanka, na gama na sanya kaya na tayar da sallar la'asar dan har huɗu ta gota.


Ina juyowa bayan na idar sai ganin Saraki nayi zaune bakin gado yana kallo na, mamaki ne ya kamani sam banji motsin shigowa ba kafin kuma tsoro ya shigeni, na kama waige-waige dan ban taba ganin wani namijin gidan a cikin É—akin mu ba.


Na kallai na ce ina fatan Yaya Saraki Iyalle ba taga shigowarka ba? Murmushi ya yi ita na tambaya ma ke tace kina nan, wani abu ne dan na shigo? Kasan dai Baba Sarki ya hana, dan Allah ka fita kada ya shigo ya ganka.


Kwantar da hankalinki, Baba Sarki baya nan, kema kinsan in yana nan ba zan shigo ba, na gyara zama nace to meya kawoka? Ba abinda ya kawoni, na zo ganin lafiyarki ne ko nayi laifi? 

Na miƙe na koma wajen window ina kallon harabar lambu, dan Allah ka tashi ka tafi, kuma ce maka akai ban lafiya? Sai na jishi dab da ni, hucin numfashin shi yana sauka kan bayana, a razane na juyo zuciyata na bugawa, mi...miye haka Yaya dan Allah ka matsa, bana son irin haka fa, idanuwa ya kafa man baice komai ba, sai ma matsowa yake yana niyyar haɗani da jikinshi.


Wallahi Yaya zanyi maka ihu kana taba ni, kina man ihu zanyi maki abinda baki taba zato ba, kuma in kinyi ihun me kike zaton zai faru? Ke kaÉ—ai za'a tambaya kice ma Iyalle me? Kinsan dai ba zata taba yadda da abinda zaki ce ba, saboda kowa ya san halina na rashin son yin magana.


Toh naji matsa, me kake sonyi mani? Yaja baya yana ɗaga hannuwa sama, mefa zanyi maki, kina tunanin zan maki wani abu ne, ya kai ƙofa sai kuma ya juyo yana murmushi yace ki shirya anjima da Baba Sarki ya dawo zance mashi kince ni kike so, yayi ficewarshi ya barni tsaye, wai meke damun Saraki yanzu, da can ba yayi man waɗannan halayen, na tabe baki nima na fice inje inci abinci daga nan musha firarmu da Iyalle.


Firar Ć´an'uwana muke kafin nace Iyalle kina ganin Baba zai barni na ziyarci Ć´an'uwa ko wacce naje nai mata kwana biyu? Ban sani ba Ummu amma ki gwada tambayar kiji, na É—an marairaice, a'a ni dai ki fara mashi magana ki tambayar mani tukunna ni tsoro zai hanani, tayi dariya toh shikenan zan gwada mu gani Ummu, muka É—anyi shiru a zuciyata ina aiyana kamar in faÉ—i mata abinda Yaya Saraki ke mun sai kuma na fasa kada tayi mana wata fassara ta da ban.


Da daddare ina zaune falo ni kaɗai sai ga sallamar khalipha, na miƙe da sauri shima yana ganina ya taho da sauri, sai kawai naji ya rungumeni, na zame jikina ina murmushi ina mashi sannu da zuwa, yace kinsan ko yadda nayi kewarki? Khalipha na ashe tare muka yi kewar juna, ina magana amma daka kalle ni zaka gane jikina rawa yake.


Saboda rashin sabo da rungumar da yayi mani, gashi ƙamshin turaren shi irin na Saraki ne, muka zauna yace shikenan yanzu kin zama Doctor Rumanah? Kai ma gashi har kayi nisa da soma zuwa office, ka daiyi mana fatan Allah ya bamu sa'a ya shiga lamarin mu kawai, Iyalle ta shigo tana kallona tace kije inji Alhaji, na miƙe khalipha bari in dawo.


Na nufi falon Baba Sarki, har ƙasa na duƙa ina gaishe shi, yana yiman murnar kammala karatu na lafiya, zuwa can yace naji saƙonki wajen Iyalle, hakan yana da kyau raya zumunci, amma dai duk inda zaki wata ɗaya na baki kuma khalipha zai soma kaiki inda zaki fara zuwan, nace toh na gode Baba, ya zuba man ido har yasa gabana ya soma dakan uku-uku, yace zonan kusa dani Rumanah, na matsa inda yake, yana man wani kallo yace Saraki ya tabaki ko?


Ai nan take gabana ya bada wani dammm...kar kice man a'a dan gashi nan kina ƙamshin turarenshi, tabbas rungumar da khalipha ya yi man tana neman jawo bala'i, na daure na ce Baba bai tabani ba...kada kiyi man ƙarya Rumanah, babu yarda za'ayi ace tsawon shekaru bakwai kuna waje ɗaya bai taba kama hannunki ba, da ina da ina ya tabaki, nan take hawaye suka soma zubowa a idona, Baba bai tabani ba da...gaskiya ta faɗi Baba aka faɗi daga ƙofar shigowa.


Gaba ɗaya muka kalli ƙofar, Saraki ne tsaye a bakin ƙofar yana kallanmu, yawwa shigo kaima dan dama yanzu zansa Khalipha yayi man kiranka, Saraki ya shigo ya zauna yana kanne man ido, kome yake nufi oho! Baba Sarki yace wato ku biyun nan kune masu karya man doka ko? Saraki yace a'a Baba turare na, na bata kyauta da nata ya ƙare ya kalleni haka ne Rumanah? Na ɗaga kai da kyar.


Shikenan ku tashi kuje, ke kuma sai ki shirya jibi khalipha ya kai ki gidan wanda zaki fara zuwa, nace toh, na fita ina tunanin halin Baba Sarki na ƙure mutum, wannan ai shi ne tambayar yaya aka haifi uwarka.