KI YADDA DANI

7&8

by @realeshaa

KI YADDA DANI.*

_Kishiya Ko Baiwa_ 

   _Return_



 _Na Marubuciya_ 

 *REAL ESHAA*


_WATTPAD_ 

*Realeshaa* 


 _Like my page on Facebook_πŸ‘‡πŸ»

***


 *_Ya Allah Ubangiji kajikan mahaifina ya Allah kakai haske kabarinsa ya Allah kagafar tamasa zunubansa ya Allah kajikan duk kan musulman dasuka rigamu gidan gaskiya ya Allah kasa idan namu yazo mucika da imani._*



 _Wannan littafin na kudine akan farashi mai sauki naira dari biyu seki turo da katin MTN ta wannan number πŸ‘‰πŸΌ*** tare da tura shedar biya ta Wannan number ***.ko kuma ta account dina Abdullahi Aishatu keystone bank 6030406548._



 *FREE Page 7&8πŸ–ŠοΈ* 


______________________πŸ“–Cikin karfafawa kansa gwiwa tare da yaki nin samun nasara yace"Hakika Malam na fahimci abinda kake nufi,dakuma gudun gutsuri tsoma irin na 'yan bani na Iya,kayi gaskiya domin mutum se Allah.Ya muskuta tare dacewa sede kasani duk abinda zakayi domin tserewa kananun maganganun mutane baza ka Iya ba saboda dan Adam Allah ne kadai ke iyar masa Anma ba mutum ba. saboda yanzu mutum ake kiwo ba dabba ba,mutum ba shida gadon anma yanada na maganan ka.Bari na baka kissan wani Bawan Allah Wanda meyuwa kasani,ka manta ne ,kaga idan kasani kamanta se intunasar da kai"Idan kuma baka saniba yau zan sanar dakai domin kadauki darasi aciki. _(Wata rana wani bawan Allah suna tafiya shida 'dan sa akan jakinsu.suna cikin tafiya Sega wasu mutane suna tafiya,Se suka kalli wannan bawan Allah da 'dan sa akan jaki.se 'daya daga cikin wannan mutanen yaka'da baki yace"Kai Wannan mutumin bashida imani dubi yanda suka hau kan jakin nan shida 'dan sa babu ko tausayi.Jin haka yasa Wannan bawan Allah sauka akan jakin bayar 'dan nasa akai domin gujewa maganganun mutane.Tafiya suka cigaba dayi gaba kadan se suka sake haduwa dawasu mutanen,cikin kada baki Wannan mutanen sukace kai anma Wannan yaro bashida imani kadubi yanda yahau jaki yabar babansa,na tafiya akafa.Dajin Wannan bayanin da mutanen keyi se yaron yasauka akan jakin tare dacewa Baban nasa yahau,se Baban yahau sukaci ga ba suna cikin Wannan tafiya.Suna cikin tafiya ne suka sake haduwa da wasu mutanen agaba.Cikin kada baki suma wa'annan mutanen sukace kai anma Wannan tsohon bashida imani taya ze hau jaki yabar yaro natafiya da kafa.Koda wannan Bawan Allah yaji haka seya yanke shawaran sauka akan jakin idan yaso sutafi dakafa saboda gujewa maganganun da mutane zasuyi,yayinda suke Jan jakin suna gaba yana biye dasu.Suna cikin tafiyar ne suka sake haduwa da wasu mutanen agaba.Budan bakin wa'ananan mutanen se sukace kai anma Wa'anan Uba da 'dan akwai wawaye taya zasu tafi akafa bayan ga jaki bazasu hauba!?.)_ Numfasawa Alh Ali yayi yace"Ina fatan ka fahimci wannan labarin dakyau,Badan komai na baka Wannan labarin ba sedan kacire damuwar cewa mutane zasuyi magana akan rayuwar ka.Kaga ko labarin Wannan bawan Allah mai jakin zeyi maka nuni da ba wanda ya isa ya iyawar mutum se Allah"Dan haka aduk sanda mutum zeyi Abu tofa kada yadamu da maganar mutane,yayi Abu da zuciyar sa daya.l kana yaro ki Allah yadafa masa acikin al'amuran sa.Ya 'dan tsagaita kafin yaci gaba dacewa".


Banaso ka kalleni amatsayin dangin ko kuma uba ga Ahmad.Domin yin wannan tununin zesanya zuciyar ka waswasi akan bani Sukainat.Yagyara zama tare da fuskantar su da kyau yace"Inaso ne ku kalleni amatsayin Uba kuma jigo ga rayuwar Sukainat"A yanzu danake zaune agaban Ku banaso kuyimin kallon baffan Ahmad ko kuma Wanda ke da alaka da Ahmad, Ina so Ku kalleni amatsayin baffan Sukainat,Wanda suka fito ciki daya da Mahaifinta,hakika Allah yasanya min tsananin tausayi da kuma kaunar ta araina, irin wanda ko wanne uba keyiwa 'ya'yan sa.Ya numfasa tare dacewa."Nasan dole zuciyar Ku Na cike da tambayoyin meyesa nakeson rike Sukainat awajena ko??.


Daga Ummi Har Malam Ahmadu kai suka jinjina masa alamar eh"batare dasunce komai ba.Murmushi Alh Ali yayi yace"Bari nabaku tarihina atakaice domin ina so musamu kyakykyawan Alaka atsakaninmu.Mu biyu ka'dai Allah yabawa iyayen mu nida kanina Sulaiman Wanda shine mahaifin Ahmad tun daga kan Sulaiman Allah besake bawa iyayen haihuwa ba mun tasu cikin so da kaunar mahaifan mu.tun ina dan shekara goma sha biyu mahaifinmu yamutu inda yabar mana tarin dukiya mai yawan gaske.Mahaifiyar mu ita taci gaba da kula da mu har na kammala karatu na nayi aure.Ban Dade dayin aure ba itama mahaifiyar mu Allah ya amshi abarsa.Ya zamto muna rayuwar ka'dai ci nida kanina,rufun asirin mu daya shine muna da tarin dukiya.Bayan Sulaiman ya kammala karatun sane ya fada harkan kasuwanci inda Allah yasanya mana albarka baki daya acikin rayuwar mu.Cikin ikon Allah Sulaiman yasamu mata maisuna kultum sukayi auren soyayya.Inda Allah ya azurtasu da 'ya'ya Uku Ahmad,Jamila,Samira.bayan haihuwar Samira babu dade wa Allah yakarbi rayuwar kanina Sulaiman sakamakon hatsarin mota dayayi ahanyarsa tazuwa wani taro,hakika naji rashin domin nafi sati ko abincin bana Iya daga baya kuma na fawwalawa Allah komai na rungumi kaddara komai na ya'yan sa yadawo hannuna kasancewar basu da Wanda yafini dan ni ka'dai narage musu adangin mahaifi.A kwana atashi ba wuya awajen Allah,Ahmad ya mallaki hankalinsa kana nadan ka masa dukiyarsu ahannunsa domin yaciga ba da juyawa,cikin Ikon Allah shima Allah yasanya masa Albarka a sanar'sa.A lokacin dayazo min da zancen zeyi aure nayi matukar farin ciki,kana natam bayesa yarinyar Yar waye,baya yafada min ne nasa akayi min bincike akan iyayenta.Bayan dana gama jin komai akan binciken danayi sena kirasa,koda yazo sena nuna masa banaso ya auri yarinyar dan banya ba da tarbiyan ahalinta ba.Cike da ladabi ya amsa tare dacewa insha Allah yafita hanyarta.Sosai naji dadi,kasancewar sa yaro me matukar biyayya.Kamar kimanin sati biyu yadawo min da maganan yarinyar.Sosai nayi mamaki anma sena danne mamakin tare dacewa ainayi zaton mun gama Wannan maganan.Sosai nashiga mamaki ganin yanda lokaci daya Ahmad yatashi han kalinsa kan shifa Nadiya yakeso.Ganin haka yasa na kwantar masa da hankali tare dazuwa muka Nema masa auren yarinyar.Tun daga lokacin da ya auri Wannan yarinyar rayuwar sa ta canza bakaman yanda muka san shiba.Ya numfasa tare dacigaba dacewa lokacin daya sanarmin dazekara aure bakaramin farin ciki nayiba domin kullum addu'a na Allah yakawo Matar dazata sa yadawo hanya sede kashs!!Se asannan ma abin yafi muni...


Murmushi Malam Ahmadu yayi yace"Allah sarki Allah yajikan iyayenka da kanin ka da rahma dama daukakin musulman dasuka rigamu gidan gaskiya.Ameen thumma ameen"Alh Ali ya amsa.Da murmushi afuskarsa yace"sekuma tarihina nako?Murmushi Malam Ahmadu yayi akaro nabiyu yace"Hakane kai muke sauraro.Muskuta wa Alh Ali yayi yace"Matata dayace mai suna Bilkisu wacce mukayi auren soyayya, Bilki macece mai hakuri dakuma biyayya,uwa uba tarbiya.'Ya'ya biyu Allah ya azurta mu dasu aduniya,dukan su mazane Wanda tun daga kansu bamu sake samun haihuwa ba.Mu'azzar da muzaffar,muzzafar shine Babba inda yayi karatun primary da secondary akasar sa tagado wato Nigeria, daganan kuma natura sa kasar maleshi'a yaciga ba dakaratu inda yakaranci fannin law bayan kammala karatunsa se suka dauki shi aiki kasancewar jajur cacce akan aikin sa,sede idan yasamu Hutu yazo inda awani zuwan sa hutune yayi aure Wanda ayanzu Allah ya azurtasa da Yaya Uku mata biyu da namiji.Shikuma mu'azzar akasar Spain natura sa karatu inda yakaranci fannin likitanci tabangaren mata shimade a can yake aiki,sede shi beyi aure ba kasancewar bawani shekaru bane dashi duka duka shekarunsa ashirin da biyar ne.sede inya samu Hutu yazo anma daf yake da ajiye aikin yadawo gida yacigaba da temakon Al'ummah kasarsa yanda zasu wadatu da ilimin sa". hakika ina matukar kewar 'ya'ya na,Gidan shiru baya mana dadi gashi Allah yajarabci Bilkisu da son diya mace sede Allah be bamuba wa'anda Allah yabamun ma basa tare damu.Ya gyara zaman sa tare da fuskanta Malam Ahmadu cikin gaskiya da gaskiya yace"badan komai na baka takaitaccen tarihina ba sedan inaso mukasance yan uwan juna, kuma kana da Zuciya daya nake son rike Sukainat. INA mai rokon Ku akaro na karshe dan girman Allah idan ba zan takura wa rayuwar kuba to kubani rikon Sukainat yadawo gareni nima insa mu diya wacce duniya zatayi alfahari da ita,yakarashe cikin raunin murya dan baki daya yakaraya daganin yanda suka ki amincewa a farko,gashi yafama mikin rashin iyayen sa da 'dan Uwansa...


Kai Malam Ahmadu ke girgizawa cike da kaunar mutumin aransa tare da tausayin sa.Cikin taushin lafazi danuni da tsantsan yarda da amana yace"Hakika na yadda dakai dari bisa Dari kuma Insha Allah zan baka Sukainat takoma wajen ka Har gaban abada,Allah Ubangiji yabata ikon yi muku biyayya hakika bakina be isa yafurta tarin godiya agareka ba,ayanzu Sukainat batada wasu iyayen dasuka fiku mun bar muku ita duniya da lahira tsakanin mu da ita sede ziyara.


Cike da matsanancin farin ciki Mara misaltuwa Alh Ali ya kankame hannun Malam Ahmadu acikin nasa,Malam Ahmadu jiyake kamar yamike yagoya sa saboda farin ciki.Magana yakeson yi Anma yakasa saboda tsananin farin ciki, se motsa bakinsa yake.Murmushi Ummi tayi tace"Alh mungode da kulawar ka agaremu Ubangiji Allah yabaka masuyi ma fiye da abinda kayi mana.kuma insha Allah gobe zata dawo muku.


Kai ya girgiza still hannunsa na cikin na Malam Ahmadu da har zuwa yanzu yake Adam ke.yace"a'a Nide yau nake son takoma gabana dan Allah karkuce a'a dan gani nake kamar zaku canja shawara kafin safiya kuce baza kubani ita ba.

Murmushi malam Ahmadu da Ummi sukayi ganin yanda yake rawan jiki akanta"Allah sarki haduwar jini kenan duk da tarin dukiyarsa hakan basanya shi girman kai ba suka fada cikin ransu.Cikin sanyin murya Malam Ahmadu yace"haba Alh ai babu wani canza shawara da zamuyi tunda mun riga mun baka ita.In ko hakane toh kubarni intafi da ita cewar"Alh Ali Cikin za kuwa.Kallon Ummi Malam Ahmadu yayi yace"je ki kira Sukainat din."Toh ta'amsa tare da mikewa tafita.


Da sallama tashiga dakin,jingine ta hangota jikin gadon idanunta alumshe hawaye nazuba daga kodaddun idanunta da kuka yadafar dasu.Cike da matsanancin tausayin ta ta karasa kusa da ita,yayin da akasan ranta take addu'ar Allah yasa koma wanta gidan Alh Ali yazame mata sanadiyyar farin cikin ta tare da gushewar duk wata damuwar ta!.Ahankali tadafa kafadar ta,tare da kiran sunan ta anutse.Atsorace na bude kumburarrun idanun na ina Kallon mahaifiyar tawa da ban san lokacin data shigoba.

Cikin sauri na sanya tafin hannu na ina goge hawayen dake kan fuskata,domin banaso ta fahimci kuka nake.


Murmushi mai ciwo Ummi tayi ganin takasa,tseda hawayen 'Yar tata tsawon lokaci,Yarinyar datafi kwanci acikin ranta saboda biyyayyanta abin kaunar ta mafi soyuwa daraja da kima a idanunta"Hakan yasa taji idanunta sun cika da hawaye.


Ganin hawaye akormin idanun tane yasanya ni rungumeta,cikin raunin murya tare da kokari danne damuwa ta nace" Dan Allah Ummi kada hawayen ki su zubo saboda ni!,kibari nawa ka'dai su cigaba da zubawa anma,domin sunfi cancanta su zubo a idanuna,Hannu nasan ya nashare hawaye na cikin dakewa da son kwantar mata da hankali nace" Idan har naki suka fara zuba bansan ranan daza sudena naba Ummi.Ni ka'dai yakama nayi kuka bake ba,ni ka'dai nake cikin damuwa bake ba,Damuwar dana sanya ku na tsegumin da mutanen unguwa keyi ma kadai ya isheku base kun sake zubar min da hawaye ba dan Allah Ummi na kada kijefa kanki cikin damuwa saboda ni,nakarashe Cikin wata raunanniyan murya mekarya zuciyar duk wani mai Imani.


Hawayen da Ummi ke kokarin boyewa ne sukayi nasaran zubowa baki daya kalamaina sun shigeta.Bayana tashiga bubbuga jin yanda kuka ya kufce min da karfi.Cike da matsanancin tausayina tace"Dan girman Allah Suky kiyafe min,domin nima inada laifi acikin Wannan wahalar dakike sha,A lokacin daki kace afasa auren dana amince miki da baki shiga cikin Wannan halin dakike cikiba anma se naki baki goyon baya gashi sanadiyya ta kina cikin kunci, takarashe hawayen takaici na kwaran ya daga idanunta nakin amincewa da maganan suky tun farko. Dasauri nashiga girgiza mata kaina tare da sanya hannu ina share mata hawayen fuskarta"cikin rawan murya nace"Ummi kada fa ki manta kaddara tari ga fata sannan,tun farko haka Allah yakadarta,sannan Ahmad zabi nane Baku kuka zabamin ba,bare kuce kun cutar dani.Na tabbata da ace kuka zabamin da ban shiga Wannan kuncin danake cikiba ayanzu,duk dakuwa nasan 'Dan Adam baya taba kaucewa kaddaran sa. Cike da matsanancin so Ummi tace"Ubangiji Allah ya albarkanci rayuwar ki,Allah yabaki 'Ya'ya masu biyayya tamkar yanda kike mana,Allah ubangiji yakawo miki sassauci acikin rayuwar ki,Allah yajibanci al'amuranki,Allah yamiki sauyin alkhairi, Allah ya kawo karshen zubar hawayen ki cikin gaggawa...Cike da jin dadin addu'ar data yimin nace"Ameen Ummi na Allah yajamin kwanan ki kitayi min addu'a.Murmushi tayi tarike hannu na tace"taso muje Abbanki nason magana dake,mikewa nayi tarike hannuna muka nufi dakin Abba na yayin da nakejin sassauci acikin zuciya ta hakika iyaye rahma ne,wannan addu'ar datayi min yasa naji sanyi cikin zuciya ta...



A can dakin Malam Ahmadu kuwa ganin shiru ne yasa shi,kallon Alh Ali cike da kulawa yace"Bari nadu bo su naji shiru."Toh Alh Ali yace"shi kuwa Malam Ahmadu mikewa yayi da niyyan fita.Sallamar su ta katse shi,hakan yasa yakoma yazauna yana mecewa yanaga kin jima.Cike da ladabi tace"afuwan.


Zama nayi daga gefen Ummi,Cikin girmama wa Na gaishe da su.Amsawa Alh Ali yayi Cike da sakin fuska yana sake jinjina tarbiyanta aransa...Gyaran murya Malam Ahmadu yayi tare da kallon Sukainat da kanta ke kasa cike da so yakira sunan ta.Ahankali nadago kaina tare da amsawa.Zama Malam Ahmadu yagyara tare da fuskanta ta yace"Inaso kibani Aron hankali ki,toh na amsa tare da mai da hankali na kan abinda zece.Numfasa wa yayi,kafin ya zayyane min duk yanda sukayi akan koma wata gidan Alh Ali... Shiru nayi kaina akasa narasa shin farin ciki zanyi ko bakin ciki,shin meyesa iyayen na keson nakoma gidan baffan Ahmad Wanda nakeji bani da makiyi kaf duniya sama dashi,natsanesa natsani komai nasa,!!...Muryan Ummi na ne yakatse min tunani jin tana cewa bari nadauko mata kayanta..Fita tayi ba dadewa segata da trolley da kayana acike.mikewa Alh Ali yayi yakar ba tare dacewa nagode da Wannan karrama war taku Allahu yabar zumunci.Ameen Ameen suka amsa...Jinayi Idanuna sun tara kwalla shin me suke nufi dani?, Cikin rawan murya da kafewar zuciya nace".....




```Daga Wannan page daya zankara free yakare duk mai bukatar karanta wa yabiya Dari biyun sa ya karanta,Cikin kwanciyar hankali.*** fan's and Facebook kar kibani kunya mana ya banga kuna motsa wa bane,ta hanyar siyan book dina ne zan tabbatar da irin Kaunar da kuke nuna min. I known kunfi karfin Dari biyu pls show me love``` 



 _VOTE COMMENTS SHARE_




     *_ESHAA CE~_*πŸ€™πŸ»