7
SADAUKI!!🏹
_OMAR💫👑_
Free pege
7
''Fada tayi shiru kafin Mai Martaba yayi gyaran murya a nutse ya kalleta yace. " Nana Aysha mai babban suna Aysha matar manzon Allah (saw)ta hidimtawa ma'aiki tayi bautar aure taso manzon Allah so me tsarki Aysha ina fatan kiyi koyi da halayen Uwar muminai Nana Aysha." Tayi 'kasa da kanta cikin sanyi jiki kusan da ko wane lokacin idan zama ya had'a su da Sarkin sai yayi mata wannan nasihar.
Sarki ya cigaba da cewa"Yanzu ina zama Dan uwana ya Sanar dani abunda yake faruwa gaki ga Omar din sai ki fada min korafin ki a kansa yau fada zata fara sulhu akan Ku."
Muryar ta na rawa tace"Allah ya baka yawan nasara da tsawon rai me amfani."!! Fadar ta amsa da "Ameeeen!."" Ta cigaba da cewa"Dama ina so Abi min hakkina kan wannan baw....... Zata karasa Sarki ya katse ta ta hanyar fadin" Ashsha! Aysha wannan kalma ta daina futowa daga bakin ki Omar ba bawa ne a cikin masarautar nan tuntuni na 'yan tashi ya zama mutum mai 'yanci da iko saboda haka kada in kara jin kin kirashi da wannan suna."
Taji zuciyarta ta tsinke tana ji ma kamar ta tashi ta tafi tun ba'aje ko ina ba ta soma fuskantar matsala."
Yace."Ki cigaba da jawabin ki."! Cikin INA!INA! Tace." Dama na kawa kararsa ne don min yana jifana da mugwayen kalmomin yana kirana da lalatacciya Mara tarbiya dazu kuma ya zo kofar d'akina ya fasa glass na fito na taka Yanzu haka akwai glass cikin kafata guda."!
Sarki yace." Abunda kika fad'a daban da Wanda Dan uwana ya fada min Omar kai fad'a min gaskiyar abunda ya faru tsakaninka da ita." Aysha da galadima ransu yayi mugun b'aci wato ta tabbata kenan bai yarda da maganar su ba ta Omar din ce gaskiya saboda shine Wanda baya karya lallai al'amarin babban ne.
Omar ya gyara zama a nutse yace." Allah ya baka nasara da tsawon rai me amfani." Fada ta amsa da "ameeen."! Ya cigaba da cewa" Abunda ya faru tsakanina da ita shine......... Tiryan tiryan ya fada masa abunda ya faru dashi da ita can bayan gidan...... Rai a 'bace yake kallonta kafin yace." Aysha Ashe baki da d'a'a Ashe baki da kunya?? Kuka ta farayi tana shakar hanci da ta sani kawai take na zuwa fadar Sarki yace." Banga laifin sa ba don ya kira ki da Mara nutsuwa shin wai ma me ya shigar dake wannan gurin da yake da hadari! Tayi shiru rai a bace ya cigaba da cewa"To daga yau sai yau kar ki 'kara zaginsa karki 'kara kiransa da Wawa! Bawa makasanci ki bar ganin kina cikin gidan sarauta to watak'ila shi din da kike kira da wad'annan sunaye ya fiki daraja don haka ki kiyaye da magana ta."Tana kuka take fadin"Allah ya huci zuciyarka."! Yace." Bashi hakuri kafin in sallame ki."! Galadima ya kalleshi ransa duk a bace girgiza kansa kawai yayi hukuncin da ya dauka Sam baiyi masa ba. Sanin da tayi da cewar Sarkin baya maimata magana yasa ta kalli Omar din hawaye na zubo mata tace"Yi hakuri."! Mai Martaba yace." Sunansa zaki kira ki bashi hakuri.... Tace"Omar! Yi hakuri." Wani irin yanayi yaji a jikinsa lokacin da yaji ta ambaci sunansa *Omar!* kamar a bakinta a ka rad'a sunan. Yaji wani irin motsi da 'kasan keyi sha'awa na ta so masa abun ya bashi mamaki K'warai da gaske ya kasance saboda tsananin jarumtar shi da tsantsenin sa yasa kwata kwata baya tsayawa yayiwa mace cikkaken kallo saboda kar ya d'arsa wani Abu Cikin ransa yana ganin mata duka kayan damuwa ne gani yake zai iya rayuwarsa shi kadai a haka amma ganin da yayiwa Aysha a dazu ya sauya masa tunaninsa jin muryar ta a yanzu ya sanya yana jin wata gawurtacciyar sha'awa na yunkuro masa.
Mai Martaba yace." Yanzu kina iya tafiya amma kafinan ina fatan kin dauki nasihar da nayi miki ina so kiyi min alkwarin baza ki kara ba daga yau."
Tace." Insha Allah zan kiyaye." Yace." Allah yayi miki albarka." Maga takarda yace." Zaki iya tafiya Gimbiyar mata Sarki! Ya sallame ki." Ta mike jikinta babu kwari ko na kwabo.
Omar ya nemi izinin tafiya sarki! Ya hana shi yace." Ya zauna yayi zaman fada shima Omar yaji dadin hakan don haka sai ya zauna aka cigaba da tafiyar da al'amuran fada dashi.
*******
Washe gari ta kama Juma'a ce tun safe ma'aikatan gidan ke aikace-aikace Omar dama akinsa kula da dokona ne yana gama kula Dana sashen su ya futo ya nufi wani keban taccen fili Wanda dokona ke daure a gurin sun kai su Dari ko sama da haka d'aya bayan daya ya shiga ya dudduba su ya basu abinci da ruwa ya futo daga gurin wanka yake so yayi domin ya futa bakin masallaci yaga abunda yake wakana a gurin duk da cewa akwai jam'an tsaro sosai hakan baya hanashi kaikawo tsakanin masallacin da Cikin gidan duk domin a samu a sallaci sallah juma'a ba tare da wata tarzoma ta tashi. Yana daf da shiga sashen su Ikilima da Atika ne tsaye duk suna cikin kaya irin daya da alama uniporm ne hannunsa rike da tsintsiya sai kus-kus suke suka hangi tawowar sa da sauri ko wacce ta kama aikin gabanta yana zuwa gurin ya bata fuska kamar zaiyi magana sai kuma ya FASA ya wuce sai da suka ga shigewarsa sannan suka saki ajiyar zuciya Atika tace"Zo mu bar gurin nan. " hannunta taja suka bar gurin suna tafiya suna kara maganar Ikilima tace"Allah da gaske nake lokacin Dana shiga gurin babu kaya a jikinta shi kuma naga ya futo daga gurin."
"Ikilima ki daina wannan zancen ina ji zuciyata kamar zatayi binduga kishi nake wallahi ina sonsa da gaske." Ikilima tace"Atika ki kama kanki fa bana son wani Abu ya faru dake."
A Dan fusace! Tace"Kamar yaya? Shin ban kai matsayin da zai aure ni ba? Kar ki manta fa da cewar matsayinmu daya dashi a cikin masarautar nan bawa ne nima baiwa ce gwara ni akwai iyayena cikin gidan shi kuwa fa? Ikilima tace"Duk da haka dai ki kama kanki kin San yafi mu 'yanci a gidan." Atika tace"Aikuwa ina son sa bazan cuci kaina ba idan ta kama ma na fada masa zai fada masa ne." Girgiza kai Ikilima tayi tace"Shikkenan ai." Can cikin gidan suka nufa suna cigaba da maganar.
****
Tsaf ya shirya cikin wani farin yadi mai sauki kudi dinki Riga da wando rigar tazarce har kasa da botira hannun matse da links yanda yadin yayi masa kyau sai ka dauka da cewar me tsada ne saboda yana ya amshi jikinsa takalmi rufaffe ya sanya kafafunsa ya dadura kwallinsa a ido k'wayar idon ta kara girma da shek'i saukakken turaran shi ya fesa ya sanya takalmi baki mai gidan ya tsa a nutse ya futo hannunsa rike da carbi mai maddanai babbar kofa ya nufa domin futa daga gidan.
Tana tsaye jikin window ta hangi futowar sa tun da al'amarin ya faru ta kasa samun nutsuwa haka ta kwana batayi baccin kirki ba tsabar bakin ciki da damuwa kasa dauke idonta tayi da kansa ta dinga kallonsa yana tafiya a nutse bayin dake aikace-aikace a gurin suna ta gaishe shi sai kace wani basarake! Tsayawa yayi suna magana da Yunusa jikinsa ya bashi ana kallonsa yana d'aga kansa ya hangeta jikin tagar dakinta cikin wata irin rikar bacci cotton ta futo mata da shatin jikinta gashin ta duk a hargitse da sauri ya dauke kansa yana Jan tsaki. Ita bata kunyar futo da jikinta waje. Itama tana ganin sun hada ido ta saki labulen komawa tayi tq zauna kan gado ta rufe fuskarta da tafikan hannaye ta wani irin ciwo kanta yake mata babu irin tunanin da batayi ba akansa na yanda za'ayi ta dauki mataki idan ta tuni nasihar mai Martaba sai taji ta sare amma fa ta dauki alwashin komai daran dadewa sai ta rama wulakacin da yayi mata.
****
"Safara'u kina ina ne."? Ke Safara'u!!! Yarinyar da aka kira da wannan sunan ta futo daga wani daki wanda ko labulen arziki babu tana zumb'ura baki tazo ta tsaya gabansa " Gani."!! Ta fad'a kamar bata so." Hannu yasa yana laluben sandar sa yace." Kina sane da cewar yau juma'a ko? Jikina na bani lokacin sallah ya gabato."! Hannu ta sa ta dauko masa sandar tasa ta mik'a masa tana fad'in" Baba kai ba ido ba kace dole sai kaje massalaci ni wallahi yau bazan maka jagora ba ka tafi kai kad'ai."!!! " Buhun Ubanki! Safara'u."! Ya fada yana kokarin kai mata duka da sandar duk da baya ganinta yace." Sallahar juma'ar kike min bakin ciki na samu." Tace"Ni baba ba haka nake nufi ba kawai nafi son ka daina yawo ka zauna a gida Yanzu idan muje massalacin nan haka mutane zasuyi ta baka sadaka kana 'kar'ba kamar almajiri." Yace." Safara'u!! Zanci kaniyar ki fa! Mik'o min buta in d'aura alwala zuwa massalaci babu fashi." Ta wuce tana kunkuni "Ni nagaji kawai mutane sai su dinga baka sadaka kana karba ni kuma jama'a nayi min kallon yar jagora ni dai Umhum! Umhum!!! Kunkuni take tana so tayi kuka." Yace." Karkiyi kuka Safara'u nayi miki alk'awarin yau bazan tsaya karb'ar sadaka ba ana idar da sallah sai mu tawo gida.".
Ruwa a buta ta mik'a masa ya fara alwala tace"To naji dadin haka baba bari inyi sauri inyi wanka." Yace." Maza kije kiyi gashi nan ana kiran farko." Ruwa ta jawo a rijiya ta shiga band'aki minti biyar har tayi jika-jikanta ta futo." Dakin da ta futo dazu ta shiga tana shirya wa Safara'u yarinya 'yar shekara goma sha uku kenan yar Fulani me tsamurmurin jiki abun mamaki tana da Wannan k'ananun shekarun har ta fara kirgan dangi gashinan sunyi car-car dasu Riga da siket ta dauko na wata kodaddiyar atampa yaluwa ta dauko siririn mayafi da tattare ta yafa tana futowa ta taddashi a tsaye yana lalabar bango bulallan takalmin ta tasa ta kama sandar ta tsaya ya sanya takalmisa sannan suka futa daga gidan a bude suka barshi sanin da sukayi babu wani kayan arziki a cikin gidan. Sai tsummo karansu.
Duk Wanda zai shigo massalacin kan idonsa yana dogare bakin kofar shiga hannunsa rike da wata k'atuwar gora idan ka kalli fuskarsa zakayi tunanin bai taba dariya ba tunda Allah ya hallice shi. Kan idonsa suka shigo massalacin tana Jan Sandar tana surutai da kunkuni hangoshi tayi tsaye bakin kofar shiga tace"Baba ga Wannan katon mutumin nan a tsaye a bakin kofar shiga cikin massalacin wallahi zan juya ni kam ka shiga da kanka tsoransa nake." Yace." A'a Safara'u daure ki shigar dani." Sakin sandar tayi ta ruga da gudu.... Sai ya fara lalube lalube yana kiran sunanta Omar da duk abunda yake faruwa kan idonsa sai ya tawo da sauri ya kama Sandar ganin yana Neman fad'uwa. Yace." Yawwa yar albarka duk da bana ganin wannan k'aton da yake furgita ki naji dadin samunsa a wannan gurin nasan zai kawo tsaro da samun nutsuwa a gurin Allah ya biyashi da alkairin abunda yake." Omar dai shiru yayi masa ya shigar dashi Cikin massalacin kebantaccen guri ya aje shi sannan ya koma bakin aiki. Yana mamakin wannan wace irin 'yar jagora ce Mara hankali
Sarki ya futo yayi hud'uba kamar yanda ya saba lokacin tada sallah nayi ya tada ikama guri yayi tsit!!! Cikin nutsuwa da kwamciyar hankali aka idar da sallah sarki yayi masiha da addu'oi kafin kowa ya fara kokarin futa daga cikin massalacin Omar kwata-kwata ya manta da Wannan makahon hankalinsa na kan jama'ar dake futowa ta kofofi gaba da baya.... Hayaniya ya jiyo daga cikin massalacin ya shiga da sauri yana kutsawa Cikin mutane kafin ya isa gurin yaji wani yana fad'in"Innalillahi wa'ina ilahi raji'un! Ai ya mutu ." Da sauri ya isa gurin kawai sai yaga Wannan makahon kwance a 'kasan gurin gabansa ya fadi da sauri ya d'ago shi ya Dora a jikinsa yana dubushi tabbas babu rai a jikinsa, nan ya soma tambayar ba'asi wadanda suke kusa dashi a zaune suka ce yazo tashi ne kawai ya yanke jiki ya fadi a gurin Shikkenan rai yayi halinsa...... Kafin kice kwabo labari ya isa kunnen Sarki Wani makaho ya mutu. Sarki da kansa yazo ya ga abunda yake faruwa take ya sanya Omar din daukar shi ya shiga dashi cikin gidan domin a suturtashi jama'a suka futo suna jajanta al'amarin.
Tana tsaye jikin wata k'atuwar bishiyar darbejiya tana jiran futowar sa tunda yake sallah cikin massalacin bai taba samun nasarar shiga ciki ba a waje yake samun guri shiyasa Daga an idar take zuwa ta kamo hannunsa Yanzu kuma tunani take ta wace kofa zata shiga asalima bata San ta wace kofa ya shiga ba da ta sani take tayi masa shimfid'a a waje kamar yanda ta saba.
Duk Wanda zai wuce ta gabanta sai taji yana fadin "Allah sarki Allah ya jikansa. Bata kawo komai ba ta dinga waige-waige ko zataga irin abokanan sa da suke zama guri daya a massalacin bata ga kowa ba, wasu dattijai ne suka zo wucewa taji suna fadin" Allah Sarki Malam Abdu Makaho lokaci yayi Allah ya jikansa ai yayi shahada." Taji gabanta ya fadi *Malam Abdu Makaho* shine sunan mahaifinta da kowa yake kiransa dashi iya saninta tasan babu wani Makaho mai irin sunan sa Wanda jama'a ke kiransa shi. Duk da take da k'ananun shekaru sai daji wata fargaba da tashin hankali ta nufi kofar massalacin tana sharar hawaye Allah yasa ba Babana ne ya mutu ba abunda take fada cikin ranta kenan.
5/3/2020
BINTA UMAR ABBALE