Part 1
by @kwalisa
Fita ta 2
JARUMI DAN BAIWA
A shekarun baya da suka gaba akwai ranar da sarki mazwan ya tava fita ran gadi da kansa ya saka aka saka masa hemomi a bayan gari ya zauna yana shan iska fadawa suna fadanci.
Suna zaune sai ga wani matafiyi da matarsa suna tafiya cikin nutsuwa da kamala tana haye akan raqumi shi kuma yana qasa yana janye da ita.
Koda sarki mazwan ya gansu sai ya yi duba zuwa ga dakarunsa ya basu izinin maza su gabato masa da wannan matafiyin ai kuwa kafin ya kammala rufe bakinsa harma sun cika aikinsu sun qarasa gaban matafiyin suka dakatar da shi.
Ya xaga kai yana kallonsu xaya bayan xaya kamar ba zai yi musu magana ba zuwa can yace musu “Mene ina kan hanyahta ta tafiya za ku dakatar da ni” Dakaru suka kalli juna suka bushe da dariya.
“Mu ‘yan aike ne daga sarki mun zo amsar harajin hanya” mutumin mai suna sham ya kalli dakarun su duka cikin alamun jarumtaka yace musu.
“Ku koma ku faxawa sarki mazwan cewar ni sham ba zan biya haraji ba sai dai ya yi amfani da qarfin dakarunsa ya amsa” Jin wannan kalamin ya saka dakarun suka zare makamansu suka saka shi a tsakiya suna kewa ya shi.
“Ahir xinka xan saurayi giggiwa ba taka bace ba a faxar gaka a gaban mashahurin sarki daka biya haraji ka wuce daya fi maka tsayawa yin taurin kai” Wani qato yace masa lokacin guda yana tunkarar shi cikin alamun fushi na zuciya yana qarasawa ya kai masa sara da zumar raba kansa da jikinsa amma ga mamakinsa sai yaga ya yi zamiya cikin sauri yabar wajen saran ya wuce.
Ya zare takobinsa shima take ya yi wa wannan qaton tsargen kaxanya ya rabashi biyu ko wane sashe ya faxi qasa jini ya soma kwaranya qasa. Ganin irin wannan mummunan kisan daya yiwa wannan qaton sai ya fusata sauran dakarun suka yo xauki kansa su duka nan fa kasuwar yaqi ta soma ci cinikin rayuka ta soma wanzuwa.
Duk wajen da sham ya saka kai sai dai kaga kawuna suna tashi sama kamar tsintsaye jini yana famtsama a wajen kafin wani taqin lokaci ya yi wa dakarun sarki mazwan kaca-kaca, amman hakan bai tsorata su ba yana kashe su suna qara danowa haka ya riqa xauki babu daxi da su shi kuma sarki mazwan yana zaune a cikin hemomin da aka saka mishi yana kallon wannan jarumtaka da wannan sadaukin yake yi.
Ganin yanda yake masa varna jama’a kuma yasan idan ya barshi zuwa wasu daqiqai babu shakka zai masa varna dakaru hakan yasa ya juya ya kalli dakaren dake kusa da shi ya miqa masa hannu alamar ya bashi takobinsa cikin gagawa ya zare takobin ya miqa masa.
Ya tashi tsaye yana juyata a hankali a hannunsa lokaci guda kuma ya yi wata fitar burtu a guje ya yi xauki akan sadauki sham yana zuwa ya kai masa sara akaikaice sham baiga zuwan shi ba hakan ya saka kafin ya Ankara sarki mazwan ya yi masa wani wawan sara a hannu take wajen ya buxe jini ya soma gudana.
Saran sai daya saka sham ya yi baya can ya faxi qasa sarki mazwan ya dube shi cikin qasqanci yana ci gaba da juya wuqar da take hannunsa.
“Bana son xaukar makami a fagen fama don haka yana nufin rayuka da dama za su salwanta idan na fito da makamina” Sarki Mazwan ya qarasa magana, da qyar sham ya dafa ya tashi saboda saran ya galabaita shi.
“Ai tsoro shi yake sawa ‘yan maza suna bin cikin duhu, daka san kai jarumi ne sai ka bari muyi gaba da gaba da kai” Sarki mazwan ya shafa goshinsa.
“Kai yaro ne ai kuwa babu shakka yaro bai san wuta ba sai ya takata don haka kai yanzu ka zama ribatace sai wani ba kai ba” Ya yi nuni ga dakarunsa.
“Maza ku kamo shi cikin sarqa” Sham yanzu bashi da wani kuzari saboda saran da sarki mazwan ya yi masa irin saran da babu shiri ya so tirjewa amman bai samu ikon yin haka ba a haka dakarun qasar Hindu suka kama shi suka saka shi cikin sarqa.
Sarki mazwan ya koma cikin himarshi ya zauna yana kallon sham da aka kama, wasu suka kama raqumin aka kwantar da shi aka kamo macen dake kai aka gabatar da ita gaban sarki mazwan ya yi duba ga fuskarta ya ganta kyakkyawar mace ta gaban kwatance tunda yake bai tava ganin kyakkyawa kamarta ba.
“Ya sunanki?” Ya tambayeta.
Ta xaga kai cikin nuna tsana da qyamarsa tace “Mene amfanin sanin sunana bayan babu amfanin da zai yi maka” Sarki mazwan ya bushe da dariya ya ci gaba da kallonta can ya tashi daga kan karagarsa ya qarasa har zuwa wajen da take ya dubeta karo na biyu.
“Ya sunanki?” Ya qara tambayarta.
“Wahala da uquba ba zai saka ka ji sunan dab a zai maka wani amfani ba” Ya dubeta wannan karon babu fara’a akan fuskarsa.
“Idan kin qi faxa min ni sai na baki suna, daga yau sunan ki Hasma kuma na maida ke saxakata, shi kuma mijinki zan saka a xaure shi a gidan yari xaurin rai da rai kuma kullum sai an gana masa azaba” Sham ya xago kai cikin sauri jin abinda sarki mazwan ya faxa take idanunsa suka kaxa ya dubi matarsa yace mata.
“Kinga yanda Allah ya maida mu ki zama mai tawakali akan wannan qaddara da Allah ya jarrabemu da ita da ikon Allah waxan nan ba za su samu nasara akan mu ba” Itama hawaye ya soma gangarowa daga cikin idanunta tana kallon mijinta sham tace masa.
“Ai na yarda da ikon ubangiji musulunci kuma ina da yaqinin ba zai bari wannan Azzalumin ya samu nasara akan mu, kai ka san cewa sun kashe maciji ne basu sare kan ba” Sarki Mazwan ya bushe da dariya jin abinda ta faxa.
“Kina da matakin da za ki xauka kenan akan wannan abun dana yanke akan ku?” Ya qarasa magana yana mai xora hannunsa xaya akan xaya.
“Na yi imani da abin bautar mu, na kuma yi imani yanzu da za ku zagaye wannan duniyar zan biku har sai na kamo ku sannan zan daina farautar ku” Tayi murmushi tana kallonsa wannan karon cikin jarumta tayi magana.
“Ka yi sani babu makawa sai na kuvuta daga hannunka, ba zan dauwama a qarqashin maqasqanci kamar ka ba, koman daren daxewa sai na dawo”. Sarki mazwan ya bushe da dariya ya dubi dakarunsa yace.
“Kunji fa wai zata kuvuta daga hannuna, sai na ji maganar kamar tatsuniya” Dakarun suka bushe da dariya.
“Shi lokaci baya qarya, su kuma mashahuran jarumai ba a tava kama su a hannu su dauwama, don haka duk daren daxewa sai mun kawo qarshen zalluncinka” Sarki Mazwan ya dubeta da qananun idanunsa ya taka a hankali ya matsa zuwa wajen da take ya tsuguna ya kamo gashin kanta ya cizge sumarta yace mata.
“Ba irin mu ake yiwa barazana ba duk duniya babu daula mai girma da xaukaka kamar tawa, babu wani sarki daya kai ni qarfin iko da isa da kuma faxin qasa” Ya saukar da ajiyar zuciya yana kallon Dakaru.
Kafin ya gama kallon su Hasma tayi wuf ta zare takobin da take jikin kuben ta a jikin damtsen sarki mazwan ta yi wani ihu na nuna tsantsar jarumta ta ture shi ya faxi can gefe guda ta kai masa wani sara cikin gwaninta da zumar tsarge shi gida biyu amma cikin tsananin zafin nama ua janye jikinsa duk da haka sai sai data yanke masa rabin kunne jini ya zuba qasa.
Dakarun da suke wajen suka zare makamansu aka tsaya carko-carko ana kallon juna da su.
Sarki mazwan ya shafi wajen data sare shi ya ji rabin kunnensa ya fita, nan take ya saki wata qara ta fusatar rai da qunar zuciya ya dubi dakarunsa ya daka musu tsawa.
Kafin kace wani abu tuni sun yi xauki kanta tayi xauki itama kansu kaifin takobinta ya haxu da su walqiya da qara mai tsanani suka cika wajen, kasuwar yaqi ta dawo sabuwa.
Kafin kace wani abu tuni har ta qarar da dakarun da suke gabanta tayi wuf ta kaiwa sham xauki tana zuwa ta sare sarqoqin da suke jikinsa ta xora shi akan wani ingaraman doki lokaci guda tayi masa qaimi suka nausa cikin daji a guje kamar fitar kibiya daga kwari.
Ganin haka ya sa sarki mazwan ya dakawa dakarunsa tsawa da zumar su bi bayansu su kamo su, nan mahaya doki suka hau suka rufa musu baya amman sun makara domin tuni Hasma tayi nisa a cikin daji.
Haka suka yi ta yawon nemanta, amma basu samu ikon ganinta ba, suka koma cikin tsananin fargaba na tunanin abinda za su faxawa sarki mazwan saboda sun san halinsa na baqin zallunci.
A haka suka koma suka same shi yana tsaye a qofar shiga birnin Hindu fuskarsa tayi baqi kamar an sassaqo daga itace ransa ya yi matuqar vaci, tunda suke basu tava ganin fushi irin na yau a fuskar sarki mazwan ba. Hakan ya saka tun daga nan suka soma fargabar abinda zai faru.
‘Ina fatan kun saro min kawunansu sannan kuka dawo?” Suka yi shiru suna kallon juna ganin haka yasa ya zare takobi cikin fushi ya yi kansu da sara da suka sai daya ga babu ko guda xaya da yake numfashi a cikinsu sannan ya kwarara wani uban ihu da ilahirin birnin Hindu sai daya amsa.
Ya yi saurin komawa cikin birnin ransa a matuqar vace, yana shiga cikin gidan sarauta a lokacin Bokan shi ya bayyana a gare shi sarki mazwan ya tsaya yana kallonsa cikin tsananin vacin rai.
“Da wane bayani ka zo min?” Bokan ya dubeshi ya yi shiru yana nazarin fuskar sarki mazwan sannan yace masa.
“Babu dama na gyara maka wannan yankaken kunnen da aka yanke tunda saran da tsafaffiyar takobinka aka yi maka, ka kuma san duk abinda aka sara da ita yake kasancewa” Ya yi shiru yana nazarin fuskar sa sannan ya ci gaba da magana.
“Babu shakka ya zama dole ka saka sarkin yaqi da mayaqa su bi su a baya zuwa birnin nur yanzu suna daf da shiga cikin wani qauye da ake kira da Yaxama shi wannan qauyen yana qarqashin ikon sarki Nur kuma babu shakka idan suka qarasa birnin nur to sarki lambu na qasar nur zai mallaki tsafafiyar takobinka idan kuma ya mallaka zai iya cinka da yaqi ya rusa birnin nan.
Sanin kanka ne tun tsawon zamani akwai gagarumar gaba a tsakaninku da sarki lambu kuma babu abinda yake fargaba a game da kai sai wannan tsafafiyar takobin, idan har ya mallaketa to qasar Hindu tana cikin wani hali na qunci da tashin hankali kuma mulkinka yana gaf da zuwa qarshe” Wannan maganar da Boka ya faxa masa ba qaramin xaga masa hankali ta yi ba.
“Mene mafita?” Boka ya kalli yankaken kunnen sarki mazwan ya yi murmushi sannan yace masa.
“Rashin sani ya fi dare duhu, shi yasa suka yaqi wannan macen don lokacin ina cikin halwa ta tsafi kuma babu ikon na tashi amman dana hana ku yin wannan fafatarwa saboda tana da wani sirri da babu wanda yake da ikon cin nasara akanta idan ya yaqeta.
Ita kaxai da kake gani zata iya qarar da dakarun Birnin Hindu ta kuma rushe duka ganuwar garin. Wannan matar da kake ganinta Macen sirri ce, wani boka daya shahara a duniyar bokanci shi ne ya qirqireta, kana tsamanin mutum ce kamar mu? Amman ba haka bane” Wannan maganar ta boka ba qaramin xaure kan sarki mazwan ta yi ba.
“Kamar ya ya macen sirri?”
“Wannan macen da kake gani kamar yadda na soma faxa maka kuma ka ganta kyakkyawar gaske, matace ta wani mashahurin boka wanda ya hardace kalaman sirikan tsafi guda miliyan xari duk duniya babu boka kamarsa. Yana da mace guda xaya wacce duk duniya babu abinda yake so sama da ita, sun xauki tsawon lokaci suna soyayya, kwatsam sai aka wayi gari matar tashi ta kamu da ciwon ajali har ta mutu, ya wanzu tsawon lokaci yana kukan baqin ciki, haka ya wanzu tsawon lokaci ba ci ba sha saboda baqin ciki da begen matarsa kullum yana zaune a gefen kushewarta yana kallon kushewar cikin tsananin bege na soyayya da qaunarta.
Haka ya wanzu tsawon lokaka yana zaune a gefen kabarinta. bayan shekara uku yana cikin wannan halin na zama a gefen kushewar duk yabi ya lalace ya rame ya qanjame ya koma kamar ba mutum ba.
Mu kwana nan Zan kawo muku ci gaba.
Ga mai bukatar kammalalen labarin akwai shi a kasuwa.
Ko ka biyo mu a group din whatapp.
***