2
by @mssxoxo
CENTRO MEDICO*
Cikin temakon gaggawa suka karasar da gadon da suke tura Hafez har cikin emergency unit. Gwaje gwaje suka fara yi masa. Hade da temakon karin ruwa, Da allurori. Yasa mu bacci sosai sai wajen tsakiyar dare ya farka. Yana farkawa yaci karo da mahaifin sa prof. Basheer a tsaye ya zuba masa idanu yana kallon sa shima.
“Ka tashi...?”
“Uhm..”
“Toh ya jikin?”
“Da sauki.”
“Ka tabbata?”
Gyad’a kai kawai yayi yana cije lebe. Prof basheer ya girgiza kansa yana sake kallon Hafez a karo na biyu.
“Ba kai mamakin zuwa na nan ba?”
Nan ma Hafez yai shiru yana jan leben sa.
“Hafez meyasa kake neman canza halinka ne? Giyaa Hafez? Kasan hukuncin me shan giya kuwa? Me yayi zafi da har zaka sha giya? Kamar ba musulmi ba, Sarai kasan haramcin ta, I’m highly disappointed.”
Shi kuwa Hafez a nasa bangaren gaba d’aya ya lula duniyar tunanin Dalaal. Bai san taba, Bai san sunan taba, Uwa uba kuma bai san musulmaa bace ko arniya? Ya Kasa tantance yanayin dayake ciki. Tamkar ya rushe da kuka. Gaba d’aya muryar Dalaal ce ta dazu ke masa kara-kaina a kunnuwan sa.
“Magana nake maka Hafez.”
“Papa.. Kayi hak’uri.”
“Ba ni zaka bawa ha’kuri ba Hafez. Kayi k’ok’ari ka sauya halin ka, Ka kuma nemi gafarar mahaliccin ka. Bara na biya kudin magungunan senazo mu tafi.”
Gyada kai kawai Hafez yai, Bakin sa dauke da addu’oin neman gafara. Ribbon din Dalaal ya ciro yasa ka a hancin sa yana shak’ar kamshin jikin sa,
“primer amor (first love)”
“Magana kake Hafez?”
Cewar prof. Basheer daya zo wajen a lokacin.
“No! Papa.”
“Okay muje ko.”
“Toh papa.”
Mikewa yai dakyar da temakon Prof. Basheer suka fita har wajen k’ofar asibitin.
“Papa na manta abuna bara na karba.”
“Bara na karbo.”
“No papa zan karba. Na mayi stretching k’afa na.”
“Ok!”
Tafiya yai yana sosa keya. Ya shige cikin asibitin yana dube duben inda zai hango ma’aikatan lapiar dazu dayaga suna magana da mystery girl dinsa. Can ya hango daya daga cikin su yana cike ciken wasu takardu. Cikin harshen Spanish ya shiga yi masa magana,
“Hola! Ni.. ni ne marar lapiar nan na dazu..”
“Eh na gane, Ya jikin naka?”
“Da sauk’i. Nagode.”
“Yayi kyau.”
“Dama... Dama akan matar nan ta dazu zan maka magana.”
“Wa kenan?”
“A beautiful lady.. who has light-colored curly hair, Data temakamun kafin kuzo.”
“Oh.. resident ce ai a wani asibiti.”
“Ina kenan..?”
“Bata gaya mana ba gaskia, Lokacin muna k’ok’arin baka temako, Tace dai sauri take kar ta rasa jirgi.”
“Damnit!!!”
Ya furta yana harhada hannuwan sa. Murmushi ya kakaro kawai yai masa sallama ya fita wajen papa suka tafi gida. Koda sukaje gida Haj Ziyadah har Hawaye seda tayi ta rungume Hafez tana tambayar sa,
“Meya faru son! Meyai zafi da har kake neman halaka kanka Eh?”
Langwabar da kai yayi kawai yana sauraron sautin hawayen ta ahankali. Cikin sanyin jiki dana murya ya shiga kwantar mata da hankali,
“Kiyi hakuri Maa! Bazan kara ba. I promise.”
“Ka tabbata...?”
“Sure Maa. Cross my heart.”
Murmushi dukkanin su sukayi, Ciki harda Papa dake kallon su cikin so da kauna,
“Brother!”
“My cute little twins.”
Bushra da Basma suka makalkale Hafez suna murna. Wasa ya dan tsaya sukayi sannan ya haye d’akin sa. Bayan dik yaran sunyi bacci. Parlor ya zama daga Haj Ziyadah se prof. Basheer.
“Dear har yanzu baka gano abunda yasa Hafez ya fara halayen nan ba?”
“A’ah Habibty! Shi dai ya nunamin babu komai, Amma zan sashi agaba muje asibiti. Ya kamata ya fara ganin therapist.”
“Hakan ya kamata gaskia. Domin abun da akwai daure kai, Be kamata ace da can baya beyi ba se yanzu da yake matakin phd. Dinsa, Allah yasa mu dace.”
“Akwai alamar tambaya gaskia, Allahumma Aamin.”
*SAINT LOUIS UNIVERSITY, MADRID CAMPUS HOSPITAL*
*DEPT. OF NEUROLOGY/PSYCHIATRY*
“Papa.. Lapia na k’alau fa! Meyasa zakai booking session na therapist? Wallahi kalau nake papa.”
Cewar Hafez. Tamkar zaiyi kuka don takaici, Ransa ya kara kololuwar takaici ganin ga masu matsalar kwakwalwa ma na neman guduwa ana cafko su, Shi kuwa lapiar sa lau amman an kawo shi wajen likita.
“Muje dai, Banason musu.”
Kansu tsaye suka shiga office din Dr. Fabio dake zaune akan kujerar sa yana daddanna na’urar computer gaban sa. Gaisawa su kayi sosai ya basu kujera suka zazzauna. Cikin yaren Spanish Prof ya cigaba da magana kan abinda ya kawo su.
“Dr. Fabio wannan shine yaro na da nake gaya maka, Sunan sa Hafez. Shima yana phd (Doctor of philosophy/ graduate of doctoral programme/ Matakin karatu na gaba da master. Wato degree na 3.) yana karantar ilimin computer. A saint Louis campus”
“Ohh that’s great! Nice to meet you Dr. Hafez”
Idan Hafez ya tanka Dr. Fabio kujerar da yake kai ta amsa. Ransa a matukar dagule yake. Kamar shi ace an kawo shi wajen likitan abunda yashafi tabin kwakwalwa? wato ga sabon hau-hau. meyai zafi da har za’a tattago shi a kawo shi wajen specialist?
“Hafez!!!”
Cewar papa yana tab’o kafad’ar sa. Dak’yar Hafez ya ka’karo murmushi ya mikawa Dr. Fabio hannu suka gaysa.
“Thank you Dr. Fabio.”
“Toh Hafez ni zan tafi.. Idan kun kammala session dinku na yau zasu dawo da kai gida”
“Gida kuma Papa?”
“Eh.. Menene?”
“Papa shikenan na dena driving? Papa lapia na kalau fa, Dan Allah kayi haku’ri ka kyaleni na tashi mu tafi.”
Girgiza kai Papa yai alamun a’ah! Ya dan bubbuga kafadarsa ta baya ya fice ya bar Hafez yana waigen sa. Bak’in ciki da takaici suka tattare suka tsaya masa a wuya.
“Hafez ko...?”
“Uhm..”
“Ok ka dawo nan kan kujerar zan fara maka tambayoyi.”
Mikewa Hafez yayi, yana kukkumbura fuska ya zauna a kujerar da Dr. Fabio ya bashi.
“Inaso ka gayamun cikakken sunan ka da shekarunka da tarihin ka a takaice”
“Sunana Hafez Basheer Ahmed, Shekaru na 28 a duniya.. Matakin karatu na kuma Papa ya gaya ma.”
Dr Fabio ya kad’a kai yana mai rubuta maganar da Hafez ya fad’a a takarda. Cikin yaren Spanish suke magana da Hafez. Dr. Fabio ya sake cewa,
“Ko zan iya sanin dalilin da yasa kake shaye shaye? Meye damuwar ka.?”
“Shaye shaye? Ni? Lalle bakaji dai dai ba.”
Dr. Fabio ya girgiza kansa yana dudduba takardun hannun sa,
“Eh! Kai.. Gashi Nagani kana smoking Hasheesh, Cigarette, Kuma yanzu ka fara shan giya. Meye damuwar ka ne?
“Oh shysa papa ya kawo ni nan? Kaga Dr Fabio. Bana smoking se ta kaini ma’kura, bantab’a shan giya ba sai jia, Kuma sau d’aya na kurba ban sake sanin inda kai na yake ba.”
“Toh meyasa ka sha?”
“Strictly Private.”
“Kana nufin kacemun ba zaka fad’a ba saboda Confidential (sirri) ne? Are you for real?”
“Ehh.. Bazan tab’a fa’da ba.”
Dr. Fabio ya jijjiga kai kawai, Can ya danna wani madanni dake gaban sa, wasu securities suka shigo suka saka Hafez agaba fitar dashi waje, suka shigar dashi mota, Har k’ofar gidan su suka kai shi sannan suka juya, Bai shiga gida ba ya wuce ya tafi wani wajen. Dr. Fabio kuwa drivers na fita da Hafez ya kira Prof. Basheer a waya,
“Kayi hak’uri zakaga nasa an dawo da Hafez gida. Bana tunanin zai fad’i musabbabin abunda yasa yasha giya yanzu, Mu Kara bashi dan lokaci kalilan.”
“Okay Dr. Fabio. Nagode sosai.”
Ran Prof. Basheer ya sosu sosai, Amman a dole ya hak’ura yabi maganar Dr. Fabio. Ya cigaba da yiwa Hafez addu’a har lokacin da zai fito ya furta koma menene.
*DALAAL*
Tana zama a kujerar jirgi taja doguwar ajiyar zuciya. Kanta ta shafa taji babu ribbon ajiki. Tunawa tai da kila awajen ceto matashin saurayin nan ta wullar, Siririn tsaki taja, Saboda tafison shi din da ta daure kanta dashi duk cikin ribbons dinta, 🥴 ta zura hannunta cikin aljihun wandon ta, Ta dakko wani ribbon din acikin fakitin sa, Ta daure gashin ta dashi. Agogo ta kalla kafin ta sake sauke nannauyar ajiyar zucia, Da alamun akwai abinda ke damun ta a k’asan zuciar ta.
“Le damos la bienvenida a AirMadrid. Por favor, abroche sus cinturones de seguridad. La duración total del vuelo desde Madrid, España a Lagos, Nigeria es de 5 horas y 15 minutos. Gracias por elegir AirMadrid, Fly safe, Fly AirMadrid (You are highly welcome to AirMadrid.. Please do fasten your seatbelts. The total flight duration from Madrid, Spain to Lagos, Nigeria is 5 hours, 15 minutes. Thank you for choosing AirMadrid, Fly safe, Fly AirMadrid..)”
Tana k’arasa sauraran maganar da ma’aikatan jirgin ke fada ta na’urar lasufika ta zura iPod earpiece a kunnenta, Tunani tashiga yi sosai na tarihin rayuwarta a k’asar spain, Yau gashi zata waiwayi gida, Batamasan ta ina zata fara ba, Kano ko lagos?
Kwantar da kanta tayi akan kujera tashiga lumshe idanu, Wani bacci ne ya fara fusgar ta, Ala dole ta rufe idanun ruf ta lula baccinta mai dauke da mafarkai kala kala.
*LAGOS—NIGERIA*
*Murtala Muhammed International Airport*
Tana fitowa daga ciki ta tsaya a waiting area tana duba sakonnin da suka shigo mata tun jia, Number da taga Uncle Sam (sameer) ya tura mata ta kira. Ashe mutumin na daga can gefe da alama shine wanda aka turo mata,
“Ranki ya dade.. Ni ne wanda oga ya turo” Ya fada yana mai nuni da kansa da kuma wayar sa dake ringing.
Gyada kai tayi ta yi gaba yana biye da ita abaya,
“Kawo akwatunan na rike, No hausa? Yes English?”
Daria ya bawa Dalaal jin abunda yake fada, Duk Kuwa da tayi shekaru da barin kasar nan hausar ta na nan, Tana jin komai, Wasu kalaman ne kawai ba zata iya fada ba ta mance saboda sauyawar harshe data samu.
“Yes english madam? Yes give the jakar kayan, Yes me, Yes take. Yes you, Yes you yes hear madam?”
Tsayawa tai tana kallon sa, Ya takarkare bil haqqi turanci yake, Gumi sai kwaranyo masa yake.
“A’ah!...”
Ta bashi amsa a takaice hade da wucewa gaba ta barshi a tsaye.
Sandarewa Gali yai a tsaye yana mamakin jin kalaman baturiyar data rera hausa ras. Da sauri ya bita a baya har yanacin tuntub’e.
“Motar na waje Madam. Sunana Gali.”
Sake gyada kai itade tayi, Ta cigaba da tafiyar ta tana mai jan akwatun ta. Glasses dinta ta zaro a ajakar dake rataye a kafadarta ta zura shi a fuskarta, Saboda yanayin yadda mutane ke bin ta da kallo. Har wajen motar suka karasa. Kalu driver ya fito da sauri ya karbi kayan ya zura a booth.
“Madam Oyinbo (sunan farare yan kasar waje da yaren yoruba) Welcome to Nigeria.. And this is lagos.”
“Gracias.. (Thanks/Nagode)”
Suna tafe akan titi, Gali da Kalu se zuba suke mata, Gali yai da hausa, Kalu yai da pidgin, Wani zancen tagane wani bata gane ba. Ita dai dariya ce kawai tata, Har suka karasa unguwar su Uncle Sam.
*MARYLAND*
*SAMEER SA’ED RES.***