33
by @shooly84
💘 нalιn dana ѕнιga...💘
~Labarin gaske ne~
© ᴬYˢᴴᴬ ᴹᴬᶜᴴᴵᴷᴬ
*Arewabooks@shooly84*
*_Not edited_*
*33*
Kwananmu biyar da aure zuwa wannan lokacin na gane kuskurena na kiranshi Yaro ƙarami domin kuwa takowane fanni ya nuna mani yaron ne amma da aƙidar manya, naji jiki har wata ƴar rama na soma yi ta fargaba.
Shirya kayana nake cikin ɗan madai-daicin akwati na lefena, na gama sanya duk wani abu dana san zan buƙata na rufe na saukeshi ƙasa, daga nan wanka na faɗa na fito na shirya cikin riga da zani na wata Holland yellow da ratsin kore ajiki, na ɗauko babban gyale shima kore da takalmi na aje gefe , na zauna bakin gado ina jiran Labid ya dawo daga gidan yayanshi ɗauko mota, domin wai ƙauye zamu wajen mahaifiyarshi naga danginshi suma su ganni.
Babu wani ɓacin rai a tare dani dan zani ƙauye danni tun asalina rayuwar mutanen ƙauye tana birgeni domin akwaisu da zumunci da kuma kara, zaman minti ashirin nayi sai gashi ya shigo yana faɗin na taso mu wuje kafin rana ta ƙarayi, ya ɗaukar mani akwatina ya fice zuwa mota, sai da na tabbatar da na kulle ko ina sannan na fita muka wuce.
Ana kiran sallar magriba muka shiga cikin garin, inata ware ido naga ƙauyen ƙayau sai naga ashe babban ƙauye ne domin local gov't guda ne, ƙauye ne babba da tarin jama'a acikinshi, na gyara zama ina kallon garin har muka iso wani layi mai jar ƙasa ya shiga akan gida na biyu naga yayi fakin motar.
Gida ne ginin sumunti da fenti ruwan madara, akwai ƙatuwar baranda daga wajen gidan shafe da sumunti sai ƙaramar ƙofar da zata sadaka da zauren gidan sannan ka shige babban tsakar gida da tarin ƙofofin ɗakuna irin tsarin ginin karkara dai.
Hayaniya ce tako ina cikin gidan ta yara da manya, aka hau yi mana barka da zuwa har falon mahaifiyar tashi, falon yasha saitin kujeru masu ruwan ƙasa sai tails ƙasan falon an malala kafet samanshi, sai kuma tv ƙarama da madubin gado afalon, babu laifi arayuwa irinta karkara yayi kyau.
Kafin ƙanƙanin lokacin anyi dafifi cikin falon ana zuwa kallon amaryar Labid, duk wanda ya kallan muka gaisa saiya riƙe baki yana faɗin masha Allah, Labid wannan bafullatanan mata taka haka kyakkyawa ina ka samota?
Ins jin sanda yake maida ma wasu amsar toh kada dai kusa kanta ya yi ƙato tayi tunanin kyawon nata ya shahara ne, wata daga cikinsu tace kai ja can shiyasa ashe ka kwanta ciwo kamar zaka mutu ka gano kyakkyawar mace duk ka ruɗe mana ciwon zuciya zai kamaka, ya yi dariya yana faɗin to ku tona mun asiri kuja ta rainani, ayadda suke taƙalar juna na fahimci abokan wasanshi ne.
Sai can bayan isha'i mutane suka tsagaita sannan ne muka samu gaisawa da mahaifiyar tashi, kallo guda naima mahaifiyar tashi na gane inda ya samo baƙi da siranta, sai dai ga fuska ko alama basu kamanni danya fita kyau nesa ba kusa ba.
Duka ni da ita kunyar juna muke ji, dan tun gaisuwa babu maganar data sake haÉ—amu, sai dai ina kallonta tana satar kallona , ko mamaki take ya akai na auri É—anta oho.
Ya shigo falon da sallama ya zauna kusa da mahifiyar tashi suna ƙara gaisawa, sannan yace mata Mama bari mu ƙarasa can gidan Yaya sai gobe afara kaita taga dangi ko? Tace toh abinci fa ba zakuci bane, ya matso wajen wasu kululi guda biyu da aka aje mani tun ɗazu ya buɗe.
Tuwo ne na dawa baƙiƙƙirin dashi sai miyar kuka data sha manshanu, yayi saurin rufe kular yana faɗin nikam dai bana ci bansan Asiyah ba, Mama babu fura ne?
Tace akwai sai dai ba'a dama ba gashi babu nono, yace abashi haka nan, ta ɗauko mai na miƙa hannu na karɓi ledar lokacin da muka miƙe da shirin tafiya, muka yi masu sai da safe muka fice zuwa waje.
Munyi tafiya kaɗan ya tsaya bakin wani shago ya sai robobin yoghurt guda biyu ya matsa gefe wajen mai nama ya sai balangu sannan muka wuce, tun daga wajen gidan danaga ya tsayar da motar yana horn na gane inda zamu shiga ba ƙaramin gida bane, domin ƙaton get ne ruwan ganye, mai gadi ya janye get ɗin muka shiga ya maida ya rufe, nabi gidan da kallo ina mamakin tsaruwarshi daga wajema kenan, muka fito mai gadi na mana sannu da zuwa.
Labid yace Sule gafa amarya na kawo maku, Sulen ya washe baki yana sosa kai yace masha Allah ƙaramin Alhaji naga amarya ƴar gayu, mukayi murmushi muka gaisa, Labid yace an dai sawo man Gen ko?
Eh an sawo ai tun É—azun, yace to kunna mana kayi fonfin ruwa sai ka barshi zuwa sha biyu ka kashe, muna atsaye wajen har ya kunna haske ya bayyana sannan muka shiga cikin gidan.
Gida ya tsaru ko danko a Kano wannan gidan sai mai hali, wani É—akine guda mai haÉ—e da kewaye muka shiga yana faÉ—i mun Yaya ya bar mana wannan É—akin na sauke amarya, ya faÉ—i yana dariya, É—an murmushi nayi kawai bance komai ba.
Munyi wanka kowa ya shirya cikin shirin bacci, na dama mana fura muka sha da nama sannan muka kwanta a gado ya janyoni jikinshi yana sauke ajiyar zuciya tare da shafa man sumar kai ya soma magana ahankali.
Asiyah a halayenki dana sani na fahimci baki da wulaƙanci baki da ƙyama kuma, dan haka in roƙonki dan Allah duk inda zamuje kada ki nuna komai ko a fuska ne ki nuna sakewa da jin daɗi, kinsan shi mutumin karkara baya son anuna mai ana kyankyamin shi ko wani abu makamancin haka, daka sake wajenshi ka nuna mai duk ɗaya kuke shikenan, ba ina faɗin haka bane dan wani abu, a'a bana son bayan idanunmu a aibanta mani ke ne.
Cikin ɗan ɓacin rai na kallai na ce kana zaton zan iya wulaƙanta danginka ne ko nuna masu kyama, duk wanda baida kyauye aduniya ai bashi da asali, ni da Allah yayi rayuwata a birni aiba finsu nayi ba, ganin kamar raina ya ɓaci yasa yaɗan ƙara matseni ajikinshi yana faɗin na sani shiyasa nace maki bada wani abu na faɗi ba, amma kiyi haƙuri in maganata ta ɓata maki rai, nasan Asiyata zata ƙaunaci dangina kamar nata.
Zan sake magana ya rufe bakina da nashi daga magana tasha banban, washe gari sai sha biyu muka isa gidan mahaifiyarshi, an kawo mana ƙayan kari shayi ne da biredi kaɗan nasha aka haɗamu da ƙanwarshi dake aure anan garin tana yara biyu muka fara zaga dangi, duk da cewa ba wani nisa bane amma shida kanshi yake kaimu a mota mu shiga gaba ɗaya, haka muka dinga yi har wajen magriba sannan na dawo hannuna cike da kuɗi wanda na samu dan daga mai ɗari biyar mai ɗari biyu haka aka ɗinga bani.
Washe gari ma haka muka nausa wani ƙauye kusa da wannan shima munsha yawo sai can bayan la'asar muka dawo anciko mana buhu da yatsi su barkono, wake, dawa dasu masara hadda gero da kuma kuɗi.
Mun dawo cikin garin muka gidan wata mata inda ta bani kyautar ƙaramar atamfa, kwananmu uku agarin yace ma mahaifiyarshi gobe da safe zamu tafi, tace kai na zaci sati zakuyi mana, ya girgiza kai yana faɗin a'a gwanda muje tunda kowa ya ganta itama taga kowa, akwai abubuwa agabana, ni dai shiru nayi inajinsu dan nasan domin ni yake son mutafi, danya lura ba komai nake iyaci ba, tunda ba abunda ake dafa mana daga shinkafa da wake da mai sai kuma dare tiwon dawarnan da miyar kuka, nikam dukansu ba cimata bace gwanda ma tuwon naci sau ɗaya, kullum sai dai nasha fura ko kuma naci kwaɗon ganye zogala ko rama da kuli.
Washe gari wajen goman safe muka tattaro kayanmu daga can masaukinmu zuwa gidan mahaifiyarshi, muna nan har sha biyu sannan mukai haramar tafiya, inda Maman ta sanyani ɗaki ta bani kyautar dubu goma da wata atamfa naita godiya, muka fito falo ta haɗamu gaba ɗaya tai mana nasiha da kuma muyi haƙuri da juna.
Muka fito na shiga har ɗakin matar ƙanin Maman tashi nai mata sallama sannan muka tafi anata mana Allah ya kiyaye hanya, a cikin mota yake cewa ki sake shiryawa kwana biyu zamuyi muje Jigawa gidan Yaya suma ku gaisa ko, nace toh ina ƙirga kuɗin dana samu wajen dubu ashirin da wani abu, ga atamfa guda biyu, ya kallan ya maida kai ga titi yana murmushi, hajiya Asiyah kuɗi kikayi haka ne, me za'a bani ciki toh, harararshi nayi na maida kuɗina jakka ina faɗin ko sisi.
Yace haba dai nima ai dani akai wahalar yawon kuma naita tuƙaƙi kya bani ko dubu goma ce ko? Ya ida maganar yana dariya, banza nayi dashi na lumshe ido ban daɗe ba bacci ya ɗaukeni domin gajiyar yawo da kuma ta fitinar Labid dan bai barni nayi baccin kirki ba jiya.
***
Kamar yadda yace bayan kwana biyu muka sake shiryawa zuwa Jigawa, amma kaya kala uku na É—auka dan yace kwana biyu kawai zamuyi masu, sai da muka fara biyawa gidan Babban Yayanshi mai mata har huÉ—u cikin gida guda ko wacce da É—akinta.
Ya gaya masu Jigawa zamu muyi masu kwana biyu, mukayi sallama inda matan suka bani dubu biyar sai kuma saƙon mijin nasu da bamu iskeshi agida ba, dubu ashirin ya bayar abani, muna shiga mota ko jakkata ban sakasu ba na miƙa ma Labid ina cewa ya riƙe ahannunshi, ganin ya karɓa babu gaddama na fahimci yana buƙatarsu.
Sai can wajen ƙarfe uku muka isa Jigawa, matan Yayan biyu agidan sai dai ko wacce da flat ɗinta dan gidaje biyu ne acikin gidan, ɓangaren amarya muka sauka domin uwar gida zata amshi girki ranar, mun iska tarba mai kyau dan an haɗa mana abinci na ƴan gayu kayan ciye-ciye domin amaryan ƴan gidan Labid ce duk da cewa ƙaramar yarinya ce dan mun girmeta sosai amma tana da mutunci sosai.
Sai bayan mun huta Labid yace na tashi muje ɓangaren uwar gida mu gaisa, muka tai aka kawo mana ruwa da lemo muka zauna ana kallo da hira har magriba, sannan mukai mata sallama zuwa sashin amarya.
Sai wajen goman dare Labid yai shirin zuwa masauki dan kwanciya, ganin nai mai sallama daga nan falonta ya fice yasa amarya mai suna Jauharah ta kallan cikin mamaki tana faÉ—in ba dai iyakar sallamar da zaki mai kenan ba Asiyah?
Na ɗan kalleta na kawar da kai, ta riƙe baki oh wai kunya kike ji, lallai duk.da cewa kin girmeni ashekaru amma na rigaki aure kuma yayan mijinki nake aure kinga na zama Antinku kenan ta faɗa tana dariya, nima murmushi nayi bance komai ba, taci gaba da faɗin dan Allah bi mijinki kuyi sallamar kirki, kuna sabon aure ai yanzu ne ya kamata kiriƙeshi da kyau.
Miƙewa nayi tace nasan yana falon mai gidan inda kuka ci abinci, ina shiga kau na ganshi sai kallan ƙofa yake, yana ganina ya taho ya rungume yana sauke ajiyar zuciya, haba Asiyah da banyi ma Jauharah msg ba ta turo manke haka zaki ƙyaleni naje na kwanta?
Na turo mashi bakina agaba ina faɗin toh me zanyi maka ni, kai har gidan mutanenma baka iya haƙuri, haɗa bakina da nashi yayi ya hau tsotsa hannayenshi kan ƙirjina lokaci mai tsawo sannan ya sakeni yana faɗin ga abinda zaki man nan, da, da halima har ogan sai nayi kafin na tafi, kinsanni da rashin haƙurin kamar yadda kika ce, na sake turo mashi baki yaja hancina yana dariya nina tafi sai da safe, ki kuma shirya ina zuwa sai na sake tsotse maki baki na murje waɗannan albarkatun ƙirjin shine barka da safiyata tunda zaki barni na kwana da rungumar filo.
Ya fice yana mun dariya nima murmushi nayi na koma inda na fito, ganin ban ganta a falon ba yasa na shiga ɗakin da nai salloli sai na ganta ciki tana sanya kayan bacci, nima na buɗe akwati na ɗauko kayan bacci zan sanya tace a'a ga ruwan zama can yana jiranki a toilet, inkin fito zanyi maki wani haɗi na aje kan madubi saiki shanye, bansan mijinki ba amma ni mijinmu baida ɗagin ƙafa ranar girkina kullum saiya raya sunna, nayi murmushi araina ina faɗin duk kanwar ja ce ai.
Sai da muka kai ƙarfe biyun dare muna fira tun ban sake ba har dai na sake da ita, yawanci labarin dangin mazanmu take bani da nuna man na fahimci kowa saina san yadda zan zauna dasu, sai kuma labarin kishiyarta da irin zaman da suke yi.
Kwana biyu da mukai a Jigawa munyi mugun sabo da Jauharah, domin ita ɗin babu ruwanta mace ce mai sakin jiki da faran-faran, ga surutun tsiya duk yadda bana son magana saita sanyani, acikin kwana biyun nan nasha haɗe-haɗen kayan mata domin ita ɗin ƴar Sokoto ce zaman aure ya kawota Jigawa, na tsimu wanda har marata ta soma ciwo kaɗan-kaɗan, na kuma ƙaru ta fannin rayuwar aure , haka dai ranar da zamu tafi amarya ta bani turmin atamfa da turare ɗan sauɗi *Oud Alshams* na shiga ɓangaren uwar gida itama ta bani wani turare mai sauƙin kuɗi da dubu biyu, shi kuma mai gidan ya bata dubu ashirin ta bani, haka mukai masu sallama kamar karmu rabu.
A ranar kam na gaya ma aya zaƙinta domin Labid kasa haƙuri yayi dani yaita abu guda har asuba, yadda naci wuya yasa washe gari shiyayi aiyukan gidan tas, abincima sawo mana ya yi na rana da dare, ni kam na wuni bacci, da dare kuma bai hana ya sake nemana ba, aikau na rushe mashi da kuka ganin ya yi na farko yai na biyu yana shirin ƙarawa.
Ya rungumeni yana faɗin sorry kice Baby sai na rasa inda ni'imar nan taki take fitowa, sam bana gajiya dake in zan kwana ina abu ɗaya, yanzu dai ki ɗanyi haƙuri na ƙara kona minti goma ne kinji ahankali zanyi maki, na girgiza kai na ce ni dai ka ƙaleni gaskiya na gaji haka nan, ya rungumeni yana faɗin shikenan na haƙura ina samun aiki zan ƙara aure danna fahimci ba zaki iya da lalurata ba.
Ƙirjina yai wani irin bugawa jin abinda yace, na sake sautin kuka na ina faɗin kai tayi har sai ka gaji amma bana son maganar kishiya dan Allah, ya kyalkyale da dariya yi baccinki da safe nayi, yanzu kwanta abinki ki huta wasa nake, na harareshi yana share mun hawaye yana mani murmushi.
******
Watanmu guda da aure zamanmu gwanin sha'awa, bani da matsalar komai sai dai fitinar Labid wanda zuwa yanzu na soma sabawa da ita, a cikin wannan lokacin ne kuma ya samu aikin koyarwa a wata private school a kaduna sai dai primary ce dan haka tunda babu abinda yake a Kano ya saki gidan cikin kwana uku aka samu mai kamawa ya biya, agabana ya kira wani abokinshi ya nemo mashi gida ƙarami mai sauƙin kuɗi, washe gari yace ansamu dan haka ya tura mashi kuɗin ƴan gyare-gyare da fenti.
Bayan kwana biyu mukayi ma ƴan uwa da makwabta sallama muka miƙa kaɗuna tare da motan kayanmu, a Malali aka samu gidan irin gidan nan mai flat da yawa ko wanne ɗaki biyu da falo sai kewaye a falon sai kuma kitchen, kayana sunma gidan yawa dan haka aka tafi da gado ɗaya da kuma wasu kayan kitchen zuwa gidanmu aka aje, nima sai da nai kwana huɗu agidanmu wajensu Mami sannan na koma can gidana.