Sadauki Omar

4

by @bintaumarabbale

SADAUKI!!🏹

  _OMAR💫👑_

 



Free Pege

4






 A jare suka dunga shigowa sun kai su goma mazansu da mantasu suka ja layi Kansu duka a kasa suna sauraron suji dalilin da ya sanya aka tara su


Cikin kasaita ta nufi gaban wata k'atuwar frezar ta bude ta dauko Goran ruwa mai sanyi don har ya soma kankara ma ta nufi inda yake tsaye Omar dake sunkuye da kansa 'kasa ya hangi zuwanta ta kasan idonsa ya Dan dago kansa yana kallonta lokaci guda yayi saurin dauke kansa yana me ya mutsa fuskarsa a rayuwarsa ya tsani mace mai fidda tsaraicin ta Sam bata burge shi ba. Bata Kuma bashi sha'awa ba.


Aysha na isa ta bude murfin Goran ruwan ta fara tsiyaya masa a jiki!!! Wata irin ajiyar zuciya ya saki! Ya dago jajayen idonsa yana kallonta cikin b'acin rai..... Ta watsa masa ruwan sanyin a fuska tare da tofa masa miyau! Yayi kasa da kansa da sauri jikinsa na wani irin tsuma! Na b'acin rai! Hannu tasa ta dago kansa tana kokarin kallon k'wayar idonsa yaki bata damar hakan. Dariya tayi tana Dan cizan lips dinta tace"Wawa! Jaki kawai kana tunanin abunda kayi min ya tashi a banza wallahi daga yau mun sanya k'afar wando daya dakai a cikin gidanan har ni zaka murdewa hannu ka taba min jiki da wannan kazamin hannun naka me kirci da daud'a! Wallahi daga yau sai yau kar in sake aikwaa kiran ka kazo min da wata banzar maganar ka ranar sai na Tara bayi irin ka sun mammare ka wannan shine hukuncin ka kana a matsayin bawa makaskanci kana wa mutane iko a cikin gida to baka isa ba."!! Ta k'arashe maganar tana girgiza jiki. Wasai take jin ranta ta rama abunda yayi mata Omar kansa na kasa yana jin idan mataki zai dauka kan yarinyar zai iya kakkaryata a gurin ya zubar da banza zuciyarsa sai wani irin tafasa take tana turiri.



Kofar futa ya nufa! Cikin tsawa Kulu tace"Waye ya sallame ka da zaka kama hanya ka tafi kai isashshe ko."! Yaja ya tsaya ba tare da ya juyo ba.""""" Aysha ta kalli jerin bayin dake tsaye a gurin Tace." Daga yau sai yau kar in kara ganin wani ko wata a cikin Ku ya baiwa wancan wawan! Girma duka matsayinku daya dashi Cikin gidanan kila ta wani gefen ma kunfi shi matsayi tunda Ku kuna da Asali da iyaye mun shaida da hakan tunda wasu daga cikinsu muna tare dasu shi kuwa fa tsinto shi akayi a ruwa a kawo shi masarautar nan Idan kuna tunanin ko da wata alaka tsakanin sa da wannan masarautar to babu duk Wanda ya sake bashi girma to zai fuskanci hukuncin gurin Sarkin Horo! Ina fatan kun gane."!!

 


Suka amsa da "Mun gane ranki ya dad'e." Tace"Wannan shine dalilin da ya sanya ni na Tara Ku anan kowa ya koma bakin aikinsa. "! Daya bayan d'aya suka fuce.... Ta koma ta zauna Cikin kujera tana jin wani irin sanyi a zuciyarta



Kulu tace" Kana iya tafiya idan kunne yaji jiki ya tsira. " Omar ya futa daga palon cikin tsananin damuwa gami da wata irin tsanar Aysha Cikin ransa dama shi can yarinyar bata kwanta masa a rai ba domin tun tana yar k'aramar ta take da isa da iko da wulakanta mutane Sam bata ganin kowa da daraja a masarautar saboda d'aurin gidin da take dashi gurin Uwar rik'on nata shiyasa take yin Abunda ta ga dama take yi abunda take so yau ta wulakanta wancan gobe ta wulakanta Wannan ya lura yan iskancin nata sun dawo kansa, wannan karon shine na farko shine na 'karshe Da zata daina kaskantar da mutane babu shakka sai ya bata mamaki duk sanda ta kuskura ta sake aikata masa Abu makamancin wannan sai ya nuna mata cewar mulki ko sarauta shi basu isa yasa ji tsoron ta ba, babu Kalmar da take mugun daga masa hankali idan ya tuno yake jin kamar zuciyarsa zata buga *Wawa!* wannan Kalmar tana mutukar kona masa rai yayi alkwarin duk sanda ta sake kiransa da wannan suna babu shakka ranar zai nuna mata shi din wawa ne na gaske.



Yana daf da futa daga sashen shi kuma ya sawo kai Yarima Faisal kenan kallon kallo suke wa junansu Omar ya dauke kansa ba tare da yace masa komai ba ya wuce! Rigar sa ya jawo yana fadin"Kai din jakin ina ne! Dabbah kamar ni ka had'a kafad'a da kafad'a dani ka ganni kana kokarin wuce wa ba tare da ka gaishe ni ba."!!! Omar ya fuzge rigar sa yana masa kallon Raini kafin yace." Idan zan gaisar da kowa cikin masarautar nan to kai baka isa na gaishe ka ba domin baka kai Wannan matsayin ba.'''


A zuciya! Ya d'aga hannu zai kwada masa mari! Hannun ya rike yana sakin miskilin murmushi yace." Da ka kuskura ka mareni sai na jigata ka a gurin nan sai na baka 'kasar gurin kaci! Idan kayi gangancin Dora hannunka a jikina sai na baka mamaki sai nuna maka cewar Bawa makaskanci baya daukar raini!  " Yana gama maganar sa ya saki hannunsa ya wuce cikin kakkarfan taku. Jiki a sabule Faisal ya bishi da kallo yana jin mugun takaicin da bakin cikin d'aurin gindin da ya samu dole ne ya samu mai Martaba ya shaida masa abunda ke faruwa ga dukan alamu yana so ya wuce gona da iri da mamakin abun ya bar gurin......"Mammah! Wani irin dadi nake ji wallahi yau na wulakanta wannan Dan iskan." Dariya kulu tayi tace"Duk abunda kikayi yayi dai-dai nasan kuma gaba zaiji shakkar tunkarar ki da wani abun duk sanda ya sake miki wani Abu to ki fada mun zan sa a kirashi ki kasanta shi." Alkyabatar ta dauka tana kokarin sanyawa tace"Wallahi Mommah! Na tsane shi."!! Sallamar Faisal ce ta katse maganar da za tayi ta saki fuska da fara'a take fadin"Sarki Mai jiran gadon mulki Yarima Faisal da daya tamkar da dubu yau an shigo gaishe ni kenan. "!?


Kusa da ita ya zauna ransa a bace yace." Maman! Me ya shigo da wancan bawan nan daf da zan shigo naga Yana kokarin futa. " Tace." Aysha ya 'batawa rai dalilin kenan da yasa na Tara bayi na nuna musu shi din ba kowa bane cikinmu kamar yanda wasu daga cikinsu s ganin kamar ba bawa bane shi.


Yarima Faisal ya kalli inda Aysha ke zaune lashe lebensa yayi ya tsira nata ido tana kici-kicin mai da alkyabar sa ba tun yau ba yake mutukar kaunar tsarin jikin yarinyar dirin jikinta na mutukar gigita shi. Shagala yayi da kallonta ta dago kanta suka hada ido dashi tsaki taja tana fadin"Nifa bana son kallo kai kuma kamar maye in kana kallon mutum." Ya sake lasar lebensa a karo na biyu wata lafiyayyar sha'awarta ce ke taso masa yace." Don na kalleki aibi ne? Kar ki manta daf kike da kizama mallakina ki aje a ranki baki da miji saini."


Harara ta banka masa yace." Koma ki zauna muyi magana." Ta zauna tana zumb'ura baki. Yace." Me ya faru tsakaninki dashi." ? Cikin shan kamshi ta fada masa duk abunda ya faru ya dunga jin wani irin jarabbaben kishi na cinsa jin cewar Omar din ya rike wa Aishar sa sannu har yana matsawa shi gani yake kamar ma da wata munufar yayi ba don mugunta ba yace." Amma kin dauki mataki me tsauri a kansa ko." Daga kanta tayi yace." Nima yanzu da zan shigo nan kasa kauce min yayi kafada-kafada muka hada dashi yayi kamar zai bangaje ni sai da na jawo shi na bashi lafiyayyun maruka sannan ya dawo nutsuwar sa."



Aysha da Kulu suka kalleshi cike da mamakin jin Abunda yace wai ya mari SADAUKI anya kuwa!?? Kulu tace' kayi min dai-dai maganin sarki haka nake son ka zama jarumin namiji domin rago baya iya mulki." Aysha kam dariya take boyewa tace"Anya Ya Faisal Wannan mutumin fa karfi ne dashi ina ganin bugu daya zai maka ka fadi gurin... Ka tuna dai ko shine dai ya mareka."!! Bata fuska yayi yace. " Kin ranani ko."!! Mik'ewa tayi tana yar dariya ya mike yana fadin muje muyi hira yau ina son ni dake mu tsayar da magana. " Futa sukayi tare...... Ta bisu da wani shu'umin kallo kafa daya kan d'aya ta d'ora tana girgiza kai tace"Duk zaku fi ubanku shegu 'yan iska nayi alk'awarin sai na hana Ku zaman lafiya sai na lalata Ku ina bakin cikin inga kuna walwala da farin ciki gidanan ina bakin cikin wayo gari inga bani da ko kowa a gidanan nice Uwar gida ni ya kamata na haihu na haifi magajin sarki ban haihu ba to saboda haka kuwa nayi alkwarin lalata farin cikin duk wani d'a dake gidanan idan ta kama ma nayi kisan rai zan iya mutukar bukata ta zata biya a kanku da iyayen Ku."!

Ita kadai take wannan zantukan a fili sai kace wata tababbiya.


Tofa!!






4/3/2020


BINTA UMAR ABBALE