Chapter19-20
🪴GIDAN BALARABE🪴
BY
🪴MAMAN NABEELA🪴
***
*MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION*
💃💃💃💃💃
*AUTAR MANYA*
_Ramadan bononza_
*AUREN BARE*
*ZUMA A BAKI*
*BAƘAR FATA*
*DA IZZATA*
*ƊAN MAJALISSA*
*RABON WANI*
*H A S K E*
*KOBA SO*
All in 1500 for more infor chat me up ***
*DEDICATED TO GIDAN BALARABE FAN'S* 🥰🥰🥰🥰
*MUCH* *LOVE* 😘😘😘
🅿️1️⃣9️⃣↔️2️⃣0️⃣
*MU DAWO LABARI*
.....Toh Allah ya kiyayi hanya"ta faɗa tana ƙoƙarin maida ƙwallar dake neman Zubuwa ya tabbata Zarginta ya zama gaskiya.
"Na Shiga uku ni Asiya kardai gidan So ƴarinyar Zashi"nan ta tashi ta kai ta kawo batun ɗaukar Waya Ma ai ta latsawa babu dumin ba kwanciyar hankali'
ƙannun idanonta Masu zube dana ƴan'chaina nan suka ƙara kuma wa ciki,yadda kasan ji tayi yace Mata gurin buduruwa zashi.
😏nikam nace Asiya kina ruwa,Hhhh
Ɓangaren Balarabe yana fita Motarsa ya hau ya bata Wuta, gani nai yayi Hanyar Rijiyar Zaki nan na ƙara Sauri karya bace min.Lol
Gidan Mahaifanshi ya koma inda yana zuwa ya danna Uban horn,ɗiiiiiiiiit,ɗiiiiiiiit, nan Buzu ya kwaso da gudu yana Wangale gete ɗin ƙasa-ƙasa yake faɗin "toh'Shi kuma Alhaji ƙarami ko me ya dawo dashi daga tafiyarsa!ina ga Mantuwa yayi"ya faɗa yana Zuwa gurin Motar bayan ya rufe gete,yana Dai-dai ta perkin Buzu ya Buɗe masa Motar ya fito yana zuba fara'a'yadda kasan Wanda yayi Sabon Aure.
Ƙofar Sashin Abby ya nufa Wadda take ta Waje Norking yayi daga Ciki yaji an bashi izinin Shiga,tura ƙofar yayi bakinsa ɗauke da Sallama, Abby dake zaune yana kallon Labarai Shi da Ammy kwanun kayan Marimari ajiye a gabansu Suna Sha,Suka amsa jin Muryar Ɗan nasu yasa Abby Daɗa Faɗaɗa Fara'arsa yana cewa"A'a Son kaine da daren nan!"
Susa kansa yayi yana me ƙarasa Shiguwa cikin Falon,Kusa da ƙafafun Mahaifinashi ya Zauna yana cewa"Abby Barka da Dare,Ammy Barka da dare"ya faɗa yana Satar Kallon Mahaifiyarshi.
Abby ne ya Amsa yana cewa"Lafiya lau Baffana,Ina fatan dai lafiya"Susa kansa ya ƙarayi yana Sunkwi da kai yana Daɗa Kallon Ammy ta gefen ido,Ammy da batai Magana ba tunda ya Shigo tace"Son"Ɗaguwa yayi Amma be kalle ta ba,kallonshi tayi Sosai nan ta fahimci akwai abinda yake buƙata dan So tari in yana buƙatar Abu tun yana ƙarami haka ɗabi'arsa take baya iya fitowa kai tsayi yayi magana Sai dai kaga yana Sosa kai cewa tayi"Menene?"
Abby dariya ya farayi yana cewa"faɗi kaji Baffana"
Susa kansa ya ƙarayi Sanan yace"Abby dama Yarinyar da Suka zo gurin Huda ɗazu Nake So a tambayar min In ba'ayi Mata miji ba !"ya faɗa yana Murmushi yana ci gaba da Susa kansa.
"ahf dama na lura dakai ɗazu"Ammy ta faɗa tana dariya,Abby ne yace"toh' Masha'Allahu da alama kai ka biyu Arɗo Mahafinsu Baffa tunda ka ɗauko hanyar Mata huɗu"Dariya Ammy tayi tana cewa"ƙwarai kuwa ai indai yarinyar da Nimrah tayi ta kuka ɗazu Sai ta bita ce nima na yaba da nutsuwarta"
"Wacece yarinyar kuma ƴar ina ce?" Abby ya faɗa yana kallon Balarabe.
"uhm tace min a Hotoro gidansu yake amma gidan Alhj-Mujahid kwangila ɗazu Suka kuma Wanda nake kyauta Zaton ƴan'uwansu ne"
"ah indai haka ne bari gobe in Allah ya kaimu zan nemi Alhaji Mujahid ɗin Sai muyi Magana"Abby ya faɗa.
Balarabe fara'ar fuskarsa ce ta ƙara yawa yace"Abby Allah ya kaimu" "Amin"Su ka amsa nan Suka ci gaba da harasu Ammy na tayi mai tsiya Shikuwa Sai fara'a yake,
Be bar gidan ba Sai tara da rabi yayi musu Sallama ya tafi'yana hanya ya fara gwada layin da I'man ta bashi
nan yaji Busy da alama amfani ake da Wayar,kuka kira yayi nan Allah yasa ta shiga nan ya rage gudun Motarsa.
Khadija kuwa tunda ta idar da Sallar Isha'i Salman ya ke kira taki ɗauka sai da ta gama duk abinda zatayi ta kwanta lokacin ƙarfe tara a lokacin ya kuma kira I'ma da Wayar ke hanunta tana kallo ta miƙo mata tana cewa"gashi ya kuma buguwa Allah sarki Wallahi har ya fara bani tausayi dan Wallahi Wannan Mutumin na dazu yasin kwaf ɗaya Ziyi Masa naga alama, dan na tabbata da Shine baza kiyi ta kallo yana kira ki ƙe ɗauka ba"
ba tare data kula Maganar daI'man keyi ba ta ɗaga Wayar Haɗe da faɗin"Assalamu alaikum"tana jiyu a jiyar zuciyar da ya Sauke me ƙarfi Sanan yace"Amin Wa alaikissalam Gimbiyata Wallahi kiris ya rage zuciyata bata buga ba yau Wuni sir banji da da ɗar muryarki ba"numfashi ta Sauke tana cewa"uhm Bana kusa da Wayar ne" "kun dawo lafiya ɗazu ance min bakya nan"
"Lafiya lau"Khadija ta faɗa,nan ya fara zubo Mata hira har ƙarfi tara da rabi inda nan ma Sai da tace barci take ji Sanan yayi mata Sallama cire Wayar tayi a kunenta nan kira ya kuma Shiguwa,Number ce nan ta tsaya tana Kallonta ganin Wata Special Number yasa ta tsaya tana Kallonta har ta katsi ba tare da ta ɗauka ba Wani kiran ne ya Shigo ɗauka tayi ta kara a kunenta ba tare da tayi magana ba.
Ɓangarensa Shima jin an ɗaga yasa ya perker Motarshi gefen hanya jin taƙe Magana yasa ya Sauƙe numfashi yace"Assalamu alaikiii"Jin Sautin Muryarshi Me daɗi yasa ta gane Mutumin ɗazu ne Lumshi Idanonta tayi Sanan tace"Amin Walaikumussala"cikin zazaƙar muryata,ta faɗa,
kwantar da kujerar Motar yayi Yana lumshi lumsason idanonshi masu kama da na Mejin barci,Sanan yace"ina fatan kin gane Me magana!"
"a'a ban ganeba ta faɗa tana jan filon dake kusa da ita tana rungumewa"dagaske Baki gane ni ba ko dai kin gane kawai kike nuna kamar baki gane ba!"
"da gaske nake Mana"Khadija ta faɗa "toh' ni dai ban yadda ba dan Zuciyata ta gayamin kin gane ni,kawai dai kina jamin aji ne"Balarabe ya faɗa Muryarsa na fitar da Sautin Murmushi "uhm" Khadija ta faɗa
"uhm me?" Balarabe ya faɗa yana daɗa gyara kwanciyarshi a kujerar Motar"Ba kumai fa"
"Ke dai faɗi gaskiya!"Sautin Murmushinta yaji ta cikin Wayar Wanda ya daɗa kashi Masa jiki yace"toh ya kuka je gida!"
"Lafiya lau,ina Baby!" Khadija ta tambaya.
cikin Son Sai ya Sata Magana duk da ya gane Wa take tambaya yace
"Wace Baby!"Murmushi tayi cikin Shagwabar da bata Sanin tayi ta tace"kawai dai kanaso ka rama ne dan nace ban gane ka ba Shine kaima Kace haka!"
Cikin Shauƙin Soyayyarta da tunda ya ɗora idonsa a kanta take hauhawa, cikin ƙwaiƙwayon Muryar da tayi Maganar da ita Shima yace"Nifa ban gane ba"jin yadda yayi Maganar yasa Khadija Sakin dariya,
Shiro yayi yana Saurarar Sautin Muryarta a Ransa yana cewa " ohh' Wannan yarinyar zata kashini da Salonta"
"toh'Nimrah nake nufi"yaji Maganarta tana faɗa
"oh tana nan lafiya"Balarabe ya faɗa,
Nan Su ka ci gaba da Hira Khadija kamar ba ita tace Wa Salman barci take ji ba.
Shima gogan Yadda kasan ba Shine Mara Son Magana ba ya Zage Sai zubo ta yake,Basuyi aune ba Har Goma da rabi tayi Shima Sai da Balarabe ya duba agogon Hanunsa Sanan yaga ashi lokaci yaja
Sallama yayi Mata yana cewa "da fatan zakiyi Mafarkina Anty Me kyauuuu"Saurin kashi Wayar Khadija tayi tana daɗa rungume filo tana Sakin ƙaya tacen Murmushi Adu'a tayi ta Shafa tana gyara kwanciyarta ta jima tana tunaninsa kafin barci ya ɗauke ta me daɗin gaske...
*******
Balarabe yana jin ta kashi Wayar ya Saki Murmushi yana gyara Sit ɗin Motarshi key yayi Mata ya nufi gida
cike da tarin farinciki.
*******
Asiya zaune take a Babban falon gidan yara tuni Sunyi barci Wanda Nimrah kafin tayi Barci Sai da tasha rigimar rigimar ita a kaita gurin Anty Me kyau Wanda Asiya da ta Ishita Nan ta da doke ta tana cewa ta kuma ji tana Zancan a kaita gurin Wata Sai ta fasa Mata baki nan tayi ta Kuka Meme ta Ɗauke ta Su ka tafi Ɗaki nan tayi barci.
Agogo take ta faman dubawa tunda ta Zauna har ƙarfe goma tayi' tashi tayi bayan ta daɗa duba agogo taga goma harda Minti goma Sha biyar Ɗakinta ta Shiga cike da tarun damuwa banɗaki ta Shiga ta jima Sanan ta fito tana ƙara duba agogo rigar barci ta ɗauko doguwa tasa ajikinta ta faɗa gado tana goge ƙwalar da ta Silalo daga idanonta,ƙarar horn ɗin da taji yasa tayi Saurin tashi tana leƙawa ta Wendon ɗakin tana tsayi har ya perker Motarshi Sanan ta Saki Labulen ta fito,
Yana Shigowa Babban falon ganin ba kowa Sai kayan kallo daketa aiki So kaɗai ya ƙarasa ya kashi kayan kallon ɗagowa yayi Wanda yayi dai-dai da Saukowar Asiya cikin Sanyin jiki tace "Sannu da dawowa Abban Aiyman"Kallonta ya tsaya yana yi ba tare sa ya Amsa Sanun da take Masa ba Matsuwa yayi yana Cewa Asiya Lafiya naga kamar kuka kika yi ko Barci kika fara?"
Kukan da take riƙewa ne ya ƙwace Mata nan ta faɗa kan fafaɗan Ƙirjinshi tana ci gaba da kuka be hana ta yin kukan ba dan be San Ke yasa takeyi ba Sai da tayi me Isar ta Sanan ya kama hanunta Ya nufi Sashinsa da ita Zaunar da ita yayi gefen gado Sanan ya Shiga banɗaki ya ɗauki lokaci Sannan ya fito ɗaure da toweel a ƙogonsa da Wani a hanunsa yana tsane ruwan kansa,
gaban Mirow yaje ya Shafe jikinsa da Maya mayansa Masu ƙamshi ɗauko kayan barci yayi ya Saka Ya feshi jikinsa da turare Sanan ya dawo kusa da ita ya Zauna ya fara tambayar ta Me yake faruwa?
Cikin Sha Shikar kuka tace "Dan Allah kayi haƙuri Abban Aiyman Wallahi zan gyara halina Dan Allah karka ƙara Aure!"
Dariya taso bashi amma Sai ya dake yace"ki kwantar da hankalinki koda ace na ƙara aure duk Mace da na auro a bayanki fa take ko kin Manta keci Uwar gidan Abdussamad dan haka karki ɗora wa kanki damuwa kinji"
Ya faɗa yana fara rikita mata tunani da Salonsa,nan naja muso ƙofar nace asuba ta gari....
_WASHI GARI...?_
Tun dare Abby ya sanar da Alhj-Mujahid yana son su haɗo Wanda Alhj Mujahid yace yabari zai zo ya Sameshi dake Weakend ne goma na Safe Alhj Mujahid yazo gidan Abby Nan Soka fara tatauna Maganar,Abby yana Sanarwa Alhj Mujahid Nan ya gane Wa ake nufi Yace Zai bincika dan baya tunanin anyi Mata Miji dan da Matarsa ta faɗa Masa amma zai tambayi Shi Mahaifin yarinyar'Nan Su ka yi Sallama inda M.D yace duk yadda ake ciki zai Sanar dashi............
*SHARE & COMENTS*
*MAMAN* *NABEELA CE...* ✍️