Chapter 3-4
*🪴GIDAN BALARABE🪴*
BY
*🪴MAMAN NABEELA🪴*
🅿️3️⃣↔️4️⃣
TUDUN YULA
"Ya'isa har tsahun wane lokaci zan ringa nuna miki bana son wannan halin naki!kin bawa waya mahin manci fiyi da yadda zaki bamu kulawa nida 'ya'yanki,wannan wace iriyar rayuwace ki keyi Asiya,narasa me kike yi da waya Wanda yasa kike neman hallaka mu,ki ke nema ja mana gobara agida"Abban ayiman yayi maganar yana maida numfashi sabuda shi dai Allahn da yayi baya 'kaunar abinda zai sa shi yawan magana.
tu sai dai yagamu da mata marasa jin magana har gwara Asiya akan Laila dan ita zaman gidan ma bayi take ba in anyi magana tace business take,idan kuma tazauna agida ma bazaman lafiya.tu dai ko me take yi in munyi wai-waye maji.
Tahuwa Asiya tayi tana yin kalar tausayi ta rungume shi tana shafa bayansa alamar rarashi like a baby tana ciwa"Dan Allah kayi hakuri kaji Balarabe na insha'allahu na dena bazan sake ba"'kasa 'kasa take maganar cikin salon irin abu-buwan da take kuya a wajen 'kawayinta DA take mu'amala dasu take maganar.
Abban Ayiman ture ta yayi daga jikin sa yana fad'in "matsa ni kar ki karya min alwala,kulum haka kike fad'a amma kin kasa Dena wa tu wallahi maga ninku zanyi daga ke har wannan sarkin yawon"yayi maganar yana me juya wa ya fita daga gidan ma gaba daya.masalaci ya nufa Wanda yaki li'ke da gidansa bayan ya idar da
Sallah be kuma gida ba mota ya shiga ya dauki hanyar gidan iyayin shi,Wanda aikin da yayi masa yawa kwana biyu yasa be samu zuwa ba sai dai ta waya yake magana dasu,yau da ya dawo daga office da wuri shiya sa yace baya leka gidan naso.
*********************
HOTORO
Khadija bayan sun dawo daga makaranta,sunci abinci sunyi sallah daya ke Alhamis ce babu makarantar islamiya,takadu ta d'au ko tana making na d'alibanta da take koyar wa a islamiya tana ciwa "Ummy yau kinyi waya da 'Yaya Khalil kuwa!"Ummy dake zaune gefen su tace"a'a yau be Kira ba nima d'azo nake gwada layin sa naji bata shiga"Khadija tace "Allah yasa lafiya"Ummy ce tace "Ameen insha'allahu lafiya lau yake,ni nafi tunanin Ku jarrabawa ci tasa be Kira mu ba ya kashi wayar kuma"I'man ce tace"Ummy jiya da muna waya baya ce yau jarrabawar me zafi baci ba mu taya shi da Adu'a" Ummy tace "ahf namanta shaf daya fad'a,tu Allah ya bako sa'a gaba dayan ko"dukan so suka had'a baki suna fadin"ameen"
Khalil shene Babba 'Yayan su Wanda gwamnati ta Kai su Indiya dumin suyi digiri a fanin likitanci.
Wanda suka kwashi Shikaru Wajen uku,a indiya yanzu hwka Suna gab da kammala karatunsu Su dawo ƙasarsu ta haihuwa.
_BALARABE_
Ko da ya 'dauki hanyar tafiya gidan mahaifanshi yana ji ,wayarsa na tsuwa daya duba ya ga me kiran, kawai ya danna wayar a silent dan baya bu'katar komai yanzu sai son ya ji shi a jikin Ammynshi,ta na shafa kanshi ta na samai albarka.
a hanya ya tsaya ya sai kayan mar-mari dan Ammynshi na matuƙar son kayan fruits, sannan ya ɗauki hanyar Rijiyar zaki, cikin 'kara gudun motarshi, wani katafaren gida yake dannawa Horn jikake yana bada d'iiiit-diiiit
Da gudu wani matashin me gadi ya zo ya wangale tangamemen get ɗin wanda kallo ɗaya zaka yi wa me gadin ka gane Buzu ne, saboda shigarsu irin ta Buzaye da ke jikinSa.
Balarabe na shiguwa Perkin ɗin motar shi ya yi, ya bud'e motar ya fito hannunsa ɗauke da ledar kayan marmari.
me gadi ne ya ce "barka da zuwa Alhaji 'karami fari me farar aniya " hannu ya ɗaga masa dan ji ya ke kamar kansa zai rabe tsabar ciwo, kuma ya san wannan dogowar maganar da yayi da ɓacen rai yasa haka juyawa yayi ya fara tafiya, Buzu ya ce “Alhaji kawo na shigar maka da ledar " kad'a masa kai yayi alamun baya buƙata, hanya 'kofar falon gidan ya nufa,tura 'kofar ya yi ya shiga bakinSa ɗauke da sallama wata kyakkyawar mace ce zaune a kan kujerar falon wadda kallo guda za ka yi mata ka gane hutu da jindad'i sun ratsa ta, sanye take da wani d'and'asheshen leshi Wanda ya hau farar fatarta, Wuyanta da hannunta sanye da gwalagwalai, kai ba ka ce ta aurar da 'ya'ya ba ma.
'karasowa yayi gurinta a shagwaɓe kamar wani yaro yana 'bata fuska. cikin fara'a da tsananin soyayyar 'Dan nata ta ke fadin "waye ya ta'ba min jarumin yaro na ne? " zube guiwowinsa ya yi a kusa da ƙafafunta ya na d'ora kansa a kan cinyarta yana faɗin "barka da yamma Ammyna", Ammy tace "ya office ɗin naku komai lafiya dai ko", “lafiya lau Ammy, sai tarin ayukka, yunwa naki ji" dariya tayi tana cewa "oh'ni Aishatu kai son ka ji tsoron Allah matanka har biyu amma Karin ga 'korafin yunwa", “Allah first love ina dawowa ban tsaya neman abinci ba nayo nan",ya faɗa yana shafa kan",Ammy ce tace" tu naji ina kishiyoyi na da me gidana","sunanan lafiya basu taso daga makaranta ba da tare zamuzo daso,"ya faɗa yana jawo wata ƙaramar kula da ya gani kusa da Ammy, buɗe ta yayi wani ƙamshi daya daki hancinsa yasa shi........
**********************
TUDUN YULA
ASIYA
Koda ya fita ya bar ta a kicin ta san ransa yayi mugun 'baci shiyasa ta na gyara kicin ɗin ta d'ora girkin abinda tasan yana matu'kar so, bayanta 'Dora d'aki ta kuma tayi sallah ta ɗauko wayarta tana kiran sa be ɗauka ba haka ta tura masa sa'kon ban hakuri shi ma ba amsa.
*******************
HOTORO
Khadija bayan ta gama making din cewa ta yi "Iman shiga ki kwaso kayan wankin nan yau tunda Alhamis ce mu wanke su" tashi Iman tayi ta shiga domin had'o kayan,"UMMY ki had'o kayanki mu had'a mu wanke gaba ɗaya ", Ummy ta ce “Khadija ba zaki bari Ku huta ba gobe kwayi",
“Ummy kin manta gobe za mu je gidan Anty Kubra shiyasa naci muyi yau" Khadija ta fad'a tana tashi tsaye", "to Allah yayi muku albarka ya baku maza nagari", "Ameen" su ka ce .Ummy ta shiga ɗaki ta had'o kayan wanki, Khadija kuma ta tafi bakin rijiya ta fara jan ruwa.
tace da Saudat "Saudat ki ce da Ummy ta baki kud'i ki siyo omo", Saudat tace "to" bayan Iman ta fito da kayan ta kar'bo na mahaifiyarsu suka fara wankin, Saudat ma da ta dawo daga Siyan omo wankin ta fara, suna yi suna hirarsu.
yaro ne yayi sallama suka amsa yace"wai ana kiran Khadija", Iman ce ta ce "inji wa!" yaron koma wa yayi ya tambayo ya ce "wai yace Salman ne" Khadija ce ta ce "je ka ce bata nan"Ummy ce ta fito daga ɗaki ta ce "ya haka ban san ki da wulaƙanci ba ki ka san daga ina ya taho zaki ce bakya nan, kai ce masa tana zuwa", yaron fita yayi ya ce "an ce tana zuwa" cike da farin cikin yau ta taki sa'a ya zaro naira d'ari sabuwa fil ya bawa yaron, yaro ya tafi yana murnar ya samu kud'i.
"ki tashi ki je kafin ranki ya ɓaci" , tashi tayi tana matso k'wala a idanunta ta shiga ta d'auko hijabi ta saka tayi hanyar waje, Iman da ke k'unshe dariya ce ta hauyin ta a fili, juyo wa tayi ta maka mata harara tana kwafa tayi gaba, tana fita ta tsaya a jikin 'kofar gidansu tana me 'kara d'aure fuska.................
*Maman Nabeela ce✍️*