Sadauki OmarFree

ArewaPen original

RomanceFreeOngoing

Sadauki Omar

  • 1views
  • 19chapters
  • 0audios
  • words
  • 0likes
Start reading

Share:

The story

Synopsis

Ongoing

No synopsis yet.

Sample · 1

SADAUKI!!🏹 _OMAR💫👑_*MALLAKAR:**BINTA UMAR ABBALE🍎*Bisimillahir rahamanir rahim.ARASHI 'kirkirarran labari ne daga ni marubuciyar banyi don inci zarfin wani ko wata ba Wanda yaga yayi dai-dai da yanayin na rayuwarsa to a rashin sani ne.*GARGADI DA JAN KUNNE!*Ban yarda wani ko wata ya juya min yanayin labari na ta ko wace siga ba ba tare da izina ne ba ban yarda ka/ ki siyar min da littafi ba duk Wanda yayi d'aya daga cikin biyu na barshi da Allah!*SADAUKI! OMAR*Kai daga jin sunan littafin kasan ya tsaru zai kuma bada ma'ana Ina ma'abota karatun littafan Hausa kuyi maza Ku garzayo ku samu naku littafin SADAUKI OMAR yazo muku da sabon salo mai sanya Ku nishadi ilimantar wa fadakarwa nishadantarwa duk a cikin wannan littafin babu shakka! Wannan daban yake da sauran!! *SADAUKI OMAR🏹* Iya sarauta iya mulki tsantsar soyayya muskilanci bakin kishi! Bak'ar gaba! Tsananin jarumta!!! Duk a cikin wannan littafin kar ku sake abaku labari!!!!Free PegeMasarautar KANOCikin wata 'kwaleliyar rana na hangoshi tsakiyar filin motsa jiki ya na sanye da 'bakar vest had'e da wani bugujejen wando mao dogon madauri vest din ta matse jikinsa sosai kamar ma taso yi masa kadan saboda yanayin halittar jikinsa mutum ne murd'adde 'kakkarfa! Wanda ko daga nesa ka hangoshi zaka shaida hakan wani 'katon 'karfe me mugun nauyi yake d'agawa yana saukewa gumi sai yanko masa yake daga ko wace ga'ba ta jikinsa. Duk girman gurin shi kadai ne tsaye daga can sama kuma ko wace baranda ka kalla mutane ne keyawe da ita suna kallonsa kana kallon fuskokinsu zaka fahimci jarumtar *Omar* din na burge su.Cikin isa da kasaita take tafiya tun kafin ta 'karaso jama'ar da sukayi dafifi gurin le'kensa suka fara kaucewa suna zubewa 'kasa hade da sunkuyar da Kansu suna mik'a gaisuwa gare ta, ko kallonsu bata yi ba ta wuce tana ya mutsa fuska wata baiwa na biye da bayanta. Can karshen barandar ta 'karasa ta d'ora hannayen ta akan 'karfen tare da rankwafawa jikin 'karfen tana 'kare masa kallo. Minti biyu ta d'ago kanta tana jan siririn tsaki! Ikilima dake tsaye kusa da ita tace"Allah ya taimaki Uwar dakina ko a dauko abun zama ne."? Girgiza kanta tayi da kyar tace"Kira min Tafida." Da sauri Ikilima tace"Angama ranki shi dad'e."Can 'bangaran maza ta nufa minti uku sai gasu tare da Tafida ya zube kasan gurin yana kwasar gaisuwa ba tare da ta amsa ba tace"Je ka kira min wancan Wawan."! Tafida ya kasa fahimta Wanda take nufi cike da ladabi yace." Ranki shi Dade ban fahimci Wanda kike nufi ba." Filin gurin ta kalla har yanzu yana nan yana abunda yake ta 'kara Jan tsaki a karo na biyu Cikin 'yar tsawa tace"Ina na kalla yanzu. "!? Tafida yace." Filin Hazo!  Kauda kanta tayi ba tare da ta sake cewa komai ba. Tafida ya mike jikinsa a sanyaye ya bar g...

Continue reading free chapter

Contents

Table of contents

Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.

chapters19
premium4
16

16

Premium
Updated 8 months agoAvailable now
17

17

Premium
Updated 8 months agoAvailable now
18

18

Premium
Updated 8 months agoAvailable now
19

19

Premium
Updated 8 months agoAvailable now

Continue in the ArewaPen app

Unlock offline reading, audio mode, and sync your bookmarks instantly.

Download on the App StoreGet it on Google Play