Halin Dana Shiga...

35 final chapter

by @shooly84

 ðŸ’˜ Ð½alιn dana ѕнιga...💘



~Labarin gaske ne~



© ᴬYˢᴴᴬ ᴹᴬᶜᴴᴵᴷᴬ



*Arewabooks@shooly84*



*_Not edited_*




*35* 


*{Final chapter}*





Wani irin *Dum*! naji arayuwata kalmar ya sakeni tana ci gaba da yawo cikin kunnuwa na, azabure na miƙe nabi bayanshi zuwa ɗakinshi, tsaye na iskeshi bakin madubi, cikin kiɗima na rungumeshi kafin wani irin kuka ya ɓalle mani, kayi haƙuri Labid ban sake fita bada izninka ba, ina sonka ina ƙunarka bazan iya rayuwa mai daɗi ba babu kai, ka rufa mani asiri dan girman Allah ka janye wannan sakin tun kafin kowa yaji, ya ɓanbaroni yana girgiza mani kai, Asiyah zamanmu ya ƙare ban sake ki ba sai da na gaya ma mahaifiyata komai ita ta bani wannan umurnin..


Jin abinda yace yasa na sakeshi jikina asanyaye, na kalli cikin idonshi nace Mama da kanta tace ka sake ni? Ya ɗaga mun kai ahankali, na hau girgiza kai hawaye na kuma wanke fuskata no ban yarda ba Labid, me na taɓa yi mata da zatasa ka yanke man wannan mummunan hukuncin, kaima kana son rabuwa dani ne.


Dama ka aureni saboda sha'awa, Labid ba sona kake ba tun fil'azal sha'awa ce kake, tunda ka gama jin binda zaka ji shi ne zaka maida bazawara aure ko shekara baiyi ba.


Nasa hannu na fincikoshi ina sake fashewa da kuka, hannunshi na kamo na ɗora bisa cikina, ba wai dan inada haƙiƙanin tabbatarwa ba zan dai faɗi ne ko zaiji tausayina ya janye, kan marata na ɗora hannunshi ina faɗin dan darajar gudan jininka dake maƙale da marata ka janje batun saki...


Labid ina da shigar ciki na sati biyu atare dani, ya ɗauke hannunshi yana juyawa cikin wani irin tashin hankali yace, kiyi haƙuri Asiyah ki ɗauki wannan ƙaddarar, aure ne ya ƙare tsakaninmu, ko da saki ɗaya ne babu komawa, Asiyah bana fatan sake zaman aure dake, kin fita azuciyata fit bana jin sonki kwata-kwata.


Na share hawaye ina murmushin takaici, Labid ba zaka dubi wace irin rayuwa abinda zan haifa zaiyi ba? Baka tausayin gudan jininka ya taso ba'a gaban iyayenshi duka biyu ba? Shin Labid wane irin mummunan huƙunci ne haka?


Yanzu yaya kake so nayi da cikin jikina? Asiyah bansani ba, inba zaki iya ba ki zubar, nai saurin ja da baya ina mashi wani irin kallo hawaye na sake ɓalle mun, fita ɗakin nayi kawai na koma nawa na zauna bakin gado ina wani irin kuka na tausayin kaina, gani nake duk abinda ke faruwa mafarki nake zan farka zuwa anjima.


Ta yaya ma zan amince da cewa wai Labid ya sakeni daga ƴar ƙaramar magana, shin haka dama aure yake ko kuwa nawa ne ya zo ahaka?


***


Ban yadda cewa lallai na rabuda Labid ba sai da naga bayan kwana biyu ya aiko mani da tarkacen kayana na aure kaf zuwa gidanmu, wanda tunda nazo nake kuka mutanen gidan na lallashina, wannan saki ya ɓatawa iyayena rai matukar gaske, babu kalar zagin da Labid baisha ba wajen mutanen gidan inka ɗauke Mami, ita kam sai cewa take ƙaddara ce kawai.


Ban yadda cewa ina da cikin da nai ƙaryarshi sai bayan sati huɗu da rabuwar mu laulayi ya tasoni agaba, bana iyacin komai koda ruwa na sai amai, zazzaɓi da komai ma damuna yake, cikin wata biyu sai gani nayi wata irin muguwar rama ta damuwa da yawan kuka da kuma laulayi.


Tunda muka rabu ban sake jin ɗuriyar Labid ba, ni kam inka ganni baka taɓa cewa Asiyah ƴar kwalisa bace, duk na rame na fita hayyacina, wuni nake kuka inkwana kan sallaya ina roƙon Allah ya dawo mun da Labid, dan bansan ina mashi wani mahaukacin so ba sai yanzu daya sakeni.


Ji nake kamar zan mutu na bar duniyar saboda baƙin ciki, Mami tun tana lallashina harta koma ta sanya mani ido kawai, Bashir ne rannan daya shigo yaga yadda na koma kamar wata majinyaciya ya hauni da faɗa yana sake jaddada man dama na haƙura na cire Labid araina domin ba sona yake ba, ba kuma zai taɓa maidani ba.


Mami tace ni na rasa wannan irin abun Asiyah, taƙi sanyama ranta salama ga laulayi tana fama dashi dan fa ba abinda take ci ya zauna mata, sai kuma ya sauko ya koma lallashina yana shafar kaina.


Asiyah kiyi haƙuri munsan kina cikin damuwa da tashin hankali, amma dan Allah ki rangwanta ma kanki saboda mu ƴan uwanki mu samu sukuni, baki tunanin damuwar da kike ciki zai shafi abinda ke cikinki?


Kiyi haƙuri duk abinda kike buƙata aduniya wanda muke da halinshi ki gaya mana zamuyi maki, shi Labid ɗin da kika danshi bakiga ko waiwayarki bai sake yi ba, haka ma magabatanshi babu wanda ya taɓa kira yaji ya akai.


Kinga kenan basu ƙaunarki dashi, basu maraba dake cikin ahalinsu, dama can rabon cikin dake jikinki ya haɗa aurenku, ki ɗauki wannan ƙaddarar da hannu biyu ki nemi zaɓin Allah kinji?


Na ɗaga mashi kai daga kwance ina share hawaye, tun daga wannan lokacin na daina kuka gaban kowa, ganin yadda kowa keson sanyani cikin farin ciki yasa nake ɓoyewa nashaƙi kuka na.


Ba zasu taɓa ganewa ba, ba zasu taɓa fahimtar farin cikina ya ƙare ba, gaba ɗaya sai rayuwar ta fita akaina, gani nake shikenan na gama walwala da farin ciki aduniya.


Ahaka naita rainon cikina cikin baƙar wahalar jiki data zuciya, ban taɓa fidda rai da cewa kafin na haihu Labid zai dawo yace ya maidani ba, dan haka kullum bana baccin kirki haka nake sallolin dare ina kuka kan darduma ina roƙon Allah ya maido man da Labid, sai da cikina ya shiga wata bakwai sannan na soma cin abu ya ɗan tsaya, wani lokacin kuma ina fara ci amai zai taso naita kwarawa.


Duk wanda ya sanni ya zo ya ganni yanzu ba zai taɓa yadda nice ba a kallo guda, nayi rama ta fitar hankali sai cikin agaba kawai shima ba wani girma gareshi ba.


Tunda cikina ya shiga wata uku nake ganin aiken kuÉ—i ta acct É—ina dubu biyar duk wata daga Labid, bana ko dubansu yadda suke shigowa haka nake barinsu domin babu abinda na nema na rasa agida.


Cikin na shiga wata takwas da sati biyu ya aiko man da naira dubu saba'in sai kuma saƙon massage da cewa kuɗin siyayyar haihuwa, nayi murmushin takaici ina kallon yawan kuɗin acct ɗin naira dubu casa'in da biyar 95k.


Karo na farko bayan fita awo tunda na dawo na kira Rabi'a nace ta shirya muje kasuwa yin siyayyar haihuwa abinda ya sawwaƙa, danaje yi ma Mami sai mun dawo take cewa kuɗin daya bada zasu isa ko, ko kuma inƙara maki?


Na girgiza kai zasu isa Mami, mukayi mata sallama tana faÉ—in mubi ahankali, muka fita araina ina faÉ—in duk abinda ya bada dashi za'ayima É—iyarshi siyayya, gwanda tun tana jaririya tasan halin ubanta, akasuwar duk kaya masu sauÆ™in kuÉ—i na sawo muka dawo na gaji lilis.


***


Add ɗina ya cika harna haura da kwana tara, ina zaune muna kallo ranar lahadi wajen ƙarfe takwas da rabi, ba zato naga kiran Labid acikin wayata, kamar kada na ɗauka saboda tunda muka rabu yaune karo na farko daya kirani, amma sai wata zuciya tace inɗauka, dan haka na sanya akunne banyi magana ba, jin muryarshi adodon kunnena nayi yana faɗin ɗan fito waje minti biyu Asiyah saƙo zan baki kinji.



Banyi tunanin komai ba na miƙe na fice babu wanda yasan fitata, jikin wata ash fijo 206 na ganshi tsaye, yana nan yadda na sanshi saima alamun kwanciyar hankali dake tattare dashi, kenan ni kaɗai ke kewarshi ni kaɗai na damu dashi, kafin nayi magana naji kamar anɗan tsunguleni amara, na yamutsa fuska na basar.


Bayan motar na buɗe na zauna saboda ban iya tsayuwa mai yawa dan ƙafafuna akunbure suke, shima gida motar yayi mazaunin mai tuki, Asiyah ya kwana biyu ya lafiyar baby? Nayi mashi shiru dan bansan abinda zance mashi ba, zaici gaba da magana marata ta sake katsawa, na duke ina faɗin wash wayyo Allah, arazane ya juyo yana faɗin lafiya, ina yarfe hannu nake ƙoƙarin buɗe motar na fita amma sai na kasa, lokaci sai wani irin ciwo ya taso mani.


Cikin kiÉ—ima yake tambayana wane asibiti nake zuwa awo, da kyar na faÉ—a mashi ya tada motar muka wuce, lokaci zuwa lokaci yana waigowa yace man sannu, shiya kama har cikin asibitin, ana sanya mani hannu akace haihuwa ce amma sai tsakar dare ko asuba zan haihu, ya zaunar dani É—akin da zansha labour yana faÉ—in bari na koma gida na gaya masu sannu kinji.

Minti ashirin tsakani sai ga mai aikin gidanmu wata ƴar matashiyar mata da kuma Rabi'a sun shigo ɗakin naƙudar da kayan haihuwa, sannu suka hau yi mani, haka mukaita fama cikin wannan dare, lokaci zuwa lokaci Labid yana kira ya tambayi ya ake ciki, tun ana miƙo mani wayar ina amsawa da yawwa intace sannu har nayi jifa da ita muna cikin magana da wani ciwo ya taso, daga nan babu wanda ya sake kuskuren bani waya, naji jiki na galabaita na gane kuɗata kuma.


Ƙarfe takwas da rabi da munti biyar na samɓalo jaririyata ta iso duniya, nan take ta cika ɗakin da kuka shaidar ta iso duniya lafiya.


Bayan an gama kintsamu ne nai wanka na sanya wata doguwar riga ta atamfa, ina ɗakin ƴan jinya na masu haihuwa mutane suka far shigowa yin barka daga ko ina ƴan uwa da abokan arziki, Labid ya sake kira yana tambayar dame-dame nake buƙata, nace ya sawo ruwa da kayan tea kawai.


Ba daÉ—ewa ya shigo shida wani abokinshi lokacin ni kaÉ—aice zaune ina kallon babyta dake bacci kan É—an gadon jarirai, Rabi'a taje yin sallar la'asar, su kayi man barka Labid ya É—an zauna bakin gadon kusa da Æ™afafuna yana kallona yana É—an murmushi yace duk kin rame Asiyah kamar bake ba, na tsuke fuska na kawai da kai bance mashi komai ba.


Ya É—auko babyn yana faÉ—in kinga kyautar da Allah ya bamu ko? Allah ya rayata ya albarkaci rsyuwarta amin, sai da aka tabbatar da komai lafiya sannan aka bamu sallama muka dawo gida.



Tun ranar da akai haihuwar Labid ba kunya ba komai ya maida gidanmu wajen zuwanshi, da anyi mata wanka tasha mama zaice amiƙota, da daddare ma sai ya kashe fiye da awa uku tare da ita sannan ya tafi masaukinshi.


Ranar Æ™auri ya kirani falon gidan yana tambayata naman nawa muke so, nace duk yadda ya sawwaÆ™a na juya abuna, ya fita can anjima sai gashi da naman sa da kuma kaji guda goma ya kira Rabi'a ya bata, ana jibi suna haka ma ya kuma kirana ya danÆ™a mani naira dubu talatin wai na abincin suna, ya kuma É—auko dubu biyar ya bani wai nai É—inkin kayan suna koda Æ™aramar atamfa ce, na amsa nace an gode na wuce, Mami kawai na miÆ™a ma kuÉ—in ina gaya mata abinda yace, tace Allah ya kyauta ni dai bana son kuyi wata rigima kan haihuwar nan, duk abinda ya baÉ—a kiyi haÆ™uri dashi.


Ana gobe suna yake tambayata banda wani suna da nake so na girgiza kai, yace toh nai mata huÉ—uba da *Yumnah* Allah ya raya mana ita nace hakan, washe gari bayan raÉ—in suna akaci gaba da walima inda akaci aka sha cima mai kyau, nasha kyaututtuka kowa ya tafi ana Allah ya raya Yumnah.

Tun daga nan muka faɗa jego, duk da cewa ni ruwan zafin sati guda nasha daga nan na koma wanka da ruwan ɗumi domin har lokacin ƙafafuna a kunbure suke, jini na kuma asama yake tun na naƙuda yaƙi sauka, dan haka da muka asibiti likita yace na daina wankan jego na kuma daina shan kunun kanwa.


Toh haka dai rayuwar take tafiya, Allah ya ɗora ma Labid son ɗiyar kamar me, kullum sai ya zo ganinta har sati uku sannan ya koma Kano dan tun bayan rabuwar ashe ya bar kaduna yana kano, ni kam dai tun ranar dana haihu na sanya ma kaina salama, nayi haƙuri da irin rayuwata, na kuma ɗauki kaddarata da hannu biyu, duk da cewa mutanen gidan mu sun maida komai ba komai ba, dan babu wanda ke nuna ma Labid wani abu ko'a fuska ta ciki na ciki suke, haka yasa shima bayajin fargabar shigowa gidan kai tsaye duk inya shigo gari ganin ɗiyarshi.


Nima tun ina basar da shi harna sake muna gaisawa tunda yaya zanyi rabo ya shiga tsakaninmu nasan har abada bamu rabu ba, kuma bayan wannan har na daina numfashi da son Labid a cikin zuciyata wanda nasan jarabta ce kawai, Allah ne yake jarabta ni domin nima É—in na wahalar da rayuwar maza masu tarin yawa, ina girbar abinda na shuka ne.


Nayi nadama ba kaÉ—an ba, gaba É—aya wata abu soyayya na ajeta agefe, auren ma gaba É—aya na cireshi araina na rungumi Æ´ar É—iyata dan ita kaÉ—ai nake kallo naji sanyi azuciyata.



*_TAMMAT..._*



( *To masu karatu anan zan dakatar da rubutun Halin Dana Shiga badan angama ba sai dai dan anzo inda aka tsaya a rayuwa, Asiyah na nan a halin yanzu tana rainon Æ´arta tana kuma neman zaÉ“in Allah ga rayuwarta, nayi maku alÆ™awarin inda aron rai da lafiya in an samu cigaban rayuwa zan ci gaba dayi maku shi insha Allah, zan É—an sami hutu kafin kujini a sabon littafina mai suna *RUMANAH* da yardar rabbi, masoyana a duk inda kuke ina Æ™aunarku ina kuma godiya da addu'o'inku*)


Iya wuya muna jone😘😘😘