GIDAN BALARABE

Chapter21-22

by @mamannabeela

🪴 *GIDAN* *BALARABE* 🪴

      BY

🪴 *MAMAN NABEELA* 🪴

 _TAURARUWAR MOONLIGHT_ ✨


  ***



 *MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION* 



 *DEDICATED* *TO GIDAN BALARABE FAN'S*        

 *MUCH* *LOVE* 😍😍😍


🅿️2️⃣1️⃣↔️2️⃣2️⃣


 ..........Khadija tun tashinta daga barci ta ke jinta kamar a Wata Sabuwar Duniya,Wanda baya rasa nasaba da Mafarkin da ta yi Wanda ya sa yau Har sai da ta Makara bata tashi da Wuri ba. 


Aiyukan gidan ma cike da kuzari ta ke yinso Wanda yasa I'man Sarkin Sa'ido ke cewa"Anty Khady Wai fara'ar me kike tayi haka! ko dai kinyi Mafarki da uhm bari dai nayi Shiru"


Harar Khadija ta Maka Mata tana cewa"toh' Sarkin fassara ni ba Wata fara'a da na ke yi data banbanta da yadda kika Saba gani na dan haka Sai ki tashi Mu tafi Makaranta "Khadija ta faɗa ta na Saka Hijab ɗinta tana dariya.


I'man Ma dariya tayi tana cewa"Wallahi Anty duk Wanda ya kalle ki Sai yaga fara'ar ki ta banbanta da tada nasan Ummy ma kawai ta kyale ki ne bata tambaye ki ba,ko Ma dai Menene Nidai Adu'a ta Allah ya tabbatar Mana da Alkairi,Wai Mutumin jiya be kira ki ba?"

I'man ta faɗa tana Saka Hijabin Islamiyarta.



"Wayi Mutumin jiya ! ke kika Sanshi kinga tafiya ta Sai kin tahu dan naga Surutun ki kullum ƙara gaba yake"

Khadija ta faɗa tana fita,Saurin biyo ta tayi Hanunta ɗauke da Jakar Makarantar tana cewa"Dan Allah tsaya mu tafi, dan Wallahi banason keta gurin Lurwanu Me Shayi ni ɗaya Su bi Su zuba ma ido kayi kamar ka faɗi" Dariya Khadija tayi ba tare da tace komai ba.

Sallama Suka yiwa Mahaifiyarsu Suka tafi Khadija na riƙe da hanun Saudat.



**********


BALARABE



Bayan yayi Sallar asuba barci ya koma Me cike da Mafarkan Abar Sonshi, Banda juyi ba abinda ya ke a Makeken gadonshi,alam ɗin daya Saita Shiya farkar dashi daga da daɗan Mafarkin dayake,yamutsa fuska yayi yana jin dama alam ɗinan be yanke Masa Wannan kyakyawan Mafarkin ba Adu'a yayi ya Shafa yana me ruƙar Allah ya tabbatar Masa da abinda ya gani a Mafarkinan ya zama gaske.




Wani lafiyayin Murmushi ya Saki da ya bayyana kyawa wan haƙuransa Haɗi da beutypoint ɗin dake kumatunsa,tunu hirarso ta jiya da ita

tashi yayi ya nufi Barthroom ya ɗauki minti kusan goma a ciki Sanan ya fito Wasu kaya ya Saka irin na Mutsa jiki Sannan ya nufi falonsa Wata ƙofa ya nufa ta daban Wadda ta Sadashi da ɗakin Mutsa jiki Wanda ke ɗauke da Wasu Machings kala-kala na Mutsa jiki'nan ya fara Mutsa jikinsa Wanda ya ɗauki kusan awa guda yana yi Sannan ya Sauka daga kan Machines ɗin ya nufi Wani Madai-daicin frige Ruwan roba ya ɗauko yayi Bismillah ya kafashi a bakinsa Sai da ya Shanyi Shi tas Sannan ya Ajiye robar ya nufi ƙofar fita Ɗakinsa ya koma ya Shiga Barthroom ya jima Sannan ya fito ƙogunsa ɗaure da toweel jikinsa na ɗigar ruwa alamun Wanka yayi,

Gaban Mirow yaje yana daɗa tsane gashin kansa Wayarsa ya jawo ya danna kira"Ki kawon Coffee"Shine abinda ya faɗa ya katse kiran.



Shiryawa yayi cikin Wasu kaya Marasa nauyi,Wandon treecoter ne Sai riga Amless Me gajeran hannu turare ya feshi jikinsa dashi Sannan ya ɗauki Laptop ɗinsa da Wayoyinsa ya fito Falonsa'Zama yayi kan Luntsuma luntsuman kujerun falonsa ya Zube Wayoyinsa kan Madai-daicin table ɗin dake gabansa 

Laptop ɗinsa dake kan cinyarsa ya fara latsawa cike da ƙwarewa.

"Sallamu alaikum"Asiya ta faɗa hanunta ɗauke da ƙaramin faranti ta ƙarasa Shigowa falon tana Ajiye Wa.


"Chan ƙasan Laɓɓansa ya amsa da "Amin Wa'alaikumus Sallam"ba tare da ya kalle ta ba,

"Ina kwana Abban Aiyman"Asiya ta kuma faɗa 

"Lafiya lau kin tashi lafiya!"ya faɗa yana karɓar Coffeen da take Miƙa Masa.

"Lafiya lau"

Danna Laptop ɗin ya ci gaba dayi ƙarar Wayarsa ya sa ya dakata da danna Laptop ɗin yana ɗauka Murmushi yayi Wanda yasa gaban Asiya faɗuwa.



"Barka da Safiya na Asiya da Laila"Haidar daya kira ya faɗa yana dariya 

"Barkan ka dai tuzuru" Balarabe ya faɗa yana dariya 

ƙaƙarfar Ajiyar zuciya ta Saki gane dawa yake Magana Wanda yasa har ya ɗago yana dubanta yana Mamakin Ajiyar Zuciyar da ta Saki.



Haidar ne ya ce "au haka Ma za ka ce toh ka sha kuruminka na kusa nima na shiga Sahun ko" 

"Allah yasa da gaske kake da nafi kowa Murna"Balarabe ya faɗa 




Haidar ne yace"Allah da gaske nake ka taya ni Adu'a Dady ma yace Wai nan da two Month na fito da Mata kaga kuwa da nayi kuskuren ƙin fito da ita Wallahi duk Wadda ya ga dama aura min Zaiyi"



"ai Wallahi ya yi dai dai inba haka ba ai ba yi za ka yi ba"

Balarabe ya faɗa"ai kuwa kai ma zuwa zanyi na zuga Abby ya ƙaro maka ta uku"Haidar ya faɗa 

"da kuwa na ji daɗi" dariya Haidar yayi yana cewa"ka san Me ya sa na kira ka, zancen gidan nan da Mu ka yi na Sultan rood kwanaki ne ya kamata kazo Muje ka gani dan Angama komai"



"uhm toh'yaushi kake da lokaci Muje!"

Balarabe ya faɗa ya na ci gaba da danna Laptop ɗinsa "ka ga yau Weekend ya kama ta Mu je yau dan nima akwai aikin da nasa ayi min a gidana na ke so na duba" 

"ok Anjima Sai mu haɗo a Sultan rood ɗin kenan"

"eh idan ka fito ka kira ni"

"ok "balarabe ya faɗa 

"ka gaida yara da Mamansu"ok Zasu ji,kace ina gaida Mumah"

"ok "

nan Su ka yi Sallama ya ci gaba da aikinshi a Laptop

Ƙarfe goma Sha ɗaya ya Shirya cikin Wani Lalausan yadi bayan ya karya ya fito ya nufi Mota yana kiran Haidar yana Shaida Masa gashinan ya taho.....





**************





Alhaji Mujahid yana barin gidan Abby nan ya koma gida yake Shaidawa Anty Kubrah Abinda ke faruwa cike da farin ciki take cewa"ai Alhaji bana tunanin anyi wa Khadija Miji dan da Yaya Hauwa ta Sanar dani Amma kaje kaji daga Bakin Shi Mahaifin Yarinyar"

"eh Insha'Allahu bayan Azahar zanje gurinsa,amma karki faɗa wa Mahaifiyar yarinyar ki bari Muji ta bakinsa "da "toh"Anty kubrah ta Amsa tana Me jin tsananin farin ciki Aranta tana adu'ar Allah ya tabbatar da Alkairi.

Bayan Azahar kowa ya tafi gurin Baban Khadija da yayi Masa Waya tun Safe ya Sanar Masa Zai zo a Shagon gidan Baban Khadija ya Sauke shi inda Bayan ya sha Ruwa Sun ga gaisa ya ke kurawa Baban Khadija bayanin Meke tafe dashi

"Alhaji Mujahid Zancan gaskiya ba a yiwa Khadija Miji ba,Kuma Naji daɗin yadda kayi min Bayanin Yaron da kace yana Sonta,Wannan ya nuna Yaron da gaske yake tunda Har ya Sako Iyaye a cikin Lamarin yanemi a tambayar Masa an Mata Miji ko ba'ayi Mata ba,duk da Bansan ko Waye Shi ba Naji ya Kwanta Min dan haka yazo So dai-dai ta da ita Yarinyar Allah ya Shige Mana gaba ya tabbatar da Alkairi"Baban Khadija ya faɗa.


Faɗaɗa Fara'arsa Alhaji Mujahid yayi yana cewa"toh'Masha'Allahu,Amin Amin,Insha'Allah Zan Sanar Wa Mahaifinsa" Sun ɗan taɓa hira Sanan ya yiwa Baban Khadija Sallama ya fito ya yiwa Ummin Khadija Sallama,Ummi tace "ya gaida ƙanwarta da yara" Nan yace "Zasu ji " fita yayi ƙofar gida nan yasa Yara Suka Shigo da Kayan alkairin da ya kawo Musu,

Nan Baban Khadija yarin ga gudiya yana faɗin "Alhaji baka gajiya toh Nagude,Nagude Allah yaji ƙan Magabata"


"Babu kumai Malam Adamu ai yiwa kaine" ya faɗa yana Shiga Motarsa "toh'ka gaida iyalin" 

"Zasu ji Sai kuma Mun dawo neman"ya faɗa yana dariya .


"Allah ya kawo ko" Baban Khadija ya faɗa 

"Amen Summa Amin"Alhaji Mujahid ya faɗa yana tada Motar ya bar layin.


Gida Baban Khadija ya kuma Nan yake Cewa"Ummy ina yaran nan kuwa naga banji Mutsinsu ba?"

"Khadija da I'man Sun Shiga nan Makota yiwa Maman Murja ƙonshi da kitso Saudat kuma tana ɗaki tana barci Nasir na aike Shi gurin Me kayan Miya"



"toh Madalla Miƙo min Hula ta Nasan ana chan ana jira na, idan na dawo Zamuyi Magana Kan yaran nan"

"toh Baban Khadija Allah yasa lafiya dai"dariya yayi yana cewa" kidai bani Hular lafiya lau Sai Alkairi"Hular ta ɗauko ya Saka yana ce Mata "Sai na dawo"

"Allah ya kiyayi hanya" Ummy ta faɗa "Amin"Baban Khadija ya faɗa yana fita..


***************


NASSARAWA G.R.A SULTAN ROOD


Wani katafaren gida BALARABE ya dan horn Me gadi ne yazo ya leƙo ganin Me gidan ne yasa ya Wangale gete ɗin,Motarsa na Shiga ta Haidar ta Mara Mata baya perker Wa Sukayi A katafaren gurin perkin ɗin Motoci Wanda a ƙalla Zai ɗauki Motoci Sama da Ashirin gurin perkin ɗin Ma abin kallo ne yadda aka ƙawa ta gurin da Wasu Shuke -Shuke Masu ɗan karen kyau da tsari ga Wani irin ƙamshi da Sanyi dake tashi irin na flawoyi Abin dai Sai Wanda ya gani.


Gidan pert uku ne a cikinsa kowane pert na ɗauke da bene yayinda Pert biyu akayi musu fenti pert ɗaya kuma ba'ayi Masa ba ko Wane pert Zagayi yake da Wasu kyawawan flawers Mas ɗan karen kyau yana yin gidan kana Kallonsa kaga Sabon gini dan Sai Walwali yake,


Futuwa Sukayi daga cikin Motocinsu nan Suka fara takawa Haidar nayi Masa bayanin komai dalla dalla dan Balarabe tunda ya Siyi filin gurin ya danƙa komai hanun Abokinsa kuma Amininsa Haidar Shi ya tsaya tsayin daka har aka kammala gini da komai da komai na gidan Wanda Shima Haidar gidansa yana jikin gidan.


Zagawa Sukayi har bayan gidan inda Wasu bishiyo Suke Bishiyar mango,gwaiba,lemon tsami,unbreler,D.S gurin ya ƙayatu Matuƙa gefe guda Kuma ga Sweeminpol Balarabe ya yaba yadda tsarin gurin yake dan Sai da ya tsinki gwaibar gurin yana cewa da "Haidar "kaii Mutumi na tsarin guri nan yayi kyau kaga gurin chan har na hangu ni ni da My Khady Muna Shan Love"ya faɗa yana nuna gurin Wasu kujero da akayi na ƙasa ga Shuke Shuke harda rumfa a gurin


"Wace kuma Khady?" Haidar ya faɗa yana kallon Balarabe "uhm Ashi fa kai baka Santa ba ,toh'Matar da zan aura ce"ya faɗa yana kallon Haidar 

"ban gane ba yaushi har ka gamu da Wadda ta Sace maka Zuciya amma bani da Labari!"Haidar ya faɗa cike da Mamaki dan yasan abokin nasa Sam baya Shiga hulɗar Mata.


"Jiya Mana"

"kai dan Allah ka faɗa min gaskiya inko haka ne Gaskiya Zanso naga yarinyar da ta tafi dakai har haka" dariya Balarabe yayi yana Cewa"uhm Zaka ganta So'on"


"toh Allah ya tabatar da alkairi" "amin"Balarabe ya amsa.

futuwa Sukayi Suka nufi pert ɗin da aka yiwa penti tura ƙofar glass ɗin Balarabe yayi bakinsa ɗauke da Sallama Shiga Sukayi cikin Ƙatun falon Wanda yaji tears kalar ruwan gold fentin kuma Mlik babu kumai a ciki Sai tashin Sabon penti da yake tashi Wasu ƙofufi ya buɗe ƙofar farko ɗaki ne babu kuma a cikinshi Shima yasha tears ƙofa ta biyu kuma kata faren kicin ne Wanda har an zuba kicin covers Sama da ƙasa ƙofa ta uku kuma daga chan gefe banɗaki ne irin Safaya ɗinan da akeyi a falo,


Benen Suka nufa Waw Shi kanshi ƙarfen benen abin kallo ne dan ya haɗo over Saman benen ma abin kallo ne dan Suna hawa naga Wasu irin ƙofufi Masu azabar kyau dama da hagu Hanun damar Suka fara Shiga Wani ƙatun falo ne Wanda Shima babu kumai acikinsa Sai Wasu ƙofufi guda biyar rass a cikin falon Suma duka babu kumai a cikinsu.



fituwa Sukayi Suka Shiga na hanun hagun Wanda Shima haka yake.




"kaga yanzu Saura Zuba kaya ya rage"Haidar ya faɗa 

"uhm gaskiya tsarin ya burge ni dan kasan rabo na da nazu na duba tun ba'a gama gini ba fa"

"eh ba ina ta fama dakai ba kaki zuwa danma Allah yasa nasan irin ra'ayinka kuma ina tura maka pic na abinda akeyi"Haidar ya faɗa "eh haka ne kai dai Allah ya Sakamaka da alkairi"


"Haba Balaraben Ammy ai tsakanin mu ba gudiya"

"toh yanzu inaga zan yiwa company Magana Suzu So Saka Mana kaya yanzu Muje naga naka yadda tsarinsa yake"


"au baza ka duba Sauran ba!" 

"kai na fara gajiya Muje naka kawai"

"ok"

Futuwa Sukayi suka nufi gidan Haidar Shima tsarin gidansa kusan iri ɗaya ne da na Balarabe ban bancinsu kawai Shine na Balarabe pert uku ne Shi kuma Haidar pert biyu ne amma gini iri daya ne kumai da kumai.


Bayan Balarabe ya gama gani Sallama yayi Wa Haidar yana cewa Zai kuma gida ya danyi barci dan ya gaji"

dariya Haidar yayi yana cewa"kai dai faɗi gaskiya ko dai uhm bari nayi Shiro dai abar kaza cikin gashin ta"

"a'a faɗi Mana ɗan Sa ido kawai"dariya Haidar ya kece da ita,Balarabe kuwa futuwa yayi ba tare da yayi kuma yi Masa Magana ba Motarsa ya Shiga inda ya nufi hanyar kuma Wa gida.



*********


Alhaji Mujahid daga gidan Baban Khadija gidan Abby ya nufa inda ya faɗa Masa duk yadda Suka yi da Mahaifin Khadija,cike da farin ciki yake cewa"ai ni kaga badan kar Suce Munyi gagawa ba da cikin Satin nan Sai Muje So tsayar Mana da rana dan yadda naga Son yana nuna zumuɗi akan lamarin Nasan bazai kyale ni na huta ba har Sai yaji ta zama Matarshi"



"Allah dai ya tabbatar da alkairi yayi ƙo ƙari yaje Su dai dai ta da yarinyar in yasu Sai muje da batun"

"toh Shikenan ko kiransa bazan yi ba nasan ana jimawa zaka ga yazu"Abby ya faɗa yana dariya


."ai yarannan Sam basu da kawaici kan abinda Suke So,Alhaji ni zan Wuce Allah ya bamu alkairi"

Alhaji Mujahid ya faɗa 

"toh ga Wannan ka ƙara Mai a Mota " Abby ya faɗa yana Miƙa Masa Wasu rafar dubu dubu 


"Alhaji ayi haka ai da ka barshi"

dariya Abby yayi yana cewa"ai ka karɓa kawai ka ƙara Mai" 

"toh gudiya nake Allah ya ƙara girma"

fituwa yayi ya Shiga Motarsa ya nufi gidansa........






 *SHARE & COMENTS* 🙏🙏





  *MAMAN* *NABEELA* *CE.....*✍️