KI YADDA DANI

9&10

by @realeshaa

KI YADDA DANI.*

_Kishiya Ko Baiwa_ 

   _Return_



 _Na Marubuciya_ 

 *REAL ESHAA*


_WATTPAD_ 

*Realeshaa* 


 _Like my page on Facebook_πŸ‘‡πŸ»

***


 *_Ya Allah Ubangiji kajikan mahaifina ya Allah kakai haske kabarinsa ya Allah kagafar tamasa zunubansa ya Allah kajikan duk kan musulman dasuka rigamu gidan gaskiya ya Allah kasa idan namu yazo mucika da imani._*



 _Wannan littafin na kudine akan farashi mai sauki Naira Dari biyu se ki turo katin MTN ta wannan number πŸ‘‰πŸΌ*** tare da tura shedar biya ta Wannan number ***.ko kuma ta account dina Abdullahi Aishatu keystone bank 6030406548._



 *LAST FREE Page 9&10πŸ–ŠοΈ* 


______________________πŸ“–Nace"shikenan yanzu Abba kuna nufin gidan Baffa zan koma da zama?.Ahmad da matarsa suci gaba da cin zarafina suna aiban tani,shikenan zasu cigaba da kirana da 'yar matsiyacita,'yar kwadayayya,'yar maula,so kuke suci gaba da jifan mu da mugayen kalamai masu barazanan tarwatsa min zuciya!? Cikin sheshshekan kuka nace",a'a ayanzu bazan Iya juran Wa'anan kalaman Mara ma'ana ba,Na numfasa tare da fadin"Abba dan girman Allah kuyi hakuri mu ciga ba da zama a yanda Allah yaso ya gan mu kada mu butulce masa saboda be bamu dukiya ba kuce zaku kasa rukeni.Najuya kallona ga Ummi data kafeni da ido,Cikin gunjin kuka nace"Ummi nasan duk abinda kukeyi kunayi dan Ku faranta min ne!, anma naroke Ku dan girman Allah kada kutura ni wani wajen saboda tunanin dawainiya ze muku yawa na amince zanyi sana'a domin in temaki kaina anma,muddin kuka turani Nadiya zata samu damar cigaba da kiran mu damasu son abin duniya dakuma rashin godiyar Ubangiji!....Kasa karasa maganan nayi sakamakon wani irin kuka mai 'kuna daya kuf cemin,Har wani irin shidewa nake saboda yanda kukan yaci karfina...


Baki daya Shiru sukayi tare da zuba min idanu yayin da tausayi na ya mamaye ilahirin zuciyo yin su.Cikin rauni Ummi tayi kasa da kai hawayen tausayi na nazuba daga idanunta"Baki daya sun kasa furta komai agareni se ido dasuka zuba min tamkar yau suka fara kallona a rayuwar su.


Alh Ali ne yayi karfin halin matsowa kusa dani tare da dafe kai na,cike da so yace"Sukainat ki kwantar da hankalin ki Insha Allah abinda kike tunani baze taba faruwa ba,Ahmad da matarsa bazasu taba sanin cewa kina gida naba,bare har suyi miki gori,Kai koda sun sani ma basu isa su kalubalance ki akan wani Abu ba.Cikin kaushin murya,tamkar Ahmad din na gabansa yace"Ashirye nake da in hukunta duk Wanda ya tunkare ki da maganar da bata dace ba domin bazan lamunci sakarki da wulakan ciba.Ya numfasa tare dacewa,Inajinki tamkar 'Yar da na haifa aciki na,dan haka bazan taba bari a wulakan takiba muddin ina numfashi Adoron kasa babu wani mahaluki daya isa ya ya musguna wa rayuwar ki in kyalesa,zakiyi rayuwar farin ciki da jin dadi agida na zaki mance wani Abu me suna bakin ciki ko kunci.Insha Allah ba Zakiyi danasanin kasancewar ki atare damu ba _KI YADDA DANI..._ 


Sanyayyar ajiyar zuciya nasauke,tare da sanya hannu nashare hawaye na.Hakika naji dadin kalaman sa duk dacewa bawai,zuciya ta tayi na'am da komawa gidan bane anma Alhamdulillah naji sassauci sosai fiye da farko.Cike da lallashi yaci gaba dacewa"bakice komai ba daughter ko haryanzu baki yadda zaki bini bane.??Kasa nayi da kaina cike da ladabi nace"Zan bika Baffa.


Murmushi sukayi dukan su,jin na amince har suna hada baki wajen sanya min albarka"Amsawa nayi da Ameen.Wannan karon Abba nane yarike hannu na,tare da mikar dani muka fita har jikin motar,najuya zan shiga motar najuyo sakamakon rike hannu na danaji anyi.Ummi nagani cikin sanyin murya tace"Sukainat nasan ki da hakuri dakuma biyayya anma kikara akan Wanda kike dashi,Kiji kiki ji kigani ki ki gani kiyi musu biyayya tamkar yanda zaki mana kar naji karna gani kin batawa dayansu rai.Kinga kamar sabon rayuwa zaki fara agidan,ko kuwa ma ince sabon rayuwar zaki fara, dan Allah ki kula da kanki duk abinda ya dace shi zakiyi.ki kula da kanki Suky ki rike mutunci ki, kikuma kama kanki kada kice zaki sakan kance tamkar gidan Ku komai zakiyi to kiyi shi anutse,Ba ruwan ki da sanya kanki acikin abinda beshafe kiba,Idan ansanya ki acikin Abu kishiga idan kuwa ba asanya kiba toh kija gefe,tsakanin ki da 'ya'yan su mutuntawa ne dakuma girmamawa.Ina zub da hawaye nace"Insha Allah Ummi zan kula da kaina nayi miki alkawari sannan zanyi duk abinda yadace zan kuma kare kaina da mutunci na,sannan bazan shiga harkan kowa ba,Nayi miki Wannan alkawarin. 


Inagama fadin haka na rungumeta inajin kaunar ta Cikin raina tare da kewar ta da zanyi.Muryan Abba ne yakatse mu tare dacewa,Suky taho mana kun barsa yana jira.Sake ni Ummi tayi nashiga motar ina matsar 'kwallar kewar iyayena da zanyi yayin da wani bangare na zuciya ta kejin sanyi da nutsuwa na ratsa ta.Hannu Ummi da Abba na kedaga mana har mukasha kwana.


Tun da nashiga motar babu Wanda yace"komai kowa da tunanin dayake aransa agaban wani tangamemen gida Wanda yajiko da Naira yayi hong,cikin sauri mai gadin yamike ya wangale mana gate.Ya ilahi,ya lillahi nafurta asanda idanuna ya sauka atsakiyar gidan,wani irin ginine me matukar daukar hankali akayiwa gidan,baki daya fentin gidan fari ne yayin da koren ganye yazagaye ilahirin gidan(grass carpet).kaina nadaga sama ina kallon tsawon ginin,asanda yayi parkin nafito,Masha Allah nace"domin arayuwata ina matukar son gida me beni.Wasu irin fulawowi masu kayatarwa ne,suka zagaye ginin,Wanda mafiya yawa kasashen waje ne ke amfani dasu. wata kofa dana hango daga can gefene yayi matukar tafiya da imani na tamkar glass haka kofan yake,gawasu kayatattun koren ganye dasuka kawata shi.Muryan Baffa ne yakatse min kallon kauyen danake,inda yake cewa Daughter karaso mushiga mana,Cike da kunya nace"toh,kana nabi bayansa,ina mai jinjina kyau da tsaruwan gidan.Lumshe idanuna nayi tare da furta Alhamdulillah,Ala kulli halin,asanda nasanya kafana acikin falon,yayin da wani ni'imantaccen Kamshi da sanyin AC yadaki hancina,lumshe dara daran idanuna nayi akaro na biyu kana na sake budesu cike da shauki.Kujerun falon da labulayen na zubawa ido Wanda suka kasance golden color ne,komai na cikin falon kalan golden ne se ratsin fari kadan kadan"Aljannar duniya na furta akasan raina,Inama Nadiya zata zo taga Inda arziki yake,taga yanda masu arziki ke karramawa da mutuntawa,hakika duk Wanda ke wulakan ta talaka toh begaji arzikiba,anma Wanda yataso cikin arziki Sam be wulakan Wanda bashi dashi.Rungumar da akayi minne yasani dawowa hayyaci na.Ido nazubawa matar da tarungumeni ina kallon tsantsar baiwar kyau da Allah yamata,Sanye take cikin shigar alfarma,fuskarta shar da kwalliya,dakuma kayataccen Murmushi. Cike da matsanancin farin ciki tace"Alhamdulillah Allah nagode maka,barka da zuwa Autah na,hakika nayi matukar farin ciki wanda baki be isa ya misalta miki ba.Murmushi Alh Ali yayi yace"Hmm naga alamar tun daga yanzu kinfara manta wa dani saboda Autar ki tazo.Langwabar da kai tayi tamkar yarinya tace"Afuwan Dadyn Autah na, Bansan lokacin da Murmushi ya subce min ba ganin yanda suke nunawa junan su kulawa tamkar yara"lokaci daya kuma hawaye yataru a idanuna jin yace"Aikuwa nayi fushi yafada cike da so da kuma nuna shakuwa mai karfi atsakaninsu.


Dasauri nasanya hannu na share hawayen gudun karsu gani"Allah sarki duk da sun manyanta hakan behana su nunawa junarsu kulawa ba nafada akasan raina.Cike da ladabi nace"Hajiya barka da warhaka,fatan mun sameku lafiya??.Murmushi tayi tarike Hannu na batare data amsa gaisuwa taba tace"Ina so ki dauke ni amatsayin Ummi ki, wacce ta haifeki,dan haka banaso kisake kirana da Hajiya kikirani da momma kamar yanda su Auta na mu'azzar ke kirani,tafada asanda take zaunar dani akan rantsatstsun kujeran alfarma,Wanda naji tamkar zan nitse aciki saboda taushin su.Kai na jinjina cikin sanyin murya nace"Insha Allah momma.Murmushi tayi,cike da so tace"Yauwa Autah na,tafada asanda tamike daga kusa dani,Wani waje nufa na musamman Wanda aka kewayesu dawasu irin labulaye na alfarma masu daukar hankali suma golden kolor ne.Zuge labulayen tayi wasu irin kujerun dining na masu matukar kyau da daukan hankali suka bayyana,kujerune me cin mutum takwas,se babban fright dake gefe gakuma wani Mirrow da akayi mai ado na kawa,hakika tsayawa tsaro muku kyawun wajen bata lokaci ne.


Dasauri na Kawar da kaina ganin kamar zata juya,cikin dan daga murya tace"Auta na zokici abinci,cike da kunya nace"nakoshi momma.Bata fuska tayi tace"No kizo kar muyi haka dake bana son gardama,kafin ince wani Abu Alh Ali yafito daga wani bedroom sanye da jallabiya da alama mallakin sane.Yace"momman Auta barta akoshe take dan zuwa na sukaci abinci.Jin haka yasanya Hajiya Bilki cewa toh shikenan, kusa dani tadawo ta zauna tana jana da hira,yayin da Alh Ali ke sanya mana baki kadan kadan domin baki daya hankalin sa nakan system,to nima dayake bawani hiran nake ba saboda kunya da bakunta,duk yawancin hiran momma keyi.,kasancewar ta mace me saukin kai da sanyin hali.


Lumshe idanu nafara yi tare da hamma,dan sosai nake jin bacci,ganin haka yasa Alh Ali ya kalli Hajiya Bilki yace" 'yarki najin bacci yakamata kinuna mata masaukin ta taje ta kwanta.Kallo na tayi cike da kulawa tace"Autana muje ki kwanta kafin gobe kizabi part da kikeson zama,ahankali nace"Nagode Ubangiji Allah yakara girma da daukaka Ameen tace"tare da rike hannu na muka shiga bedroom din dake kusa da dining,Masha Allah na furta saboda tsaruwan dakin dake dauke da toilet din sa aciki,komai na cikin bedroom golden ne daya daga cikin bedroom din tanuna min tace in kwanta.Godiya nayi mata kana nashige, ina mai kalle kalle,kan tangamemen gadon daya sha shimfidar alfarma na kwanta ina mai lumshe dara daran idanuna yayin da zuciya ta ke cike da tunane tunane,ina cikin tunani bacci me dadin gaske ya daukeni batare Dana shirya ba wanda rabon danayi irin Wannan baccin na manta lokacin...



Ahankali nafara bude lumsassun idanuna wanda naji sunyi min mugun nauyi,dishi-dishi nafara gani kafin naci gaba da budewa ahankali harna karasa budesu tangam,ganin haske ya mamaye baki daya ilahirin dakin ne yasanyani saurin daga kaina na kalli window. Gani naye har rana tafito.Cikin sauri nashiga toilet nadaura alwala,asbah nafara gabatarwa kafin nayi raka'atanil fajir,Bayan na idar ne nashiga yin azkharul sabah,ina shafawa.Hajiya Bilki tashigo tana Murmushi itama tashafa addu'ar.Fuskarta dauke da yalwataccen Murmushi tace"Auta na kinsha bacci zuwa na biyu baki tashi ba.Kaina akasa nayi Murmushi cike da kaunar ta arai na nace"Ayyah momma Aida kin tasheni nayi sallah nafada cike da ladabi.Kaina tashafa tace"Ina fatan kintashi lafiya ya kwanan bakunta??.'yar dariya nayi nace"Ai babu bakunta momma tunda ina tare daku.Cikin jin dadin maganata tace"taso muje muyi break, toh na amsa tare da mikewa.Hannun na tarike ,muka fito,akujeran hadedden dining din tazaunar dani.Inna Lami me aiki ce takaraso wajen dasauri da niyyan serving dina momma tadakatar da ita ta hanyar daga mata hannu,Cikin mutuntawa tace"Koma kiyi aikin ki.Ni zanyi serving din ta,toh tace"kana takoma kitchen.Cheaps,da soyayyen kwai tazuba min a plate kana tahada min shayi mai kauri Kofi daya,gabana tatura tace"ci Autana,Kallon ta nayi nace"nagode momma na Allah yakara girma,tana Murmushi tace kici niban San wannan godiyar inde Har kin dauke ni matsayin mahaifiya toh kidena yimin godiya.Kai na gyada tare dacewa Insha Allah momma nadena.oya ci abinci kar yayi sanyi tafada tana kokarin serving kanta.toh nace"kana nafara ci.


Bayan mun kammala cin abinci ne nakalleta tare dacewa"momma ina Baffa,Yafita dan yanada baki da ze sallama.Allah sarki Allah yadawo dashi lafiya nace da ita.Ameen ta amsa tare dacewa,tashi muje kizabi part din da kike son zama aciki.Kaina akasa nace "duk Wanda kika zabamin yayi.'Dan bata fuska tayi tace" kinga banson gardama maza tashi muje ki zaba inda ranki keso domin bana son kizauna inda zaki takura,tafada asanda take mikewa.Ahankali nima namike nafara bin bayan ta,sede mukaje dede matakalin steps din.Tajuya takalleni tace"kozaki zauna akasa ne??.Cike da kunya na girgiza kaina alamar a'a domin Har akasan raina nafison zaman up-tsair kodan na natsaya ajikin window inga iska na kada labulayen.Hannu na data rike yadawo dani duniyar tunanin dana lula.Ahankali muke taka steps din Har muka isa hawa na biyu ya salam na furta ganin tsaruwan falon duk da be kai falon farkon girma ba anma ya tsaru domin komai na falon silver kolo ne kama daga labulayen,kushin shina dama lafiyyen kafet dake kasan falon.Katon hoton su nazubawa idanu Wanda su hudu ne ajiki,Hajiya Bilki,Baffa,sekuma maza guda biyu wanda bansan su ba anma ga alama 'ya'yan sune saboda kamannin dake tsakanin su,ko wanne fuskarsa dauke yake kayataccen Murmushi.

Matashin dake gaban su adurkushe nazubawa Idanuna ina kallon baiwar kyau da Allah yamasa,dimple dinsa daya lotsa natsurawa idanu,hakika duk kyan ya Ahmad be isa ya nunawa wannan komai ba sede suyi kunnen doki.


Murmushi Hajiya Bilki tayi ganin yanda nakafe hoton da ido,dafa kafadata tayi tace"Wannan sune 'ya'yan da Allah ya azurtani dasu,Wannan shine babban 'da na muzzafar ta'fada tana nuna min shi da hannu Wanda sukai matukar kama Alh Ali,sekuma kaninsa mu'azzar,tafada tana daura hannun ta akan fuskarsa,yayin da take shafa tulin sumar kansa tamkar shine agaban ta ba hoto ba,kallo daya zaka mata ka fahimci tayi kyewan su.


Masha Allah nace"tare dacewa toh ina suke momma??.Murmushi tayi tare dacewa suna can abroad, dazama anma nanda wata biyar mu'azzar zedawo domin ya kammala yi musu aikin dasuke bukata, tafada da Murmushi afuskarta. Allah sarki Allah yakawo sa lafiya"Ameen thumma ameen nace".


Wannan shine sashen muzzafar da iyalinsa aduk sanda yazo Hutu anan suke sauka.Duk da kasancewar yana da gidan sa anma mun hanasa komawa domin mun fiso yazauna akusa damu.zaki zauna anan? kinga idan sukazo hutu zaki samu abokiyar hira domin matarsa Huwailat bata da matsala.Dan dariya nayi nace"Eh yayi zan zauna.


Murmushi tayi tare dacewa toh shikenan muje kiga sashen karshe na Autana.Toh nace"tare da bin Bayan ta muka fara taka step din.Hannu tasanya tabude kofar falon .Masha Allah nace"ganin tsaruwan falon komai,na Cikin falon iri daya ne dana biyu kama daga girmansu Har kayan cikin sede kala daya banbantasu domin Wannan komai nasa farine.Gashi akimtse suke tamkar da mutum aciki.Jin kukan tsuntsaye yasanya ni nufar jikin window dasauri,kana nadaga labulen,Masha Allah nace"cike da matsanancin shaukin ganin garden awajen gawasu irin tsuntsaye masu daukar hankali,da swimming pool daga gefe kana ga korayen ganyayyaki iska na kadasu.


Cikin sauri najuyo da kallona ga Hajiya Bilki dake Murmushi,Cikin shagwaba nace"gaskiya momma nafasa wancan wannan nakeso.Dariya tayi tace to shikenan tunda nan din yamiki,ina Murmushi nace sosai ma momma,bedroom uku ne acikin tace inzabi Wanda raina keso,cike da farin ciki nafara bubbudewa,har nabude na karshe Wanda shima komai na acikinsa fari ne.gawasu manya flowers guda biyu dake jikin plasma da wufa.Se manyan hoton sa dake jikin bango Wanda duk da kananun kaya yayi su bakaramin kyau yayi ba,tamkar kasace sa ka gudu...


Ganin yanda nake Kallon dakin ne yasanya Hajiya Bilki cewa"ko Wannan yamike ne?Cikin sauri na jinjina kaina alamar eh"Hannu tarike tace"zomu koma kasa zan sanya lami takawo miki komai naki.Cike da kaunar ta nace"toh momma Ubangiji Allah yakara girma da Nisan kwana tana Murmushi tace"Ameen...


Bayan sallah la'asar Alh Ali yadawo bayan sa me gadi ne da manya manyan ledoji.Cikin sauri namike tare da karban karaman ledan hannunsa, nace"Barka da dawowa Baffa. Yauwa daughter ya karfin jikin?cike da kunya nace dasauki.Hajiya Bilki ce takaraso falon tare dayi masa barka da dawowa kana takawo masa ruwan sanyi da lemo.Bayan yasha ne yace"ga sakon Autar ki,yafada yana nuna mata manyan aunty jumbo da mai gadi yashigo dasu.Bubbudewa tashiga yi,dogayen riguna ne se mayafai da takalma dakuma kayan make up,se karamin leda dake dauke da waya.Inna Lami takwalawa kira tana zuwa tace"dauki kayan nan kijerawa Autana adakinta.Juyowa da Kallon ta gareni tayi tace"Kinga sakon ki ko.Jinayi idanunna sunciko da hawaye, ganin irin hallacin da mutane ke nunamin.Cikin rawan murya nashiga yi musu godiya tare da fatan gamawa da duniya lafiya,Ameen suka amsa kana sukace nabi Bayan Inna Lami da inga yanda za a shirya kayan,amsawa nayi da toh kana namike...Bayan nashiga daki na ne,nasameta tana ta shirya kayan agefen da babu komai dan baki daya gefen tulin kayan sane,Sanya Inna Lami nayi ta tattare kayan sa duka gefe daya nasanya,English Wear dina awajen. Bayan ta kammala ya nadauko wayata number Sofia nakira tare da sanar mata da inda nake,sosai tayi farin ciki tare dayi min fatan alkhairi, hira muka taba kafin muyi sallama kowa yakashe wayarsa....



******

 *BACOLORNER SPAIN.* 


Kwance yake atanga memen bahon wankan dake cike da kumfa yayin da,wata kyakykyawar baturiya wacce ke sanye da mini skirt da half best ke cu'dasa da lallausan soso,shower tabude tashiga dauraye masa jiki,yayin da Hannun ta ke yawo agaba daya sassan jikin sa tana mur zashi dasu nan wanka.Cike da Izzah yamike,cikin sauri tajanyo towel tashiga goge masa ruwan jikin sa.Hannu tasanya tana kokarin janye masa boxer,Cikin tsawa yace" Me kike kokarin yi.Cikin harshen turanci tace"Cire maka zanyi,kallon banza ya watsa mata tare da fadin"Wannan shine gargadin karshe da zanyi miki akan sake tabamim boxer yafada afusace,tare dafice yabarta a toilet din.Yana shiga bedroom dinsa ya tsaya gaban mirrow tare da cire boxer ya daura towel.Cikin sanyin jiki,tabiyo bayansa,lotion din sa tadauka tana kokarin Shafa masa yabuga mata wata razananniyar tsawa yace"fice min adaki,tunda ban isa nafada miki magana kiyi amfani dashi ba.Kuka ta fashafe dashi tare da fadawa jikinsa,cikin harshen turanci tashiga basa hakuri akan bazata sake ba.Fuska adaure yatureta daga jikinsa tare dacewa fice min daga daki bana kaunar ganin ki...Tana kuka tamike tafice daga dakin tasan muddin yafadi magana ba Wanda ya isa yasa shi yasake wani.Yana ganin fitan ta yaja tsaki,hadaddiyar wayar sa yadauka yayi Dearling wani number befi maganar second talatin yayi ba yakatse wayar tare da lumshe idanunsa.

Kamar kimanin minti ashirin da gama wayar wata matashiyar budurwa tashigo wacce bazata kai ta farkon yawan shekaru ba,cikin yauki take kiran sunan sa,Sweetheart, yana jinta yamata banza.Dagudu takarasa bedroom din tare da fadawa kansa.Ahankali yabude lumsassun idanunsa tare dayi mata nuni da kan dressing mirror,atake ta fahimci abinda yake nufi,lotion din tadauka tafara murza shi cikin wani salo,atake idanunsa sukafara canza kala zuwa tsantsar jaraba.Ganin haka yasa tahade bakin su waje daya, tare da aika masa da zazafan sakonni.Atake ezer ya birkice,mata,suka shiga aikawa da juna zafafan sakonni.Sede yasamu nutsuwa kafin yajanye ta daga jikin sa ya lumshe idanunsa atake bacci me dadin gaske yadaukesa,ita kuwa jitake Kamar ta kwalla kara dan romance ka'dai baya wadatar da ita tafison yayi having sex da ita shi kuwa baya ra'ayin zina sede romance....



 *Bayan wata uku* Alhamdulillah rayuwar farin ciki da jin dadi nakeyi agidan Alh Ali, tundaga ranan dana dawo gidan hawayen bakin ciki besake zuba daga idanuna ba sede na farin ciki,kulawar dasu ke bani ko iyayena iyakacin abinda zasuyi min kenan,musamman ma yanzu da ciki na yashiga watan haihuwar sa se tattalani suke tamkar su karba min sukeji.Ummi na da Abba kuwa muna waya dasu akai akai,domin kusan kullum se sun kirani suji ya lafiya ta.Sofi'a ma nazuwa sannan tana kirana sosai tatayani farin cikin yanda nake samun kulawa,domin momma taso mudin ga kwana tare koda na kudan dare ze tashi anma Sam naki amin cewa domin banaso in takura mata,badan taso ba ta hakura...


Tun waye war garin yau natashi,da wani matsanancin ciwon baya,da mara tun ina iya daurewa Har abin yafi karfina,gashi ayanda nake ji bazan Iya saukowa kasa ba,da kyar na Iya mika hannu na najanyo wayata na kira Hajiya Bilki.Tana ganin kirana tamike dasauri batare data amsa kiran ba dan dama tana shirin zuwa duba ni kenan kiran yashigo.Ganin kiran ya yanke ne yasa namika hannu da niyyan sake kira anna ina,nakasa koda motsa Hannu na ne sakamakon wani azabebben ciwon daya ziyar ceni...Hajiya Bilki nafita tashiga dakin Inna Lami takira ta,Suna shiga sukaga halin dana ke ciki hankalin su bakaramin tashi yayi ba musamman ma Hajiya Bilki,cikin sauri Inna Lami tajanyo hijab tasanya min kana suka rirrike ni da kyar suka iya mikar dani se runtse ido nake dan tunda uwata ta haifeni bantaba jin ciwo me tafadi 

Irin Wannan ba...


Muna fita compound din Hajiya Bilki ta kwalawa Iliya driver kira,cikin sauri ya janyo mota tare da parking agaban mu, yana parking momma suka sanya ni yaja direct asibitin dasuke zuwa ya kaimu.Muna isa aka karbeni tare da bani temako gaggawa ganin haihuwar ce gadan-gadan anna ina abin yaci tura.sun shafe sama da minti talatin babu wani cigaba da aka samu se galabaita danake.Dr ne yafito yana sharce ce gumi da hankif yace" Hajiya Bilki da Baffa subisa office, Wanda tuni Hjy Bilki takira Alh Ali tasanar masa.Bayan Dr yazauna ne yakallesu,tare dacewa duk Iya kokarin mu munyi anma munkasa temakon ta,Dole in kunason ceto rayuwar ta dana abinda ke cikin ta ayimata C'S inba haka ba za'a Iya rasasu duka muddin ba yi gaggawa ba....



Wannan shine fejin karshe acikin Free duk Wanda yake da ra'ayin karanta cigaba seya turo da Dari biyun sa domin karanta wa Cikin lumana da kwanciyar hankali. Dan Allah Ku daure kubiya base kun jira ansato antura mukuba.



 _VOTE COMMENTS AND SHARE_



          *ESHAA CE~*πŸ€™πŸ»