Miss Nigeria

The sisters

by @azizat

*MISS NIGERIA*




*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*


Ɗaya



***

*The Sisters*


Fadwa Shafi'u ta ajiye backpack ɗinta a cikin mota sannan ta ja ta tsaya jikin murfin motar tana jiran 'yaruwarta ta fito. Babu abinda ta tsana irin latti kuma jazaman ne wannan, kusan kullum se sun yi latti indai zasu jira Raudha. Ta tsani zama ta ƙarshe wajen shiga aji amma saboda Raudha kusan kullum itace ƙarshen shiga ajinsu.

Habu direbansu ya danna horn da ƙarfi da alama shima ya ƙagu Raudha ta fito su tafi. Kusan minti biyar Fadwa na tsaye jikin mota sannan 'yaruwarta ta fito tana tafiyar catwalking kamar wata model a fashion show. Irin tafiyar nan Fadwa ta tsana, dogayen ƙafafuwan Raudha, shafaffen cikinta wanda ya baiwa hips ɗinta damar fitowa fili yadda ya kamata. Ko cikin uniform ɗinsu na farin riga da grey pinafore sai da yanayin surar jikinta ya bayyana.

Kafin ta ƙaraso wajen motar Fadwa tayi saurin shigewa motar ta zauna. Kyakykyawar fiskar 'yaruwarta na mata gizau a idanu.

Anya gidan ku ɗaya da Fadwa? Ko dai ita 'yar aiki ce? Amma Fadwa irin 'yanuwanku nan ne na ƙauye ko?

Ta sha jin irin waɗannan tambayoyin a bakunan abokan Raudha kuma ko sau nawa Raudhar za ta faɗa musu cewa ubansu ɗaya baya chanja yanayin kallon da suke mata.

Idan kaji ana faɗin yarinyar nan kamar ubanta sak, to kyaunsa ta ɗauko. Amma idan ana faɗin wannan 'ya da namiji Allah ya yita da babu banbancinta da ubanta to munin uban ta ɗauko.

Ba zata ce mahaifinta mummuna bane amma kuma duk wani halittar fiskarsa shi ne ke nata fiskar, tun daga ƙananun idanu zuwa ƙaton hancinsa wanda ƙofar hanci ɗaya ya fi ɗaya faɗi. Da ace ta ɗauko farar fatar mahaifiyarta to da sai ace abin yayi sauƙi amma kusan tafi Daddynsu ma baƙi.

Har wa yau tana sawa ranta cewa inama ƙaninta AbdulHaq ne ya ɗauko kamannin mahaifinsu ba ita ba. Amma sai akasin haka ya faru. Ita ɗin ta tattaro komai na mahaifinsu ne shi kuma AbdulHaq ya ɗauko komai na Mommyn su. Shi kuma autansu Fawwaz ya ɗauko baƙin fatar Daddyn su da kuma kamannin Mommy. Ba abinda Fadwa ta ɗauko na Mommy sai jiki.

Wasu lokutan tana fata a ranta inama Raudha ce ta ɗauko kamannin Daddy ba ita ba. Yadda ita ta ɗauko Daddy haka Raudha ta ɗau kamannin mahaifiyarta, duk da dai a hoto suka ganta amma kamannin har ta ɓaci. Wani lokaci idan Fadwa ta dubi hoton mahaifiyar Raudha dake ɗakinsu sai ta fara tunanin taya ma kyakykyawar matar nan ta yadda ta auri Daddyn su? Lallai kam ba kyau ko kuɗi ta gani ba. Dan ta fishi komai.

Raudha na yawan faɗin cewa zunzurutun ilimin Daddy ya sa mahaifiyarta ta amince da soyayyyarsa wai haka Aunties ɗinta suka faɗa mata. Da gaskiya a cikin maganar dan wannan kyakykyawar mata 'yar babban gida ta fi ƙarfin Justice Shafi'u Jibrin.

Wani lokaci takan yi tunanin inama mahaifiyar Raudha bata mutu ba, da yanzu ƙila mahaifiyarta wani mijin daban zata aura sai ta haiho wata Fadwar daban ba wannan ba. To amma aikin gama ya gama, babu wanda ya isa ya goge ƙaddara. Mommyn Raudha ta rasu kwanaki kaɗan bayan haihuwarta, Daddy ya auri Mommynta dan ta taya shi rainon Raudha, watanni shaɗaya da kwana ashirin da biyu da auren ta haifi Fadwa.

"Fadwa love, dan Allah duba min assignment ɗin maths ɗin nan ni nayi birbir ne kawai ba wai ganewa na yi ba"

Fadwa ta girgiza kai gefe. Ba yau ta fara yiwa Raudha assignment ba, wannan nema ya sa ta karɓi notebook ɗin ta fara bubbuɗewa ba tareda ƙorafi ba. Kafin su iso makarantar ta riga ta gama gyara mata assignment ɗin.

Suna sauka daga mota ƙawayen Raudha suka mata chaa yayinda Fadwa ta sulale a hankali ta wuce ajinsu. Allah yasa ma da sauran lokaci basu makara ba.

Fadwa za ta iya cewa tun daga aji ɗaya har yanzu da suke aji shida bata taɓa yin ƙawa na azo a gani ba. Kusan mutane biyu zuwa uku za ta iya cewa suke magana sama-sama a ajin nasu. Gara ma a Islamiyya tana da kusan biyar wanda yanayin son karatunsu ya zo ɗaya.

Bayan sun tashi daga makaranta ta tsaya jiran Raudha a ƙofar ajinsu. Kusan kowa ya bar ajin sai Raudha da ƙawayenta uku wanda ko ba a faɗa ba Fadwa ta san ba zai wuce hoto suke ɗauka ba. An hana zuwa da waya makarantar amma Raudha da gang ɗinta ba su san wannan ba.

Bayan sun gama hotunansu suka fito wajen aji suna ta dariya. Fadwa ta bi bayansu tana tafiya kammar ta nitse cikin ƙasa. Sai da suka kai bakin gate kowa yai nasa hanya Fadwa da Raudha suka tsaya jiran direbansu.

"Fadwa yau yaya J zai dawo. Allah yasa shi zai zo ya ɗauke mu, wallahi dole ya kaimu shan ice cream"

Fadwa ta gyaɗa kai. Yaya J bai taɓa faɗa mata yaushe zai dawo ba, bai taɓa kiranta a waya ba a shekaru uku da ta fara riƙe waya. Ko zai dawo daga tafiya tsarabarsa kullum ta Raudha ce kaɗai sai dai Raudhan ta sammata a ciki. Ta sani muninta yasa ya ke ƙinta. Amma ai tafi Raudha ƙoƙari tafi Raudha yi masa hidima. Like idan ya dawo daga makaranta itace ke share masa ɗaki da arranging masa kayansa. Idan ta ga kayansa sun yi datti ita ke baiwa dry cleaner dake musu wanki. Raudha bata taɓa ko gyara masa pillow ba balle wai ta gyara gado ko ta masa shara.

Lokacin suna yara idan za shi gidan abokansa ko wani yawonsa Raudha ya ke ɗauka su je tare. Ba za ta taɓa mantawa da wani rana da ya nuna mata banbanci a fili ba. Suna shekara bakwai lokacin, ana hidimar sallah. Ita da Raudha an musu ado cikin kaya iri ɗaya amma kala banban. Ya zo ya ce da Mommy zai ɗauki Raudha su je yawon sallah. Mommy ta ƙolo musu kira dukkansu biyu sai da suka fita waje zasu hau babur ɗinsa ya shafa kan Raudha yace 'Fadwa je ɗakina ki ɗauko min agogo akan gado'. Bayan shigarta cikin gida ya burga machine ya tafi. Lokacin data fito da gudu dan ta sanar da shi bata ga agogo ba ta ga compound ɗinsu wayam, ba machine, ba Raudha, babu yaya Jabir...

Suna tsayen kuwa motar gidansu ta tsaya tunma kafin ta gama tsayawa suka san Yaya J ke tuƙa motar. Raudha ta daka tsalle ta shige gaba ta ɗan rungume Yaya J ta gefe tana masa oyoyo, shi kuwa ya shafa kumatunta yana faɗin "na missing ɗin ki my beauty"

Fadwa ta maida kanta jikin window tana jin takaicin abubuwan da su ke yi. Yaya J ba muharraminsu bane, ɗan ƙanwar Daddyn su ne, amma ya maida taɓa jikin Raudha tamkar ba komai ba. Yo ko muharraminsu ne ai irin taɓe-taɓen nan yayi yawa.

Sau ɗaya ya kira sunanta ya tambayeta ya school bai sake bin ta kanta ba. Fadwa ta cigaba da kallon titi, mutanen da suke wucewa, machina da motoci da ke tsala gudu kamar zasu tashi sama...

Kamar yau duk gidan sun haɗu ne dan su ɓata mata rai. Fadwa na shiga kitchen bayan ta yi sallah ta chanja kaya ta samu abincin da Mommy ta yi favourite ɗin Raudha ne. Ta ja tsaki ta rufe murfin warmer data buɗe. Jiya ma stir fry spaghetti aka yi saboda Raudha tace tana son ci, yau kuma white rice da chicken pepper soup. Fadwa ta tsani haɗin nan ba wai dan babu daɗi ba sai dan favourite ɗin Raudha ne.

Dai dai zata fita daga kitchen ta ci karo da Raudha.

"Fifi mi Mommy ta girka?"

Fadwa ta tsani Fifi da Raudha ke liƙa mata. Tana son sunanta, yana mata daɗi yana yiwa mutane daɗi. Amma Fifi kamar wata sabulu ko cartoon.

"Ga ki ga kitchen ɗin ai" ta faɗa tana tura baki.

"I'm sure best food ɗina aka yi shiyasa kike ɓata rai. Woow ƙwalelenki Mommy ta fi sona"

Fadwah ta yi murmushin yaƙe ta wuce ɗaki, duk wani yunwa data ke ji ya koma ciki.

Ta kwanta a gadonta tana shafa cikinta dake ta ƙugi tun ɗazu. Idan ta ƙi cin abinci ma tayi wa kanta ne dan ba zai chanja cewa shinkafa da pepper soup ɗin kaza shine favourite ɗin Raudha ba, sannan ba zai chanja cewa shi Mommy ta girka kafin ta fita ba. Ta fara tunanin ko dai ta je ta ɗau noodle ne ta dafa ko kuma ta ɗauko cookies a fridge ta ci ta sha juice a kai. Ko kuma ma dai ta ɗebo shinkafar ta haɗa da yaji ta ci?.

"Fadwa, Fadwa"

"Na'am" ta miƙe da sauri, kiran Yaya J na da mahimmanci a wajenta duk da ta san yana kiran ta kawai idan zai sakata aiki.

A falo ta same shi zaune kusa da Raudha wacce ke savouring girkin Mommy hankali kwance tana yi tana kallon wani Indian film.

"Gani yaya" Fadwa ta faɗa da muryanta mai sanyi wanda idan akwai abu ɗaya mai kyau da take alfahari da shi a jikinta to muryanta ne, shima ya samo asali ne saboda yawan gwaɗa shi da ake yi. "Fadwa you have a sweet voice" comment ɗaya kenan dake faranta mata rai wanda kusan shekaru uku da suka wuce Yaya J ya taɓa faɗa mata shi bayan ta lashe wani gasar debate competition da suka yi tsakanin makarantu. Lokacin tana shekara shauku, lokacin yanayin halittarta bai fara tasiri akan yadda take gudanar da lamurranta ba.

At 15years ta fara wani buɗewa, halittar ta na jiki ya ƙara bayyana wannan kuma ya sa ta fara damuwa da yananin ta musamman saboda kullum aka ganta tareda Raudha banbancin halittarsu ake fara magana a kai.

Ba tareda Yaya J ya kalleta ba yace " ki je ki gyara min ɗakina".

Da Raudha ya faɗawa haka tabbas ƙorafi za ta yi koma ta fito ƙarara tace ba zata iya ba sai dai Fadwa ta yi. To amma Fadwa ce, Fadwa bata jayayya da nagaba da ita, Fadwa akwai hankali.

Kafin ta gama share ɗakin da mopping Mommy ta dawo. Yunwa yaci ƙwal ɗinta dan haka tana wanke hannunta ta wuce kitchen da niyyar cin shinkafar ɗazu amma wayam ba komai. Ɗazu da Mommy ta shigo tareda baƙi ta ke dan haka duka abincin ta juye ta kai musu. Fadwa ta hangame baki ta rasa abun yi, idanunta suka yi raurau kamar zata yi kuka.

Ta buɗe fridge zata ɗauki cookie jar ta ga wayan babu ko crumbs na cookie a ciki balle ta ga chocolate cookie da Mommy ta baking shekaranjiya. Wannan shi ake cewa biyu babu.

Ta rufo ƙofar fridge ɗin da ƙarfi suka yi ido huɗu da Mommy

"Eh, ɓalla shi ki huta"

"Mommy an cinye abinci, an cinye cookie ni mi zan ci?"

"Mi ya hanaki cin abinci tun ɗazu?, ki gama sakalcin ki ki zo ki fere min doya kafin ku tafi hadda, Daddyn ku zai dawo yau, pounded yam zan yi"

Fadwa ta fara bubbuga ƙafa tana tura baki. Mommy ta wuce ta barta a gurin. Ba yau ta saba bori ba idan aka dafa abinda Raudha ta fi so.



***

Raudha ta mirgina gefe a karo na biyu sama-sama take jin abinda Fadwa ke faɗa dan gaba ɗaya wani shegen bacci ke cinta.

Yau Asabat ta san ba zai wuce maganar zuwa hadda ba. Gaskiya ba zata je ba dan rabonta da ta bita ayayoyin da aka ƙara mata ya ɗan kwana biyu. Yau kusan wata biyar kenan ta kasa ƙarisa suratul Ankabut. To Mu'allim ɗinsu da zai tsawata mata dan ta sa himma ta yi hadda sonta yake, dan haka maimakon kausasawa ko duka kamar yadda yake yiwa sauran ɗaliban sai ya maida ƙarfinsa wajen lallashinta akan ta amince da soyayyyarsa. Soyayya da Malamin ajinsu ke mata ya haddasa ƙara sukurkucewar karatunta. Gaba ɗaya ta sake jiki ta dena maida hankali a kai.

A lokacin da Malam Saleh Maiguduma Allah ya jiƙan rai ya ke ɗaukan ajinsu kusan har cikin dare tana iya tashin Fadwa dan ta bita mata hadda. Malam Saleh ya ɗauke su ne da iron hand, ko kaɗan baya wasa da karatun yaro, idan yaga kana da raunin ɗaukan karatu to haka zai sa maka ido ya jawoka jikinsa ya dinga takura maka ta yadda dole ne sai ka ɗauka. Shiyasa har wa yau irin haddar da ta yiwa izufi goman ƙasa daga suratul Ahqaf zuwa suratul Nas daban ne da sauran haddan da ta ke yi yanzu wanda kusan kullum tana yi ana cin gyaranta, a haka kuma idan tace a ƙara mata Mu'allim Sadiq zai buɗe Alqur'ani ya ƙara mata wasu ayayoyin bayan ya sani itama kuma ta sani cewa haddar da tayi guragurbi ne ba shi da ƙwari.

Akwai watarana da Malam Saleh Maiguduma ya sakata maimaita aya ɗaya har sau ɗari saboda kuskuren ƙarshen ayar da ta yi maimakon Zhaalimuun tace Kaafiruun. A ranan tun tana maimaita ayar na daɗi har ta koma karanta ayar cikin kuka duk da haka Malam Saleh bai sarara mata ba sai da ta cika sau ɗarin nan cif.

Mommy ce ta shigo ɗakin dan itama akwai Islamiyyar mata da take zuwa duk Asabat da Lahdi. Sai dai maimakon nasu da ake zuwa ƙarfe takwas na safe zuwa shabiyu na rana ita nata ƙarfe tara ne zuwa shaɗaya na safe.

"Raudha tashi ki sha magani"

Ta faɗa bayan Raudhan ta tashi zaune tana musissiƙa idanu.

"Ga breakfast ɗin ki ki ci sannan ki ɓalli paracetamol biyu ki sha. Idan baki ji relief ba idan na dawo daga makaranta sai na kaiki Asibiti"

Raudha ta gyaɗa kai.

Mommy ta miƙe daga kan gadon tace "kin yi brush kuwa?"

Raudha ta gyaɗa kai ba tareda ta cire mug ɗin shayi da take sha ba.

"Allah ya ƙara sauƙi, barin je"

In between mouthful na chips tace "sai kin dawo Mommy"

Allah Sarki Mommy Maimunah. Ba abinda matar nan ta raga mata na soyayyar uwa. With her ba ta taɓa jin cewa bata da uwa a raye ba. Duk abinda Mommy ke mata ko mahaifiyarta na raye iya abinda zata iya yi kenan.

Raudha ta jawo wayarta daga ƙarƙashin pillow. Wayar nan shine silar ciwon kanta. Like jiya tabi dare in between chatting da Yaya J da kuma surfing instagram. Kafin ta kwanta sai kusan ƙarfe biyu saura shiyasa ma koda Asuba da ƙyar ta tashi sallah a nan ne ma take faɗawa Mommy cewa kanta na ciwo.

Ta connecting wifi na gidansu dan Daddy na buɗewa ne daga ƙarfe takwas na safe zuwa takwas na yamma shiyasa idan aka kulle wifi ɗin duk wani chatting ɗin dare daga aljihunta take siyan data.

Tana gama yin breakfast ta tura plate da mug ɗin gefe ta koma ta kwanta. Bata jima da fara yawo a social media tsakanin facebook, instagram da whatsapp bacci ya ɗauketa.

Cikin bacci taji ana shafa cinyarta. Ta basar da hakan ta sake gyara kwanciyarta. Juya ɗaya ƙafar da ta yi ta sake ji ana shafa ƙafan a hankali tana jin wani zirrrr a ranta. Fadwa ba zata tasheta haka ba, Mommy ma ba zata tasheta haka ba. Mutum ɗaya ke tashinta haka...

Ta yi saurin buɗe ido lokacin da ta ji hannunsa a cikinta yana aiming ɗinsu zuwa ƙirjinta.

"Yaya J ina kwana" ta faɗa da muryan bacci.

"Wani abu na gani kaman ya crawling saman cikinki"

Yaya J kenan. Still yana son justifying banzar ɗabi'ansa ta taɓa mata jiki. He graduated from taɓa mata fiska da hannu zuwa occasional taɓa mata hips, cinyarta ko kuma nonuwanta.

Ta tsani hakan dan ta san su ba muharramai ba ne. Taɓa mata hannu da fiska ba komai bane a wajenta, kamar norm ne ai. To amma sauran sensitive parts ɗinta kamar wuce gona da iri ne koda muharraminka ne balle wanda ba muharraminka ba.

Ta tsani cewa a wasu lokutan ɗan daɗin da take ji idan ya taɓa ta hakan yana hanata dakatar da shi, tunatar da shi cewa babu kyau.

Ƙila tsoro ne, ƙila soyayyar da take masa ne, ƙila kuma sanin cewa ai shima ya san babu kyau kuma yake yin hakan yasa take haɗiye ɓacin ranta a lokutan da ya mata haka, afterall Yaya J ya mata nisa a al'amurran duniya dana addini. Shifa yayi saukan qur'ani lokacin tana shekara bakwai..

Yaya J bai yi yunƙurin cire hannunsa daga cikinta ba amma ya dena movement ɗin da yake yi ɗazu kafin ta buɗe ido.

"Kina da perfect body shape Raudha. Allow me to see this bounty, this curve da Allah ya miki a nan" ya ƙarisa maganar yana tracing hip bone ɗinta.

Ɗan muskutawa tayi kaɗan fiskarta ɗauke da murmushi maimakon ɓacin rai. Maimakon ta yakice hannunsa ta kausasa murya tace masa kar ya sake taɓata haka, amma sai daɗin da ta ji daya yaba halittarta ya sa ta mance da taɓata da yai inappropriately.

Ba yau bane farau. Ko lokacin da take ƙarama, ages of 6,7,8, ta kan iya tuno lokutan da yake taɓata, lokutan da ya ke cewa zai chanja mata kaya duk da sunan ya taɓa mata jiki. Sai da take 8years nema watarana da Mommy ta kama shi yana saka mata riga ta taka masa birki akan kul ya sake cire ko sakawa yaranta mata kaya. Bayan ta masa faɗan ne ta samu Raudha a gefe tace ta dinga saka kaya da kanta ko AbdulHaq ƙaninsu kada ta bari ya ganta babu riga. Mommy tayi maganar ba tareda zargin Yaya J da wani abu ba, afterall shi ɗin kamar yayansu ne, yaro mai tarbiya ga ƙoƙari da hazaƙa ba zai yi mummunan tunani akan 'yaruwarsa ba.

Lately ko suna chatting ya kan faɗi buƙatarsa na son ganin nudes pic ɗinta. Akwai ranan da yai convincing ɗinta har tayi yunƙurin ɗaukan hoton ta tura masa sai kuma ta fasa. Ƙila dan Fadwa ta buga ƙofar banɗakin ne lokacin da take ƙoƙarin ɗaukan hoton, ƙila kuma zuciyarta ne bai aminta da tura hoton ba.

"Yaya J kamar yau zaka gama school kayi bautar ƙasa nima kafin nan na shiga university. Then sai ka faɗawa Daddy maganar aurenmu."

Juya idanunsa yai irin ko oho da maganarta.

"Yaya J ka ƙara haƙuri nan da two years zamu kasance tare"

"Har yanzu ke yarinya ce Raudha, ba za ki so ki shiga halin da nake shiga duk dare ba saboda soyayyar ki. I love you kin sani, and ba zan taɓa yin abinda zai cutar da ke ba. All i want shine na saki cikin farin ciki, naga kina cikin farin ciki, cikin nitsuwa. I won't hurt you My Beauty"

She fell for it, dan murmushi mai sauti ta sake.

Ƙoƙarin kai bakinsa dai dai nata yai sai kuma suka jiyo sallamar Mommy a falo.

Jawo bargo tayi da sauri ta fara baccin ƙarya yayinda Yaya J ya fice daga ɗakin. Tana jiyo muryansa yana faɗawa Mommy cewa yanzu ya shigo duba jikin Raudha ya samu tana bacci.

Lokacin da Mommy ta shigo ɗakin ta taɓa goshinta zuciyarta kamar zai yi bindiga saboda tsoro. Bata tashe ta ba, sai kawai ta gyara mata bargo ta ɗauke plate da mug ɗin da Raudha ta karya da shi ta fita daga ɗakin.

Raudha ta sauke ajiyar zuciya daya tafi da sautin Hmmmmm...




Mun shiga kan biyu daga cikin jaruman mu, ko sun burge ku?

Na san dayawa ba za su so Fadwa ba, sannan wasu zasu bi jirgin Raudha to amma...keep reading dai

Barin birkito muku sauran jaruman namu mu gani kafin mu bi su a baya muga ya tafiyarsu zai kasance.