GIDAN BALARABE

Chapter 1-2

by @mamannabeela

*🪴GIDAN BALARABE🪴* 

        BY

 *🪴MAMAN NABEELA🪴* 


 *MOONLIGHT WRITER'S* *ASSOCIATION* 



بِسم الله الرحمن الرحيم


 👯‍♂️ *INA TAYA* *ƊAUKACIN* *AL'UMMAR DUNIYA* *MURNAR ZAGA* *YUWAR* *SHIKARA ALLAH YA SA MUN SHIGA A SA'A* 

 *AMEN* 👯‍♂️



 ~_TSOKACE_~ ;wannan littafin ƙirƙiraren labari ne duk wanda yayi dai dai da rayuwar sa yayi hakuri a rashin sani ne.




🅿️1️⃣↔️2️⃣


“Wallahi Hauwa baki isa ba kinyi kad'an, ni da gidana ni nake da ikon faɗar abinda na ga dama akan ku ke da 

'ya'yana kuma dole a bi in ba haka ba ranki yayi mummunan ɓaci" Adamu ne ke wannan maganar cikin faɗa, yayin da Hauwa ke sauraronshi tana daga gefe kanta akasa a ranta tana tunanin ko yaushe Baban Khadija zai daina wannan halin nasa na saurin hassala, magana kaɗan sai faɗa in dai magana ba tai dai-dai da ra'ayinsa ba, ba zaman lafiya, maganar Adamu ce ta dawo da ita daga duniyar tunanin da ta lula,cikin da d'a hassala yace “wato gani mahaukaci, ina magana kina jina kinyi banza inna gaji nayi shuru ko!" cikin kasa da murya Hauwa Tace “Dan allah kayi ha'kuri Baban Khadija wallahi banji ba ne.", Baban Khadija yace “to kinji dai na faɗa miki ba zan sake biyan kudin makaranta ba, su yi zaman su a gida Wanda su kai Allah ya amfana, ilimin boko bana addini ba ace kullum daga kawo wannan sai kawo wannan to na gaji ba zan iya ba", "amma Baban Khadija, da kayi ha'kuri ka biyawa ko Khadija ne tunda ka ga ita ajin ƙarshe take a sakandire kuma ta ci NECO, WAEC za'a biya mata",Hauwa ta yi maganar cike da lallashi saboda ita har ga allah tana so Khadija tayi karatu me Ɗan zurfi saboda yarinyar akwai ta da ƙoƙari .Baban Khadija ya ce “to naji zanyi tunani" .


**********************

TUDUN YOLA

 

Wata mota ce ta watso da gudu tun daga nesa take ba za Horn diiiit-diiiiit da gudu me gadi ya taho ya wangale get,motar nan ta shigo a guje ko dai-daita parking na cikin motar beyi ba ya bud'e motar ya zura kyawawan ƙafafunshi wanda ke cikin wani kyakkyawan takalmi, me gadi yana rufe get ya kwaso da gudu Dan ya bud'ewa me gidansa ƙofar motar sai ya tarar har yana shirin fitowa ya buɗe da kansa. Ya duk'ar da kai yana fadin “barka da dawowa Alhajin Allah ...... hannu ya d'aga masa alamar baya buk'atar wannan kirarin na Yawale me gadi, cikin da dadar muryar sa yace,“ka kwaso kaya a boot ka biyo ni da su" ya miƙa masa makulin motar yana futuwa da wasu takardu a hannunshi, ƙara ba Yawale yayi, Yawale na faɗin “angama Alhajin Allah ".shi kuma Wanda aka kira da Alhaji takawa ya fara yi ya nufi hanyar da zata sada shi da cikin gidan! masha Allahu na ce domin wani kyayawan matashi na gani fari ne tass dogo me sufar jaruman maza,tafiyar tashi ma abar kallo ce,cike da izza da zafin nama yake nufar cikin gidan kofar palon ya tura bakinshi ɗauke da sallama shiru palon ba kowa, sai ƙarar tibi dake ta tashi , Wanda ya ke masa nuni da yara basu dawo daga makaranta ba agogon palon ya kalla yaga huɗu ma bata yi ba sashinsa ya nufa wani haɗaɗɗen palo na kuma gani Wanda yafi Wanda muka baro kyau wannan shi kumai na cikin sa blue & White ne takadun hannun sa ya zube, ya nufi bedroom shi kuma kayan cikin sa gaba ɗaya White ne fentin dakin kuma blue ne haduwar da dakin yayi baki bazai iya lisafuwa ba,amma nabarku ku kiyasta da kanku.


Wani Hoto na gani ya ja hankalina hoton na Alhaji ne da wasu kyawa wan 'ya'ya su uku, mata biyu namiji daya a jikin hoton naga an rubuta MY KIDS

Shikuma dayan hoton dana ga shi kaɗai ne ajiki naga an rubuta (ABDUSSAMD ABDALLAH BALARABE)wanda da alama shi ne sunan sa. wanka Balarabe ya shiga bayan ya fito ya saka jallabiya ya ɗan fesa turare ya fito yana tunanin ku ina matan gidan suke yau ba hayaniyar su ɗakin uwargidansa ya nufa, ya tura ƙofar ya shiga bakinsa ɗauke da sallama zumbur ta mik'e tana amsa sallamar tana ciwa..



 *HOTORO* 



Bayan Khadija tagama koya wa ‘kanin ta karatu kamar yadda suka saba in suka yi sallar asuba,azkar sukayi bayan sun gama azkar d'in "I'man wada take sakuwar Khadija tace“anty Khadija barka da safiya"Khadija tayi murmushi tana ciwa " barkan kidai I'man watu shi ne ki kai sauri kika riga ni, dan kar naci muku barka da safiya ko!dariya I'man tayi Saudat da Nasir na taya ta.har had'a baki suke gurin fad'in haba "haba Big Anty kulum fa ki kike fara mi‘ko mana gaisuwa me makun mu mu gaishiki a matsayin ki na kice gaba damu”cikin jin dad’i da fara'ar da bata gushiwa a fuskar ta in tana tare da kanenta tace" tu naji kun dai yimin wayo, lokaci na tafiya kutashi mi aikin da zamuyi da wuri kar mu makara a tafiya makaranta"tashi sukayi Khadija da Nasir suka fita tsakar gida Nasir wajin rijiya yayi yafara d'iban ruwa yana cika musu kayan su,Khadija kuma kicin tashiga ta sharo shi tafitu da kayan wanke-wanke sannan ta d'ora abin karin kumallo,ita kuma I'man sharar d'akinso tafara ita kuma Saudat wanke-wanke tafito tanayi suna ta ayukanso daya ke Khadija ta kunna radio shiya sa basuji duk fad'an da baban su yake ba tsaka nin sa da mahaifiyar su.bayan sun gama ayukan su shirin makaranta suka fara yi,mahaifyar su ci tafutu tana yaba hankali da sanin yaka mata irin na ‘ya'yan nata yadda da sun tashi sai sunyi duk wani aiki da suka san zata yi kan su tafi makaranta. A zuciyar ta tana adu'ar Allah ya dad'a shirya mata ‘ya'yanta ya had'a su da abokanin zama nagari.Khadija ce a tsakar gidan sanda ta fitu tana ganin ta tafara fara'a ta tsuguna tana ciwa"ummy barka da safiya,ina kwana"ummy tace "lafiya lau kun tashi lafiya maza tashi kiyi sauri ki shirya kar Ku makara bari na karasa abun karin kumallo" Khadija tace "lafiya lau tu ummy" bayan sun shirya sun je sun gaida mahaifin su sunyi karin kumallo Ku wanin su ya kama hanyar tafiya makaranta.


**********************

 *TUDUN* *YULA* 


Zumbur ta mi‘ke tana amsa sallamar da yayi tana ciwa"barka da dawo wa Abban ayiman,wallahi banji dawo warka ba shiyasa ban fitu ba"tayi maganar tana susa kai alamun rashin gaskiya,kafe ta yayi da idanon shi masu sa mara ji ya shiga tai tayin sa.nan ta sunkui da kai tana fadin "Allah Abban ayiman ba chatin naki ba" fita yayi daga d'akin bata re da yayi mata magana tana ganin haka ta mi‘ke ta nufi ‘kofa kaurin da taji na tashi a kicin yasa ta da sauri ta nufi kicin d'in,dumin ita shaf ta manta da ta dora Abu akan wuta.tana shiga ta ganshi a kicin d'in har ya kashi gas d'in,cikn murya me amu yace"ki yanzu fisabililahi wannan rayuwar da kika daukar wa kanki ita ce dai-dai kina chan kina latsa waya ki ‘Dora abu a wuta har ya 'kune batare da kin sani ba.ki waya tafi kumai mahimmanci a gurin ki'haba Asiya yaushi zaki dena wannan ‘Dabi'a.Abban ayiman ki wannan maganar cikin takaicin halin matayinsa mata har biyu amma kuwaci da tata matsalar. Tsuro Asiya tayi tafara kami-kamin abinda zata fada masa. Hannu Abban ayiman ya daga mata yana fadin "ya'isa.





 


 *Maman Nabeela ce✍️*