ZAYN MALIK

Scandal

by @maidambu41

_....ZAYN MALIK....✿_

*EXQUISITE WRITERS FORUM*

  NA

Mai_Dambu

*FREE PAGE♡*

CHAPTER-01

Scandal 💔

بسم الله الرحمن الرحمن

*Wannan littafin sadaukarwar ne ga , Aunty Mamie Allah ya saka da alkhairi Nagode sosai 😍🤩🥰 ina alfahari da samun ki a gefe na Allah ya barki da oga giwar Mata*

_ALHAMDULILLAHI YAU GANI NA DAWO A SABON LABARI ME TAKE A SAMA! INA MATUKAR GODIYA DA BIBIYANA DA KUKA YI A KALLABI NAGODE SOSAI LABARINA NA KUDI NE DAN HAKA MU CIGABA DA CANCAREWA POSTING BA KULLUM BA DUK BAYAN KWANA BIYU_

_____________________________________

SAUTIN ƘADDARA..💔

"Ya Allah kamar yadda ka nisanta sharri da alkhairi Ya Allah ka nisanta Kaltumah da Alhaji Abba Yerwa! Ya Allah kamar yadda ka raba wuta da ruwa ka raba Kaltumah da Alhaji Abba Yerwa.!"

Shiru yayi na wani lokaci, yana cigaba da had'a siddabarun shi, kafin ya d'aga wani abu a cikin keji sama, bude kejin yayi tare da juyawa ya kalli inda garwashi yake, ya tako zuwa wurin sannan ya cigaba da zagaye garwashin kafin ya zuba wasu irin tarkace wanda suka had'a da barkono da wasu itacce, sannan ya watsa su a cikin wutar kaskon. Tashi sama bayanin yayi shi kuma ya gyara rikon tsuntsuwar ya fara kiran sunan Kaltumah.

  "Kaltumah! Kaltumah!! Kaltumah!!! Ki shiga duniya, a manta dake a manta da kome naki, dangin ki da Alhaji Abba Yarwa ya manta dake ta manta da kome naki, Kaltumah ki Haukace ki lalace karki mori kowa kar a more ki, Aljani zinkidu ku tafi da ita ta shiga duniya ta b'ace kamar yadda ake binne gawa. Kaltumaaaahhhhhhh! Hhhhhhh"

 ***

KADUNA STATE

Millionin Quarters

Zaune suke sun nutsu kana ganin su kasan ba ƙaramin abu bane ya ajiye su a wurin. musamman dan matashin cikin su da ya kwanta a restchair, yana dan jijjiga shi. Kyakyawar gaske kuma shugaba a cikin su.

  Fari ne me kyau, idan ka dube shi zai iya kiran shi da Balarabe, ko irin buzayen nan, tashi yayi ya zauna yana kallon su, kafin a zare glass din idanun shi, sai da ya lumshe idanun kafin ya ware su akan dayan su, blue eyes din shi suka bayyana, har suna bada wani irin haske kamar an watsa musu oil, lashe lips din shi yayi cikin yanayin shi da yake kara tsorata abokan shi. Dan kimanin shekaru ashirin da biyar.

    Saka hannun shi yayi a cikin Aljuhun wandon shi ya zaro lighter. A hankali ya zaro mandular shi, wato wiwi. Bude takardan yayi a hankali ya murzata, kafin ya nad'e ta, ya kunna ta yana me manna ta a bakin shi, zuka daya yayi mata yana kallon su baki ɗaya. Idan akwai abinda ya tsana a rayuwar shi, shine sharri.

Zuka na biyu yayi mata ya gama da wiwin hayakin na fitowa ta hanci da bakin shi.

"Easy ZM! Za a samu mafita fa" basu gama magana ba, suka ji sarin na yan sanda. Bude idanun shi yayi cikin bakin ciki da takaici, kafin ya sake murmushi yana me kallon abokan shi da suke niman hanyar arcewa.

"ZM tashi mu tafi don Allah kar ka bari su shigo" kallon abokin shi yayi sannan ya wani dauke kai yana faɗin.

"Inji gidan uwar wa?" Dafe kai abokin yayi yana kara jin tashin hankali.

"Don Allah tashi mu tafi kaji wallahi zasu kama mu" abokin ya faɗa.

Gyara zama yayi ZM yayi yana kad'a kafar shi, bakin shi kuwa fiduwa yake.

"Don Allah kaga duk sun ware tashi mu gudu" abokin ya faɗa kamar zai yi kuka,

"Kasan dai ko cikin uwarka ka shiga ba zasu kyale ka ba, just go zan tsaya" Dabas abokin ya zauna yana kallon shi.

 Abu uku yake saka shi kaunar ZM na farko bai da tsoro na biyu kome dacin gaskiya sai ya fade shi, sai dai a mutu. Na uku mutum ne da yake da wata irin zuciya ko bashi yayi laifi ba zai tsayawa abokan shi. Bubbuga kofar da ake ya katse mishi tunanin shi,mikewa ZM yayi ya nufi kofar da zai kai shi inda ake bugawa. Rike hannun shi abokin yayi yana girgiza mishi kai. Juyawa ZM yayi da sauri ya sungume shi, bai tsaya ko ina ba sai bakin window da sauran abokan suka dira, ganin yan sanda yayi, dan haka ya sauke shi yana kallon shi,. murmushi yayi sannan ya riko hannun shi suka nufi wata kofa, dauko kujera yayi tare da nuna mishi kofar silif din dakin ya ce mishi.

"Abul Khair bi nan zan ji da su."

"Zayn!" Abul Khair ya fada idanun shi a waje.

"Zanci ubanka haura ka tafi."

"Ba zan iya tafiya na bar ka ba" inji Abul Khair,

"Ko mahaifa guda muka wallahi ba zaka bi ni ba"

Ya fada yana juya mishi baya, tunda ya fadi haka yasan halin abokin shi dan haka ya haura cikin silif din ya zauna shi kuma ya fita tare da rufe kofar dakin. Yana fita falon ya samu har sun balla kofar falon zasu shigo.

Zama yayi yana kallon su, har suka shigo yana zaune.

   Cirko cirko suka yi suna kallon shi kafin suka ce mishi.

"Zo mu wuce!"

"Kofar da kuka balla waye zai gyara min?" Ya tambaye su,.kan shi yana kasa kamar ba shi yayi maganar ba, dan Allah bai daura mishi tsoro yan sanda ba.

"Zaka tashi mu tafi ko sai mun shiga jikinka"

Banza yayi da su, ya dauki kafa daya ya daura akan ɗaya. Yana kallon su kamar ba da shi suke magana ba. Sun san halin shi da Masifar taurin kai, ko kashe shi zasu yi tunda ya daura daya akan daya da zai tab'a bin su ba, dan haka suka karya murya tare da ba shi umarni cikin lallume.

"Kazo mu wuce"

"Gidan uwar wa zan tafi?"

Ya fada yana kallon kofar da suka balla mishi.

"Ok za a gyara maka amma muje"

Kallon su yayi sannan ya dauke kan shi.

"Kunsan dai ni ba barawo bane?"

"Mun sani, zamu kai ka kamar yadda ake raka gwamna ko wani me muƙamin gwamnati."

Tashi yayi suka saka shi a matsayin su, suka fita da shi wallahi idan ka ga yadda yake tafiya da buga takama zaka rantse da Allah wani mukami ne da shi, a madadin ya shiga bayan motar su sai gashi sun bude mishi gaban motar ya shiga ya zauna, sauran yan sandan suka shiga baya, aka wuce da shi office din Yan sanda.

  Da gudu Yaran Makotan su, suka nufi gidan su.

   Da gudu yaran suka shiga.

"Assalamu alaikum, Hajiya Umma yan sanda sun tafi da Ya ZM yanzu nan" suka fada tare da kallon dattijuwar da ta sake kofin hannun ta. Cikin tashin hankali ta shiga kiran surukanta.

"Talatu!!"

"Ina kuke ne?" Da sauri matan gidan baki daya suka fito, suna kallon ta.

"Hajiya umma lafiya?"

Cikin tashin hankali ta zauna tare da fashe musu da kuka.

"Innalillahi wa'inna alaihil raji'un, Hajiya Umma me aka Miki?"

"Wayyo Zaynu na yan sanda suka kama Allah ya isan mishi Yaron da babu ruwan shi."

    A hankali sauran matan gidan suka fara juyawa suna watsewa a wurin.

"Talatu ki kira min Uban shi ya zo ya ciro shi" ciki matsanancin damuwa. Ta ce mata.

"Kiyi hakuri zai dawo Insha Allah, Kinsan baban su ya ce kar na kuma mishi maganar Zayn Malik, ban san ya zan yi ba" ta fada itama cikin damuwa sosai, babu uwar da zata so a ce nata ya lalace, sai dole amma ina ba dan haka ba yaushe Zayn zai zama haka a cikin unguwa duk da bata san abinda ya faru ba, tana da yakinin yana da gaskiya baya aikata kome sai da hujjar shi.

  Tun karfe biyu ake niman wanda zai amso ZM a hannun yan sanda har dare,

A bisa al'adar gidan idan mazan suka dawo kasuwa, dakin Hajiya Hajiya Umma suke fara shiga kafin su wuce na manta su, Alhaji Uwaisu shi ya fara shigowa gidan, dan haka aka gaya mishi. Be yarda ya shiga wurin Umma ba sai da ya tura Bashir kanin su, kuma babban Uban dakin ZM.

"Assalamu alaikum!!" Aka rangad'a sallama daga bakin kofar Hajiya Umma.

Sai da ta kunkure bakinta sannan ta mike a hankali tana daura zanin ta, ta bude kofar ban dakin ta watsar da ruwan bakin ta. Sannan ta amsa sallamar da kyar.

"Wa'alaikumunsalam" daga haka ta tashi ta koma saman kujeran ta zauna tana taunar goro hannunta dauke da casbil. Sake sallamar aka yi nan ma ta amsa. Sannan ta cigaba da abinda take.

"Umma kiyi hakuri gani nan sai yanzu na samu labarin abinda." Wani lafiyayyen harara ta wurga mishi wanda ya bashi damar hàdiye sauran kalaman ta. Suna cikin haka aka sake sallama, daure fuska tayi tam.

"Wa'alaikumunsalam" har da sauran da suke cikin dakin kana ganin su kaga Yaran ta, watsa musu harara tayi iyaka sannan ta juya musu baya tana zumbura baki.

"Umma kiyi hakuri! Insha Allah na tura Bashir ya tawo da shi. Amma maganar gaskiya ki mishi magana ya daina abinda yake domin wallahi"

"Idan ka shirya koran mu a gidan ba sai ka rantse ba, ai na jima da tanada kudin hayan da muke a gidan ku. Kawai Yaro bai da ikon yayi dan wasa jinin shi sai a shiga tsatsagar shi me ye da ake niman kama min kurwan Yaro kawai idan ka gaji da zama damu Abdulmaliku ka kare ni da Baban Umma ka huta ganin mu kawai"

Kallon sauran Yaran tayi da suka sunkuyar da kawunan su, ta zabga musu harara kamar idanun ta zai fadi ta ce musu.

"Kun wani sunkuyar da kai kamar wasu Na Allah, nan kuwa munafukai ne baki dayan ku, sai gyada kai kuke kamar kadangare yasha hantsi. Ku tashi ku bani wuri munafukan banza munafukan wofi, ku da zaku boye shi kune kuka mika shi ga yan sanda masu rusa-rusan kai kamar tukwanen shuka."

"Allah ya huci zuciyar ki" inji mahaifin Zayn Alhaji Abdulmalik Yanzu haka Bashir yana can! Amma Hajiya a mishi magana abin da yake janyowa yana tab'a martabar siyasata"

"Na kwad'a siyasar na cinye aikin banza, anya AbdulMalik anya kana kaunar Malami kuwa? Yaro karami ka mishi kawon zuga!"

"Hajiya Zayn din ne karami? Shekaru talatin da shida, sau nawa ina nima mishi aure yana ki

Office din Yan sanda.

Kallon shi ispetor na yan sandan yakin yayi, sannan ya kalli wani babban mutum da yake gefen su da wata budurwar yarinya. Murmushi yayi sannan ya mai da Idanun shi kan dan sandan.

"Officer kace me dan ban fahimci abinda kake nufi ba?"

Kallon yarinyar yayi da mutumin gefen ta ya ce mishi.

"Wannan yarinyar me suna Radiyah, tace kai ne ka mata cikin jikin ta"

Dariya yayi sannan ya juya yana kallon yarinyar, kafin ya ce mata.

"Ke!" Da sauri ta d'ago kai tana kallon shi.

"Kika ce abinda yake cikin ki nawa ne?" Yadda yayi maganar yasata girgiza mishi kai.

"Magana nake dake, kuma magana zaki yi"

"Yallabai kaga yana bude mata ido"

Wata ƙatuwar harara ya wulla mata, tare da mikewa.

"Officer ka tambaye ta na tab'a had'a hanya da ita?" Ya tambaye ispetor yana zare idanun shi.

"Mr Malik calm down! Wannan case din bana nan ne aka shigar da kara amma kasan ba zan tab'a barin wani abin kunya ya faru da kai ba, balle Alhaji AbdulMalik Zain Malami ba, dan haka ka kwantar da hankalin, kasan case din is About money by..."

Mikewa yayi tsaye ya zuba hannu a kugun shi, ya kalli Yarinyar sannan ya cewa baban ta.

"Zan kebe da Yarka?"

"Yaro bana son abin kunya" juyawa yayi gaban ispetor din ya gyada kai, mikewa dan sanda yayi ya fitar da tsohon waje, takowa yayi gaban Yarinyar yana kallon ta from toe to head. Cikin wani killer smile ya ce mata.

"Chilling yan mata let me serve you"

Cak ya dauke ta sama, tare da kallon yadda take kokarin magana.

"Don Allah ka rufa min asiri, wallahi biyan mu aka yi dan Majalisar dokokin na garin nan Alhaji Musa Me gari" wurga da ita yayi sannan ya gyara tsayuwar shi.

"Sanata ko?" Girgiza kai yayi sannan ya juya ya fita.

Daga shi sai gajeran wando da rika open chears, yana tafiya kawai zaka fahimci shi din kiran mutanen farko ne, ko ba a gaya maka ba, domin gefen hannun shi tattoo, tsayawa yayi a gaban Uban Yarinyar. Ya ce.

"Kaci Arzikin furfuran ka, da sai nayi ta kwallo da kai wallahi sai na kareraya kashin ka. Akan dan karamin kudi zaka bata shekarun ka!"

"Muje my Boy an gama na yau!"inji wani mutum da yake dauke da takardu da brifcase.

"Uncle bash kafin nan bari na fara zuwa gidan Sanata Musa Me Gari"

"That's my Boy naji kome a wurin ispetor" suna fita kuwa yan jarida suka musu caaaa.

Daga can wata yar jarida ta wurgo musu tambaya.

"Brrst Bashir Zayn Malami shin dama dagaske an jima ana zargin Mr Malik da abin kunya?"

Body guard din Brrst Bashir Zayn Malami ne, suka fara kokarin kare su.

"Zayn Malik Malami dama da gaske kai dan dan daba ne? Dama an jima ana zargin ka da Safaran miyagun kwayoyi da lalata Yan mata shin da gaske ne?" Juyawa yayi sannan ya Zubawa yar jaridar idanu.

Murmushi yayi sannan ya taka har gaban ta, duk da Brrst Bashir yana jan shi bai fasa ba, sai ya ya isa gaban ta sannan ya rike abin nad'an murya ya ce mata.

"Waye ya sani tunda kina cikin su!" Yana fadar haka ya juya abin shi, har dai tafi ya koma dawowa gaban ta ya wani fisgota sai da ya haɗa da kirjin shi.

"I like your dress, you look sexy, amma idan kika sake ba iya gidan jaridar ba hatta wanda ya tsaya miki sai na saka buldoze na binne ku da ranku make my words"

Wani shegen tsoro ne ya kamata, yan jarida basu fasa saukar shi a hoto, hakan ya shiga motar yana me kwantar da kujeran shi.

"ZM"

"Kaci kutmar Ubanka sauka a motar shege" ya fada zafaffe.

"Muje Sam" inji Brrst,

"My Boy!"

"Meye?"

    "Ka kwantar da hankalinka"

"Sam ka kai ku resident na Sanata Musa Me Gari!"

Babu musu sam ya bawa motar wuta. Suka nufi gidan sanata Musa Me Gari. Har cikin gidan ya shiga, ya samu sanata yana tattaunawa da wasu yan jam'iyyar shi. Cikin fushi ya bude motar sannan ya nufi inda sanata yake.

 Bodyguard din sanata ne suka fara kokarin dakatar dashi, cikin fushi ya mangare daya ya kuma saka kafa ya kwashe dayan.

Yana isa gaban Sanata ya riko kwalar rigar shi.

"Zayn Malik!" brrst Bashir Zayn Malami ya daka mishi tsawa, amma ina jan Sanata yayi ya nufi wurin da aka tara ruwan da agwagi suke wasa ya tsuma kan shi.

"Ban damu ba idan ka tafi gidan Yari dan ka karya wuyar dan iska mara mutunci, ko ciwo dan Allah ya saukar be dan ya kankara zunubi amma da ina da iko ahalina ba zasu yi jinya ba, kai ne zaka kai min ahali matakin bakin ciki, toh wallhi na kuma ganin haka dai na kashe banza irin ka" sannan ya cire kan shi ya cilla gefe guda. Yana tsaki,

    *Hi Habibity na fara zayn Malik sabida wasu dalilai, kuma nan da karshen wata zai zama ana azumin arfa so kwanakin Ibadat ne ba na shiririta ba! And ZM na kudi ne 300₦🔞 abu na gaba labarin zai zo yadda ba zaku yi nadamar shi ba thank you fanmily's*

PAID BOOK