Darkness's-Chapter-4
by @maidambu41
_....ZAYN MALIK....✿_
*EXQUISITE WRITERS FORUM*
Mai_Dambu
CHAPTER-04
Darkness
"Sannu d'anan! Sannu tako a hankali karka motsa domin Allah kadai yasan iya adadin lokacin da ka dauka kana jele da ciwo ikon sai lillahi, dama haka kake da hakuri da alamu duk matasan gidan nan babu na biyun ka a jarumta, sannu kaji zauna maza zan tsaya ka karya mu tafi asibitin"
Zama yayi tare da wani narke mata yana kara kwantar da kan shi a kafadar ta.
"Hajjos! Good morning?"
"Ayya zafin ciwo yasa ka min Yaren nasara bayan kasan na yashe mishi albarka sannun kaji"
Daga saukowa shi zuwa zaman shi ta mishi sannu ya kai sau bakwai zuwa goma.
"Kallon Yaranta tai da suka zuba musu ido, itama sake baki tayi tana kallon su kan ta a karkace.
"Hala kun tashi daga cutar makanta ne?"
A firgice suka kalle ta, suna fadin.
"A'a " lokaci guda.
"Yoh daure bakin ku aka yi da ba zaku mishi ya jiki ba ko sai na roka?"
"Atta hajiya"
"Uwaka auta!" Ta dankwalawa Uncle bashir hannu bibbiyu.
"Sannu son ya jikin ka?"
"Meye Sannu soooo ya jikin ka Banu tausayi da Imani ne? Wani sooon sai kace dan kasar masu kananun ido wadancan masu magana da hanci!" Wato china,
"Zayn ya jikin ka?" Inji Baban shi.
"Rashin kunya sunan Ubanka kake kira gatsau? Kaii" ta kalli Alhaji Uwaisu da bai yi magana ba dama Uncle Bashir da Abba suka yi magana.
"Sannu ya jikin naka Babana?" Ai kuwa fadada murmushi Hajiya tayi tana cewa.
"Ai Uwaisu yaron nan jiya da kyar yayi barci," kallon juna suka yi, kamar ance ta kalle su, sai kuma ta gimtse fuska.
"Nayi karya ko ? Tabawa, maza wuce sama ki dauko min jakata, da akwai kudi a kasan matashina ki hada ku tawo min dash" Ta tambaye su tana bada umarni, cikin sauri Tabawa ta cika umarninta.
"Wane mutum Hajiya ta, ai bani da ta ukun ki" inji Zayn.
"Ikon Allah Zaynu akwai ta daya na da ta biyu na kenan?"
"Inji waye? Ai hajjos kaf Naija babu wanda ya isa shan gaban ki, ke da nake cewa idan na tashi aure gidan nan zamu bari mu kama haya"
"Yo na sani ko an mana farraku? Tunda muna da masu baki da mudu. Yanzu dai bari Talatu ta kawo abinci sai muje na kaika asibitin"
A zabure ya ce mata.
"What??"
Wani mahaukacin dariya Uncle Bashir ya sake yana cewa.
"So curious and Hilarious"
Abban Zayn shima murmushi yake yana kallon yanayin Zayn yadda mood din shi ya sauya once.
"Ai zan kai ka ne da kaina na musu bayani, lokacin kana yaro idan ja cilla fitsari daga bakin kofa sai ya wuce waje, sannan a lokacin lafiyar na lau" ta fada in comfort, kallon Uncle bashir yayi yana mishi magana da ido.
"Kace mata lafiya ta lau"
"Ayya Hajiya kiyi hanzarin kai shi dubi yadda yake zare idanu alamar ciwon yana cin shi"
"Ai shi yasa zan maza na shirya mu tafi kar mu makara!"
Dafe Goshi yayi yana faɗin.
"Wallahi lafiya ta lau Hajiya Umma"
"Ai kowa haka yake gani lafiyar ka lau shi yasa basu damu da kai ba, zan kai ka domin idan nace Bashir ya kai ka, yanzu zai dauki kundin su na lauyoyi yana rabtabo bayani, idan kuma mace Ubanka ne gashi nan yanzun zai mike yana cewa halo. Idan kuma Uwaisu ne zai ce min ya makara wa kake da shi da ya damu da kai?"
Shigowar Mama da hajiya Umaima kishiyar ta, sai Aunty Rukayyah matar Uncle Bashir, sai Hajiya Maimouna matar Alhaji Uwaisu, dukkan su dauke da kayan abinci, a hankali suka shiga jerawa suna kallon Hajiya da Zayn dinta.
"Son idan ka karya zan baka aika zuwa gidan mu kaji" inji Aunty Rukayyah,
"Bafa inda zai je tam"y inji Hajiya, kallon Uncle bashir tayi taga ya D'aga kafadar shi, Murmushi Hajiya Maimouna tayi tana son ganin draman Hajiya da Zayn dan haka cikin son sanin Meke going tace .
"Hajiya ina kwana ya nauyin jikin"
"Alhamdulillahi nauyin jiki kuma Allah ya sauke min ya daurwa dan ku jiya kamar ba zai rayu ba kin gan shi" ta nuna mata Zayn, da yake ta had'e rai.
"Ayya Baban Umma Meke damun ka?" Hajiya Maimouna ta tambaye shi.
"Allah sarki Maimunari baiwar Allah, ke daga shigowar ki har kin damu da Zaynu keda mijin ki Allah ta shiga lamarin ku, masu mana mugun alkaba'i ya Allah kasa suna gani zamu kama gidan haya a garin Habuja ko Yarona"
Kunshe dariya suka yi, wannan shine cigaba me tonan rijiya, (😂🤣😂 hajiya zata kashe ni)
"Babana ya jikin ka?" A sakalce ya sauko a kujeran ya zauna a kasa tare da daura kan shi a kafadar ta.
"Maam!"
Tallafe fuskar shi tayi tana jin wani tausayi da kaunar Yaron a yanzun yana yawan fama mata kukan da tayi na tsawon shekaru baya, a ƙalla auren ta da Alhaji AbdulMalik Zain Malami ya kai shekaru arba'in da takwas tunda Fatima babbar Yayar su Zayn ta kai arab'in da wani abu.
"How you feeling?"
"Alhamdulillahi Maam ki ce mata bafa inda zani?"
"Ikon Allah talatu cin amana ta kike da malami karami? Wato kina kintsa mishi yadda zai ce ba zai yarda ba kai shi ganin likita ba?"
Tayi maganar rai a B'ace.
"A'a Hajiya tambayar shi bake ya jikin nashi asha ashe abin ya kai haka ne?"
"Ban sani ba, kawai mun gama shirya yadda zan kai shi ganin likita kizo ki sauya min ra'ayi"
"Allah ya huci zuciyar ki" ta fadawa Hajiya tana zuba mata abun karyawa, abincin ta ta mikawa Zayn din tana faɗin.
"Maza ci sai mu tafi" babu yadda ya iya haka ya tura abincin sai lallashin sa take tana gaya mishi.
"Ai cuta ba mutuwa bane"
Yana gamawa ya mike, wayar shi ce tayi kara.
Duba screen din wayar yayi, lumshe idanu yayi sannan ya dauka yana haurawa sama.
"Okay I will be there insha Allah"
Sannan ya katse wayar, ajiyar zuciya yayi sannan ya tura sako.
A hankali ya sauko yana kallon Hajiya da ta zuba mishi ido.
"Auta maza kira Jauro ya kai mu"
"Hajiya ga Zayn!" Ya nuna mata Zayn ɗin.
"Eh nasan da shi na ce kai, idan kuma zaka nuna min bani da iko da kai bismillah"
"A'a Hajjos, bari na kira shi."
"Ayya kai da baka da lafiya!"
Kallon su Mama take, Zayn Malik sunan da da ya samu matsuguni a ranta tun daga ranar da ya diro duniya, ba wai dan yana jika ga Alhaji Zayn Malami Malik bane a'a sai dan sunan ya dace da shine, Bata sani ba Allah ya kawo shi cikin su ne dan ya zama abun alfahari a gare su ko kuma ya zo ne a matsayin Jarumin ƙarni, a duk lokacin da zata yi kuka zata iya cewa shi yake share mata hawayen ta.
"Toh idan kika ji shiru bako yayi halin shi mun tafi ganin likita"
"Allah ya dawo daku lafiya"
"Yawwa Munarih" tana fita suna sauke ajiyar zuciya a tare.
"Wai da gaske bai da lafiya ne?"
"Ina fa tsagwaron rikicin Hajiya mana wallahi lafiyar shi lau."
Shiru suka yi kafin Uncle bashir ya mike yana faɗin.
"Matukar Zayn yana tare da Hajiya ba zai mori kan shi ba, sannan idan ita kanta ba zata tab'a barin ya tafi wani wuri nesa da ita ba." Inji Mama.
"Sai a bar shi yayi ta lalata Yaran mutane a gari ai"inji Hajiya Umaima.
"Bai min kama da me haka ba domin da halin shine da tuni ya bayyana kan shi"
"Ina ga ku ajiye wannan sa'in'san ina da tafiya Sweden, kuma zai yi shekaru daya da rabi ne, ya zata kaya idan na dauke shi?"
"Me zaka je yi can? Ka shirya kome idan akwai abinda kake bukata a gaya min zan bada."
Da haka suka tashi ran Hajiya Umaima a B'ace bata kaunar cigaba Zayn duk da tana da Yara maza Uku da suke manyan aiki a kasar nan bata ki ta ga Zayn a lalace ba, domin lokacin da aka ce an dakatar da shi a aikin soja sai da tayi sati biyu tana sakewa Mama habaici, da gori babu wanda bata yi ba, amma ko a jikin Mama asalima uzuri take mata, shi yasa yanzu take jin zafin tafiya da shi Sweden da Uncle bashir zai yi, bata ki ta hana shi ba.
Tana shiga dakin ta, wayar ta ta dauka zata yi kira Jud ta shigo, kallon ta tayi sannan ta ce mata.
"Hajiya ya zamu yi da Zayn don Allah ki cewa Mommy tayi wani abu!"
"Yanzu zan yi waya idan na gama zan kirata kin ji jeki zan gaya miki yadda aka yi"
Tana fita ta bita da wutsiyar ido, sannan ta kira wayar ta.
"Hello Hajiya Hanne? Yaron nan fa Sweden zai tai da kanin mijina, mijin Rukayyah"
Ko me aka gaya mata tace mata.
"Ban damu ba, kawai duhun da yake zagaye da shi nake son sani, ina son sani abubuwa akan shi? Yaron duk abinda zan yi mishi baya fushi, kin ga ba zaki gane yana nake ji ba, but am out of my mind bana kaunar Yaron, zan iya tsayawa ya dawwama in darkness, please a dakatar da tafiyar."
Kome aka gaya mata dafe goshin ta tayi, tana jin wani irin bacin rai.
"Ai na gaya Miki Mother in-law na bata son laifin shi. Kinsan malam ya gaya min kashin arziki ne da shi, duk inda ya taka idan so samu ne kome ya zama na Yarana, shi yasa aka mishi aikin da ya zama haka "
Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta ce mata.
"Good abinda nake son sani kenan, ko jiya akan Idanuna Alhaji ya ware mishi shareholders din shi wanda muka zuba a JIKAMSHI GROUPS, dan haka nake son sanin Meye yaron yafi sauran"
Can kuwa ta ce mata.
"Alhamdulillahi abinda nake nufi Kenan dan haka zan nime ki bari na kira Yayar Alhaji muyi magana da ita!"
**
Tsayawa yayi a bakin hanya ya dauki Abul Khair da ya fito cikin shirin zuwa wurin aiki amma da yaji Zayn zasu fita yace mishi.
Ya tsaya ya dauke shi ya fasa zuwa aikin shima dama niman hanyar kin zuwa aikin yake, kawai sai ga kiran Zayn.
"Amma Malami da salula kake shawara da uwar kishiya, uwar me wannan me wuya kamar markin lema fa zai mana?" Kallon wuyar Abul Khair yayi yaga da gaske maganar da Hajiya tai kusan gaskiya ne, murmushi yayi ko banza ba shi daya zai yi fama sa tujarar hajiya ba.
"Umbrella..!" Sai ya fada yana kallon hanya.
"Hajiya kin ga Zayn yana tsokana na ko?" Inji Abul Khair.
"Ikon Allah, kai jariri ne da zai tsokanne ka? Ko sabo dayi gawa da gatsine, dan Albarka yi shiru kayi fama da ciwon ka, Allah ya baka lafiya mata hudu zaka aura rana daya muga shegen da ya isa d'aga maka kai duk fadin Kaduna"
"Ai kuwa Hajiya babu shi." Inji Abul yana kallon Zayn.
"Four for like russss"
"Zan cin Ubanka"
"Wayyo Allah na, kunci kaniyar ku wai hauka kuka fara ne?"
"Toh hajiya baki ji shi ya tsokane Ni ba"
"Ikon Allah, Allah sarki Allah ya baku lafiya" daga haka bata kuma magana ba, domin idan ta cigaba da magana ranta B'ace zai yi haka suka isa asibitin shi dai Abul Khair bin su yake bai san me ya kawo su ba, dan haka ya dauka hajiya ce ta zo ganin likita. Agaban reciption ta tsaya tana kallon matar da take wurin sayan kati ta ce mata.
"Yawwa likita daga ganin ki da katon tabarau nasan kece likita bokan Turai, ao ba banza Allah ya ajiye ki anan ba, toh kin gan shi bai da kuzari ne ki kadan."
"Hajiya wani irin kuzari?" Shi Zayn da Abul Khair suna can suna gaisawa da wani class mate din su, juyawa tayi tana rabtabo bayani.
"Ke ba wancan tsololon ba, ba kuma wancan dan dukushin ba, shi wancan jibgegen yawa shi dai da kika gani kamar jarumin nan shi fa na kawo ganin likita ashe yaron nan ya jima yana jinya bai da kuzari kina mishi maganar aure zai kama rigima, yo ai a tunani na aljanar dare ce ta aure min shi ashe ke dai babu kuzari ina Aljana zata samu biyar bukata, kawai sai dazun Judaal ta je ganin shi yake gaya mata ai shi ba namiji bane, kin ga yadda ya kwana yana matagugun, ai na zata mutuwa zai yi toh kin ga da gari ya waye ya tashi kyam kamar namijin doki, babban tashin hankali na matar da zata aure shi a wannan yanayin ai kin san an cuci yar mutane, iyayen shi basu da d'igon imani, karshe ka karya tashi suka yi wai lafiyar shi lau, shima da kike ganin shi ai kunya ce da shi dakyar ya biyo ni, yawwa wani magani zaki bashi."
Ajiyar zuciya Matar tayi sannan ta ce mata.
"Hajiya ni ba likita bace, kati nake sayarwa."
Sake baki Hajiya tayi sannan ta ce mata.
"Toh sai ki had'a ni da likitan ko, bayan gama jin sirrin yaron kirki kice zaki wani ce ke ba likita bace, kowa a duniya ya zama munafuki da katon tabarau kamar na waziri aku. Kuma sai na gaya mishi kin ji sirrin shi"
"Allah ya baki hakuri Hajiya anan zaki sayi kati dubu biyu ganin likita dubu da dari Biyar "
Wata uwar harara ta wurga mata.sannan ta d'ago jakarta ta ciro kudin ta mika mata.
"Ina son ganin likita akan lokaci ya samu yi?" Ta dan matsa kaɗan tana mata alama.
"Yadda kika ce haka zamu yi Hajiya na wanke hannu da sabulu zaki bada kawai."
Aikuwa Hajiya ta kirga dubu biyar ta mika mata, kuma kudin fa jiya take gayawa Alhaji Uwaisu zata tura gudunmawar bikin wata jikar su a Zaria, toh karshe dai ga sh nan ana kashe shi a iska, ai kuwa kafin kace me an tura file din su.
Suna gama hira da abokin su, kawai suka tawo wurin ta.
"Yawwa tako a hankali, jeka zauna a can huta kaji ai lalura irin naka sai da kulawa "
Zama yayi yana ya tsina fuska kamar yaga kashi, itama matar kallon Zayn take, musamman yadda yayi dress ya daura wata jack a saman kayan shi kuma abun burgewa yadda jack din me hula, zuwan abokiyar aikin ta ne, ta fara bata labarin da Hajiya ta bata, suka shiga kallon shi domin bai musu kama da mara lafiya ba.
"Wallahi he look hot, irin wadannan idan suka rike mace ko? Wow"
"Haba Aunty ai kin girma da wannan aikin sai yara."
Kiran shi aka yi Hajiya ta mike, tare da mishi magana da idanu, mikewa yayi shima suka shiga cikin dakin.
"Yawwa sannun likita, ya aiki ya aka ji da jama'a, yawwa sannun ka gan shi nan na kawo shi bai da lafiya ne ya ce shi ba namiji bane, kai zo ka gaya mishi baka da kuzari, ko kallon mace baka yi, likita jiya kwana yayi yana juyi da ihun ciwon ciki."
"Toh mama ko zaki fita na duba shi,"
"Hmm yaushe na gama mishi tsarki? Toh kaji dai dan albarka idan ya ce ka kwabe wandon karka yi musu ka kwabe zai duba ka ne kaji" dafe Goshi Zayn yayi bakin ciki kamar zai kashe shi...