FreeArewaPen original
KWANTACCIYA (2nd Edition)
- 1views
- 17chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
About the author
Army of BTS馃挏
Sample 路 Chapter 1
Hidimar biki ake cikin ahalin da ya zamto su ne cikin unguwar daga farkon layi har karshenta. Ahali ne da iyaye da kakanni suka tara a gurin wanda yawansu ya zamto sun 茩wace unguwar kusan gaba 蓷aya. Tsakaninsu suke aurarwa basa bawa bare, don yawansu da kuma 茩in bare da ya zamto hakan cikin zukatansu yake tun iyaye da kakanni. Ahali ne babba manya da yara, 拼a拼a da jikoki kowa hidimar bikin yake da gobe za'a 蓷aura auren 拼an uwan junan....Tun da ta tabbatar da gaske auren fa za ayi ba fashi ta ji hankalinta ya tashi duk da kullum cikinta take, ya za tayi to? Dabararta ta 茩are? Ta gudu kawai tabar gidan shine mafitarta, to wani hali ahlinta zasu shiga?Ta musu bayanin sun kasa fahimtarta? Ta ro茩esu, tayi kukan tayi jinyar duk sun kasa janye 茩udirunsu a kanta?Buga 茩ofar 蓷akin da aka yi take, tana kwance kamar kayan wanki shi ya sata bu蓷e kumburarrun idanuwanta ta kalli 茩ofar, kamar ba za tayi magana ta bu蓷e dishashshiyar muryarta tace."Waye?""Ni ce nan Innarki?" Muryar mahaifiyartan ya ratsa dodon kunnenta wanda ya sakata ta tashi daga kan gadon ta nufi kofar tare da bu蓷ewa.Da kallo mahaifiyartan ta bita dashi yadda daga jiya zuwa yau duk ta 茩ara fita hayyacinta.Kan ba kitso duk da ba wani datti ne dashi ba amma duk ya hargitse, 茩afarta da hannunta ba lalle, idan ba fa蓷a maka aka yi ba ba za ka kace amarya ba ce."Shigo mana Innah." Zaina ta fa蓷a tana bawa mahaifiyarta ta hanya ta shiga ta zauna bakin katifa, kafin itama ta rufe kofar ta nemi gurin zama ta kasa cewa komai.Kallon ta take, ba ita 蓷aya Allah ya bata ba amma tana sonta sosai, ko dan ta kasance KWANTACCIYA ce kuma itace 拼a mace ka蓷ai da Allah ya bata sauran mazane.Ajiyar zuciya ta sau茩e tana 茩iran sunanta."Zaina!""Na'am Inna?" Zaina ta amsa idonta a 茩asa."Har yanzu ba ki sawa zuciyarki hakuri da dangana ba? Umarnin iyayenki ne ba za ki iya bi ba? Ko kuma soyayya ce ta rufe miki ido? Shin kinsan waye Hashim a wajenki? Kin fi kowa saninshi, Yayankin 蓷an uwanki da duk cikin dangi yafi kaunarki tun kafin ki zo duniya? Hashim ya nuna miki so tun kina ciki har girmanki, ke kanki shaidace kin san hakan amma me yasa kika ka sa hakura da ra'ayin ki?"Kuka Zaina ta fashe dashi tace."Innah shi fa Ya Hash kallon Yayana nake masa tamkar su Yaya Ado da Tahiru, don Allah kuyi hakuri ku janye maganar aure tsakaninmu.""Hmmm Zaina kenan kamar har yanzu kin mance waye Hashim a gurinki." Fa蓷in Innah.Girgiza kai Zaina tayi hawaye na zuba a idanuwanta ta kasa magana, hakan yasa Inna tace. "Hashim shine masoyinki duk fa蓷in duniyar nan ki saka haka a ranki ko bayan raina za ki tuna kalamaina."Daga haka Inna ta tashi ta fita a 蓷akin, Zaina ta fa蓷a kan gadon ta fashe da kuka zuciyarta yana yna zafi duk da son yayanta da take amma haushinsa take ji da ya kasa fahimtar ta ya rabu da sonta ya barta da wanda take so ya茩...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.