KWANTACCIYA (2nd Edition)

Chapter 7

by @phartybb

Da safe Hashim ya wuce Kaduna bai samu damar sanar da Zaina ba, da ma kuma sun yi sallama tun daren jiya.

Ƙarfe goma Zaina tana karin kumullo Tahiru ya shigo gida, kasancewar ƴan biki sun watse ya samu Zaina saman taburma a baranda, ya zauna kusa da ita.

"Ina kwana Yaya Tahiru." Ta ce ta ci gaba da cin abincinta.

"Lafiya lau ya hidimar biki?" Ya amsa mata da tambaya.

"Lafiya lau." Ta amsa mishi da shi.

Ya miƙe don tuna aiken Hashim na safe, ɗakinsa ya shiga ya fito ɗauke da ƙaramar leda da kwali a ciki ya isa gurinta, ya miƙa mata ya ce. "Ga shi Hashim ya bada a ba ki, ya wuce Kaduna."

Kallon ledan tayi ta amsa ta ajiye a gefe, ganin haka yace. "Ki buɗe mana ki gani."

Hannunta ta cire ta wanke ta ɗauki ledar ta buɗe, ta ga kwalin waya tecno touch screen mai kyau. Ihu ta fasa da ya saka Tahiru yin baya tana kallonshi ta ce. "Allah sarki Ya Hash ɗina, nagode mishi sosai wallahi."

"Ki ƙira shi ki mishi godiya idan kin ma wayar caji, ga wannan ki sa kati." Tahiru ya ce yana miƙa mata ɗari biyar, ta amsa tayi godiya ta wuce ɗaki don nunawa Inna, abincin da ba ta ƙarasa ci ba kenan.

Da ta nunawa Inna ita ma ta ce ta mishi godiya tace to. Haka ta saka wayar caji ta fita don sayo kati.

Ka sa barin wayar tayi ya yi caji bayan ta dawo, ta cire ta saka katin ta fita ta samu Tahiru baya nan ya wuce aiki da ya samu, haushi taji ta koma cikin ɗaki ta saka wayar a caji ta fita ɗan ɗaura abincin rana.

Kusan karfe ɗaya ta gama ta kwashe a cooler ta cirewa Baba nashi da Tahiru, sai nata da Inna kafin tayi wanka ta shiga ɗaki.

Tana cikin shafa mai taji ƙara, ta kai dubanta gurin wayarta ta ga shi ne, barin abin da take yi tai ta isa gurin ta cire a cajin ta ɗauka, ta ga sunan Ya Hash a rubuce ya bayyana, da sauri ta ɗauka ta kafa a kunne tace.

"Ya Hash!"

"Yes My Zayn." Yace daga bangaren shi ya lumshe lumshashshun idanuwansa ya buɗe yana kwance saman kujera.

Ɓata rai tayi kamar tana ganin shi tace. "Ba na son sunan nan."

"Ni ma ki daina ce min Hash, kuma ba ki san naki ma'anar sunanki ba shi yasa kike son hanani." Ya faɗa mata ƙasa ƙasa cike da shauƙi.

"Ni dai bana so." Tace tana turo baki, sannan ta tayi saurin cewa. "Ya Hash na gode sosai naga sabuwar waya, Allah ya saka ya ƙara budi."

Murmushi ya yi ya ce. "Ameen Zayn, amma ki riƙe godiyarki idan na dawo zan nema."

Dariya sanyayya ta sanya mishi kawai, daga nan hira suka yi sosai da shi, har aka ƙira sallah suka kashe wayar, ta mayar caji ta saka kaya ta zauna jiran Inna don ba sallah take ba.

...

Sati biyu da faruwar haka aka fara bada admission, Tahiru ya sanar da ita ta shirya ya kaita ta karɓa ta ƙira Hashim ta sanar da shi ya ce. "Registration fa zuwa yaushe?"

"Gobe mana Ya Hash, duk na gaji ka san wahalar gurin karɓa kuwa." Ta faɗa a gajiye. 

"Sorry Zayn, da ina nan ni zan karɓa miki kin san bana so ki wahala?" Ya ce mata cikin kwantar hankali.

Cike da ƙaunar yayan nata ta ce. "Ai na sani."

"To Allah bada sa'a." Ya faɗa mata.

Ta amsa da amin ta kashe wayar suka ci gaba da tafiya. Tana koma gida ta nunawa Inna, kallo ɗaya ta mishi tace Allah sanya albarka.

Da dare ta nunawa Baba, shi ma ya mata addu'ar samun nasara.

...


Washegari ƙarfe bakwai Zaina ta tafi makaranta don fara screening da registration. Har yamma wajen karfe huɗu kafin ta samu ta rage wasu abubuwan duk ta gaji lis, ta samu abin hawa ya dawo da ita gida.

Wanka ta soma yi ta nemi abinci ta ci, tana cikin yi ta tuna da wayarta ta tashi ta ɗauka cikin jakarta ta buɗe, ta ga missed call ɗin Hashim biyar, murmushi tayi ta ƙirashi ringin ɗaya ya ɗauka ya ce. "Zayn tun kafin a fara zuwa makarantar an fara mantawa da ni."

Marairaicewa tayi tace. "Ya Hash wallahi duk na gaji, kuma a hakan ban gama ba."

"Sorry haka kowa yayi wahalar bayan wuya sai daɗi." Ya faɗa mata cike da kulawa. 

Hira suke tana cin abincinta, duk yawanci labarin wahalar da tasha yau take ba shi, har magriba ta yi ya kashe ya ce zai ƙirata da dare tace to.

Aikace-aikace kaɗan ta iya taya Inna, bayan magriba ta yi shimfiɗa ta kwanta don duk ta gaji.

Karfe takwas Hashim ya ƙirata, bayan ta ɗauka ya ce mata. "Ki min hira."


"Hira kuma ai ban iya ba." Tace tana murmushi da yake jin sautinshi har cikin ranshi. Ya furzar numfashiya ce. "To bani labari?"

Dariya tayi tace. "Bani da wani labari duk na ba ka ɗazu ai."

Murmushi ya yi ya ce. "Shikenan to in tambayeki?"

"Ina jinka." Ta ce tana sauraronshi.

A hankali ya ce. "Samarinki nawa?"

A tsorace ta zaro ido kamar yana ganinta tace. "Ai ni bani da saurayi ko ɗaya."

"Da gaske ki ke." Ya faɗa yana murmushi jin kamar a tsorace take.

Kai ta ɗaga ta ce. "Um fa."

Shi kuma ƙasa ƙasa yace. "Shikenan but soon za ki samu."

"Ni bana so wallahi."Tace tana shagwaɓe masa, da hakan ƙara narkar da zuciyarshi yake.

 A hankali ya sake cewa. "Saboda me yasa? Baki kai kiyi saurayin bane ko auren? Kina ji dai Baba Fatime ta ce za ta aurarki."

"Ni dai bana so karatu zan yi." Zaina tace tana turo baki.

"Karatu yana hana aure ko aure yana hana karatu." Ya tambayeta.

Shuru ta mishi don ta kasa ba shi amsa, ya ci gaba da cewa. "Aure baya hana karatu haka karatu baya hana aure, in har kin saka hakan a ranki kar ki damu kin ji."

Kai ta ɗaga kamar yana kallonta, haka ya dinga cusa mata ra'ayin aure in har ana karatu.

Sun kai kusan goman dare suna waya, kafin ya mata sallama zuciyarshi fari tas gani yake komai ya kusa zuwa ƙarshe.

...

Washegari Zaina ta koma makaranta don gama registration, a ranar ta gama tayi komai sai zaman jiran ranar fara lecture, da wuri ta koma gida ranar ta ƙira Hashim don ta sanar da shi, baya ɗauka ta haƙura tasan yana aiki ne.

***

Idanuwanta da suke zubar da ruwan hawaye ta buɗe ta zuba jikin ginin ɗakin da take ido, kamar akwai abunuwan da ta manta cikin abin da ta tuna na rayuwar su.

Wani hawayen ne ya taru gefen idonta, ta ka sa saka hannu ta ɗauke su ta barsu suka zuba, su kaɗai ne take jin daɗi idan ta zubar.

Ta ka sa hana kanta zubar su tun da da ta tabbatar ta kusa rasa shi, kuma ba ta ga ranar hana su zuba ba domin shi ɗin shine ya koya mata son shi. Runtse idanunta tayi ta fara tuna ranar haɗuwar su.

....


Tun bayan gama registration da sati biyu Zaina ta fara fita lecture cikin kwanciyar hankali, kullum Baba zai bata ɗari uku kuɗin mashin da na kashewa, banda nasu handout da yake ba ta duk da Hashim ya aiko mata kuɗi ta hannun Tahiru.

Cikin dangi da ƴan uwa in har Inna ta shiga sai an yaɓa mata magana ta tura ƴarta iskanci, idan ba haka ba ina mace ina karatun boko, musamman Adda Adama da Mama Hadizatu da yanzu suke da damar neman hanyar raba Hashim da Zaina.

...

Yau asabar karfe sha ɗaya da mintuna talatin sai sauri take ta shirya, don lecture da zasu yi lecture 12-2pm Gst(General studies). Bayan ta gama shiryawa ta yiwa Inna sallama ta fita.

Abin hawa ta nema wanda ya shigarta har cikin makarantar ya sauƙeta a bus stop, ta sauƙa ta biya shi tana kama hanyar hall ɗin da anan ake yin karatun.

Tururuwan ɗalibai ta tarar kowa yana ƙoƙarin shiga don an sanar lecturern yana zuwa, kuma in ya shiga ba zai bari a shiga ba.

Haka bata so ba ta shiga tsakanin ɗaliban don samun shiga, aka hankaɗata daga baya ta tura na gaba da ita da ya sashi yin gaba kamar ya faɗi ƙasa ya samu ya dai-daita kansa, ya juya don ganin wanda ya mishi haka ya masa rashin mutumci ya ganta gefe tsaye, ya dumfarota rai ɓace. 

Kallo ɗaya ta mishi ta sunkuyar kanta ƙasa, kafin ya ƙaraso yadda zai ji tace. "I'm really sorry please."

Cak ya tsaya ya kasa ƙarasawa wajenta, hakan yasa Zaina yin gaba ta samu gurin zama ta zauna.

Kafarshi yaja ya isa gurinta, bench ɗin da ba kowa na gefenta ya zauna yace. "What's your name? Mine is Moses."

Kallo ɗaya ta mishi ta ɗauke kanta, za ta tashi ta canza gurin zama lecturer ya shigo, haka ta mayar hankalinta kai.

"Na tsani musulmai da mai yin shi." Kalmomin shi suka daki kunnuwanta yasata kai dubanta gareshi, idonshi cikin nata da kallo ɗaya ta mishi ta ɗauke kanta.

Zubinsa da tsarinsa ba zai nuna maka cewa wani addini ba ne, sai ka dubi shigan jikinsa jeans da t-shirt da ya kama shi, amma kyakkyawa ne matashin saurayi da zai kai 27 years.

Tsorone ya kama Zaina kar fa ya cutarta, hakan yasa ta matsa nesa da shi cike da tsoro, don bata fahimtar komai akan karatun da ake yi, Allah-Allah take a tashi.

Attandance aka miƙa masa ya rubuta wanda yau shine ya fara rubutawa tun tsawon fara lecture na semester, ya gama ya miƙawa Zaina tsammanin duk department ɗinsu ɗaya.

A tsorace ta karɓa taga department of Economic, ta miƙawa ƴan bayansu duk yana kallonta, ganin haka ya ce. "You're not from Eco?"

Ƙin mishi magana tayi ya sashi cewa. "Ina miki magana ba kya bani amsa, tambayarki nake."

Kamar ba ta san yana yi ba ta ƙi mishi magana, ya matsa daf da ita ta juya ta samu jarumtar watsa mishi harara tace."Wai ina ruwanka da ni, ka rabu da ni mana."

Tsaki ya mata yace. "Ban taɓa tsammani zan kula musulmai ba sai a kan ki, na tsani duk mai yinta so dole kema ki kula ni."

"To ina ruwana, kuma ka daina zagar min addini saboda shi ne addini na gaskiya." Ta faɗa tana ɗauke kanta.

Kallonta yake, ya yi murmushi ya ce."I like your attitude."

Zaina takardunta ta fara haɗawa don ganin lecturer ya gama, ta kwashe ta zuba a jaka tana tashi, ganin ya fita ita ma ta yi hanyar waje da saurinta.

Moses bayanta ya biyo, tana juyawa ta ganshi ta haɗa rai ta ƙara saurinta, Allah Allah take ta samu abun hawa ta shiga.

A bus stop ta samu adaidaita ta shiga ciki, ta ce. "Cikin gari."

Yana shirin ja yabar gurin ta ga moses ya shigo ciki, a fusace ta juya tace. "Ka fita dalla wani irin abu ne wannan."

"Mai mashin muje." Moses ya cewa mai adaidaita. Shi ko yaja ya bar gurin.

Tafiya kawai suke ta juyar kanta tana kallon titi, ba ta ankara ba taji ya wafce wayar hannunta, ta kalle shi ta ga ya buɗe ya yi danne dannensa ya ɗaura mata saman hannunta, ya ce mai adaidaita. "Ka tsaya."

 Ya sauƙa ya kalla Zaina ya ce. "See you pretty, bye."


Ba ta mishi magana ba, ya ciro dubu ɗaya ya bawa mai mashin ɗin yayi wucewar shi kafin mai adaidaita yaja suna barin gurin.

Wani mashin Moses ya nema ya maidashi cikin makaranta, ya ɗauki motarshi tare da abokansa biyu da suka rakosa lecture, don jiranshi suka yi a filin makarantar.

A cikin unguwarsu ya sauƙe su, kafin ya wuce ya tsaya wani babban gida, ya danna horn da ƙarfi ga kiɗa yana tashi.

Da sauri mai gadin ya buɗe get ɗin, ya shiga yayi parking ya sauƙa ya nufi entrance na gidan. Da ƙanwarshi ya fara haɗuwa, ya dubeta da ƙananan kaya kanta duk attachment ya ce. "Sai ina?"

"Gidan Uncle John yau birthdayn twins." Ta ba shi amsa."

Kai ya ɗaga mata ta wuce, shi kuma ya shiga ciki, ba kowa falon gidan ya nufi ɗakin Mommynsu ya tura.

Tare da ƙaramin ƙaninsu ɗan shekara tara ya sameta zaune saman darduma, da alama sun idar da sallah ne tana addu'a yana amsawa.

Tsaki yaja iya karfin shi da ya jawo da hankalin Momy da Jawad, suka kalleshi ya fita tare da buga ƙofar da ƙarfi, ta girgiza kai tana mamakin halin ɗan natan da ita ta jawo masa komai, da ta bi bayanshi a baya da duk haka bai faru ba.

Moses ɗakinsa ya wuce, ya shiga bathroom ya sakarwa kansa shower, ya fito ya faɗa saman gadonshi wani bacci ya ɗaukeshi.

...


Zaina tana isa gida ta samu Inna ta gama abinci, alwala tayi tai sallah azahar ta ɗiba nata tana ci, ta jawo wayarta a jaka tana dubawa ta ga missed call ɗin Hashim ta ƙira shi, bayan ya ɗauka tace. "Ya Hash nayi missing ɗinka, ka ƙi dawowa na ganka."

"I miss you too My Zayn soon za ki ganni, ya karatun?" Ya faɗa cike da nishadi.

"Uhm sai wahala, ka san me ya faru ɗazu." Ta faɗa mishi tana son faɗa mishi abin da ya faru. 

"No sai kin faɗa ƴan matana." Ya faɗa mata. 

Har za ta buɗe baki ta sanar mishi wani abu ya hanata, tayi saurin rufe bakinta ta canza hiran tace. "Ba wani muhimminci ne da abin da zai faɗa maka ba, bar shi kawai."

"Hakane?" Ya ce yana murmushi, yasan wani shirmen tayi.

Kai ta ɗagata ce. "Eh mana, ni dai ka dawo, in kuma ba haka ba za ka ganni na zo maka."

Dariya yayi yana shafa gashin kansa dake fitar da ƙamshi, ba ta san ya fita buƙatar ganinta ba ya ce. "Ina kan hanya ki saka a ranki za ki ganni koyaushe."

Hira suka yi sosai tana mamakin kanta da ta iya ɓoye masa abin da ya faru, amma in ta tuna ba wani muhimminci ne da abin ba sai ta bari.

Ƙarar da ya yi ta damunta suna waya da Hashim ne yasa ta mishi sallama, ta duba ta ga sabuwar number ne, kamar ba za ta ɗauka ba ta ɗaga tare da sallama.

Daga ɗaya ɓangaren bai amsa ba yace. "Kina magana da Moses, fatan kin isa gida lafiya."

Shuru tayi tana mamakin ina ya samu number nata, sai kuma ta tuna ɗazu ya wafce wayarta. Haka ta ƙi ba shi amsa, karshe ma tsaki ta yi ta kashe wayar. Daga haka ma ta kashe wayar gaba ɗaya wani haushinsa ne ya kamata.

Mutumin da yace ya tsani musulmai da musulunci kuma me zai ƙirata ya faɗa mata.


Don mallakar sabon littafina GOBE DA NISA. #300 2028167156 

First bank Fatima Bello Bukar 

Evidence of payment ***