Halin Dana Shiga...

31

by @shooly84

 ðŸ’˜ Ð½alιn dana ѕнιga...💘



~Labarin gaske ne~



© ᴬYˢᴴᴬ ᴹᴬᶜᴴᴵᴷᴬ



*Arewabooks@shooly84*



*_Not edited_*







🕳 *31* 🕳







Tunda Abbah yai zancen wata guda za'ayi bikina Mami ta soma shirinta na gyarana kamar yadda ko wace Uwa keyi idan bikin É—iyarta ya tashi, Tsimi nasha da kuma suran kayan da ke sha da madara zuwa su gumba sune aketa É—ura mani, wasu da daÉ—i wasu kau sai bauri ko É—aci.


Haka dai nake ta sha ba kama hannun yaro, duk da cewa ban nuna ko'a fuska ba cewa banji daÉ—in wannan aure ba, amma ta ciki na ciki ne, abunda yafi É—aga mun hankali inna tuna shine wai Labid na aura.


Yaro Æ™arami tsarana sannan gashi sam ba irin zubin mijin danake ma kaina mafarkin rayuwar aure dashi bane, ni wallahi ma kunya ce take kamani in ana faÉ—in mijin Asiyah kaza da kaza, ni agani na wannan bai kai matsayin miji agareni ba.


Ga yarinta ga baƙi kamar me, danta talaucinshi ba damuwata bace danni tuntuni kuɗi basu gabana, bana cikin mata masu kwaɗayin naira, bana so dan arziki haka ma bana ƙi danshi, barni dai da namiji fari kyakkyawa sannan ya bani tazara wajen haihuwa.


Dan haka gaba É—aya gidan babu wanda yasan inda na nufa, ba yabo fa fallasa haka naci gaba da wanzar da al'amurana, bana farin ciki kazalika bana cikin damuwa ga fuskata.


Shiyasa babu wanda zaice ga yanayinda nake ciki.


Ana saura sati biyu suka kawo lefe akwati saiti mai uku sai ɗan karaminsu, ba wasu kayan azo agani bane ciki, duk masu sauƙin kuɗi ne dai-dai ƙarfinsu kamar yadda yace man basu da komai sai rufin asirin Allah.


Saura kwana biyar bikin gida ya cika yai maƙil da ƴan'uwa da abokan arziki, mutanen Jalingo da kuma na nan cikin kaduna, su Anty Farida da su Ruƙayya da sauran matansu Hashim suketa sha'aninsu, ni dai zuwa wannan rana ba zaka ganeni ba saboda wani irin kyau da fresh da nayi na gyaran amare, ko ina jikina ƙamshi nake na haɗin Humrar maiduguri.



Abbah yaso yai mani wani saitin akwatin na lefe amma sai ya fasa dan karsu ga kamar an raina nasu, sai dai ya bada kuɗi Mami da kanta dasu Anty Farida suka shiga kasuwa suka sawo mani manyan turamen kaya kala ashirin na fita biki, dan lefenma dai ko ƙara buɗashi ba'ayi ba dan haka ba abinda aka taɓa aciki.


Hidima aketayi ba kama hannun yaro shiko ango Labid ban sake sanyashi a ido ba, ko a waya ban sake jinshi ba, hakan kuma bai dameni ba saboda nima bana nemanshi, ko'a bikin bani fatar yazo arinƙa nunashi ana faɗin shi ne mijina, shiyasa ma na ce *KAMU* kawai zanyi shikenan kowa ya watse.


Ranar Juma'a da yamma akayi Kamun wanda nayi kyau harna gaji cikin pink nd ash kala na leshi sai takalmi da jakka suma ash, naci kwalliya harta canza mun kammanni amma ba ƙaramin kyau nayi ba dama abu ga masu kyan...


Kaina ya ɗauki zafi ban fahimtar komai awajen sai tunanin gobe iwar haka ina Kano can naji ana faɗin zan zauna, tunanuka ne barkatai suke damun zuciyata, ahaka aka ƙare shagali ansha rawa an gaji nima dole na taka ana man liƙi dan haka na gaji ga yunwa na damuna tun kalacin safe banci komai ba.


Ana tashi na samu Ruƙayya nace ta nemo man abinci, ƙaramin falon Abbah na shige dan naci anatse, waina ta samo man da miya sai ruwan gora na baje ina turawa dan yunwa, ina gama ci na baje akan kujera wani wahalallen bacci ya kwasheni na gajiya.



Ina cikin bacci na, na wahalan gajiya naji muryar Abbah yana tashina, yace nako ji daÉ—i dana iskeki anan, daman yanzu na kira Maminku ta zo man dake nan muyi bankwana ko.


Tashi zaune nayi ina hamma lokacin da Mami ta shigo ganina nan ciki tace oh ashe ma tana nan, natsuwa nayi hankalina atashe gabansu Mami Abbah naman nasiha yadda Uban kwarai ya kamata ya yi, itama Mami tayi man tata suka barni da share hawaye ina jin kamar nayi tsuntsuwa na gudu kada aganni gobe.


Washe gari bayan sallar azahar aka kama hanyar kano cikin jerin motoci sunfi ashirin ƴan rakiyata, Ina lulluɓe cikin mayafi kalar atamfar jikina, kuka nake ahankali sai jan majina nake ina ayyana irin zaman da zamuyi da Labid, abinda ban sani ba ashe yana cikin ƴan ɗaukar marya bai yadda na ganshi bane kawai, saboda yana shakkar karna wulaƙantashi gaban abokanshi da ƴan uwa.


Ƙarfe biyar na yamma motocinmu suna cikin garin Kano, da unguwar da gidan dai bamu isa cikinsu ba sai shidda saura, kaina yana lulluɓe cikin ƙaton mayafina, wata gwaggona na daga Jalingo ta ɓarayin Abbah da Mami ne suke riƙe dani, dama dai tun a mota suke gaya man in zan shiga ko wace ƙofa ta gidan nawa na tabbatar nayi addu'a sannan na shigan.


Dan haka ban mance duk inda muka ga ƙofar shiga sai sun tsaya na karantu addu'o'i sannan mu wuce, daga baya dai aka shiga dani wani ɗaki aka aje bakin gado, nayi maza na ɗare tsakiyar gadon ina ƙara gyara rufata, ɗakin cike yake da mutane dangina da kuma dangin Labid.


Sai ba'a ake ma juna, nan aka ci aka sha daga abincin da suka kawo ma Æ´an saukan amarya, zuwa bayan isha'i dangin Labid suka watse sai nawa kuma aka fara kwasarsu zuwa inda za'a samar masu masauki, domin Abbah yaba Hashim umurnin asama ma mutane wajen kwana zuwa gobe in anyi buÉ—an kai kowa ya watse.


Gida yai tsit sai su Anty Farida da matansu Hashim sai, dani da Anty Farida da Rabi'a zamu kwana É—akin, na miÆ™e Rabi'a na cewa zaki ci wani abu ne ayi mashi magana dan gashi can waje da abokanshi yace na tambaya in ba abinda ake so, nace mata saiki gaya mashi abinda kuke buÆ™ata na shige kewaye domin rage marata nayo alwalla na gabatar d sallolin dake kaina.


Ina idarwa na samu Ruƙayya ta aje man nawa kason cikin naman da suka sawo masu, sai lemon *Pepsi* mai sanyi, banyi wasa ba na cinye tas, Anty Farida ta shigo wajen sha biyu na dare tana faɗin ke Asiyah zo muje muga gidan naga ba laifi.


Gida ne babba dan ɗakuna uku ne da babban falo, sai kuma kitchen, ɗaki ɗaya yana ta cikin falo haɗe da kewayenshi, sai tsakar gida shafe da sumunti da ɗakuna biyu a gurin ko wanne da bayinshi, sai kitchen can gefe guda, Abbah kam ya yi ƙoƙari dan duka ɗakunan uku sai da aka sanya masu gadaje, falo kuma yasha manyan kujeru da kayan kallo, kitchen ma yasha kayan na'ora na girki masha Allah gida dai ya fito yai kyau.


Ranar lahadi dan wulaƙanci suna yin kalaci kowa ya hau shiri, kafin sha ɗaya an gama gyara min gida tas sai ƙamshin turaren wuta yake yana kyallin sabunta, Anty Farida matan su Hashim, Ruƙayya da Rabi'atu sune ƙarshen tafiya bayan sunyi sallar azahar, haka muka rabu inata kuka suna ban haƙuri da alƙawarin zasu zo nan da kwana biyu.


Sai gani ni ɗaya kwal agida kamar mayya, haka kuma na wuni sai can gab da magari naji motsin shigowa gidan, ina zaune afalo nai tsuru duk da cewa akwai wutan lantarki amma ba abun kallo, zaune kawai nake shiru sai facebook dana hau ina ƴan dube-dube, jin an murɗa ƙofar akaji kulle naji ana sallama, na amsa ahankali na tashi naje nace waye?


Daga wajen yace nine Labid buÉ—e mana, wata ajiyar zuciya na sauke sannan na murÉ—a key na bude....


Ban tsaya ganin yana yinshi ba, ina murɗa key kawai na kauce na koma cikin falon ina ƙara haɗe fuskata, ya ida shigowa ciki sosai na kalleshi ta ƙasan ido, yana sanye cikin manyan kaya shadda brown an mata ɗinkin zamani, duk da kayan sunyi mashi kyau amma sai baƙar fatarshi ta rage ma kwalliyar armashi, na ɗanja ƙaramin tsaki ina ayyana dan Allah jibi wannan yaron wai shi ne mijina, kamata Asiyah na ƙare da auren wannan tatsitsin yaron, kome zai tsinana mani oho, shi wannan ina ya balaga balle harya gamsar da mace.


Kyau ace ƴar shekara sha takwas ya aura bani ba mai talatin, ina cikin nazarin zucci na ganshi tsaye akaina, na ɗago muka haɗa ido ya sakar man murmushi, ni kuma na haɗe fuska, yace amarya na barki ke kaɗai ko? Sorry yanzu ma fita zanyi masallaci daga can naje samo kazar amarci, kina buƙatar wani abu ne na taho maki dashi?


Bansan lokacin dana banka mashi harara ba na miƙe na fita falo na wuce tsakar gida na shige ɗakin dana zaɓar ma kaina, ina shiga kewaye na faɗa nayo alwalla dan naji kiran sallar magariba, ina shirin sanya hijab naji muryarshi daga baƙin ƙofa yana faɗin zoki rufe ƙofar falon kafin na dawo, nabi bayanshi na rufo na zo na tada sallah.


Har na sallaci isha'i bai dawo ba dan haka na kulle É—akin nashiga wanka, ban daÉ—e ba na fito dan aÉ—an tsoro ce na rashin sabo nake, riga da wando na sanya na bacci sannan nabi da hijab na koma falo, ko zaman minti biyar banyi ba naji sallamarshi, dan haka na buÉ—e mai ya shigo da babban leda fara ahannunshi ya aje tsakiyar falon, ya shige É—akin dake cikin falon...