Sadauki Omar

5

by @bintaumarabbale

SADAUKI!!🏹

  _OMAR💫👑_

 



Free Page

5




 Can cikin wani lambu na hango shi zaune saman wani dutse hannunsa rike da wani Abu sai Dana na karasa gurin sosai na gane kome nene *Shisha* ce yake sha'kawa a bakinsa idonsa ya kad'a yayi jawur dashi! *Wawa* Kalmar da take ta yi masa yawo a kwakwalwar shi kenan....."Duk San da na sake aikewa a kira ka kaki zuwa sai na dauki mataki a kanka."!! Wannan maganar ma tayi mugun tsaya masa a ransa, Kansa yake girgid'awa yana zukar *Shishar shi* yana kuma tunanin wane irin mataki zai dauka kan yarinyar.

****


K'arfe biyu na dare masarautar tayi shiru ko ina haske tarwai!! Sautin kukan tsintsaye sai tashi yake, dai-dai Wannan lokacin ya futo daga d'akinsa yana sanye da dogon wando na bakin yadi sai bak'ar vest wacce ta matse masa jikinsa kamar zata yage wani farin Abu ya nannad'a a kansa babu tsoro a tattare dashi ya fara bin sa'ko da luku na sashen da yake..... Futa yayi yq nufi sashen Sarki yayi dube-duben sa kamar yanda ya saba duk daren duniya haka yake bin ko wane sashe na masarautar Yana dubawa saboda tsaro da kawo zaman lafiya ko Sarki bai San yana wannan aikin ba daga shi sai Allahn da ya hallice shi. Motsi yaji yayi saurin yin lamfo makalewa yayu jikin bango har suka wuce yabi bayansu a hankali har suka futa harabar masarautar...... Baiyo ta tsunga ta fara ha'ka sai da yayi zurfi sannan tace"Allah ya taimako Uwar dalina duba ki gani zurfin sa ya isa haka."""" Kulu ta durkusa gurin taba le'kawa tace"Zurfin ya isa haka. Wani Abu ta kwabto a jikinta ta tusa Cikin ramin tana fad'in" Aysha ki tafi uwa duniya ki zama gagararriya ki zama fandararriya ki dauko abun magana ki shiga uwa duniya! Tana gama sambatun surutan tafara mai da k'asar gurin..... Dake gurin tsit!! Yake yasa duk yaji abunda take fada mamaki yake sosai wannan wace Aysha ce ake jefan ta da wannan sharrin! Mik'ewa suka tare tace"Baiyo gobe Idan Allah ya kaimu tun kafin sanin mutane ya bayyana kiyi kokon rufe gurin nan saboda tsaro."! Tace"Zan yi insha Allah da wuri zan futo in rufe gurin."



Da sauri ya Dan matsa daga inda yake sai da ya tabbatar da wucewarsu ne ya karasa gurin tsugunawa ya sanya hannu wasa duk biyun ya kwakule k'asar gurin Abunda ke bunne yw dauko ba tare da tsoro ko fargaba ya mai da k'asar gurin ya bar gurin hannunsa rikayan abun.




Ya jima yana mamakin lamarin Yanzu dama duk kauna da so da take nunawa yarinyar Ashe duk na karya ne lallai dole ne ya kara saka ido sosai kan lamarin gidan don ya lura matar bata da imani ko kadan.



Washe gari da safe ya nufi wani kebantaccen guri ya fara bude abun wani irin wari yaji ya bugi hancinsa yayi saurin rufewa ashana ya kunna ya cinna kan abun ya mike daga gurin gefe ya ja ya tsaya yana kallon yanda wuta take ci sosai abun har maiko maiko yake kome ye dalili oho sai da ya tabbatar ya k'one kurmus sannan ya bar gurin.


Daf da zai futa ne ita kuma ta dawo Kai domin shiga gurin dake k'aramar kofa ce sai aka rasa wane zai ratsewa Dan uwansa gabanta ne yake fad'uwa ganinsa taja tsaki tare da fad'in"Kauce min daga hanya Wawa bakauy.....

 Kafin ta karasa ya matse ta jikin bango ya danne kirjin ta da nasa da kyar take nishi idanunta sunyi jawur! NASA idanun yw zuba mata yace." Don ubanki! Waye Wawa."!? Bude baki tayi zatayi magana yasa hannunusa ya bude bakinta cizo ta kai masa ya take mata k'afafu sunkuyawa yayi ya debo k'asar gurin ya cusa mata a baki ya maida bakin ya rufe GAM da tafin hannunsa Aysha ta dunga sakin wani irin nishi nw azabar da yake gana mata yabi ya danne mata k'irjinta da nasa kirjin nonowanta sai zafi suke hawaye ne ya tsinke mata tana ji kamar ta saki fitsari



Ya tsira mata jajayen idonsa a murtuke yace." Dan ubanki waye Wawa."! ? Shiru tayi tana kifkita ido


Yace." Idan kina yiwa wasu iskanci da rashin mutumci ki kwana lafiya ni baki isa kiyi min in kyaleki ba ke baki da takidi sai na cin zarafin mutane! Shin kin San yanda Ubangiji yake karrama bawan sa kuwa ? Dame kike takama da har kike wannan abun? Na tabbatar da cewar da ubanki ne kan kujerar mulkin nan Abunda zakiyi sai ya wuce haka! To ki kiyaye ni wallahi ni nan da kika ganni nafi wuta zafi domin bana ta'buwa idan kika ce jurin ki ki shiga gona ta to babu shakka kina cikin hadari don sai na illata miki rayuwa shashasha Mara kamun kai mace mai futar da tsaraicin ta."!!! Janyewa yayi daga jikinta ya matsa gefe yana watsa mata makskancin kallo! Hawaye na zubo mata tace"Allah ya isa bakin mugu an kira ka da azzalimi an kira da *Wawa* kome zakayi Kay...... Kafin ta karasa ya dauke ta a kafad'a ya sa'bata ya nufi cikin gurin da ita ihu! Take tana dukan bayansa tana ciza tana harbe-harbe kamar da dutse take bai ko saurareta ba ya nufi ma tattara ta kadangaru manya manya-manyan tsofaffi yana zuwa ya jefa ta a gurin dake rami ne kuma yana da Dan zurfi sai ciyayi a gurin ta kwala wata razananniyar 'kara "Wayo na shiga uku."!!! Ko juyowa baiyi ba ys bar gurin..... Aysha nuffashinta ya fara sama jangwala yen kadangaru suka fara bin jikinta suna shiga riga idan da akwai abunda Aysha ta tsana bai wuce kadangaru ba ko karamaye ne bata kaunarsu ballanta iyayen su...... Daf da zai futa daga gurin ya sake jin ta saki ihu! Wanda yafi na dazu amo! Zuciyarsa tace koma ka gani ko Yanzu ka bata horo.... Yana isa ya ganta a sume har wani lafcecen kadangare yayi nasarar shigewa Cikin alkyabarta da sauri ya shiga gurin ya dauko ta ya futo shimfid'e ta yayi gefen gurin ya dauki wata buta dake gefe can gurin famfuna ya nufa ya taro ruwa ya dawo daga tsaye ya dinga sheka mata ruwa ta bude ido a furgice tana buge buge hade da sakin ihu!! Kamar sabuwar mahaukaciya gefe ya tsaya yana kallonta yana sakin miskilin murmushi, a dumauce ta mike tsaye dalilin wani irin gazar-gazar da take ji jikinta tafiyar kadangare ce alkyabbar take kokarin cirewa tana kuka Mara sauti sannunta ya danko mata jelar kadangaran ihu!! Ta kurma tayi kansa a guje d'afe jikinsa tayi tana ihu! Hade da zillo ya watsar da ita kasa gefe yaja yana hararata a gigice ta fara watsi da kayan jikinta yayi inda kadangaran ya samu nasarar fad'uwa kasa taja baya da sauri jikin ta sai kyarma! Yake duk da taga fad'uwar gadan garan bata yarda ba cigaba tayi da cire kayan har vest ta tsaya daga ita sai biriziya tana waige-waige zufa sai keto mata take, ganin tana kokarin yin tsirara a gabansa yasa ya bar gurin da sauri sai ya mutse fuska ....... A guje! Ta bishi ta d'ane bayansa tana kuka. Yana jin yanda zuciyarta take bugawa fat! Fat! Fat!! 








4/2/2020


BINTA UMAR ABBALE