GIDAN BALARABE

Chapter 31-32

by @mamannabeela

🪴 *GIDAN BALARABE* 🪴

        By 

🪴 *MAMAN NABEELA* 🪴

 _TAURARUWAR MOONLIGHT✨_ 

***




 *MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION* 




*AUREN BARE*


*ZUMA A BAKI*


*BAƘAR FATA*


*DA IZZATA*


*ƊAN MAJALISSA*


*H A S K E*


*KOBA SO*


*RABON WANI*


*MURADIN ZUCIYA*


*ASHE ZUMA*


_Gaba ɗaya waɗan nan zafafan littattafan na AUTAR MANYA ta sadaukar muku dasu a kan fara shi mai sauƙi naira 1500 sabida kusantowar watan azumin ramadan! karfa ku manta dukkan waɗannan littattafan babu na yadawa domin kowanne akwai tsumammiyar soyayya acikinsa wadda take tafe da darasi tare da kwanciya a zuciyar makaranci, Hankali kwance zaki karanta su domin kowanne yana haɗe ne complt babu jiran ayi posting kigani gamai buƙatar waɗannan zafafan littattafai ze tura kuɗinsa kai tsaye ta wannan asusun bankin 0078174806 starling bank sannan ya antayo shaidar biyansa ta nan *** insha Allahu ze sami dukkan waɗannan littattafai_💃💃💃💃💃❤️🥰



 *DEDICATED TO KHADEEJA INA GUDIYA DA IRIN* *ƘAUNAR DA KI KEWA WANNAN BOOK* 🥰🥰🥰



🅿️3️⃣1️⃣↔️3️⃣2️⃣



 .......BALARABE yana ganin kiran Khadija ya ƙi ɗagawa dan tabbas idan ya yarda ya ɗaga,zai iya aikata abinda beyi niya ba,dan yana Matuƙar ƙaunarta da Mugun kishinta' Wanda yasa tun yanzu yake adu'ar Allah ya bashi ikon yin Adalci a tsakaninta da Matansa,dan Shi kansa ya kanyi Mamakin irin Mugun Son da yake Mata a lokaci ƙanƙani da haɗowarsu Wanda be taɓa tunanin zai Wa Wata ƴa Mace irin Son ba.

Yana kuma Wa gida firje ɗin dake Babban falo ya Nufa,Ruwa ya ɗauko Me Sanyi ya buɗe rubar Ruwan yayi Bissmillah ya kafa bakinshi Sai da ya Shanye tas Sannan ya Sauke rubar ya Wurga ta cikin kwandon dake falon'Zuciyarshi yaji ta daɗa yin Sanyi Nana ya nufi Sashinsa Barthroom ya Shiga ya ɗauru alwala jin an fara kiran Sallah Yana yin Alwala fituwa yayi ya nufi Massalaci yana idar da Sallah Mota ya hau ya nufi gidan Mahaifanshi.


Ko da ya perker Motarshi cikin gidan ya Shiga inda ya tarar duk Suna falo Zama yayi yana gaida Ammy nan ta amsa tana tambayarsa ya aiki"

"Alhamdulilah ya amsa nan Huda ta gaishishi ya amsa Laila Ma gaishi Shi tayi ya amsa yana tambayarta jikinta ta amsa da Alhamdulilah"

"Ammy Wai yaushi zaku ko ga gidan ne inso a Satin nan fa So kuma ne dan an gama kumai!"

BALARABE ya faɗa yana duban Ammy.


"Dama gobe Muke Sun zuwa in Allah ya kaimu"

Ammy ta faɗa.


Huda ce tace"kai ai Wallahi na ƙagu naje naga gidan nan dan nasan ba ƙaramar haɗowa yayi ba"

ta faɗa tana dariya.

Dariya Suma Sukayi Sannan Suka ci gaba da Hirarsu.

Ammy ce ta tashi ta tana cewa "Son kan ka tafi ina Sun Magana da kai"ta faɗa tana nufar Sama.

"toh'Ammy" ya tashi ya nufi bayanta,Suna Shiga ɗaki,

Ammy tace "Son Batun tariyarko ba da Laila zako kuma ba daga baya ta biyu ko in an gama yi Mata Magani"

"toh amma Ammy ta yarda zata dena Wannan yawun dan ni dai nafi So ya kasance Matana duka Suna gida tunda ban gaza gurin yi Musu kumai ba!"

 

"Insha'Allahu zata dena dan na fara tunanin anya ba Mutanen jikinta ne Suke Sa ta rashin zaman nan ba, Ko da dama ita Masoyayiyar neman kuɗi ce amma abin yayi yawa"

 

 

"Allah ya Sauwake Amma ai ni gani nayi Me na ragesu dashi da har Sai antafi yawon neman kuɗi in kasuwancin ne ai anayi kana daga gida Ma" 

Balarabe ya faɗa.

  

"Amin ka daɗa haƙuri dai, zata dena in Allah ya yarda"Ammy ta faɗa cike da tausayin Laila dan ita Wallahi tausayi take bata.

Fara tatauna batun Bikinsa da yake tahuwa Sukayi Sun jima Suna tataunawa Sannan yayi Mata Sallama,ya fito Saukowa ƙasa yayi Laila dake Zaune ita ɗaya tana dakon Saukuwarshi ta Miƙe ta nufeshi tana faɗawa jikinsa, tana faɗin "Honey ina ƙaunarka,nayi kewarka da yawa"

 Cike da tausayinta na halin da ta tsinci kanta yace"Nima haka" ya faɗi hakan dan ya kwantar Mata da hankali.

"da gaske kana ƙaunata kayi kewata"ta faɗa cike da farin ciki.

"uhm"

Ya faɗa yana ɗagota daga jikinsa.

"toh Mu tafi gida kawai ai na Warke"ta faɗa cike da farin ciki. 

"uhm ba yanzu ba ki dai bari gobe zanzu na ɗaukeki in na tasu daga office"

ya faɗa yana dubanta.

"Allah ya kaimu ta faɗa cike da farin ciki Sun jima Suna hira tsakaninsu Laila najin kamar kar ya tafi haka yayi Mata Sallama ya tafi.

Ta gumi ta zuba haka kurum tana jin Wani irin faɗuwar gaba haka ta tashi ta nufi ɗakin da aka bata a gidan..



************


Khadija Zaune Suke a tsakar gida dukansu harda Su Anty Kubrah da yaranta, ana ta hirar yaushi gamu tsakanin Khalil da Su hira ake cike da farin cikin dawowarsa inda aka baje Masa kayan tarbar da aka yi Masa yake ta kwasa Adnan ne yace"toh dai kaci a hankali Wallahi kar da kazu cikin ka ya hargitsi tunda chan ba irin abincin kuke ci ba" ya faɗa yana dubansa.

Khalil da ya cika bakinsa da Wainar Shinkafa yana haɗiyewa yace" Waya faɗa Ma Muna da inda ake abinci irin na ƙasar hausa, harda irinsu kwaɗon zugale da ya kuwa"dariya aka kwashi da ita Anty Kubrah tace"ah ko dai harda Santi"

"a'a Anty Suma ƴan Nigeria ne Masu yin irin abincin"

"ah ba Shakka Shiyasa Ɗan nawa kace ya ƙara zama ƙato dan da irin abincinsu kake ci da Wuya kayi ƙiba"

dariya Adnan yayi jin abinda Mahaifiyarsa ta faɗa yace "kaji ko na faɗa Maka dama Suma Sai Sun faɗa"

"uhm naji nayar da"

Khadija dake gefe ce tace"Yaya Wallahi ka zama kamar Salman khan bambancinko beuty point"ta faɗa tana dariya 

Dariya Shima yayi yana faɗin"ai kema kin ƙara girma Amarsu tunda gashi har zamu Sha biki!"

Khadija da gudu ta kwasa Sai ɗaki tana dariya.

Suma gabatuwar Magriba yasa duk Suka tashi Suna nufar yin alwala.

Khadija Ma fituwa tayi'tayi alwala Sannan ta Shiga ɗaki tana gabatar da Sallah.

Bayan Sun idar da Sallah Khalil Adnan ne ya ɗaukishi Suka nufi gidan gwamnati inda aka Shirya Musu Liyafa taya Su Murnar kammala karatunsu.


Anty Kubrah Ma ana idar da Sallah tayiwa Yayarta Sallama Suka tafi gida.


Ƙarfe tara na dare Khadija taji Wayarta na ringing alamun kira ake ɗaukar Wayar tayi ganin Me kiran tana zuba Murmushi dan yau Sau ɗaya Suka yi Waya tun Safe, Sa ɗazu da taringa kira Lokacin da yayi Mata gizo,Ɗaga Wayar tayi ta kara akunenta tana faɗin"Amincin Allah ya tabbata a gareka Nurrulhayatee!"ta faɗa Muryarta na fidda Sautin Murmushi.

Balarabe da ke Zaune kan kujerar falonsa yana Shan Coffee Laptop ajiye kan cinyarsa besan lokacin da ya dire Cup ɗin Coffeen ba yana riƙe Saitin zuciyarsa dan da gaske Saƙon ya isa ga zuciyarsa Lumshi lumsasun idanonshi yayi Sannan ya buɗesu yana cewa "tare dake My heartbeet,ina fatan kina cikin ƙoshin lafiya"

"Lafiya lau'ya aiki?"

"Alhamdulilah,ya Shirye-Shirye?"

Dariya Khadija tayi tana cewa"ana nan anayi,Dan Allah Ɗazu kazu unguwarmu?"

"uhm nazu naganki rungume jikin Wani"

"Lah da gaske Ashi kai na gani,Wallahi na ɗauka kawai gizo kayi min"ta faɗa yana dariya.

"Waye Shi ɗin ?"Balarabe ya faɗa yana Saurarunta 

"Yaya Khalil ne fa dana faɗa Ma zai dawo,amma Me yasa ka tafi bayan ko gaisawa bamu yi ba?"

"uhm na tuna amma fa kiris ya rage kishin ki ya Sa na Samu Matsala,Shiyasa da kika kira Ni Ma ko ɗagawa na gaza yi"

"kaiii Wallahi dan ya juya bayane amma da kana ganin fuskarsa zaka gane Yaya nane Saboda kamarmu ɗaya dashi,Wai dama hakan da ka gani yasa ka tafi?"

"uhm kuma ko hijabi fa baki Sa ba idan da Wasu Sun ganki fa!"

Balarabe ya faɗa.

"toh kayi haƙuri bazan Sake fita babu hijabi ba lokacin Ma tsananin Murna yasa na Manta ban ɗauko ba"

"uhm babu kumai ya wuce"

Nan Suka cigaba da hira har ƙarfe Sha ɗaya Sannan Suka yi Sallama.


 _AFTER TWO WEAK_ 


Yau Su Khadija Suka fara zana jarrabawa,Wanda ɓangare guda kuma ake ta Shirye Shiryen Biki Wanda yanzu Bikin ya zama guda biyu Sakamakon haɗawa dana Khalil da Mame da za'ayi Wanda tuni Anty kubrah tasa Safnan Barno fara aiko Mata da kayan gyara,Wanda ta fara basu kafin ta ƙarasu da kanta ta fara tsumasu da irin Sirrikansu irin na ƴan Maiduguri.

Inda tuni Khadija ta kuma gidan Anty Kubrah daga chan direvern ta ke kai Khadija Makaranta yana ɗaukota,idan Ka ga Khadija ta ƙara kyau fatarta ta daɗa Murjewa Sakamakon gyaran da ake Mata.

Anty Kubrah Allah Allah take ta gama zana jarrabawar da take inda tace,tana gamawa baza ta barta ta ƙara fita Waje ba Sai ranar da zata Maida ta gidansu a cewarta yadda gyaran zai daɗa zama jikinta ta daɗa chanzawa fiye da yanzu.


Ɓangaren Balarabe tuni Sun kuma SULTAN ROOD NASSARAWA G.R.A inda Suma ɓangarensa Shirye Shiryen Bikin yake tamkar be tabba Aure ba Ɓangaren da Amryarsa zata Zauna tuni ya gyreshi anyi Masa fenti na gani na faɗa gida Sai Walwali yake.


ASIYA...........









 

 






 *MAMAN* *NABEELA CE...✍️*