IDON DUNIYA

episod 11

by @mrsfh

Wasila Omar (mr's f.h)


🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟

*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*

***


*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️

بِسم الله الرحمن الرحيم

~~~~~~~💞💞~~~~~~~


...........Tana fitowa falon kuwa ta hange shi akan irin kujerar nan da ake koyawa yara zama,da d'an saurin ta ta k'araso tana wa anty sannu da aiki kana ta karasa inda ARYAN yake tasa hannu ta ɗauke shi "ɗan gidan anty yau ka manta dani" tai maganar tana zama a d'aya daga cikin kuje run da suka zagaye falon,

 "haba dai shi ya isa ya manta da antyn sa, kece dai makaranta ta ɓoye ki"anty dake zaune tai zancen da murmushi a fuskar ta, " to amma shima ai bai neme ni ba"dariya maganar tata ta bawa anty dan haka taɗan yi dariya kana tace  "to ɗana yayi laifi amasa uzuri ko"ta karashe maganar tana miƙewa ta nufi kitchen dan tasan lokacin dawowar me gidan nata ya kusa,da sauri Jasra ta ajiye aryan a inda ta ɗauke shi ta bi bayan anty,tare suka shirya komai a dining sannan suka dawo falon jefi_ jefi suna ɗan taɓa hira,A haka abbu ya dawo ya same su shima ya zauna akai hirar dashi har aka kira isha kafin kowa ya nufi ɗakinsa dan sauke farali,

  Washe gari haka Jasra ta shirya da wuri ta tafi makaranta kamar jiya yauma yaran ajin ba wanda ya shiga harkar ta itama haka tana zaune ita d'aya tana ta sakawa da warwarewa taji shigowar malamin da ya kawo ta wata farar yarinya da bazata wuce sa'ar taba na biye dashi,gaishe shi sukayi gaba d'ayan su ya amsa kana ya ɗora da gabatar musu da ƙarin ɗalibai da aka samu "sunan ta khadija ita ma nan ajin zata zauna"ya dawo da kallon sa kan wacce ya kira da khadija yace "kije ki zauna nan ne ajin ku kinji"?gyad'a masa kai tayi alamun taji shi kana ta wuce kujerar da take kusa da ta jasra ta zauna idonta nakan jasran, "sannun ki sunana khadija ibrahim,amma ana cemin NANA da fatan zamu zama k'awaye" jasra dake kallon ta tai murmushi ita ma tace "sunana JASRA ABBAS"  "wow sunan ki me daɗi wallahi"murmushi jasran ta kuma yi kana tace "na gode" ita ma murmushin tayi "nagan ki ke kaɗai baki da ƙawaye ne"?    "ehh toh nima jiya na fara zuwa ban saba da kowa ba"  "ayya shike nan ai yanzu gani dani zaki saba"nana tayi maganar da saurin ta,murmushi kawai jasra tayi sannan suka cigaba da hira jefi jefi wanda ƙarfin hirar nana ce da haka har malaman su suka fara shigowa suna musu darasi.


  A ƴan kwana kin da basu wuce hud'u ba jasra ta saba da nana sosai ta fahimci matum ce mai sauk'in kai,sai dai ita har yanzu tana jin tsoron yin ƙawa domin tana tsoron dawowar IDON DUNIYA kansu ita da ɗan uwanta amma dole ta ke sake wa nana dan tana nuna mata kulawa sosai.

    Haka rayuwa taita tafiya jasra na zuwa makaranta alhamdulillah har sunyi jarabawar zangon farko yanzu suna shirin yin ta zango na biyu,ARYAN ya yi wayo sosai yana yawonshi ko ina dan yanzu ak'alla yakai wata goma sha ɗaya.

   Yau tun safe gidan ake ta shirye shiryen dawowar Habib anty ta kasa zama dan ta ƙagu taga tilon ɗan nata tayi kewar sa,sun gyara ɓangaren sa da sai a lokacin jasra tasan dashi acikin gidan,sannan suka shirya girki kala kala na gargajiya da lemo masu daɗi,bayan sun gama anty ta kalli jasra "ƴata je kiyi wanka kinga lokaci ya kusa"  da to ta amsa kana ta nufi d'akin ta domin yin wanka,itama anty sama ta hau tayo nata, cikin ƙanƙanin lokaci suka gama shiri suka fito domin tun tuni abbu ya tafi d'akko shi,tana zaune falo taji shigowar motar abbu haka kawai taji gaban ta ya faɗi,dafe ƙirji tayi tana karanto innalillahi wa inna ilaihirraji'un bata gama dawowa dai dai ba abbu ya shigo riƙe da hannun wani farin dogon saurayi suna shigowa kuwa idon jasra ya sauka anashi wata zabura tayi ta miƙe tana nunashi tana ja da baya tashin hankali ya hanata furta ko kalma d'aya baya tai luuu ji kake jib ta faɗi a sume..............


Tofah fans me ya tsorata jasra game da habib,


ku biyo alƙalami mr's f.h domin jin yadda zata kaya



MR'S F.H✍️✍️



share and comment