Chapter 3 chapter 3
DR MUHSEEN
Bismallahi Rahamir Rahim.
PAGE 3️⃣
📝....................ganin wani mugun juyi da tayi hakan yasaka doguwar rigar jikinta yakicewa site daya inda santala-santalan fararen jinyoyinta suka bayyana ras akan idon muhseen.cikin kasala ya dafe kanshi Yana juyawa zuwa falo ganin haryanzu ba kowa ya nufi freaged din Kaka dan dauko hura.cikin sa'a kuwa ya samu jin yadda hurar tayi sanyi karara yasaka shi Kara sauke ajiyar zuciya,Dan shi mutum ne mai son hura hakan yasa yake jin dadin zaman Daura.saida ya gyara zaman shi sosai saman kujera kafin ya fara kurbarta,har wani lumshe ido yake yi saboda gardinta.
SEYERMA kuwa ta kasan idonta taga ficewar Muhseen daga dakin, da sauri ta tashi zaune tana gintse dariyar da take cinta Dan tunda ta ji motsin shigowar shi ta farka ,A ranta tace "Kaine mai karyar iskanci tunda ka yarda na gano lakonka to ka shiga ukku,saina rama duk wulakancin da kake yiman ta wannan hanyar"tana saukowa daga Kan bed din.Murmushi ta karayi a fili ta furta "Amma fa na tsorata da ganin wannan abun cab wallahi matar shi kam ta shiga ukku,Dan datayi mai laifi da ita zai rinka hukunta ta"rike habarta tayi tana mamakin girmanta da tsayi.daidai ta kawo bakin kofar.taba kanta da tayi jin alamar babu dankwali yasa tayi sauri hayewa bed din ta dauko shi.da haka dai tayi wanka bayan ta sakama kofar dakin key,gudun kada ya Kara dawowa.
Harya karasa shanye hurar babu alamun dawowar Kaka,Dan haka ya wuce part din shi saboda yadda ya ji idon shi na rufewa alamar Yana jin bacci.yana shiga ya sakama kofar key ya cire rigar jikinshi tare da saka wayar shi a flaymode yayi konciyar shi.
Sosai SEYERMA tayi kolliya tabi duk illahirin jikinta ta feshe da turare da wasu humra masu kanshin dadi.weardrop din Kaka ta daga site daya duk kayanta ne,Dan siyama Bata zama guri daya hakan yasa duk gidan da tasan tana zuwa ta zauna to akwai kayanta a wurin saboda idan taje.Bayan ta gama shiryawa cikin doguwar riga ta atamfa mai ratsin green da black a jiki ta kashe daurin dankwali a gaban goshi bata wani sha wahala ba dan Daman kanta a konce yake Kara gyara shi tayi.ta manta takalminta a dakin Ya Faruk Dan haka ta saka wani plant tare da karamin mayafinta ta fice zuwa part din Mama inda nanne asalin wurin zamansu.tunda ta fito ya Faruk ya hangota ta wendorn falonshi,sosai yake kallon yadda yarinyar take taku cike da natsuwa,shikam yayi Imani da Allah kaf estates din nan yarinyar nan tafisu kyau da cikar halitta dukda kasancewarta karama Wanda ba kowa zai fahimci hakan ba sai Wanda yasan sirrin mace.sosai siyama take juya hips kamar tasan ana kallonta hakan bai hana gani yadda kugunta yake juyawa ba ta cikin doguwar rigar da akayima dinkin rafa ,jinta take yi cikin nishadi Amma da zarar ta tuna da abinda ta gani dazu sai ta ji gabanta ya wani bada sautin rassssss,harsai ta dafe saitin zuciyarta da hannu kafin ta ji sauki.da wannan tinanin ta tura kofar falon yadda take zato hakance ta kasance.Reras ta riske su a falon musamman yan"'matan sai samari guda biyu sauran ga dukkan alamu sun fice cikin gari.A hankali tayi sallama tana Kara nufa ciki.wasu daga ciki suka amsa,wasun su ko ko kallonta Basu yi ba, musamman Ameerah da Bahijja sosai suke jin haushin yarinyar ganin yadda kowa yake bata kulawa more especially ya Faruk duk duniya idan zai kawo wani abu to na SEYERMA ne Koda Yana son abun to zai barmata shi.ko kallon yan'mata batayi ba sai gaishe da su ya Jabeer da Zaid tayi,jin cikinta ya murda alamar Yana bukatar abinci yasa ta nufi kitchen bayan ta aje mayanfinta Kan kujera.haka Suma ba Wanda ya kulata,sauran doyar data gani cikin kula ta juyeta cikin karamin plate sai tea data hada ta dawo cikin falon zaman dirshen tayi abunta saman kafet kusa da Ya Jabeer ta fara ci.saida ta kusan cinyewa Jabeer ya ce "ohhhh ni Jabeeru yanzu dear Ina kallon ki zaki cinye ko Bismillah bazaki yiman ba,ok na fahimta kinfi son ya Faruk akan ni saboda shi yace zai saka ki a jami'a,to daga yau mun bata nima bazan Kara kawo maki cakulet ba"Yana kokarin yin dariya dan yasan SEYERMA da cakulet sai Allah.
Aiko tana jin haka tayi saurin dawowa gaban shi da plate din doyar tana murmushi har dimple dinta Yana lotsawa"sorry ya Jabeer indai doya ne gashi na baka duka ma,kadafa su Aunty Sakeena su ji kanmu zasu yimana dariya fa"tana tura plate din gaban shi.sosai taba su Zaid dariya ganin yadda lokaci daya ta rude da ta ji zancen cakulet.cikin dariya Jabeer ya ce "sorry dear da wasa nake yimaki maza ki karasa cinyewa,Kinga rana ta fara yi ko sai yanzu kike yin breakfast"itama kallon shi tayi tana murmushi a zuciyarta tana cewa "uhmmm ai nayi kokarima dana samu damar cin abinci saboda tsabar tashin hankalin Dana fuskanta.
Kamar an mintsineta sukaga ta koma kitchen da sauri dauke da plate din hade da cup,duk Suka bita da kallo Jim kadan ta dawo mayafinta kawai ta figa ta fice daga gidan da gudu .ba Wanda ya hanata.sai Jabeer da yayi ta dariya danya fahimci me zata yi,tunda ta gudu gidan Uncle Yusuf zata koma,Kuma ba zata dawo ba harsai Sojanta ya tafi,kusan duk sati haka take yi,yauma abinda ya fahimta tsautsayi ne ya rutsa da ita Dan Bata san Muhseen yayi saukon zuwa da wuri ba,a ka'ida kowane weekend sai karfe goma yake shigowa katsina.sosai Jabeer ya sha dariya Dan tun dazu ya fahimci muhseen shiya sumar da ita,ga dukkan alamu koma meye yayimata to ya tsorata ta harya sakata suma.
Fitowa yayi danya bi bayanta,Amma bat yarinya ta bacemai yasan tuni ta shige gidan Uncle Yusuf.shima juyawa yayi zuwa part din Faruk zasu Kara tattatunawa akan family meeting din da za'a gudanar a cikin karshen watan nan,Daman anayi duk bayan wata ukku inda ake hidima sosai tare Dan Kara karfafa dankon zuminci.Aunty Hajara matar Uncle Yusuf tana kitchen Dan dora girkin rana ta ji ana ta faman Danna door bell ba kakkautawa,cikin sauri ta aje kayan miyar da take gyarawa ta nufo bakin kofar.tana budewa burum SEYERMA ta fada ciki falon tana faman haki kamar wadda aka biyo da gudu."A a ke lafiya haka ko wani ya biyo ki"?ita dai bata tsaya bata amsaba saida ta zube saman kujera kafin ta ce "Aunty wani Dan duniya ne ya biyo ni,Wai ya ce saiya cinye ni"Kara gyara konciyar ta tayi kafin taci gaba da cewa "Yauwa Dan Allah Aunty idan mutum ya ce zai cinyeka meyake nufi ne"sosai Aunty Hajara ta kalleta jin abinda tace "yooo Banda ke da abinki seeyerma ai sai idan mutum maye ne shi ne zai cinyeka,Amma idan ba haka ba taya za'ayi mutum yaci mutum"tana wucewa jikin fredged.again seeyerma ta Kara cewa "A a Aunty ba maye bane kawai wani ne Wai ya ce saiya cinye ni danyaga karyar iskanci na.tana runtse idonta Dan ita maganar ta tsayamata a ranta,gashi haryanzu hoton wannan abun yaki gogewa daga zuciyarta."Subahanallahi"cewar Aunty Hajara daidai ta Miko mata ruwan sanyi a cup.batace komai ba ta amsa saida ta shanye tas kafin ta mayar da kanta jikin kujera tana cire dankwalin kanta.itama Aunty Hajara bata kara cemata komai ba ta juya zuwa kitchen taci gaba da aikinta,Amma a zuciyarta nazarin maganganun yarinyar take yi domin wannan maganace mai girma da sarkakiya,to koma waye tabbas Yana da wata manufa akan yarinyar,Amma a hankali zata tambayeta dan gano gaskiyar al'amari.
SUDAN
A daidai wannan lokacin karfe daya agogon nageria,Sudan kuwa karfe biyu daidai.Babbar masarautar sarki Abdulkareem tayi jit sai sauran hadimai da suke ta ayyukan su,kasancewar ranar ba aiki yasa sarki zama a sashen shi,sai bayan sun dawo daga masallacin sallar azahar ya wuce site din mahaifiyar su jin sakon da kanwar tashi Ummey ta Aiko na cewar jikin mahaifyar tasu ya motsa.bayan isowar family doctor dinsu ya dubata tare da rubuta magunguna ya tafi,shiyasa yanzu ya nufi part din Dan Kara ganin jikin nata.A falo ya riski kanwar tashi abin kaunar shi.bayan yayi sallama har kasa ta duka tana kwasar gaisuwa dan akwai girmamawa mai karfi tsakanin shi da kanwar tashi ta daukeshi tamkar mahaifin su,hakan yasa a kullun burin sarki Abdulkareem shi ne yaga ya faranta masu rai ita da iyalinta da mahaifiyar su,Dan su kadai suka ragemai idan ya kalle su yake jin dadi.bayan sun gaisa sosai ya kuramata ido ganin Yadda idonta yayi jawur alamar tayi kuka.zama yayi bisa kujera yana dubanta a cikin taushin harshe ya Kira sunanta da yaren labarci ya fara magana "Kanwata"kasa amsawa tayi sai karayin kasa da kanta tayi saboda wani sabon kuka da yake kokarin kufcemata.bai damu da rashin amsawarta ba ya ci gaba da cewa "kiyi hakuri kanwata, kada ki dauka na kasa Samar maki da farinciki,wallahi Ina iya bakin kokarina yau tsawon wata guda kenan da sakawa a fara sauke alkur'ani mai girma akan wannan al'amarin,sai anyi tsawon wata uku anayi kafin muga yadda Allah zaiyi da mu,ki Kara kontar da hankalin ki tare da zurfafa addu'a insha Allah komai zai wuce,Nima Ina tayaki da Addu'a,burina kullun na ganku cikin farinci kin ji"bata samu damar bude bakinta ba sai gyada Kai da tayi alamar ta fahimta.haka dai yayi ta yimata nasira tare da kara kontarmata da hankali,saida yaga tadan saki ranta kafin suka dunguma zuwa dakin mahaifiyar tasu.bayan yayimata addu'o'i Dan haryanzu bacci take yi kafin ya fito Yana Kara jaddada duk abinda suke da bukata ta sanarmai ta amsa da to kafin ya fice part din gimbiya Zulaihat ya nifa da wasu daga cikin fadawansa suna take mai baya tare da wazirin.
Sai wuraren karfe daya kafin Muhseen ya fara kokarin tashi daga nannauyan baccin daya dauke shi,Dukda badan ya gaji ba Amma dole ya tashi kodan time din sallah yayi.mafarkin da yayi ne ya fadomai a ranshi.a zuciyar shi ya ce "kardai ace abinda na saba yi yauma shi ne nayi na shiga ukku ni muhseen ya zanyi da rayuwata.kokarin tashi ya fara yi Amma abinda yaji shiya saka shi komawa ya konta Yana zaro ido tare da jin wata muguwar faduwar gaba.cikin sauri ya Kai hannun shi wurin yanason tantance gaskiyar abinda ya ji Amma jin ya tabo wani abu yasa yayi saurin mikewa zaune tare da furta s......................
By
AUTAR AREWA.
✍️✍️✍️✍️✍️✍️