Chapter 15-16
*GIDAN BALARABE* 🪴
BY
🪴 *MAMAN NABEELA* 🪴
*MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION*
💃💃💃💃💃
*AUTAR MANYA*
_Ramadan bononza_
*AUREN BARE*
*ZUMA A BAKI*
*BAƘAR FATA*
*DA IZZATA*
*ƊAN MAJALISSA*
*RABON WANI*
*H A S K E*
*KOBA SO*
All in 1500 for more infor chat me up ***
*DEDICATED TO GIDAN BALARABE FAN'S* 🥰🥰🥰🥰🥰
🅿️1️⃣5️⃣↔️1️⃣6️⃣
*ASALINSU BALARABE* ?
.....Alhaji Abdallah Abdussamad ɗan fillo haifafan garin Yola ne,dake Jahar Adamawa' Mahaifansu sun Haifesu su uku Abdurrashid Shine Babba Sanan Abdallah,Sai kuma Autarsu Halima.
Mahaifinsu Abdussamad Ɗan Fillo ba Shida Sana'ar da ta Wuce Noma da Kiwo Wanda dashi yake kula da Iyalinsa,yake kuma burin Suyi Karatun Boko da na Islama.
Abdurrashid ya tashi da sun kiwo abinda Mahaifinsu keyi Wanda tun yana ƙarami yake cewa da Mahaifinsu Wanda Suke kira da Baffa Shifa idan ya girama ya Shiga Makarranta Noma da Kiwo zai karanta" Shi kuma Abdallah Yace "Baffa ni dai Ɗan kasuwa nake so na zama na gina kamfani na kaiku Makkah"Dariya Mahaifiyarsu da Mahaifinsu Sukayi Suna Adu'ar Allah ya nuna musu lokacin'ya kuma raya musu ƴa'ƴan nasu.
Halima Wadda suke kira da Halime, dake zaune tana Wasa tace"Dada ni kuma idan na girma Na Shiga Makaranta Likita zan karanta na dinga yiwa Mutane Alura"ta faɗa tana dariya.
"toh'Allah ya raya mana ko yasa muga lokacin mu kuma" da Amin Suka Amsa.
A Kwana a tashi ba wiya ga me yawan cin ƙwana,Mahaifinsu nan ya sakasu Makaranta inda Suka maida hankali Suna Karatu, bayan Abdurrashid da Abdallah sun gama makarantar Sakandire suka zauna jiran Sakamako a cikin haka Baffa ya Haɗa Abdurrashid da ƴar ƙaninsa me Suna Alawiyya Aure,duk da Abdurrashid ba sonta yake ba amma Saboda sun samu tarbiyya be nuna baya sonta ba haka aka Sha Biki a ka kawo Amarya nan cikin gidan inda Baffa ya Ware masa'cikin haka Jarrabawa ta fito Bisa jagorancin ɗan gidan me gari Suka duba Jarrabawarsu inda saka mako yayi ƙyau Farinciki ba'a magana.
Nan aka fara ciku-cikun nema musu gurbin Karatu inda Abdurrashid ya samu gurbin Karatu anan Adamawa yayin da Abdallah ya samu gurbin karatu a Kano'Ansha fama kafin Baffa ya yarda Abdallah ya tafi Kano inda ya Shiga B.U.K ya fara karatunsa ba ƙaƙautawa, cikin Haka ya Hado da Wani Aboki Me suna Khalid Wanda ya kasance Shi ɗan Kano ne kuma Shima Kasuwanci yake Karanta tafi-tafi Shaƙuwa me ƙarfi ta Shiga tsakaninsu,Wnda lokuta da dama Khalid kance yazo suje gidansu cikin Haka Abdallah ya ƙyalla ido akan ƙanwar Khalid Me Suna Aisha, nan ya fito ya nunawa Khalid Shifa ya ga ƙanwarsa yana So Khalid yayi matuƙar farin ciki da jin Wannan Kalami na Abokinsa,Wanda yake jinsa tamkar ɗan uwansa na Jini.
Nan ya goya masa baya yace yaje su dai-dai ta da ƙanwar tasa"cikin ikon Allah daya je ita ma Aisha tayi Na'am dashi nan suka fara Shimfiɗa Soyayya Me cike da Tsabta, Wadda tasa in ɗaya bega ɗaya ba ya kan Shiga Wani hali.
Ɓangaren iyayin Aisha Suma sunji daɗin Wanan Al'amari dumin Sun yaba da ɗabi'un Abdallah da tarbiyarsa.
Cikin Haka ƙongiyar ASUU ta tafi yajin aiki Wanda yasa duk Wasu Ɗalibai suka kuma gida har sanda Za'a kumo Sannan Su dawo'Zo kaga tashin hankali gurin Aisha da Abdallah dan ji suke kamar kar su rabu, Haka Suna ji Suna gani Suka rabu badan sun so ba.
Mahaifiyar Aisha tayi Mishi Alkairi Susai tace ya kaiwa Mutan gida,nan yayi mata gudiya yana daɗa yaba Halin karamci irin na Mutanen.
Lokacin da Abdallah zai tafi yake yiwa Aisha Alƙawarin Insha'Allah daya je zai Sanar da iyayainsa ya Samu Matar Aure da jin Wannan batun nasa yasa Hankalinta ya ɗan ƙwanta.
Khalil Abokinsa ya raka shi tasha ya hau Mota Sai da ya ga tashin Motar Sannan ya juya gida.
Ya sauka lafiya inda ya tarar da gidan kowa sai Murna yake da dawowarsa bayan ya huta ne, Nan yake jin labarin Alawiyya Matar Abdurrashid ta haihu tasami Ɗiya Mace'cike da farin ciki ya ɗauki yarinyar da taci Sunan Dada Mahaifiyarsu Watu Hafsa yana me jin ƙaunar ƴar ɗan uwansa har cikin Ransa Adu'a yayi mata Sanan Mahaifiyarsu ta karɓi ƴar tace yaje ya daɗa hutawa,
Jakar tsarabar da yayi musu ya miƙawa Mahaifiyar tashi yana cewa "Dada Ina Yaya Abdurrashid ne naga banganshi ba!"
"Sun ɗan fita guna ne da Baffan ko yanzu za ka ga Sun dawo" "Allah ya dawo dasu lafiya ya faɗa yana tashi Ɗakinsu na zaure ya nufa Wanda Halime ƙanwarsa ta gyarashi bayan zuwansa har da su turare ta saka
ɗakin sai ƙamshi yake,yana Shiga ba daɗewa Baffa da Abdurrashid na dawo wa tun daga Waje aka fara faɗa musu ai Abdallah ya dawo cike da farin ciki Abdurrashid ya shiga Ya bar Baffa a Waje suna Magana da Wani Maƙocinsa,
Ɗakin zauren ya nufa yana turashi cikin tsananin farin ciki ya shiga bakinsa ɗauke da Sallama Abdallah jin Muryar ɗan'uwansa yasa ya tashi da sauri ya rungume shi' Zama Sukayi nan suka gaisa yana yiwa Ɗan uwansa Murnar ƙaruwar da suka samu.
Nan suka tashi Suka Shiga Cikin gida, Suka Shiga Dakin Baffa Abdallah zube gwiwoyinsa yayi yana me gaida Baffa cikin farin ciki da jindaɗin ganin Ɗan'nasa yake amsawa yana tambayarsa Yana yin abinda ya kaishi ko!Hadi da nuna damuwarsa Na rashin jin Wane hali yake ciki,cikin kwantarwa da Mahaifinsa Hankali yake Shaida masa yanayin karatu Susai nan yake Bashi labarin Khalid da yadda Iyayin Khalid Suka ɗauke shi Tamkar Ɗansu,yace gaba da bashi labarin harma Sun fara Shiga kasuwa Bisa jagurancin ɗan'uwan Su Khalid ɗin daya ke a kasuwar Singer,a duk ranakun da basu da Karatu Suke Shiga. Amma be faɗawa Baffa ya samu Matar Aure ba Saboda kunya irin ta fulani.
Baffa yaji daɗin Bayanin da ɗan nasa yayi masa nan yaji Hankalinsa ya ƙara kwanciya,Nan yake Shaida masa ƙanwarsa Halime ɗan wan Baffa Watu Haliru Shi zai Aure ta Har ma an tsaida rana'nan da Wata ɗaya dan haka Shima ya Shirya nan bada jimawa ba za'ayi masa Aure,ƙasa ya ƙarayi da kansa jin batun Baffa yana me cewa"dama Baffa nima na samu Wadda Muka dai-daita a chan"ya faɗa yana me ƙara yin ƙasa da kansa cike da jin nauyin Mahaifi nasa.
Cikin Sauri Baffa ya ɗagu Wanda yayi dai-dai da Shiguwar Abdurrashid Wanda Shima yaji Me ƙanin nasa yake faɗa Nan Baffa ya birkice yake ta faɗa ta inda ya Shiga ba tanan yake fita ba,Shi A ganinsa gida be ƙoshi ba ai ba'a tafi dawa ba, nan Mahaifiyarsu ta Shigu itama jin faɗan Baffa Nan take jin abinda yake faruwa Haƙuri ta fara bawa Baffa tana nuna masa fatan alkairi yaka mata yayi Masa karya ce zai Hanashi aurenta.
Da ƙyar da Suɗin gushi Suka Samu Baffa ya haƙura ya yarda Nan yace zai yi Shawara,Tashi sukayi Suka fito jin kiran Magriba'bayan Sun idar da Sallah ne Abdurrashid yake kwantarwa da ɗan uwansa hankali ganin duk ya Shiga damuwa.
Washi gari Bayan Sun karya Abdallah da ɗan'uwansa Suka zaga Yan'uwa nan duk Wanda ya ganshi yake cewa Kano ta karbeshi ya zama Babban mutum Saura Aure dariya kawai yake yi haka suka za ga dangi Suka dawo gida
A kwana a tashi Satin Abdallah biyu da dawuwa inda ta ƙaramar Wayar da ya Siya suke gaisawa da Aisha da Khalid ,Kwance yake gama Wayarsu da Aisha kenan Abdurrashid ne ya Shigo ɗakin yana ta fara'a cewa yayi "kaje Baffa Yana kiran ka Da alama sun yarda da Aurenka da ƴar kano amma dai kaje kai Suke jira"cikin Sauri ya tashi yana Me adu'ar Allah yasa haka ya fita ɗakin Baffan ya nufa nan ya ga takalma alamun ba Shi kadai bane a ɗakin.
Da Sallama ya Shiga yana me gaishi da ƴan'uwan Mahaifin nashi amsawa Sukayi Suna yi masa tsiyar Watu Shi ya tsallake gida ya tafi dawa ƙasa ya ƙarayi da kansa yana Me fargabar abinda kunensa zaiji
Baffa Ayuba ne ya fara yi masa tambayoyi akan ita Wadda yace yana So ɗin,yana bashi amsa Suna gama jin amsar sa suka ce yaje zasuyi Shawara
Tashi yayi ya fata nan Su kuma suka yanke yadda zasu nemawa ɗan naso Auren.
Ƴan Yola Sunje Sun nemuwa ɗansu Abdallah auren Aisha in da Iyayin Aisha suka ji daɗin zuwansu tarba ta musamman Suka yi musu nan Aka tsayar da Biki lokaci ɗaya da na Halima,Zo ka ga farin ciki gurin Abdallah da Aisha.
Ƙungiyar ASUU ta sanar da janyi yajin aikin da take nan Ɗalibai suka fara haramar kumawa Makarranta
Abdallah yayi Shiri Susai inda Mahaifiyarsa da Ƴan'uwa suka haɗa masa koɗi da kayan amfani Wanda zai tafi dasu,ya kuma makarranta inda suka cigaba da karatu ba ji ba gani,yayin da Biki yake ta daɗa Matsuwa duk Wasu Shiryi-Shiryi Suna ta yinsu inda Baffa ya turowa da Abdallah koɗi yace ya kama ko haya ce.
Khalil Shiyayi Masa jagora har ya Samu Wani ƙaramin gida Wanda koɗin da Baffa ya bayar Suka isa aka siyi gidan,
Biki ya zo aka ɗaurawa Aisha da Abdallah Aure inda Suka tare a gidan Soyayya Suke me cike da Tsabta inda Bayan Shikara biyu da aurensu Allah ya a zurta su da Samu Ɗa Namiji Wanda Suka Sa Masa Suna Abdussamad Wanda Abdallah yayi Wa Mahaifinsa takwara.
A lokacin da a ka haifi Abdussamad a Shikarar Mahaifinsa ya gama B.U.K a lokacin kuma kasuwancinsu yake ta bunƙasa Wanda a Shikarar Abdallah ya Mallaki Shago nasa a Kasuwar Singer Wanda cikin ikon Allah Kasuwancinsa ke hau hawa
Abdussamad yaro ne me tsananin kyau Wanda ya ɗebo kyaun Mahaifanshi Wanda Sandin kyawunsa yasa tun yana ɗan ƙarami Mahaifiyarsa kansa ayi masa rubutun baki Saboda duk inda taje dashi Bakin Mutane yayi yawa A kansa,Shikararsa biyar Allah ya kuma a zurtasu da ƴan biyu Mata Waɗan da suke Suma kyawawa A wannan lokacin ne Khalil Yayan Aisha Shima yayi Aure, Wanda kuma a lokacin ne Abdallah dukiya ta daɗa hau hawa Wanda ya biya Dada da Baffa aikin haji ya sake gida ya kuma RIJIYAR ZAKI inda ya gina kata faren gida
A lokacin kuma a ka Saka Abdussamad Makaranta
Wanda tun daga lokacin ya haɗo da Haidar abokinsa Wanda daga lokacin kuma aka fara kiransa da Sunan Balarabe a cewar abokansa Shiɗin beyi kama da ƴan ƙasar Baƙar fata ba..............
*SHARE & COMENTS* 🙏🙏
*MAMAN NABEELA CE...✍️*