Chapter 9 chapter 9
🌈🌈 *SUDESS*🌈🌈
*Written story*
*By*
*AUTAR AREWA*.
*Paid Book ne akan farashi mai sauki 500 kacal za ki sha krt cikin kwanciyar hankali ta wnn Account Nomber 3125654602 Rukayya Idris first Bank, ki turo shaidar biya ta wnn Nomber ***,ko hoton katin MTN pls Banda VTU 🥰 Idan ba ki shirya ba kada mu ɓata time*.
*Ku krnt Book ɗina da na rubuta kamar haka 👉 DR MUHSEEN,ZAFIN KISHI,ZAMANINMU sai wnn da nake rubutawa SUDESS.Kada ku bari ayi babu ku masoyan AUTAR AREWA ku garzayo na dawo da sabo mai cike da nishaɗantarwa,harma da faɗakarwa 😂🤗 daga wannan sauran page 1 free ya kare,idan baki siya ba yanzu tau sai dai ki garzaya AREWA BOOKS ki siya duk Chapter 20🙅.Idan kin siya Book ɗin DR MUHSEEN 200 to zan baki sauran Books ɗina kyauta*. 👌
*Bismallahi Rahamir Rahim*.
*Free page* 9️⃣
*Second to the last page* 👌
📝............ Washe gari tunda safe around 9 Alish ta shirya cikin kananun kayanta riga ce teasheet mai karamin hannu sai wandon juens mai kamar fela daga kasa siririn mayafinta ta ɗora saman kanta da ya sha kitson attace.Hand bag ɗinta ta ɗauka tana kallan saman bed inda har yanzu Mus'ab yake kwance,cikin yanga ta dube shi ta ce "Dear ni zan wuce sai yaushe kenan?"Ba tare da ya bude eyes ɗin shi ba ya ce "Just je ki zamu yi magana,anjima zan turomaki kuɗi idan na ta shi.Da "Ok"ta amsa kafin ta fice daga gidan tana karairaya da takalminta mai tsini.Shiko Mus'ab kara juyawa ya yi ya koma bacci hankalin shi kwance saboda yasan yanzu ba zuwa wurin aiki hutu yake yi.
A gidan su SUDESS kuwa koda Ya Jabbar ya je sallar Asuba baiga SUDESS ba,haka ya yi ta faman dubawa amma sama ko kasa bai ganshi ba,hakan ya tabbatar mai da cewar bai zo masallaci ba, tambayar zuciyar shi ya fara yi "To meye ya hana shi zuwa sallah,gaskiya may be baya da lafiya,dan ba halin shi ne ba kin zuwa masallaci sai idan baya garin,ko ya je unguwa.Da wannan tunanin Ya Jabbar ya koma gidan shi, lokacin har karfe 7:30 ta yi.Shima kwanciya ya yi saboda yau Asabar ce ba aiki,zuwa anjima yasan zasu haɗu a part ɗin Momy.
Shi kuwa SUDESS cikin dare wani zazzafan Zazzaɓi ya saukomai,cikin bacci ya ji yana karkarwa dole tasa ya tashi ya ɗauko lemu marar sanyi a fredge tare da pracitmol ya sha,ACn ya kashe tare da rage gudun fankar ya koma ya kwanta yana rufe jikin shi da blanket.Ya daɗe bai koma bacci ba har kusan gaf da Asuba,saida zazzaɓin ya sauka kafin wani bacci mai nauyi ya ɗauke shi.Har aka idar da sallar Asuba yana bacci,sai can cikin mafarki ya ga ana Sallah kafin ya yi saurin tashi da salati ɗauke a bakin shi.Saida ya yi addu'ar ta shi daga bacci kafin ya yi mika yana ziro da kafar shi ta dama kasa.A hankali ya mike tsaye yana taɓa wuyan shi da hannu dan jin ko har yanzu da zazzaɓin,jin jikin shi sanyi kalau yasa ya sauke ajiyar zuciya yana godiya ga Allah.Agogon bangon ɗakin ya kallah ganin har kusan 6:30 ya yi saurin shiga toilet yana mai karanta addu'ar neman tsari.Alwala kawai ya ɗauro ya fito,abin sallah ya shimfiɗa kafin ya canza wata jallabiyar ya tayar da sallah.Cike da natsuwa yake gabatar da sallar harya idar.Anan ya zauna yana ta jero addu'o'i.saida ya kammala kafin ya fara rera karatun Kur'ani mai girma cikin suratun tauba.Ya jima yana yi kafin ya mike ya mayar da Alkur'anin saman drower ya haye saman bed da casbaha a hannun shi yana lazimi.
Sai Around 10 manyan samarin gidan suka hallara a falon na Momy domin yin break kasancewar week end ne.Koda mutum yana da aure to ranar week end zai zo su haɗu su ci abinci da Momy da Dady.Ya Jabbar ne a gefen karamar kujera sai Ya Aliyu da shine ke bin Ya Jabbar a shekaru,a gefe ɗaya kuma ya Nura ne yana amsa waya cikin sanyin murya.House girl ce ta fara gabatar masu da abin karyawa,ruwan zafi ne wanda ya ji kayan ya ji su citta da kanunfari sai kayan haɗin tea madara da Bonbita. kulas ɗin kuwa soyayyan Arish ne da wainar kwai,sai dafaffan naman rago da ke ta faman tashin kamshi.Haka yar matashiyar ta jere su tare da plat da spoorns,sai tishue data aje a gefe.Ba wanda ya taɓa saboda sun saba Momy ce take zubamasu,cikin yan dakika ta fara saukowa daga saman step ɗin ita da Dady cikin ado da cikar kamala irin ta manyan mutane,tunda suka taho ta hango zaratan yaran nata cikin cikar haifa,shima Dady faɗaɗa murmushin shi ya yi lokacin daya hango su,tunanin ya fara yi meya hana SUDESS fitowa,dukda daman ya saba duk week sai an jira shi.Daidai lokacin suka sauko cikin parlon.Da sauri su Ya Jabbar suka mike tsaye ganin shigowar iyayen nasu cikin farinciki suka tare su kowa na cewa "Momy da Dady ina kwanan ku?da fatan kuna lpy?".
Suma Momy da Dady a tare suka amsa masu suna dafa kansu tare da sakamasu albarka.Kafin kowa ya zauna saman carpet suna kara gaisawa.Momy a wani babban trea ta zuba Arish da waiyanar kafin ta haɗa masu tea mai kauri.Saida ta kallasu kafin ta ce "Wai ina Babana?ya aka yi bai fito ba?.
Caraf Ya Nura ya ce "Momy kinsan halin shi baya san zuwa in time". Yana rufe baƙin shi sai ga SUDESS ya turo kofar falon da sallama can kasan makoshi.Kallo ɗaya zaka yimai kasan yana cikin damuwa duba da yadda fuskar shi ta ɗan yi fayau,alamun ya ɗan yi rashin lpy.
Kusan a tare suka amsa sallamar.karasa shigowa ya yi ciki ya zauna kusa da Momy yana cewa "Momy Ina kwana?Dady ina kwana"cikin fara'a suka amsa suna dafa kanshi tare da sakamai albarka.
"Babana ka yi rashin lafiya ne".
Ya ji Dady ya jefomai tambayar a bazata.
In...Ina ya fara yi ya ce "eh...eh Dady na yi maleria ne,amma na ji sauki".
"To Allah ya sauwake "cewar Momy kafin suka fara cin abincin a tare gwanin sha'awa.
"Sorry Jemima sauko ki ci abincin kafin Dadyn yara ya dawo".
Cewar Hindatu tana aje plat ɗin abincin dake hannunta kasan gadon da Jemima take kwance.A hankali ta zuro siraran ƙafafuwan ta zauna saman carpet tana cewa "Tnx U Aunty".cikin sanyin jiki ta fara cin abincin bayan ta yi Bismalla.
Saida su Momy suka kammala cin abincin kafin ita da Dady suka koma saman kujera,su kuma su Ya Jabbar dukansu suna kasa.Kallan Jabbar ta yi ta ce "Kira min wayar Mus'ab a bani wayar ina so nayi magana da shi".da sauri ya zaro wayar shi ya fara kiran Nomber,harta katse bai ɗaga ba,haka ya kara kiran shi,sai ana biyu harta kusan tsinkewa ya ɗaga.Cikin magagin bacci ya ce "Hello ya Jabbar yi hakuri ganinan zuwa,na manta tai Saturday".
"Dole kake mantawa tunda rayuwar duniya ka saka a gaba,baka tunanin nan gaba ko Mus'ab?" Cewar Momy tana jin wani kololon baƙin ciki ya tokaremata makoshi.
Firgigit ya yi ya diro daga saman gado yana kara murza idon shi,dan shi harga Allah baiyi tunanin Momy ce ba,da bazai yi picking call ɗin ba.
Kasa ya yi da Muryar shi yana cewa "Afuwan Our Mom,ki bani 5 minutes ganinan zuwa yanzu insha Allah" bai jira cewarta ba ya katse wayar yana faɗawa toilet .Momy kallan Dady ta yi cikin ɓacin rai tana mai jinjina kanta.
"Ki kyale ni da shi,duk abinda yake aikatawa ina sane da shi,badai ɗabi'ar bin mata ya tarkata ba,to zan yi maganin shi,mun gama magana da Hasan akan rana ɗaya za'a ɗaura auren su da SUDESS tunda na fahimci so suke su saka duniya ta yiman dariya a matsayina na mahaifin su.To insha Allah komai ya zo karshe dukan su anyimasu matan aure,nexst week za'a gabatar da Meeting kamar yadda aka saba duk end of month,to a ranar kowa zai ji wacce zai aura,su kuma waɗancan fitsararrun su Zaheeda duk rawar da suke yi a Tiktok ina sane da su,zasu gane kuran su".Ya karasa maganar with compidens.Danda nan idon SUDESS ya kaɗa ya yi jajur kamar garwashin wuta.Da gaske shi za'a yima auren dole?.
*Wai ina labarin su Hibbah da Meema?yana cikin cigaban Wannan Book mai suna SUDESS*.
*Sauran page 1 na kammala free page.Dan haka idan baki biya ba to ki garzayo ki biya kuɗin ki dan jin ya rayuwar wannan mutane zata kasance, akwai turka-turka,da lauje cikin naɗi haɗi da wata zazzafar cakwakiya mai tafiya da rikita-rikitar soyayya 😂😂🤗.Manyan Hajiyoyi kada ku bari ayi babu ku, wannan karin alkalamin na AUTAR AREWA ya taɓo ɓangarori da yawa na zamanin da muke ciki, za ki ilimantu harma nishaɗantu duk a cikin Book ɗin SUDESS. ZAFIN KISHI (Sunan Book ɗina ) gareta akan yar'uwarta mace,ga ruɗin ZAMANINMU (Sunan Book ɗina)daya ruɗeta haɗi da SON ZUCIYA wanda nan gaba kaɗan zai iya sakawa ta yi NADAMA*.
*By*
*AUTAR AREWA*.
✍️✍️✍️✍️✍️.