Jarumi Dan baiwa

Part 3

by @kwalisa

Fita ta 4

JARUMI DAN BAKWA

ABDUL-AZIZ MADAKIN GINI


***

Macen sirrin ta kai tsaye ta shiga cikin fada ai kuwa dakarun fada suna ganinta suka yo kanta cikin halin fushi suna daka mata tsawa.

“Ke yarinya wane ya baki izinin shigowa cikin garin nan babu shakka halaka ce ta kawo ki” Macen sirri ta xaga kai tana dubansa kafin tayi wani murmushi mai xauke da fushi tana kallon yadda suke kusanto kawunan su zuwa ga halaka tabbas yaro baisan wuta ba sai ya takata.

“Kana kallona kasan ban yi kama da yarinya ba, domin yarinta tana bayan mahaifiyarta ahir! Xinka da kuma gangancin kuma faxar wannan Kalmar, maza ku miqo min abokin tafiyata cikin ruwan sanyi idan ba haka ba fushina ya sauka akan ku” Nan wani ma gigiwa ya yo kanta cikin fusata musamman domin ganin mace ce bata da wani jarumtaka.

Rashin sani yafi dare duhu. Yana zuwa kusa da ita yakai hannu da zumar zungure mata hanci amman ga mamakinsa sai ya ji hannunsa ya soma laqwashewa yana komawa zuwa cikin hancinsa, nan yaga lamarin bana wasa bane, ya soma qoqarin hana faruwar hakan amman ya kasa take ya soma kwaranya ihu take jini ya soma fita daga cikin hancinsa ta sake ke shi ya faxi yana burgima a qasa.

Ganin wannan abin mamakin daya faru ya saka sauran dakarun suka sha jinin jikinsu, tabbas wanan macen tana taqama da sirrin tsafi idan kuma haka ne gidan shi ta zo, haka ya saka suka ja da baya wasu dakaru da aka horesu da tsafi suka dawo gaba nan suka soma tsatsuba sai kaga badakare ya zama zaki yayo kanta da gudu, kafin ya qaraso wajenta sai dai kaga ta kalle shi da ido sai kaga wata iska ta sure shi tayi watsi da shi can gefe guda.

Sai kaga wasu a cikinsu sun zama wuta kafin su zo wajen sai wani ruwa ya baiyana ya haxiye su. Ai ko da ganin sirrinta yafi na su sai suka yi xauki kanta da takobi a zare, masu kibiya suka soma yi mata ruwan kibiya amman abin mamaki duk kibiyar data je jikinta sai kaga ta narke ta zama ruwa ta zube a qasa.

Hakan bai hana su xauki kanta,ho abin kallo ya samu nan suka gauraya ta zare takobin sarki samzan data amsa nan fa kasuwar yaqi ta soma ci, mutuwa ta soma shawagi a tsakaninsu kawunan sadaukai na birnin arnan daji ya soma zuba a qasa kamar ana sassabe.

Babu abinda zaka gani sai gilmawar makamin macen sirri yana ratsa tsakanin mazaje yana fasa qirjinsu zuciya tana faxowa qasa jini yana zuba shaaa! Kamar gulbin ruwa. Kalar jan jinin dakarun birnin Arnan daji su kansu suka san cewar yau wata shaixaniya ta sauka a qasar su yau kam sun tsokano tsuliyar dodo.

Suna cikin wannan xauki ba daxi suka ji an kwatsama musu wata tsawa cikin sauri suka ja da baya suka tsaya carko-carko kamar zakaru suna kallon junansu a lokacin sarki jamhas ya fito daga cikin xakin tsatsubar shi cikin fushi ya dubi ginin fadar yaga yadda ya rine da jinin jama’arsa ya dubi qasa yaga yanda kawuna suka wadata a zube babu jikuna take ya tsorata da shu’umanci macen sirri babu shakka yanzu ya gamsu ita ce.

Ya yi saurin dakawa jama’arsa tsawa da cewar. ‘Maza ku zubar da makamanku kuma ku zube gabanta domin nemn afuwa akan zunubin da kuka aikata mata” Ai kuwa da jin wannan kalaman na sarki sai mamaki ya kama su suka zube a gaban macen sirri suna neman tuba.

Sarki jamhas ya qarasa gabanta ya kalleta cikin girmamawa yace mata.

‘Muna neman afuwa bisa laifin da muka aikata cikin rashin sani. Tun sanda naga abokin tafiyarki na shiga cikin xakin bokancina domin gano wane shi, a bincikena ne komai na ki ya bayyana a gare ni don haka muna neman afuwa a gareki bisa wannan lamarin da muka aikata miki” Jin kalaminsa ya saka macen sirri ta maida makaminta ba tare data ce komai ba ta nufi wajen da sham yake tana zuwa ta sunkuya ta xauke shi cak kamar ta xauki karmami ta nufi wajen da karagar sarki jamhas take ta kwantar da shi ta tsaya tana kallonsa har lokacin numfashinsa yana fita.

Sarki jamhas ya yo wajenta cikin sauri ya zo kanta yana kallon sham zuwa wani lokaci ya nisa yace mata.

“Takobin sarki mazwan ce tana xauke da wani dafi, kuma wannan dafin yana halaka mutum. Badon sham yana da nisan kwana ba da tuni ya halaka. Don haka mu jama’ar daji za mu karya wanna sirrin da yake jikin takobin” Take ya buxa gefen duga-diginsa ya xauko wata ‘yar buta ya xauko wani guntun xan itace ya karyo shi ya saka a baki ya taunashi ya soma marmasa masa a wajen daya ji ciwon.

Ai kuwa mintina goma da yin haka sai ciwon ya soma wata irin kumfa wajen yana tafasa kamar an saka abu a cikin wuta, kafin wani lokaci wajen ya gama zavalvala a hankali ya soma kamewa yana komawa kamar babu abinda ya faru a wajen a lokacin sham ya buxe idonsa suka haxa ido da macen sirri suka yi murmushi.

Ya miqe yana duban jama’ar Arnan daji sannan ya maida hankalinsa zuwa ga sarki jamhas. ‘Ina godiya bisa kuvutar da ni da ka yi, kuma ina yi maka jajen rashin jama’ar ka da ka yi wanda macen sirri ta yi maka, nasan idan za ku shekara kuna fafatawa ba zata tava saduda ba. Ita da kuke ganinta hata ni tsoron fushinta nake saboda bata san ayi haquri ba. Kune alqarya da kuka vata mata rai bata qarar da ku ba” Macen sirri ta yi murmushi jin abinda ya faxa ta dubi sarki jamhas tace masa.

“Kar ka damu nima zan saka maka da alheri kamar yadda ka taimake ni, zan baka maganin matsalarka ta rashin samun haihuwa, matarka zata haifa maka ‘ya mace wacce zata zama jaruma mai bajinta, kuma zan kawo wannan baqar gabar da take tsakaninka da sarki mazwan wanda hakan zai bunqasa tattalin arziqin ku” Tayi shiru tana duban cikin birnin arnan daji ta kuma kallon sarki jamhas wannan karon babu walwala akan fuskarta.

“Ina baqin cikin sanar da kai nan gaba za a haifi wani yaro da zai kawo qarshen wanan zaman lafiyan da zan samar a tsakaninka da sarki mazwan. Yaron zai zo birnin ku yana neman taimakon ka, saboda sarki mazwan yana son halaka yaron kai kuma ya zamar maka dole ka taimake shi ka kuvutar da shi, zan mallaka maka wasu dawakai guda biyu baqi da fari kuma zan yi wata tsatsuba a bayan gidanka tanan zaka fitar da yaron kuma dole ka haxasu da ‘yarka shi ka bashi farin doki ita kuma ka bata baqi ka aika da su zuwa birnin sin anan za a koya musu horo na yaqi” Ta xan saurara kaxan taci gaba.

“Ka sani yakai jamhas duk wanda bai taimaki wannan yaron ba babu shakka nan gaba zai kasance cikin qasqanci saboda jarumi ne xan baiwa. Yana da abin al’ajabi mai tarin yawa shi ne kuma zai kawo qarshen baqin zallunci sarki mazwan zai kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali, ka sani duk duniya babu wani wanda ya isa yin nasara akan sarki mazwan face wannan yaron, tabbas ya bayyana gare ni sai ya zo wannan birnin naku, kuma tsakanin kai da sarki qasar Nur xaya daga cikinku wani zai mallaki takobin sarki mazwan wacce ita ce sirrin mulkinsa.

Amman abinda sarki mazwan da bokansa basu sani ba wannan takobin ba komai bace a tarihin mulkinsa, wannan lamarin ya voyewa boka marmasi a cikin sha’anin bokancinsa kuma ba zai tava gano hakan ba sai lokacin da yaro xan baiwa ya bayyana, za su fahimci sun aikata kuskure wanda ba za su tava gyara shi ba kasan shi zallunci baya tava xorewa” Waxannan kalaman ba qaramin xaurewa sarki jamhas kai ya yi ba.

‘Mene abin yi yanzu?”

“Ka taimaka masa ka tura shi zuwa birnin sin” Cikin kaxu yace mata.

“Birnin sin fa kika ce birnin da zuwan sa yafi komai tashin hankali da hatsari na tsafafiyar birinya da kuma mashahuran ‘yan fashi ga bala’i kala-kala a hanyar zuwa qasar ta sin, haka idan mutum ya isa birnin bai tsira ba saboda acan cibiyar mashahuran bokaye ta duniya take kuma a can ake saye da sayarwa na tsafi akan hanya a ko ina zaka koyi sihiri na tsafi acan idan baka zama matsafi ba tabbas ba zaka iya zaman qasar ba” Jin wannan kalamin ya saka macen sirri ta yi murmushi har sai da haqoranta suka bayyana.

‘Wannan duk abinda kake gani lamari ne na sihiri domin a riqa wahalar da jama’a, wannan birinyar da take tsare fatake tana kashe su wani boka ne ya samar da ita domin ta adabi jama’ar da suke kai kawo a wannan dajin zuwa birnin sin. Anyi haka ne domin hana jama’ar da suke tureniyar zuwa birnin sin domin koyon tsatsuba da kuma kai bayi.

Nasan baka da sanin qasar shamawa ta kasance babbar daula data shahara wajen sayen bayi da kuma sayar da su zuwa ga manya dauloli wannan damar ya saka ta qula yarjejeniya da qasashe masu yawa” Sarki jamhas ya yi shiru yana kallon macen sirri a hankali yace mata.

‘Ina jinki kina bayani game da samuwar birinyar tsafi wacce ta adabi aljanu da mutanen da suke ilahirin dajin” Macen sirri tayi murmushi a hankali tace masa.

“Ku ‘yan adam kuna son jin labarai, bari ka ji labarin na su a taqaice, duk dana san tarihin ba zai zame maka mai amfani ba tunda nasan duk duniya babu mai halaka tsafafiyar birinya sai jarumi xan baiwa” Ta saurara tana kallonsa sannan ta ci gaba.