ZAYN MALIK

Chapter -5

by @maidambu41

_....ZAYN MALIK....✿_

*EXQUISITE WRITERS FORUM*

  

       Mai_Dambu

CHAPTER-5

Har ta fita ta kuma lekowa,

"Alhaji karka yi taurin kai ba a kunyar ciwo ka nuna dan dai kawai likita ya bukaci na fita ne ai ko da kaina zan danne ka a ga yanayin ai baka fi karfina ba"

Kamar ya nutse kasa, shi da Allah yayi shi ko abokansa baya yarda su yi maganar batsa a gaban shi, sabida kare kan shi daga zina, tana fita likitan ya mishi yaƙe.

"Da me za'a taimaka maka" dauke kai yayi yana latsa wayar shi,

"Ok sir"

Kallon Dr yayi shima ya kalle shi.

"Taya zan taimaka maka?"

"Ka ga nayi maka da me niman taimako ne?"

"A'a kwantar da hankalinka"

Mikewa yayi sannan ya ce.

"Nace maka a tashe yake?"

Ya tambaye shi, fahimtar da yayi Zayn dan zafin kai ne, yasa shi cewa.

"Ok zaka iya tafiya"

Wata uwar harara ya wurga mishi, sannan ya koma ya zauna,

"Kasan me? Ka rubuta min sunan maganin da zan nuna mata"

Daukar takarda da biro me stemp na asibitin ya rubuta mishi su Vitamins b Complex, mentors na mura, da su tom-tom, ya mika mishi yana cewa.

"Allah ya kara sauki a kula da Kaka tana son ka da yawa, shi yasa take kallon kamar baka da lafiya." Cikanka bai ce mishi ba ya bar dakin. Yana futa ya samu Hajiya da Abul ta saka masu ganin Likita a gaba tana rabtabo bayani.

"Ai tunda yarinyar nan Judaal tace min bai da lafiya na zata karya ne, ashe dai Yaron nan kwana yayi yana abu daya, ga namiji har namiji wannan da ace a lokacin mu ne ai mata uku zuwa hudu gare shi."

"Hajiya" ya kira ta da wata irin murya me ban tausayi.

"Ayya dan Albarka ba dai an fito ba, maza muje" kunshe dariya Abul Khair yake har suka bar asibitin kowa sai kallon shi yake.

A wani babban store suka tsaya suka sayi magani, sai haɗe rai yake, kamar wanda aka aiko mishi da sakon mutuwa. Koda suka isa cewa tayi.

"Zo nan nasan sarai sai ka iya ajiye maganin kawo nan ba zan yi asarar kudina ba, idan lokaci yayi ka shigo ka sha, Allah ya baka lafiya" ko Inda Abul Khair yake bai kalla ba, ya wuce part din shi ya samu an gyara ko ina tsaf, sannan ya ji motsin Abu khair.

Kwanciya yayi a dogon three siter, yana kad'a kafar shi.

"Dan Ubanka baka da mazauni a gidan nan fita kafin Naci Uban ka" dariya Abul Khair ya saka yana kallon shi.

"Haka dai Man, Ni nasan lafiyar ka lau, ya zamu yi da Hajiya? Tace baka da lafiya "

Banza yayi da shi ya Lumshe idanun shi.

"Mr Malik kwantar da hankalin ka, kayi aure sai ta daina maka kallon jiya Mama ta haife ka, ina tausayin ka tunda Hajiya tayi sanadin rashin aikin ka na soja na gane tana kaunar ka bata son kayi nisa da ita ne " bude idanun shi yayi tare da kallon Abul. Tsaki yayi yana tuna shekaru uku da suka wuce haka kawai Hajiya ta sheke mishi aikin sojar shi.

***

Zayn Malik

Cikakken sunan shi Zayn Abdul Malik Zain Malami shine cikakken sunan shi, Mahaifin shi Alhaji AbdulMalik Zain Malami dan babban malamin jami'a ne a kasar Ingila domin yana cikin mutanen da Turawan Ingila suka diba aka tafi da su Ingila suka yi karatun boko, kasancewar lokacin da turawan mulkin mallaka suka shigo sun so diban yaran manyan mutane, amma fir manyan mutane suka ki, dole aka haɗa Yaran talakawa, aka tura su kasar waje, inda suka tafi babban kwalejin gwamnatin Birtaniya koyar harshen turanci. mahaifin Zainu baduku ne, yana aikin sana'ar Jima na fata, da kasuwancin ma daukar fata daga arewa zuwa kudu, a can ya sayar sannan ya sayo wasu abubuwan ya kawo arewa.

  Wannan abin yake har aka dauke Zainu, bayan shekara biyar Allah ya dawo da Zainu daga kasar waje, sai aka bashi koyarwa a wata Makarantar elementary school anan kaduna, lokacin kaf arewa makarantar ce a kaduna. Shekaran shi biyu da dawowa aka kuma tura shi ya tafi ya haɗa diploma a harshen turanci, bai yarda ya dawo ba, sai da ya samu wata kamfani da take yin jakuna da takalma a lokacin ya nime su bashi kwangilar kawo musu fata, kuma lokacin akwai yarda da amana, sai suka gwada shi su ga yanayin shi.

Alhamdulillahi watan shi daya da dawowa ya tura musu da fatan da yafi karfin kudin da suka bashi, domin shima yayi mamakin yadda suka yarda da shi, bayan wata bakwai suka zo har kaduna aka suka bada kudin fata sama da aka kai musu.

A hankali Allah ya saka albarka gashi lokacin ta ruwa ake tafiya, idan kayi tafyya ta jirgin sama toh wasu ne daga manyan jami'an gwamnatin Birtaniya.

Ana haka Mahaifin shi ta hada shi aure da Sadiya wato Hajiya Umma, aka sha biki domin lokaci bata wuce shekara sha huɗu ba a duniya, haka tayi ta guje guje a haka har ta samu cikin Babban yarta Rabi, domin matan da idan aka yi auren su, haka suke sai su yi ta gujegujen kamar basu so, daga nan idan miji ya kama mace sai dai a ji mace da ciki.

Sai da cikin ya kai watan haihuwar shi sannan ta daina gudu,

Tana haihuwan aka saka mata Rabi, ai kuwa a lokacin babban kwalejin ilimi na nan Kaduna da yake Zaria suka dauke shi malami, sai cigaban yazo mishi a daidai ga aikin ga kasuwanci.

Bayan shekara biyar ta kuma haihuwar AbdulMalik Baban Zayn, kai an nuna mishi gata da soyayya,. Shima yana da shekara biyar aka haifi Uwaisu. Ba karamin al'amari bane ya faru a wannan shekaran domin a lokacin aka mai da shi lagos ya zauna a can ya matsayin baturen ilimi, a shekaran dai ba karamin cigaba aka samu ba,.dan ma turawan biritania sun bar kasar sai aka bashi aiki a babban office din shugaban kasa a karkashin jagorancin mulkin farar hula.

Sai da Hajiya umma ta cire rai da zata kuma haihuwa kafin Allah ya bata haihuwa Bashir wanda dama rabon ta da haihuwa shekara goma sha biyu.


Haka suka ta rayuwar su, Malam Zainu taka mataki daban daban na gwamnati, haka a lokacin AbdulMalik yana barewa College,.sandan da shine elementary school aka mai da shi barewa College.

Yana aji uku suka hadu da AbdulMalik AY da Mustapha Umar, sune abokan shi kaf Makarantar, kuma wani abin burgewa yaran manyan mutane ne a makarantar, haka yasa baka gane su waye su dan kan su a hade hatta provisions din su a hade yake, tsautsayi yasa suka tsallaka katangar makaranta, suka tafi cikin gari wurin budurwan Mustapha.

W


acce ta kasance Yar yayan Hajiya ce, Hafsat nan dai shugaban.karanta ya tura sakon ga Baban AbdulMalik da kuma shima Mustapha da AbdulMalik AY.


    Labarin na isa gidajen su, ba a dauki lokaci ba duk da lokacin suna aji biyar na Sakandire, kamar hadin bakin iyayen suka musu aure, sai Mustapha ne mahaifin shi ya ce bai kai na aure ba, dan haka suka kyale shi amma daga AbdulMalik AY da AbdulMalik Zain Malami suna da mata, kuma sai ya kasance suna jin kunyar fada suna da aure, a haka suka gama makarantar, sannan kowannen su ya kama abinda yake bukata. Shi AbdulMalik Zain Malami ya samu gurmin karatu ne a Birtaniya, yayin da AY ya samu karatu a Scotland anan ta tafi karanta shi, shi kuma Mustapha Umar ya tafi jami'ar Ahmadu Bello, domin mahaifin shi yaki yace kar dan shi ya lalace, kuma abinda yake gudu kenan sai da haka ya faru,

AbdulMalik kan ya tafi da matar shi ne, a can ya sakata a primary school,dan haka ya iya hakuri da matsa mata tana karatu, har ta samu Cikin Fatima, haka bai hana ta karatu ba.

Kuma turawan sun yi matukar maraba da haka, tana aji uku ta samu cikin, yarinta da shirme bai saka ta ji Damuwar cikin ba, asalima sai ta maida hankali sosai akan karatun har Allah ya sauke ta lafiya.

Ai kuwa turawa har misali suke da ita, Fatima tana da shekaru uku ta gama primary school, ta samu high school, sai da ta fara karatu gane tana da ciki, abin bai dame ta ba haka suma hukumar Makarantar sun kara mata kwarin gwiwa,

Haka rayuwa yayi ta tafiya har ta haifu Hauwakulu, suna kiranta Kulu.

A lokacin kokarin ta da mai da hankali yasa suka yi ta promotion dinta, Hawwa'u tana da shekaru hudu ta gama high school, a lokacin ta ce tana son ta karanci fanin nurse, bai hana ta ba, sai ma tsaya mata da yayi.


Bata kuma haihuwa ba har ta gama degree ta a nursing College of Manchester dake anan yake karatun shima yana karantar kimiyyar siyasa, har ya fara aiki dasu, Mahaifin shi ta turo mishi da sakon lallai ya dawo gida. Haka ya saka ya ajiye aikin shi. Suka dawo gida, ai ganin Yaran su mutane suka saka ta a gaba ita kanta Umma bata jin dadin haka, amma babu yadda ta iya musamman dake dangin Uban AbdulMalik ne akan maganar, tana ji tana gani aka bawa AbdulMalik auren Umaima, aure da rabo sai ga cikin bata shekara a daki ba, ta haifi Sadam sannan Wani abin shine gorin da aka saka Mama a gaba da shi, haka yasa ya nima mata aikin asibiti bata zaman gida, a lokacin Yaran ta biyu daga Fatima sai Hawwa'u, ba karamin kai zuciya nesa tayi ba,

Haka Umaima tayi ta zuba yara kuma akai-akai, sai da tayi yara maza huɗu.

Sadam, Samir, Sagir, a lokacin ba karamin gori da bakar magana Mama tasha ba, dan ma Malami da Umma basu iya hakuri suma tankawa suke suna kare Mama wacce sunan ta Abidah,

A haka Umaima ta kuma samun wani cikin inda itama Mama tasamu cikin sai dai aka yi rashin dace na Umaima bata haifa da rai ba, ai tayi tsalle tace asiri Mama ta mata, ita kuma Mama ta haifi ya mace aka saka mata Sadiya.

Ganin haka shima ya kuma rura wutar Masifar da yake ci a gidan domin takwaran Hajiya ce, Uwaisu ya auri Maimuna itama ta haifi danta Abdullahi,.sai Bashir ne kawai bayi aure ba, domin karatu yake bana.wasa ba kuma bai da uwar daki da ya wuce Mama.

Wani ikon Allah daga Umaima da Mama babu wacce ta kuma haihuwa a lokacin Allah ya kara budawa Alhaji Abdulmalik, shekarun kusan tara, Mama ta kuma samun ciki, ita kanta bata san tana da cikin ba, sai da abokan aikinta a asibiti suka sata a gaba da tsokana, suka sakata a gaba tayi test sannan aka gano tana da cikin sai tayi ta boyewa domin a lokacin za ayi auren Fatimah, aikuwa abin bai mata dadi ba, domin duk kokarin ta na boyewa sai da tayi ta laulayi me zafi. Shi ya fahimtar da kishiyar ta aka san da cikin,ina wutar da za a saka mama wato shine ta rigata samun ciki.

Haka ta sako ta a gaba sai da fitina, aikuwa Alhaji Abdulmalik yace bai iya jin magana ba, karshe sai da tayi sanadin igiyar ta daya,dan haka ta tsani cikin.

Koda ta dawo, tayi shiru amma na kasa na kasa, har Mama ta kusan haihuwa a lokacine Mijin Umma ya rasu, rasuwar shi ya girgiza Umma har surukan shi.

Watan sa biyu da rasuwa Allah ya sauki Mama lafiya yana dirowa duniya kowa yasan namiji ya dawo, tunda Hajiya Umma ta gan shi,taji duniyar nan babu jikan da take so sama da shi, haka dai suka gama hutawa,sannan suka dawo gida.

Ba karamin haushi haka yake bawa Umaima ba, soyayyar duniya aka daurawa Zayn hatta Fatima da take gidan mijin ta a Zaria, sai da tazo, Ya Rabi daga Lagos suka zo ta Zayn , haka ayi suna yaro yacu sunan malami, kusan rabin rayuwar Zayn a hannun Hajiya ne, ga shi a lokacin tana sayar da kamu.

Haka da ya fara rarrafe yayi ta zubar mata da gasara, kowa zai yi fada amma Hajiya zata daka tsalle tace kar a cinye mata jika da baki.

A hankali Zayn yake girma yana kara zama mara jin magana, da fitina a cikin gidan baki daya. Dan ko ita tayi Yayen shi, da aka zo yin kaciya, ba karamin hidima aka ayi ba, zaka dauka wani karamin kauri ake domin kajinta da zabi agwagi haka ayi ta yanke su, ga farfesun kan sa da ake mishi, hajiya tayiwa Zayn wani irin goyo ne na sakalci, yana da shekara e masu sayan kamu basu isa suyi ihu a cikin gidan ba, idan kuwa za a. Shigo saya toh insha Allah sai dai kafin ya tashi idan ya tashi kuwa ya ce Hajiya ki rufe ba zaa sayar da shi ba, Hajiya zata ce toh ranka ya dade, ai kuwa ba zata sayar ba koda kuwa baya shashinta wato yana part din Mama.

Idan ya fita kofar gida kuwa Insha Allah tara duwatsu yake yayi ta Jifar jama'a da shi,.Zayn ya fasa kan Yaran Jama'a,.ya ci zalin yaran mutane idan yara suka amso nikar gari, hka yake tare su ya zubar, ya musu Shegen duka, gashi da dan banzan naci baya hakuri idan ka dake shi, kullum fadar shi sabo ne. Har Fulani suka daina zuwa ta kofar gdan sabida Zayn domin yasha fasa musu nono akan su, haka za a kai karan shi Hajiya zata biya kuɗin, tana yawan cewa.

Allah ya bata abinda zata biya matukar bai fi karfin ta ba, ko yafi karfin ta zata ci bashi ta biya.

Haka aka saka shi a makaranta ya kama dan ajin su ya mishi duka, aka kawo karan shi har da Yan sanda. Hajiya da Mama suka tafi a ranar Hajiya Umaima ba karamin murna tayi ba. Ita burin ta kawai Zayn lalace.

Yana da shakara goma ta haifu Muhideen, lokacin yana gab da gama primary school, gashi jinin su bai hadu da na Yaran dakin Umaima ba, wai cewar ta kar ya lalata mata Yara.

Yana gama primary school, a lokacin aka yi bikin Uncle bashir Dake duk gidan baya yarda tafi kowa sai uncle Bashir, kuma dakin su daya domin a gaban Hajiya suke.

Bayan bikin Uncle bashir da Rukayya suka wuce Boston na kasar Amurka, a can ya kuma haduwa da yara marasa jin magana irin shi aka karawa Borno masu.

Amma duk shekara suna zuwa gida bikin sallah karama su koma na layya kuma a can suke, a dawowan su ne suka hadu da Abul shima fitinannen irin Zayn haba dama Zayn yana zuwa club shi ya koyawa Abul zuwa club amma shi yana niman mata, yayinda Abul ya bude idanun da niman mata dama gidan su gidan Freedom ne sai gashi kuwa yana tsulla tsiyar shi kamar me.

Amma Zayn mace bata gabansa duk abinda mace zata yi bata taɓa burge shi kawai abinda ya sani yasan duk wani nau'in kayan maye, amma yaki yarda da kowanne, sai wiwi da whiskey...

*ZAYN MALIK PAID BOOK ne 300₦ ba yabon kai ba sai dai bana wasa da zuciyar mutane*

300₦... Insha Allah'

*** a tuntube Zahrah Addah Ramlat, Yan Niger su tuntubi Nana A'ichah

+22784506476

0472282105 Ramlat abdulrahman manga GT bank

#Mai_Dambu