RAYUWAR GIDANMU

2

by @reza12

🏡 *RAYUWAR GIDANMU* 🏡





 *BY S REZA. DA CHAMSIYA .D. AMADU* 



 *ƳAN A'MANAR MARUBUTA. MUN HAƊE KAMMU DOMIN BAIWA AL'UMMARMU GUDUM MAWA WAJAN FAƊAKAR WA... ILMANTARWA GAMIDA TUNATARWA.* 




 *PAGE* 2️⃣


Wani kallo Umma ke jifan Meenal dashi,wanda ke nuna gargadi, hakanne yasa suka fasa faɗar abun da sukayi niya. Abba ne ya sake yin magana cikin ɗaga murya,"Sadiya ba magana na ke maku bane kun zuba min ido kuna ta kallona ko baku ji me nace bane? Ya ci gaba da cewa... nace miye ake maku a cikin gidannan da baku san sa? "ya faɗa a tsawace.


Cikin rawar murya Meenal ta ce"Allah Abba babu komai dama kawai dai daman muna munaa kawai de. Sai in' i'na takeyi ta kasa magana. Saida yayi magana cikin sanyin murya kafin ta ce "Dama kawai kunaso kaima ka gina mana sabon gida ne sai mu koma can mu kadai."ta faɗa tana turo baki saboda har yanzu Umma harare ta take yi.


Murmushi Abba yayi yana faɗin "Banda abin ki Mamana ai komai da lokacin sa kinji koh kar na sake jin wannan maganar kinji?. "Duk da acikin ransa yasan da cewar akwai wani abu domin kuwa yana ganin yada Umma keta zuba ma yaran harare-harare ya share ne kawai domin  yasan koma miye wata rana zai ji.



Daga nan yayi masu sallama yayi wacewar sa gudun kar ya makara, bayan fitar sa Umma ta murde ma su Meenal da Maryam kunne tana faɗin,"Wato duk faɗan da ake maku ba kwa jin magana koh?, wlh duk cikin ku na sake jin wanda ya sake ma mallam kwatankwacin irin wannan abun na yau sai na karya ma yarinya ƙafa sha-sah-shu kawai ,maza ku ɓace mani daga nan tin kafin na make ku anan.



Sum sum suka bar wajan suna murza wajan da Ummu ta murɗe masu. Suma yayun nasu kalisat da Hafsat suka tashi suka fita suka bar iyayen nasu sai kuma Sani ɗan autan su.


Bayan yaran sun fitane Mama ta kali Umma tana faɗin "Aman ni fa Yaya sai nike ganin akwai abinda yaran nan suka gani da gaske kinsan fa halin Meenal game da Iya ni wlh ina jin tsoro sosai?.



Murmushi Umma tayi tana faɗin "To ya zanyi Maman yara kin dai san halin yarinyar nan kullum ina mata faɗa akan shiga harka matar can aman kamar ƙara tura ta nakeyi, ni Walhi har bansan yada zanyi mata ba "ta ƙarasa maganar da alamar damuwa a fuskar ta, dan har ga Allah abun nan yana damun ta.



"Kar ki damu Yaya insha Allahu babu abinda zata iyayi mata da izinin Allah. Cewar Mama. Umma ta ce to maman yara Allah yasa, amma dai matar ba abar yarda bace. Haka suka ci gaba da tattaunawa game lamarin gidan nasu.




*********************

"Aikin banza kullum maganar kenan in ayi magana tace wai ita ta Allah to sai naji uban waye ma ba na Allah ba, kawai de munafurci ne ke damun ta, kuma Walhi ni dai-dai nike da kowa dake cikin gidan nan, mu zuba zuwa ni dasu shege ka fasa "Iya ce ke wanan maganar cikin hargowa.


Aunty dake sauraren ta tayi murmushi ta ce "Ai daman ba'ace ke ba ta Allah bace, ni dai wallhi abu ɗaya na daɗa maki kiji tsoran Allah Maman Abdoul, Dan ni wallhi duk yaran nan ɗaya nake ɗaukar su kuma kina da ikon da zaki iya hukunta su Sadam da Fatima ba zance maki komai ba.



"Wata dariya Iya ta fashi dashi tana tafa hannuwata sannan ta ce "Kai aman matar nan bansan ke ƙatuwar mahaukwaciya bace sai yanzu! to meye zan hukunta agurin mahaukwaci? to nace na hukunta wa? Kuma insha Allahu dake da yaranki ahaha dai zaku ƙare a gantali. Ta faɗa tana ƙara sakin wata dariya.


Anty ta ce "Duk abunda Allah bai mana ba nida yaranaba to babu shakka babu wani ɗan adam da zai iya mana shi, kuma yarona da kike kira ma haukaci haka Allah yasu ganin sa


 "Mugun halinki dai yaja masa, to menene za'a ɓoye mana? Gurin bokaye da malaman tsubbun da ake zuwane bamu saniba? To ina faɗa miki da babbar murya, kijawa wannan mahaukacin yaron naki kunne karna ƙara ganin wannan mummunar fuskar tashi a ɗakina, idan ba haka ba, Walhi sai na lahira ya fishi jin daɗi. Iya na gama faɗin haka ta bar gurin tana mai cigaba da zagin Anty da yaran ta.


Anty tayi shiru tana kallo ɗan nata da yake tsaye sai wasansa yakeyi, ga yawu sai zuba masa yake a baki. Ta share hawayan ta tana tinanin ranar da Sadam ya samu wannan ciwon hawkan. Tabbas ba a haka ta haifi ɗan taba, haka kawai watarana suka tashi suka ganshi da wannan cutar, sunje gurin malamai amma duk abun ɗayane wato aci gaba da masa addu'a, kuma tanayi amma sauƙin na gurin Allah. Haka Anty ta kama hannun Sadam suka shiga ɗaki. Shuna shiga Fatima ta taso da sauri ta na cewa "Haba Anty (kasan cewar duk yaran gidan da haka suke kiranta, harda suma yaran nata) yanzu kullum haka zaki tsaya iya tana miki duk abun da taga dama? To ni Walhi na gaji, daga yau idan ta sake zakinki a gabana Allah bazan bartaba, ai ba itace "Cikin ɓacin rai Anty ta ce "Ya isa haka, sannan ina sake sanar dake cewa karna sake jin kinyi magana akan lamarin maman Abdul in ba hakaba zan saɓa miki, kowa yasanta a gidannan ita da yaranta, saboda haka kija bakin ki kiyi shiru. Haka Fatima tayi shiru tana kallon ƙaninnata cikin tausayawa.


Kallon ƙullin maganin da ta ƙarɓo a gurin bokanta takeyi tana mai tinanin yaza'ayi ta aiwatar da aikin nata cikin sauƙi kar wani ya ganta. Afili ta ce "Wallhi kowa na gidannan ina dai-dai da shi, waccer yarinyar kuma nayi alƙawarin daga ita har uwarta sai na hanasu rawar gaban hantsi a gidannan!. Sannan mijin nasuma da suke rawar ƙafa a kansa, shida kansa zai tsanesu. Bazai taɓa saɓuwaba ace kuzo gidannan ku samemu amma kufimu komai ba, wannan haɗin kan naku shima saina tar watsashi, badai dani kuke zance ba!?. Tana cikin haka saiga ƴaƴan nata sun dawo daga tallan da sukezu. Bako sallama suka turo ƙofar ɗakin suka shiga. Zulai ta ce "Iya Walhi yaufa saide haƙuri domin kuwa tsinanun nan sun ci bashi kamar sun samu kayan ubansu. Maryam ma ta ce "Hamm ni bamma san lokacin da suke guduwaba idan sunci kayan ka.


Cikin masifa Iya ta ce "To dan uwar su da ubansu kuje ku ƙarɓomin kuɗina, ai ba ubansu bane yake bani jarin, shegu tsinannu. Zulai ta ce "Walhi iya babu inda zanje yanzu, duk uban gajiyar da na kwaso kice wai saina koma, to nidai Allah sai gobe ko anjima. Tana gama faɗa ta bar ɗakin izuwa nasu ɗakin, itama Maryam tabi bayan yayar tata.


Cikin jin haushi iya ta ce "Kai Allah dai ya tsinewa masu cin bashi kuma sugudu, toma ai wannan satane, to idan ba sataba meza'a kirashi? Kai wallhi sai sunje sun ƙarɓomin kuɗina dan ubansu, dagasu har masu cin bashin nasu. Haka Iya da dinga faɗa ita kaɗai a ɗaki kafin ta nufi ɗakin yaran nata.


Abdul ne zaune a ƙofar gidan nasu shida abokansa ƴan shaye-shaye irinsa, hira sukeyi akan ƴan mata, yayinda kowa yake faɗar yarinyar da yakeson ketawa mutunci a unguwar tasu, saida akazo kan Abdul ya ce "Ni Walhi dukkanku ma haushi kuke bani, yarinya ƙarama da zaku kama ku danne shine har kuke ɓata lokacin ku, to nidai idan nayi niyar haikewa yarinya Walhi ko ubanta waye zuwa ɗaya nake mata, kuma acikin gidannan namu ina son nasha miyar yara biyu, kuma yau ɗinnan. Aikuwa abokan na sa suka sa ihuu ana cewa...sai kayi oga mai faɗa da cikawa. Suna cikin hakane saiga Meenal da Sadiya suna dawowa daga makarantar islamiyya...


Tafe suke suna hira a kan rayuwar gidan nasu, yayinda Sadiya ta dubi Meenal ta ce "Nifa watarana sai naji kamar na shaƙe wannan shegiyar matar ta mutu kowa ya huta, domin kuwa duk abunda ke faruwa a gidannan duk itace. Amera wato Meenal ta ce "Au ke sai yanzu kikayi wannan tinanin? aini duk lokacin da na haɗa ido da ita sainaji kamar na kashe shegiya. Safiya ta ce "Fatan mudai Allah ya hore wa Abba shima ya siyamana namu. "Amin ta amsa tana cewa "Wai Ameera kema Abdul yana miki abu... "Ai bata ƙara sa ba suka shawo ƙwanar gidan su wacce suna shawota sukayi ido huɗuda Abdul da abokan sa a hanyar da zasu shiga gida. Tsayawa sukayi suna kallon juna kafin suka sakai da niyar shiga gidan. 


Saida sukazo tsakiyar su, Abdul ya miƙe ya sha gabansu ya ce "Dan ubanku baku iya gaisuwa bane? Ko ni ba yayan ku bane? Kafin suyi magana ya sake cewa ...waima daga ina kuke shegun yara masu halin uwayensu. Cikin rashin kunya Ameera ta ce "Karka ƙara zagar mana iyayenmu tundade basu maka komaiba, sannan ka bamu hanya mu huce? Abdul yayi dariya irin ta rainin hankalin kafin ya ce "An zagesu, ko bakijiba nace an zagesu, sannan sai kun faɗa min daga gidan uban wani ɗan iskan kuke da yamman nann?


Cikin jin haushe Sadiya ta ce "Daga can muke. Tana faɗa ta kama hannun Ameera suka tureshi suka shiga gida da gudu. Abokan Abdul ne suka tareshin daga faɗuwar da zaiyi, hakanne yasa baije ƙasaba. Ya kalli abokansa ya ce "Wai me a ke nufi da can? Abokan suka kwashe da dariya sannan sukace "Can fa yana nufin zagi. Cikin jin haushin maganar ya ce "Walhi sai sun faɗa min menene can. Haka ya shiga gida cikin fushi yabar a bokansa na ta masa dariya.....📝








 *Abin da yasa kukajimu shiru kwana biyu, mun ɗanyi wani gyarane a kan labarin, kasancewar labarin yafaru da gaskene, to kunga dole sai mun ɗan gyara wasu abubuwa🥰.*



S REZA ✍️ DA CHAMSIYA D AMADU.


Please comment And shering...



 *Muna muku Barka da ranar juma'a🥰🕋.*