Halin Dana Shiga...

18

by @shooly84

🤳🏻



💘 нalιn dana ѕнιga...💘



~Labarin gaske ne~



© ᴬYˢᴴᴬ ᴹᴬᶜᴴᴵᴷᴬ



*Arewabooks@shooly84*



*_Not edited_*



💘 *18* 💘






*Ƙasarmu Ta Gado Nigeria*


Mun iske gida lafiya kowa kuma lafiya, ƴan barka da zuwa mun iskesu tamƙam agida dan haka ne tun isarmu ban samu nakeɓe ni ɗaya ba, kai ko damar hutuwa bamu samu ba, mutane ne daga wannan ya fita wasu zasu shigo.


Mutanen Jalingo ko dama agidan muka tarardasu, har bayan sallar isha'i bamu natsa ba, ni dai alokacin ne na zame nai gidan Anti Lubah, da Imam na fara cin karo atsakar gida yana wasa abakin famfo, ya zama ɗan saurayi abinshi.


Farin cikin ganinshi ya lulluɓeni, na tafi da gudu nararumeshi na rungume aƙirjina ina faɗin nayi kewarka yaro na, jin magana yasa Anti Lubah fitowa daga kitchen ganina yasata cogewa abakin ƙofa cike da mamaki, da gaske kece Asiyah? 


Nayi dariya ni ɗince dai karkiyi mamaki, ta ƙaraso ta rungumeni muka hau murnar ganin juna, nayi farin cikin ganinki Asiyah, wannan daba farin sani nai maki ba ba zan ganeki ba, kinyi haske da fresh sai wani *glowing* fatarki keyi, amma fa kinban haushi da baki sanar dani zuwanki ba, nayi dariya nasan dama dole nai laifi amma ayimin haƙuri.


Nan muka dasa hirar yaushe gamo bamu muka rabu ba sai goman dare, tun agidan Anti Lubah nake neman layin Ibraheem na rasa harna dawo gida ina nema amma sam layin yaƙi samuwa, har zuwa yanzu misalin biyu da kwata na dare ƙoƙarin samun layin nake amma hakan yaci tura.


Gari ya wayemin cikin damuwa rashin jin Ibraheem, ko karyawa bamuyi ba na cimma Abdul asassansu cikin damuwa nace wai Abdul me Ibraheem ke cikine tun jiya nake neman layinshi na rasa..


ya juya kai yana faɗin nima fa rabon da muyi magana ankusa kwana tara kenan, yanzu ƙara jarabawa mu gani, ina ni da shi muka ƙara kira baya shiga dai, na koma cikin gida cike da damuwa.


Da rana Muhammad ya zo gaida Abbah, kwatsam ya ganni abin ya bashi mamaki ya koma farin cikin ganina, yini mukai hira sai wajen magriba mukai sallama na bashi tsarabar da nayo mishi.


Da nai sallah gidan Anti Lubah na wuce, acanma mun ɗau lokaci muna hira da tattaunawa game da rashin samun Ibraheem, sai da nai sallar isha kafin na wuce gida na tadda Abdul na jirana, ya tambaya kin sami layin nashi ne?


Har yanzu dai, yace to shikenan bari na fita yanzu zan binciko miki halin da yake ciki.


Har kusan sha biyu ina jiran dawowar Abdul, bai shigo ba na gaji na shige ɗaki nai zuru cikin damuwa, wajen ɗaya saura kiran Abdul ya shigo, na ɗaga wayar nace ya ake ciki Abdul?


Yace dana fita dai ban sami wanda zanji wani abu game da Ibraheem ɗin ba awajenshi, na dawo gida to amma yanzun nan Ibraheem ɗin ya kirani, ashe wai yana Niger mahaifin shi ne ya rasu shekaran jiya, to yana tambayata game da layinki na can wai yanata nema ya kasa samunki, to amma fa gaskiya bance mashi kinzo ba, danna tabbata inyaji kina gari zai iya cewa zai baro can yazo amma ke ya kika gani?


Allah sarki tuni tausayin shi ya gama cikamin zuciya, rashin uba ai babban rashine kuma abu mafi tayar da hankali arayuwar ɗan adam, rashin uba wani muhimmin ɓangarene a rayuwa, na tuna ni nawa uban rashin lafiya yayi, amma hankalinmu ya tashi bai kuma kwanta ba sai da muka ga ya sami lafiyar, to balle shi kuma ɗungurungun ya rasashi rashi irin wanda ba za'a ƙara ganin juna ba.


Allah sarki Allah ya jiƙan Abban Ibraheem kai mishi rahama kasa ita wannan mutuwa ta zamo hutu agareshi, nace Abdul hakan da kayi shine dai-dai dan gaskiya bai dace ba ace saboda ni ya baro wajan karɓar gaisuwar mahaifinshi ba ko, gaskiya ne wannan Asiyah Abdul yace haka..


Na kuma cewa amma fa nima ba zan kirashi ba, zan bari saina koma can inyaso sai nace mishi kaika sanar dani maganar rasuwar, eh hakan yayi dan gaskiya inya san kina garin nan babu abinda zai hanashi zuwa, nace sai ikon Allah yace haka ne.


***


Kwanana goma sha ɗaya a najeriya na tattara kayana na koma bakin karatuna, adaren dana koma na damu kiran Ibraheem, na ɗaga wayar ina cike da damuwa tare da tausayin shi, kamin nai magama ya rigani da cewa meke faruwa ne Asiyah na nemeki na rasa?


Na kwantar da murya nace kayi haƙuri Ibraheem wayar hannuna ce ta sami matsala sai yau na sami wata..uhm ya aje numfashi ya ɗora da cewa na wahala da yawa akan rashin sanin halin da kike ci...Ibraheem!


Na kira sunanshi atausashe ya amsa na'am Asiyah, ya ƙarin haƙurin rashin Abbah da mukayi? Yai shiru daga baya ya nida muryarshi tai sanyi yace haƙuri mun gode Allah Asiyah, tausayin shi ya sake kamani jin sanyin muryarshi lokaci ɗaya, nasan har zuwa yanzu ciwon mutuwar nan bai rabu dashi ba.


Ka ƙara haƙuri Ibraheem, na faɗa ahankali naci gaba mutuwa akwai ciwo musamman ma ace Ubane aka rasa, rashin shi yafi komai tayar da hankali, amma mafi a'ala agaremu shine haƙuri, juriya da dangana abinda akafi so kuma yawaita addu'a ga mamacin da nema mashi rangwame da samun sauƙin kwanciya amakwancin shi...


Dan haka Ibraheem amatsayin ka na babba azuri'ar daya bari saika kasanto jagaba wajan yawaita addu'a agareshi snanan kuma ka maye gurbin daya bari na nagartaccen uba awajan ƙannanka, ka kyautata masu kamar yanda yake musu lokacin rayuwarshi.


Na gode miki Asiyah, haƙiƙa kin ɗorani akan hanyar da banyi tunani ba, danme bakai tunanin hakan ba Ibraheem? Na gaya maki matsalata da ƴan uwana wanda gaba ɗaya nuna ƙabilancin ƴan Ubanci ne cikin rayuwarmu, nasan da hakan Ibraheem amma abinda nake so da kai kar kai duba da baya gaba ya kamata ka duba sai kuma ka nutsu kai nazari ka samo hanyar da zakabi dan ɗinke waccan ɓarakar dake tsakaninku.


Ka fahimceni? Na fahimceki Asiyah ma gode insha Allahu zan jarraba yanda kikace ɗin, duk abinda ake ciki zan rinƙa tuntuɓarki ina samun kyakkyawar shawara daga gareki haɗi da ƙaramin ƙarfin gwiwa.


_____________________


Sannu ahankali karatuna ya tasamma ƙarewa, gamu-gamu har mun fara nazari game da jarabar ƙarshe da zamu fara cikin satin, acikin wannan lokacin ne muka ba juna shawara na rage magana tsaninmu nida Ibraheem, yace ya kamata na tsaida hankalina waje guda dan damun nasara da sakamako mai kyau.


Shiya bani shawarar yawaita karatu a irin waɗannan lokutan wato tsakiyar dare da bayan sallar asuba, wai adai-dai lokutan karatu yafi daɗi da shiga kai, nako tattara hankalina gaba ɗaya na maida kan karatu, sai da nazo ni kaina bani da lokacin kaina, daga karatu sai bacci sai abinda ba'a rasa ba.


A ɓangaren su Abbah suma suna tare dani ta waya suna ƙara ƙarfafamin gwiwa kan na dage nayi abin kirki, dan Abbah daya zo ganina har alƙawari mai girma yaimin indai nayi abin kirki.


Kafin lokacin ya kasance duk ƙarshen wata Abbha ke zuwa ganina, da yake yanzu ya rage tafiye-tafiye aƙalla yana fin wata biyu agida bai leƙa wata ƙasar ba sai dai inya zo ganina ƙarshen wata, shima tare suke zuwa da Mami ko Hashim suyi sati zuwa kwana goma.



Tsayin sati hudu muna jarabawa, tazo mana da sauƙi dan nikam gareni na karantu shiyasa banga wuyarta ba, gashi an taimakemu ta hanyar bada tazara tsakanin paper da paper.


Ranar da muka ƙareta farin cikin tamkar an mana albishir da aljnana, danni har rasa inda zansa kaina nayi, mutum na farko dana fara samun saƙon tayani murnar kammalawa lafiya abin so nane da ƙaunata Ibraheem, haka su Mami da Abbah abun ba'a cewa komai daga kan Hashim zuwa Ruƙayya duk na amsa wayarsu, sai Muhammad da Anti Lubah.


Ranar nai bacci irin wanda na daɗe banyi irinshi ba, shawarar Ibraheem kenan, yace Siyah yau ramuwar bacci zakiyi ba doguwar hira dan haka takwas nake so ki kwanta zuwa lokacin sallar asuba ni zan tasheki kiyi sallah ki sake komawa ki matse.


Hakan ko nayi da nai sallar asuba na koma ban tashi ba sai da rana ta take, shi ɗinma wayar Abbah ce ta tasheni yana tambayata randa zan dawo, nace Abbah kasan akwai bikin da muka shirya na murnar kammala karatu da bamu kyaututtuka wanda ya zama dole na tsaya wajen bikin, kuma ai kunce zaku zo ko?


Yace eh shine nake son sanin takamaimai lokacin yin bikin, nan da kwana takwas ne Abbah, yace to zamu zo dai-dai lokacin inyaso sai mu tsaya muyi hutunmu na mako biyu daga baya mu dawo tare da ke ko, hakan yayi Abbah Allah ya kawoku lafiya, ya amsa da amin mukai sallama.

Na nemi layin Ibraheem yana ɗauka yace ba nace karki tashi ba har saina tasheki? Ba laifina bane Abbah ne ya tasheni, naci gaba da faɗin kasan mene? Saikin faɗa Siyah, Abbah ya canza tsarin dawowata, yanzu zan jirasu insun zo su gama hutunsu sai mu dawo gaba ɗaya.


Toh danme Asiyah ya faɗa cike da damuwa, ba laifina bane Abbah ya tsara hakan, yai shiru da alama dai ya shiga cikin damuwa ne, tausayin shi ya kamani danna san dole ya damu, dan mun riga mun tsara lokacin komawata nan da kwana goma, saboda shima dai-dai lokacin tafiya ce agabanshi zuwa *South Africa* ma'aikatarsu ta turasu wani taro, alissafin da mukai saura sati biyu tafiyar tashi wato inmun koma Nigeria da kwana uku zai wuce shiyasa muka shirya yanda haɗuwar tamu zata kasance, zai rigani isa kaduna ranar da zamu dawo kenan, inyaso yai kwana biyu tare damu saiya koma Lagos kashe gari su wuce.


To gashi kwaram Abbah ya rushe mana tsari, ba damar na musa ko nace ga nawa tsarin, dan haka dole ne mu shige damuwa musamman da tafiyar tashi zata ɗaukesu lokaci mai ɗan tsawo na wata huɗu ko biyar.


Ibraheem na kira sunan shi ina cike da damuwa ya amsa asanyaye, dajin yadda muryarshi ta sauya nasan yana cikin damuwa sosai, kayi haƙuri Ibraheem wallahi ni kaina banso hakan ba...ya aje numfashi damuwata ɗaya ce Asiyah sai da na gama cin buri akan son ganinki sannan haka ta ɓullo, to ya za'ayi yanzu kenan Ibraheem? Sai dai muyi sallama ta waya kenan ko?

Na ɗanyi murmushi irinna damuwa, na ce ka shiga damuwa da yawa ko?


To ya zanyi inma na shiga damuwar? Inhar ka matsu da son ganina zanma Abbah magana su zauna nina taho...a'a, a'a Asiyah ya faɗi da saurin baki, ya ɗora da cewa bance haka ba, yo yama saboda Allah kiƙi bin abinda mahaifinki yake so, amma ai kai bakaji daɗin yanda akayin ba ko?


Kada ki damu ni dai burina ako yaushe ki zamo maiji da bin Umurnin mahaifanki dan tawa mai sauƙi ne , duk damuwar tawa ta ɗan lokacine dole dai wataran zamu haɗu abinda fatanmu ako yaushe mu zamo ƙarƙashen inuwa ɗaya to maye abin damuwar, duka dai ba zamu kai shekara bamu haɗu ba.


Amma dai ba daɗi ko..karki damu ta fannina mubar ma wannan maganar yanzu uhm na aje numfashi haɗi da murmushi najin daɗi, kasan ko wane lokaci ƙara shiga raina kake Ibraheem, ko saboda me to? Sauƙin kanka mana, yayi dariya bai ce komai ba...


Abbah, Hashim da Abbas sai Ruƙayya da Rabi'a suka halacci wajan bikin murnar kammala karatunmu inda bikin ya ƙayatar matuka, ina cikin ɗabilan da aka ba kyaututtuka, anbani na ɗaliba mai hazaƙa daga cikin ɗaliban da suka fito daga arewacin Nigeria..


Kwanansu biyu da zuwa mukai sallama da Ibraheem tawaya washe garin ranar ya ɗage zuwa South Africa.


Mu kuma sai da muka ƙara wata ɗaya da ƴan kwanaki tare dasu Abbah sannan muka tarkato muka dawo Nigeria ni kam ina cike da murnar kammala karatu, abu ɗaya da inna tuna yake ɗan tayar da hankalina yanda nake ganin Abbah zai samin ido akan lallai na fito da miji cikin lokaci ƙarami, gashi adai-dai lokacin wanda zan gabatar mashi amatsayin mai son aure na baya tare dani.





Machika novel