GIDAN BALARABE

Chaper 9-10

by @mamannabeela

*🪴GIDAN BALARABE🪴* 

      BY

 *🪴MAMAN NABEELA🪴* 

   

     ***  




*MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION*




*DATA! DATA! DATA*

ABBAN HUSNA! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*


I *selling DATA with this price* 


 *MTN DATA* !

500MB@==200

1GB@==300

2GB@==600

5GB@==1500

10GB@==3000


 *validity 1month* 


 *GLO,AIRTEL,ETISALAT also available.* 


 *ACCOUNT NUMBER* 👇9985351006 providus bank

1224475018 access bank

2018717886 kuda bank


contact 👉*** or ***


  *WANNAN PG ƊIN NAKO NE MASOYA GIDAN* *BALARABE* , *MUCH LOVE A DUK INDA*                                 KUKE *SON SO* *MARA* *ALGUS*🥰🥰🥰🥰



🅿️9️⃣↔️🔟


  *WASHI* *GARI!!!*


.........Cikin Sauri yake saukowa zuwa Babban falon gidan cikin Wasu blueblack ɗin Suit Waɗɗanda suka yi masa mugun kyau, ya saka taiti fari a wuyansa sai A gogon Relux me ɗan karen tsada dake ɗaure a hanunsa ƙafarsa kuma ɗauke da covershos shima fari cikin zafin nama ya sauko yana ta zuba ƙamshi,yaransa ne dake kan teburin cin Abinci zaune suka taso Suka rungumeshi suna faɗin"Abbuuh Barka da safiya" cikin harshin larabci,shima cikin larabci ya mayar muso yana shafa kawunanasu sannan suka koma suka zauna.


Shima zama yayi yana cewa "ina mamar tako!"Meme ce tace "Abbuuh tana kicin tana haɗa Breakfast"wani mumushi yayi wanda shi kaɗai yasan manufarsa


Tashi yayi ya nufe kicin ɗin tura ƙufar yayi ya shiga, jin mutsin kamar an shigo yasa ta saurin guge kwalar da ta zubu daga idanonta tana cigaba da juye soyayyan dankali a cikin wani foodflas,ƙamshin

 turarensa yasa ta gane shine ya shigo kicin ɗin juyowa tayi tana ciwa"Barka da fituwa"tunda ya shigo ya ke kallonta dan yasan tabbas kuka takeyi juyowar da tayi ya tabbatar mai da abinda yake zato ganin fuskarta ta kumbura abinka da jar fata


Takuwa yayi zuwa cikin kicin ɗin yana cewa "Asiya saboda na karbe wayarki kike kuka ko kuma saboda nace zan ƙara Aure uhm!" cikin kuka tace "ba nace kayi haƙuri ba na dena fa,kuma ba kaine ba harfa mugunta kayi min da ƙyar nake tafiya jiki na duk ciwo yake min"Asiya ta faɗa hawayi na daɗa zuba sharrr'


Murmushi yayi yana daɗa jin-jina ragwantakar Asiya,

Yace "ah'ragwantaka dai banda raguwa ce ke daga na nemi haƙena sai kice nayi mugunta, ace 'Ya'ya uku amma kin kasa sabawa to kuwa ya zama dule na ƙara aure ko na samu wadda zata iya da ni"ya faɗa ya na ɗaukar cup coffee ya haɗa ya nufi ƙofa yana cewa"ki kawo wa yara Breakfast karsu makara"


Fita yayi ya kuma deanin zama yayi yana jawo Nimrah ya ɗorata kan cinyarshi yana shan coffeensa.


Cikin ƙonar rai ta haɗa kayan karin ta fito daso bayan ta wanke fuskarta a jiyiwa tayi ta fara haɗa musu tana

cewa"Meme ɗauki na Baba larai ki kai mata"


"to"ta amsa tana ɗauka ta nufi ɗakin ta kai mata ta dawo ta zauna 


Zuba musu tayi ta meƙa musu nan sukayi Bissmila suka fara ci komawa kicin tayi ta ɗauko basket ta saka na Abban Aiyman ta kawo ta ajiyi dan shi be fiya karyawa a gida ba, zama tayi itama 


Suna gama karyawa yaran ya tashi yana duba agogon hannunsa yana ciwa "kuyi maza kuje mota yanzu zan fito" da "to"suka amsa suna ciwa "Momy mun tafe"


"Allah ya tsare"tace 

Balarabe Sashinsa ya koma ya fito hannunsa ɗauke da breifcase yana ciwa" sai na dawo"ya nufi ƙofar fita 


saurin miƙewa tayi tace"abincin naka baka ɗauka ba"

"Idan naje ba samun lokacin cin abinci zanyi ba saboda mitin ɗin da zamu shiga,inaga kawai ki bar abincin nan sai na dawo"Bahaka taso ba sai tace "to Allah ya tsare"kafinma ta gama faɗe tuni ya fita


Yaran ya hango tsayi jikin mota danna remote ɗin motar yayi ta buɗe suka shiga,shima shiga yayi yana yiwa motar key yana me danna horn Yawale megadi ya fito daga ɗakinsa da sauri yana wangale gate ɗin 

yana zuba kirari irin yanda ya saba Balarabe yayi ƙasa da glass ɗin motar yana cewa"Kaje kace abaka abince injini" cikin tsananin farin ciki yace "angama Alhajin Allah,Allah ya kare mana kai"ya faɗa yana rufe get ɗin dan rabunsa da yace abinci irin naso tunda Laraba me aiki ta tafi ganin gida,cikin gidan ya nufa ya tsaya a bakin ƙofa yana kwaɗa Sallama 


Asiya da ta nufe sashinta ce taji Sallamar dawowa tayi ta nufe ƙofar buɗewa tayi tana amsa Sallamar cikin ɗan sakin fuska tace"Yawale kaine!"


Cikin girmamawa yace "eh Hajiya,Alhaji ne yace kibani abinci" juyawa tayi ba tare da tayi magana ba juye masa tayi a wata ruba ta dawo ta miƙa masa 

karɓa yayi yana ta zuba gudiya .


Balarabe Bayan ya sauke yara office ya nufa yana me ƙara gudun motarsa dan yasan ana chan ana jiransa 


********************



Ɓangaren Khadija bayan sun dawo daga makaranta 

wanka suka ƙarayi sannan suka fara shirin tafiya gidan ƙanwar mamarsu Anty Kubra


I'man ce ta zauna take ta faman kwaliya

Khadija ba ma'abuciyar zane-zane bace huda kawai ta shafa sai kwali da tasa da man leɓe,Wane ɗan ubanson leshi ta ɗauko maron ɗinkin riga da sikit wanda suka bi jikinta suka zauna tsabar kyan da tayi kamar ka saceta kagudo ɗan kwali ta ɗauko ta murza ɗaurin ture kaga tsiya Ya Allah yadda kasan wadda zata gasar kyau irin kyan da tayi ba'a magana 


Mahaifiyarsu ce ta leƙo ɗakin tana cewa"wai har yanzu bako gama shiryawa bane!"khadija tace"Ummy  I'man ce ta tsaya sai faman kwalliya take kamar wadda zata gidan paty,ta riga ni wanka amma kalle harna riga ta shiryawa,ni wallahi inaga tafiya ta zanyi ta sameni a chan"I'man ce tace"Haba dai yanzu sai ki tafe ki barni kaya fa kawai zansa"ta faɗa ta jawo atamfar data ɗauko zata sa "toh'dai ko hanzarta ko tafe dan ko kwa dawo da wuri"Ummy ta faɗa 


"Ahf' Khadija kinga na manta yaron nan Salmanu ya kira kuna makaranta,yake bayani akan kayan daya turo daso ranar dayazo, toh'naji na kuma gamso Allah ya tabbatar da alkairi"I'man ce tace"amin"


Bayan sun fito zasu tafi Ummy ta ɗaƙo wata leda tabasu tace su kaiwa Anty Kubra,karɓa sukai suna faɗin "Ummy mun tafi" "toh'ko gashisu karko kai Dare" "toh suka amsa suna nufar ƙofa Khadija niƙaf ta ɗauko a jakarta ta sa sannan suka fita Khadija ta riƙe hannun Saudat suka nufi titi.


**********

Balarabe bayan sun gama mitin gida ya dawo ya sake wanka,Wata Dakakiyar Shadda fara sul ya dauko yasa sai Wani agogon zallar azurfa daya sawa hanunshi 

Hula ya ɗauko asalin zanna bukar ya kafa akanshi,

Baƙin takalmi ya ɗauko Wanda ya kasance ba rufafe ba yasaka gaban mirow ya kuma turare ya ɗauko ɗan asalin ƙasar Saudiya Wanda ya kasance shine turaren dayafi amfani dashi ya feshi jikinsa,kallon mirow ya tsaya yana yi duk da ya kasance shi ba ma'abocin kallon mirow bane amma yau Saboda Wane farin ciki daya kejin kansa a ciki yasa ya tsaya yana kallon mirow,lokaci-lokace kuma ya kanji zuciyarsa na zello kamar zata fasa ƙirjinsa ta fito 


Ƙwan-kwasa ƙofar da akayi ya dawo dashi daga tunanin daya ke yace"yeas come in"Asiya ce ta shigo bakinta ɗauke da Sallama tasha adonta cikin danƙareriyar atamfarta tayi kyau susai tana cewa"Su Aiyman ɗin sun shirya"


"toh"yace batare daya bar jikin madubin ba juyowa yayi Asiya ta sake baki tana kallonshi saboda yayi bala'in yin kyau Wani kishinsa taji ya taso mata aranta tana jin dama ita kadai ce matarsa"in kin gama kallon nawa da tunani toh muje"Asiya ta tsinci maganarsa 

gaba yayi tabi bayansa ƙasa suka sauka nan ya ga yaran duk sun zaune sunsha kwalliya da alama shi kawai suke jira,suna hango shi suka miƙe suna faɗin


"Abbanmu kayi kyau"dariya yayi yana cewa"harna kai ko My Happiness" dariya suka yi Meme sarkin surutu tace"kaiii Abbuuh kafimu"cewa yayi "toh'naji ku ɗauko mayafanko muje na ajiyi ko gidan Ammy mu kuma mu wace Masallaci"cikin farinciki suka ce"toh" suka tafi ɗakinsu suka ɗauko Meme mayafe ta yafa ita kuma Nimra hijabi aka sa mata suka fito 


"Momy mun tafi gidan Granyy"suka fice waje "ina tunanin sai yamma zamu dawo,Wayarki tana kan dressin mirow ki ɗauka"cikin farinciki tace"toh'Ngude Allah ya kiyayi hanya agaida Ammy"da amin ya amsa yana fita daga falon harabar gidan ya nufa Wata galleliyar mota suka shiga Baƙa wulik,irin wadda akewa kirari da yaro ƙare kukanka dagani ba tambaya kasan motarnan ta lashi maƙodan miliyoyi horn ya danna me gadi ya tahu da sauri ya wangale ƙofa yana zuba adu'ar dawowa lafiya.


***********


Khadija me keke napep na suke so kuɗinsa ta bashi ya miƙo mata changi karɓa tayi tana maida so jaka Wani koɗin ne ya faɗi ta sunkuya tana ɗauka,Wata Baƙar mota ta kwaso da gudu saura kiris ta banke ta tayi sauri tayi baya tana cewa


"Innalilahi"Khadija ta faɗa tana dafe ƙirji saboda ta tsurata ba kaɗan ba tana bin Motar da kallo banda duka ba abinda zuciyarta kiyi,I'man dake riƙe da Saudat wadda ita kanta hankalinta saida ya tashi Saboda Motar da ta kusa bige ƴar'uwarta tace"Amma Wannan me Motar anya ba Mahaukaci bane ya kusa bige ki amma ko ya tsaya ya bada Ha'kuri kawai yayi gaba,Allah mun gode maka da be ture ki ba, da haka zai wuce ya barmu daga gani Wannan me motar ba Mutumin kirki bane ba!"I'man tafyanzu wayar Ummy nake kira na tambaya kun taho,tace kun taho tun ɗazu"

ta faɗa tana basu hanya Khadija da ta cire niƙab ɗin fuskarta tana cewa "ai munyi sauri ma dake bamu sami matsalar abin hawa ba muna fituwa muka samu"Mame ce taga Khadija ta cire Hijabi tace "kaiiii'Bisty irin Wannan Wanka haka amma kika tashi kika rufe da Hijabi harda su niƙaf,ba makawa da mayafi kika sa duk wanda ya ganki bazai iya ɗauke Ido ba,yuh'nima danake mace naga kyanki ina ga Namiji"I'man ce tace




 "Hmmm Yanzu muna sauka daga ɗan sahu saura kiris Wani Mahaukacin me Mota ya kaɗeta Allah yayi babu rabun Shan Wahala,kuma abin haushin ko tsayawa ya bamu haƙuri beyi ba ya buɗe mu da ƙura ya ƙara gaba, kuma daɗin abin haushi wai Anty Khadija har Uzuri take mai Wai ko sauri yake ya tafi Masallaci,ki jifa"


Khadija dake ta bugawa I'man harara ce tayi Saurin cewa"toh'I'man idan na nuna ɓacin rai ko na ƙi yi masa uzuri,Shifa ba tsayawa yayi ba daya tsaya ai kinga shine kuma ni yanzu ma gani nake laifi nane daban duba na ga da Mota ko babu ba"


Mame ce tace"gaskiya Shima be ƙyauta ba amma mudai mun gudewa ALLAH dayasa be kaɗe ki ba"


Khadija ce tace "Wai ina Antyn!" "yanzu bata daɗe da hawa sama ba ku zo mu haura saman nima daga nan na shirya ki raka ni inda na faɗa mikinan!"Mame ta faɗa tana miƙewa Khadija ce tace "ai Yarinya baki isa ba ,nima ina alƙawarina!" 


Dariya Mame tayi tana cewa" Wai dama da gaske kike toh'ba nazo nayi miki ya na iya tunda inaso ki raka ni"



Sama suka hau suka shiga Wani falo Mame ta fara kiran "Mom,Mom,Mom gasu Bisty sun ƙaraso fa"

Wata kya-kyawar mata ce ta fito dagaWani ɗaki tana ta zuba fara'a tace "Sanunko da zuwa ƴan albarka "


Rungumeta sukayi Sunanan suka za zauna suna gaishita amsawa tayi cikin fara'a tana tamyarsu ya suka baro Yayar ta da lafiya lau suka amsa


I'man ce ta miƙa mata ledar da Ummy ta basu tana cewa "gashi inji Ummy " karɓa tayi 


**********


Balarabe da fituwarsa gaba ɗaya cikin sauri yake murza sitiyarin Motarsa yana ƙara gudun Motarsa hankalinsa gaba ɗaya yana kan titi burinsa kawai ya isa gidan Ammy ya sauke su Meme su wuce masallaci dan sun kusa makara,


Sam be kula da wata da motarsa ta kusa bigewa ba cikin minti na ƙalilan suka ƙarasa gidan Ammy


Horn yayi me gadi na buɗe ƙofa yace su sauka su shiga ,Sauka sukayi da tai makon me gadi daya sauko da Nimrah saida suka shiga gidan Sannan ya tafe Masallaci Shi da Aiyman


**************


Khadija bayan sun gama cin Wainar fulawa,Sunyi Sallah Mame dama tayi Wanka bayan tagama suya Waina,


Shiryawa tayi cikin Wata Baƙar duguwar riga Wadda tasha adon duwatsu tayi roling da mayafin rigar,Khadija ma hoda ta Shafa Suna cikin ƙwaliyar Saudat dake falo ta shigo tana cewa"Anty I'man Yaya Adnan yace kizo!"


Mame ce ta kwashi da dariya tana cewa "kaga shalelan Yaya aje asha Soyayya"Khadija ce tace "nima nace Soyayya suke tace Wai Shaƙuwa ce da Soyayar ƴan'uwan taka kawai"cikin dariya Mame tace "intai Wari maji"


I'man fita tayi tana dariya,sukuma bayan sun gama Shiryawa fituwa sukayi Mame ta shiga tace da Anty Kubrah sun tafi,


Anty Kubrah tayi musu ALLAH ya kiyaye hanya da cewa su dawo da wuri da "toh"suka amsa Mame tace "Mom dan ALLAH ki bani mukulin Motar Dady,Wallahi zanyi tuƙe a hankali"cikin marai-raice murya kalar tausayi tayi maganar,Mom cewa tayi "a'a baruwana me yasa baki tambaye shiba kafin ya fita ba kije ki tambayi Adnan ko zai baki makulin Motarsa inba fita zai kuma yi ba"juyawa tayi tana cewa "Allah yasa ya bani" Wajen Adnan taje shima yace fita zai kuma yi haka suka nufe titi badan Ranta ya so ba Keke napep suka tare tace masa RIJIYAR ZAKI........


Kuyi haƙuri yau naso na kai har inda Khadija zata haɗo da Balarabe amma Wani uzuri ya katsini ko biyoni a pg ɗin gaba dan jin ya haɗuwar zata kaya....



 *SHARE* & *COMENTS* 

  


    *MAMAN* *NABEELA CE...* ✍️