MATAKIN ƘARSHE

episod 4

by @mrsfh

WASILA OMAR (MR'S F.H)

🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟

*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*

***


*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️

بِسم الله الرحمن الرحيم

~~~~~~~💞💞~~~~~~~

Jerin gwanon motoci ne sunkai goma sha ɗaya gaba ɗayan su baƙaƙe ne guda ɗaya ce fara kuma ita ce a tsakiya,da gudun gaske suke wucewa hakan yasa suka toshe titin dan kowa ya tsaya ya basu hanya dan gudun abinda ka iya zuwa ya dawo,

   

      Umguwar nassarawa g.r.a suka yiwa tsinke wani katafaren gida suka nufa da ganin gidan kasan mamallakin sa yaci ya tada komaɗa,tun kafin su ƙaraso me gadin gidan ya wangale get ɗin suna zuwa kawa shigewa suka yi saida suka gama parking kafin direban ko wacce mota ya fito sanye da uniform da yake nuna masu bada tsaro ne,zakayi mamakin ganin ko wacce mota direba ne kawai a ciki ko meye amfanin tara motocin haka da yawa oho,

    wannan farar motar suka zagaye wadda har yanzu wanda yake cikin ta be fito ba,an ɗauki kusan minti biyar kafin su buɗe kofar motar na ciki ya ziro kafar sa kafin ya fito gaba ɗaya, fari ne tas kyakykyawa dashi sanye yake da farar tishert da bakin jens,SA'AD kenan ɗa ɗaya tilo kenan a gurin shahararren ɗan kasuwan da kowa ya sani a nigeria AHMAD shugaban kamfanonin R.A.M LTD,yana matuƙar son ɗansa hakan yasa kome yake so shi yake yi ba wanda yake tsawatar masa,

     Takawa ya farayi cikin gidan wanda tsayawa faɗar tsaruwar sa ma ɓata baki ne domin gidan ya kai karshe wajen haɗuwa,wani daga cikin masu tsaron sane ya ƙaraso yana masa bayani

  "Ranka ya daɗe ƴammatan suna ciki suna jiran ka idan kazaɓa sai a fito da ragowar"gyaɗa masa kai kawai yayi yana duban agogon hannun sa kafin ya ɗago yana duban sa yace

  "indai waɗan da naga hoton sune ba wata ta zaɓa kawai abar su duka"

 zaro ido yayi yana kallon sa"yallaɓai dukan sufa kamar......."ɗaga masa hannu yayi hakan yasa shi yin shiru ba tare da ya ƙarasa ba 

  "bana buƙatar ka faɗa min abinda zanyi ba shawara nake nema ba"

  "kayi hakuri yallaɓai" 

be kalle shiba yai gaba abin shi ya shige cikin gidan,

       A ɗaya ɓangaren kuwa inspecter bashir ne zaune a offishin sa yana nazarin wasu files domin ya rasa ta yadda ze ɓullowa wannan case ɗin yau shekara biyu kenan cases tara kenan amma sun kasa samun madafa ko ɗaya,gashi da alama duk masuyi ɗaya ne tunda gashi suna bari alamar da zata sheda sune suke aikatawa,

 "Hmmmmm"ya sauke numfashi yana ƙara kallon files ɗin,

  "shin me yasa suke aikata wannan abu menene dalilin su nayi wannan abu FANSA!"abinda yazo ransa kenan

  "tabbas fansa ce suke ɗauka to fansa akan me kenan?"abinda ya shiga ransa kenan jin kansa ya fara ciwo yasa ya rufe file ɗin yana me lumshe idanun sa.

      

   SA'AD na ƙarasawa ya gansu zaune a falon gidan kowa wacce ta cakare da tata shigar irin ta ƴammatan bariki sosai suka yi kyau kyawawan ƴan mata ne guda huɗu ko wacce tana ban guri a bagen kyau,rufe ƙofar sace yasa suka juyo gaba ɗaya suka zuba masa ido,


ME KARATU BAƘARAMAR RAZANA NAYI BA GANIN SAFINA A CIKIN SU ME HAKAN KE NUFI MU HAƊU A SHAFI NA GABA DOMIN JIN YAZATA KAYA


MR'S F.H