RAYUWAR GIDANMU

3

by @reza12

🏡 *RAYUWAR GIDANMU* 🏡




 *By. S REZA tareda CHAMSIYA D AMADU* 


 _Yallaɓai S REZA? "Na'am Chamsiya. "Wai dan Allah na tambayeka mn?"Ok ina sauraronki? "Yanzu wannan labarin da muke rubutawa na RAYUWAR GIDANMU shin anya bama tona asirin gidanmu kuwa?_ 


 _"Haahh haba Chamsiya karki mantafa wasuma suna bamu rayuwar gidansu kuma muna rubutawa, to bare kuma namu!, ai yanda muke shiga gidajan wasu mu kwaso labaransu to haka muma dole mubuɗewa al'umma sirrin dake cikin wannan gida domin masu irin wannan rayuwar ko Allah zaisa su gyara_ 


_"Eh kumafa hakane, to S REZA muje zuwa domin yanzu na daina fargaban komai na shirya alƙalamina tsaf domin bankaɗo komai dake cikin wannan *HAOSE* ɗin_ 😃


 _Yawwa D. AMADU koke fa... yanzu dai al'umma na jiranmu domin sunjimu shiru kwana biyu, saboda haka kifara sambaɗa mana labari da wannan alƙalamin naki mai tsini da kaifi kamar bakin mashi da Reza._ 😅

 _Tom nashirya muje zuwa REZA mai yanke duk wani ɗan gulma da masu sakamana na mujiya👁️...✍️_ 




 *RAYUWAR GIDANMU* 

            *PAGE* 3️⃣



.........Da sauri Abdul ya bisu cikin gidan kamar zai tashi sama, yana shiga gidan bai tsaya tambayar ina suka shigaba kawai ya nufi ɗakinsu. Dai-dai zai shiga sukayi karo da Anty Hafsat tana fitowa daga ɗakin. Ameera da Sadiya kuwa kasan cewar sunsan halinsa na dabbanci ne yasa basu nufi ɗakinsuba sai kawai suka nufi ɗakin Umma. Ɗan ƙara tayi saboda zafin da goshinta kemata, tana mul-mula gurin ta ce "Wai kai Abdul bakada hankali ne, kana ji ka bigeni amma ka tsaya kana kallona? Waima me ya kawoka ɗakin nann?.


Abdul da zuciya tazo masa iya wiya ya ce "Dan uwarki nikikaƙira da mara hankali? Kema zan dawo gareki idan nagama da waƴannan ƙanyan naki, yanzu bani da lokacin ki. Ina sukayi? Ya tambayeta yana mata wani kallo. Ta ce "Ban saniba. Tana faɗa ta tureshi ta bar masa gurin domin kuwa ya isheta da warin sigari. Abdul kuwa binta yayi abaya domin kuwa har yanzu maganar da Sadiya ta masa ta ɗazu tana masa zafi wai daga can muke, aikuwa sai kin faɗa min menene can. Dai-dai yabi bayan Anty Hafsat ita kuma Iya zata shiga ɗakin su zulai. Aikuwa taga Abdul nabin bayan Hafsat sai ta tsaya tana kallonsu har taga ya shiga ɓangaran Mama.



Bin bayansa tayi dan gani meya kai Abdul wajan matar can kuma.


Shiko Abdul yana shiga wajan Mama kai tsaye yake ƙo karin shigewa cikin ɗaki ko lura ma da Mama dake ƙallan sa cikin mamaki baiyi ba.


Ganin dai da gaske dakin ne zai shiga yasa Mama saurin daka masa tsawa tasan ba hankali ne ya ishesa ba zai iya shiga din. "Kai!! Abdul meye haka zaka faɗo min waje kana shiri shiga mani ɗaki koh sallama babu anya kana da hankali kuwa Abdul?"



Kafin yayi wata magana Iya ta shigo tana faɗin,"A'a A'isha bangane baida hankali ba? kema ai kinsan in da mahaukauci yake agidanna aman ba yarona ba."



Tsaki Mama tayi tana fadin,"To abinda yayi ne ai mai hankali naga bazaiyi sa ba, tayaya kawai ina tsaye yana ƙoƙarin shigar mani ɗaki wani abu ya bani ajiya ne da zai ɗauko ko miye? "ta karasa tana hararen Abdul ɗin da ya dawo wajan Iya yayi tsaye yana ta kumbura kamar wani fulawa.


Su kuma su Meenal tin shigowar Abdul din suna jin sa Meenal taso fita aman Sadiya ta riƙeta doli ta koma ta zauna tana jin haushin miyasa ma suka gudu da tsayawa tayi taga ma wai zai iya dukan tane ko miye.


Jin maganar Mama yasa suka lallaɓo suka fito, Sadiya sai rarraba ido take dan ita ma duk da tsokanar ta aman akwai shegen tsoro.



Abdul kuwa yana ganin fitowar so beyi wata-wata ba ya kwaɗa ma Sadiya mari dan tafi kusa dashi, dama kuma itace ta zageshi, yana _faɗin, "dan ubanki ni sa'an ki ne dazaku zageni ku gudu, ai daman nace muku ko gaban uwarku ne sai naci uwarku shegu masu baƙin halin uwa......"kafin ya karasa yaji an kwaɗa masa wani karfe saman kai.



Wani mugun zafi ne ya ziyace sa lokaci ɗaya dan ba kaɗan ba yaji dukan ƙarfen akan nasa, "Juyawa yayi dan gani wace shegeyace tayi masa haka, Meenal ya gani tsaye da kujerar karfe irin ta tsofin da a hannun ta sai wuci take.


Cikin ɓaci rai tace"wlh duk ranar da ka sake zagin iyayenmu sai na maka abinda yafi haka, sannan Kuma wlh sai na tona asirin uwarka kowa ma yaji yasan abinda takeyi" ta faɗa tana kallan Iya da ke tsaye baki sake ganin abinda Meenal tayi ma yaron ta.



 Umma ce ta fito jin hayanir dake tashi dai-dai lokacin da Meenal ke buga wa Abdul wannan kujerar akai.


Ganin abinda tayi ne ya hana ta ƙarasawa cikin mamaki taki bin su da kallo bata fita a mamaki ba taji abinda Meenal ɗin ke cewa wanda ba ƙaramin firgici tayi ba dajin abinda take daɗi, har ta kasa mutsin kirki ma.



Iya ko da ta juyo tana kallan Umma ganin taƙi ƙarasowa sai abin ya ƙara ƙona mata rai, ji take kamar da gaiyya ne Umma taƙi ƙarasowa tayi wa ƴarta magana ɗan, haka cikin ɓacin rai tace, "Maman Hafsat kina ganin abinda wannan marar kunyar ƴar taki tayi wa Abdul amma sai dai kawai kiyita bin mu da kallo baki ce komi ba, ni ai na a'za zaki ɗauki mataki, bayan ta fasa ma yarona kai, sannan kuma kina jin rashin kunyar da take min amma duk kin tsaya kina kallonta ko? ,nice yarinyar nan ke cewa zata tonawa asiri sai kace wace take wani mugun abu, to shikenan zamu gani dani da ku waye asirin sa zai tonu!, insha Allahu sai na nuna mata jinin da da yanzu ba ɗaya bane, kuma na rantse maku da Allah muje zuwa dani da ku shege ka fasa.




Sai alokacin ne Umma ta sauke wani numfashi kafin tace,"ta Allah ba taki ba Maman Abdul, kin tsaya kinga ban mata faɗa bane zaki fara irin wannan magan ganun maras tushi, babu abinda zamu gani dani da yarana sai alkairi insha Allahu,sannan kuma maganar tonan asiri ina mai baki haƙuri kinsan dai Meenal har yanzu yariya ce ba wani hankali ne da ita ba kuma insha Allahu bazata ƙara haka ba, aman maganar wani sai kin nuna mana miye to babu abinda zamu gani."



"Au hakama zaki ce kenan?, To shikenan tinda haka kika ce mu zuba dani da ku duk wanda ya fasa bai haifu a cikin uwar saba...kuma wlh ko yanzu yarinya ta maka rashin kunyani nace ka ci uban shegiya karka tsaya komai."Iya ta faɗa tana jan hannu Abdul dake dafe da kansa dake zubda jini duk da dai ba sosai ba aman wajan ya fashe.



*Ta Allah ba taki ba" Umma ta faɗa tana banka ma Meenal harara.



"Haba Yaya dan Allah miyasa zaki biye ma matar nan kinsan ba wani imani ne da ita ba ni dai wlh naso ki ƙyaleta mu bata haƙuri kawai a wuce wajan kar kuma tazo tayi wani abu kuma mu shiga uku kin dai san komai."



Tsaki Umma tayi sannan tace, "kullum zamu zauna muna jin tsoran ta dan kawai tana ɗiyar boka, to wlh ni kam na gaji da ita bazan ɗauki ta sakamin yara gaba da hantara ba, kamar zaman ta nake a gidanba ita ba kishiyata ba amma tabi duk ta adabe mu to wlh zan nuna mata ba tsoranta nike ba, duk abinda zatayi taje tayi Allah ya fita tinda mun riƙe Allah babu abinda zai samemu da izinin Allah."



Ita dai Mama shiru tayi dan duk jikinta yayi sanyi Allah ya shaida tana tsoran matar can, dan gani ga wane akace ya ishi wane tsoran Allah, tasan babu Allah a zuciyar Iya komai zata iya aikatawa.


Iya na shiga ɗakinta, ta saki hannun Abdul ta juyo shi gabanta sannan ta ce "Wallhi kaji kunya Allah ya wadaran irinka ƙaton banza, yanzu badan nazoba haka zaka tsaya kana kallon su har su kashe minkai? Kafin tasakeyin magana saiga Zulai da Maryam sun shigo suna tambayar abun da yafaru.


Iya ta ce "Shego iyayan son jin gulma to badaku a keyiba, nidai kuje ku amsomin kuɗaɗena a gurin tsinanan can ko yanzu na haɗaku da Abdul kuje tare ya amsomin kuɗina? Zulai tayi caraf ta ce "Wani Abdul shiɗin banza, an faɗa miki shiɗin wani na kirkine, haka fa jiya ina jinsu shida..."Kafin ta ƙarasa ya bige mata baki haɗi da cewa "Dan uwarki ni sa'anki ne? "Zulai ta ce "Ba uwataba saide ta..."Innalillahi wain'na ilahi raji'un..."yanzu a gaba kuke zagina ina jinku. Cewar iya tana kama baki... Wallhi wannan yara bayaran rufawa kai a siribane, duk irin abunda nakeyi agidannan domin na ƙwatoku daga sharrin mutan wannan gidan amma ku zagina kukayi? Ta ƙarasa tana kuka. Ta kalli Maryam wacce ke zaune tana danna waya kai kace batasan me a keyiba. 


"Maryam kuje ku ƙarɓomin kuɗaɗena tin kafin raina ya ɓaci? Maryam ta miƙe tsaye sannan ta bar ɗakin itama zulai tabi bayanta. Suna fita iya ta ce "Yanzu ai saikaje gurin Anas mai magani ya wanke maka wannan ciwon tunda kazama soloɓiyo. Ai kuwa Anty dage waje taji abunda iya ta ce sai kawai sukaji daga waje ana cewa...


"Allah ka tsareni da aihuwar ragon maza wanda matane abokan dambansa, suɗinmu ba iyawa yake dasuba... Allah ka ysareni. Ta ƙarasa da cewa..." Wata uwar tafi kishiya ban haushi.


Cikin tsakanin mamaki da ɓacin rai iya ta kalli Abdul da shima yanajin duk abunda matar uban nasa kecewa, dama sun saba tsakanin Iya da Anty, shima kuma yasaba shiga faɗan iyayan nasa. Aikuwa kafin Iya tayi magana Abdul ya nufi wajan cikin ɓacin rai....📝





Please comment And shering



 *By S REZA. & CHAMSIYA D AMADU*