Part 2
by @kwalisa
Fita ta 3
JARUMI DAN BAIWA
ABDUL-AZIZ MADAKIN GINI
A rana daya cika shekara uku yana wannan zama sai ya tashi daha wajen kabarin nata a wannan lokacin sulasainin dare ya soma shiga kai tsaye ya shiga cikin xakin tsafinsa ya zauna akan buzun tsafi zuwa wani lokaci sannan ya tashi daga wajen da yake ya soma xauko wasu robobi masu kama da qirgi yana haxasu waje xaya.
Bayan sa’a shida sai gashi ya harhaxa gavai na xan adam ya ci gaba da haxa roba sashe zuwa sashe kafin wani lokaci ya haxa sura matarshi da wannan roba baya ya kammala ya zuba mata idanu yana kallonta, sak matarshi babu abinda ya rabasu kamar an tsaga kara sai dai wannan bata motsi.
Kuma ta rob ace aka haxata bata da jini taba da qashi, haka kuma shima yasan bashi da ikon busa mata rai ta tashi tayi motsi, a zaman daya yi a gefen kushewarta matarsa, yana cikin halwa ne na son gano yadda zai busawa wannan sunduqin rai amman har shekara ukun bai gano ba.
Abinda ya gano a cikin halwarsa duk abinda yake so ba zai samu ba, mafita xaya ce idan yana son ta motsa, sai dai ya samo wata budurwa macen aljanu ya sakata a cikin jikin robar mai sifar matarsa sai ta riqa motsawa.
Wannan abin daya gani shi yasa ya zauna yin halwa tsafi har sai daya nemo budurwa Aljana mafi kyawu a cikin yankin aljanu ya kamota ya sata a cikin butar tsafi ya xauki butar tsafin ya saka a jikin wannan gangar jikin roba. Da wannan ya tashi gangar jikin ya zama tana iya motsi tana iya tafiya tana iya magana.
Ganin wannan nasarar daya samu ya saka ya xauki sirrin tsafi dubu xari tara ya saka a cikin jikinta, ya kuma saka mata qarfin sadaukai dubu ya saka mata hikima da balaga ta magana, wannan ita ce irinta ta farko da wani boka a duniya ya qirqira kuma mafi hatsari a duniya.
Duk lokacin daya so ita kaxai yake turawa wani gari taje ta yaqi duk girman daular daya ga dama, haka kuma idan ta saka dakaru a gaba bata gajiya tana iya yin shekara guda tana yaqi bata gajiya ba, tunda ita bata ci bata sha bata da wani aiki sai yin biyayya ga boka, idan aka koma fanin tsafi idan tana faxar kalaman tsafi sai ka yi tsamanin duk duniya babu kamarta, hatta a wannan zamanin banda ni babu wanda ya kaita sanin sirrin bokanci, wannan fafatawar da kuka yi don na baiwa qasar nan kariya na tsafi shi yasa bata yaqe ku kuma tayi galaba akan ku ba, amman ba don haka babu shakka da kaga azaba irin wacce baka tava ganin irinta ba” Ya yi shiru yana kallonsa.
Sarki mazwan ya yi shiru yana kallonsa Boka marmasi ya saukar da ajiyar zuciya ya qara cewa da shi.
“Yanzu ya kake ganin za a yi yadda za mu qara mallakar takobinmu data karva kuma ka sanar da ni cewar kar na sake takai birnin Nur saboda sarki Lambo zai iya mallakar wannan takobin tawa” Boka marmasi ya bushe da wata dariya sannan ya dafa kafaxar sarki mazwan yace masa.
“Naga hankalinka ya tashi ka kwantar da hankalinka bisa wannan buqatar da ka zo min da ita, don haka zan aika saqo gareta bisa tafarkin tsafi kuma zan dawo maka da takobin taka domin na faranta maka rai” jin wannan kalamin ba qaramin faranta ransa ya yi ban an take fuskarsa ta washe zuwa ga murmushi.
Daga nan suka yi sallama Boka marmasi ya vace daga cikin gidan sarautar.
**
Lokacin da su macen sirri suka nausa suka shiga cikin daji tana kan ingaraman dokin data hau ganin tafiyar bata yi musu sauri sai ta tsayar da dokin ta xauki sham ta sava akan kafaxa ta ruga da gudu, kamar wacce take gudu akan iska kafin wani lokaci ta yi nisa da birnin Hindu.
Wannan karon kana ganin fuskarta kasan ranta a matuqar vace yake, saboda babu anuri ko farin ciki hakan ya faru ne saboda ganin irin raunin da sarki mazwan ya yi wa sham. Tasan sham sadauki ne wanda baya tsoro ko fargaba, amman sarki mazwan ya shamace shi ya kafta masa sara wanda tun sanda aka yi masa bai kuma motsawa ba.
Hakan yana nuni cewar akwai sirrin tsafi a tattare da takobin, don haka ta qara azama ta shiga cikin dajin a lokacin ta qarasa wani waje mai yawan rairayi da kuma ruwa mai kyau yana gudana a wata qorama gefe guda kuma ga wasu ‘ya ‘yan itatuwa jere reres gwanin ban sha’awa.
Tana qarasawa ta samu waje ta ajiye shi akan rairayi mai sanyi ta zauna tana kallonsa, har zuwa lokacin banda idanu babu abinda yake juyawa nan take tausayinsa ya kamata ta miqe ta komo kansa ta tsaya tana kallonsa da idanunta masu haske fari qal.
Zuwa wani lokaci ta soma karanto wasu xalasimai na tsafi kala-kala take abubuwa suka bayyana garai-garai gareta cikin gaggawa ta buxe idanunta daga rufewar data yi takai dubanta zuwa ga wajen da yake ga mamakinta babu shi sama ko qasa.
Ta juya ya kuma juyawa ya duba ko zata ga wata alama da zata nuna mata sawun wani abu amma sam babu wata alama, wane wannan ya aikata wannan zunibin gareta? Tabbas ko wane sai ta azabtar da shi da irin azaba irin ta yaqi, nan take ta taqarqare ta kumarma ihu wanda sai daya saka duwatsun da suke cikin dajin amsawa. Tsuntsaye da suke bakin ruwan suka bazama suka tashi sama, igiyar ruwa ta soma ambaliya kafin kace kwabo tuni launin wajen ya sauya saboda wannan ihun da macen sirri ta kurma.
Idanunta suka kaxa suka yi ja, saboda tsananin fusata da tayi kamanita suka sauya daga kyakkyawar mace zuwa wata kalar ta daban. Lokaci guda ta soma nazari akan abinda ya shafi babi na tsafinta kafin wani lokaci duk wani abu daya faru ya bayana a gareta. A gaba da wajen da yake nesa kaxan akwai wasu arnan daji da suka kasance suna bauta ga wani dodon gunki da suka sassaqa shi daga itace. Wannan abin bautar na su ya kasance suna yi masa hadaya duk qarshen wata da jinin baqon matafiyi wanda hanya ta biyo das hi, hakan ya saka suka kafa wajen wannan qorama a matsayin tarko da suke kama baqi.
Hakan ya saka suka sace sham suka nufi birin nasu na arnan daji domin yau kwana uku kenan ba su samu wanda za su yi hadaya da shi ba, wannan birnin ya kasance shi ne kusa da birnin Hindu kuma shekara da shekaru babu basa ga maciji da masarautar birnin Hindu, wannan gabar ya saka jama’ar birnin Hindu basa iya shiga cikin dajin yin farauta ko kuma yin itace domin gudun gamuwa da tarkon arnan daji.
Sarki mazwan yana sha’awar fita farauta amman saboda baqar gabar dake tsakaninsu hakan ya saka ya haqura, ya aika qashen da suke kusa da su aka sayo masa duk wani na’ika na dabobin daji ya zuba a cikin wani faffaxan waje daya kilace ya kuma qaramin kogi a gidansa yana kiwon kadoji.
Wannan birnin na arnan daji ya kasance yana da kyau da kuma tsari anyi gidajen daga duwatsu suna mulki a qarqashin sarkin su Jamhas wanda ya kasance gawurtacen jarumi mai juriya da kuma bajinta a fagen fama.
Matsala xaya take damun sarki jamhas shi ne rashin samun haihuwa, ya yi maganin ya kuma bi bokaye da ‘yan tsubu ya yi tsatsuba amman haihuwar bata samu ba hakan ya saka ya haqura ya saka sha’anin sarautarsa a gaba.
Haka suka ci gaba bauta ga wannan gunki suna yi masa hadaya da jinin duk wani baqo da suka kamo,kuma hasalin yiwa gunki hadaya ya samo asali ne daga gaqar gabar da suke yi da jama’ar Birnin Hindu wanda gunki ne yake basu sa’a a duk lokacin da suka tashi yin artabu da dakarun birnin Hindu.
Ana kawo sham gaban sarki jamhas ya tashi yana dubansa cikin nutsuwa ya xaga kai yana kallon dakarunsa yace musu.
‘Ya naganshi a cikin wannan halin na galabaita kuma ga ciwo a jikinsa? Anya kuwa abin bautar mu zai amshi wannan a matsayin hadayar da za mu yi masa?” Ya ci gaba da kallon sham sannan ya tashi yana zagaya shi.
“Wane irin ciwo ne ya samu wannan har ya kasance a kwance kamar matacce?” colom sauri ya shiga wani xakin da yake kusa da fadar wanda anan kayan tsatsubarsa yake. Ya xauko madubin sihiri ya soma bincike akansa nan yaga artabun da ya yi da jama’ar qasar Hindu da yanda suka shigo cikin dajin tare da macen sirri. Amman abinda ya bashi mamaki ya kuma xaure masa kai yadda madubinsa ya kasa nuna masa macen sirrin.
Ya yi iya yinsa domin ganin ya samu bayani akan macen sirri da kuma nemo daga wane jinsi ta fito ganin haka ya saka hankalin sarki jamhas ya tashi, cikin zafin nama ya ajiye madubin tsafin ya xauko kayan tsatsuba ya buxe kwatarniyar tsafi ya baza wuri ya soma duba bisa tafarkin tsafi.
A lokacin da yake wannan binciken game da wacce ce macen sirri ita kuma a lokacin ta shigo cikin birnin arnan daji cikin fushi da fusatar zuciya.