11
by @shooly84
...Rumanah🕊️
(Zabin Iyaye)
©️ Aisha Machika
*Page~11*
Wani irin kiss Saraki ke mani da zafi-zafinshi, saukar hannayenshi a saman ƙirjina ya haifar man da wata irin bugawar zuciya, tsoro mai tsanani ya rufeni, ga bakina cikin nashi yana ta famar tsotsa kamar ya samu alawa, tureshi nake son yi amma ya hanani samun damar hakan, can ya gaji da tsotsan bakin ya cire ya maida kan wuyana yana kissing, ina samun damar jan numfashi na fesar sai wani kuka mai ƙarfi ya balle mani, zagi, magiya da roƙo babu kalar wanda banyi ba amma a banza tamkar baya jina, sha'aninshi kawai yake yi.
Ban tabbatar da cewa nazo hannun maza ba, mazan ma irin waɗanda suka daɗe a duniya ba tare da sun kasance da mace ba sai yau, balle Saraki da duk tsawon shekarun auren shi bai taba kula Jamila ba da sunan wata mu'amula ta aure.
A wannan lokacin, a cikin wannan yanayin babu wanda ban kira ba cikin su Iyalle da Baba Sarki da sauran ƴan'uwana dan su zo su ceceni daga hannun Saraki, zuwa lokacin daya samu natsuwa nayi laƙwas numfashi ma da ƙyar nake ja, gaba ɗaya gabobina da ƙirjina da lips ɗina wani irin zogi suke.
Kuka tun ina yi da murya da hawaye har suka ɗauke sai na zuci kawai, mintuna biyar ya ɗauka akwance gefena yana maida numfashi bayan ya tashi daga kaina, ina kwance ko motsin kirki bana iya yi, abu ɗaya nayi jarumtar yi bayan ya ɗagani shi ne curewa waje ɗaya, na dunƙule ina jin yadda azaba ke ratsa ko ina nawa, ga hasken wuta tar a cikin ɗakin tunda bai kashe wutar ba.
Duk da cewa idona rufe suke ina jan majina naji lokacin daya sauka daga gadon ya shige toilet, mintuna kaɗan naji fitowar shi, sannan naji ya sanya hannu ya ɗagani a cure na, bance komai ba banyi ko motsi ba ban kuma buɗe idanuwa na ba, dan nasan taimakon da zan fara ba kaina na farko shi ne na tsaya ya taimaka mani da koma me yake shirin yi.
Ƙaton bahon wanka daya cika da ruwan zafi ya shigar damu ni da shi gaba ɗaya, yana rungume dani a cikin ruwan yana kuma jin yadda jikina ya soma kyarma da ruwan ya soma ratsa ko ina nawa, idona a rufen hawaye masu zafi suka ci gaba da tsiyaya.
Cikin kunnena naji ya raɗa man sorry, daure ki buɗe ƙafafuwanki da kyau kinji, babu gaddama nayi hakan duk da cewa wata sabuwar azabar ce ta ratsani, muna a haka har ruwan ya salamce ya fiddoni muka koma shower yace kiyi wanka tsarki Rumanah mu koma ɗaki, nayi niyya na kama wanka yana taimaka mani, shima abinda ya yi kenan.
Muka fito kowanne yana ɗaure da towel yana riƙe dani yana taimaka mani, kan kujera ya ajeni ina kallonshi ya yaye zanin gadon ya ɗauko wani ya shimfiɗa, sannan ya maidani bakin gadon na zauna a hanakali ya ce man ina first aid ɗinki yake Rumanah?
Na ɗaga idanuwa da suka yi luhu-luhu saboda kukan dana sha, ganin ina kallon mirrow yasa ya miƙe yaje wajen, drower mirrow ya janyo, drugs ne kala-kala a ciki, ya ɗan jima yana bincikarsu sannan ya ɗauko guda biyu paracetamol da pain relief ya zo ya miƙo mani na karba babu gaddama na watsa a baki ya miƙo man ruwa nabi dashi, shima ina kallo ya watsa paracetamol a baki yasha, nabi shi da harara a zuciyata ina faɗin gulma meye na wani sha, azzalumi kawai, ni kaɗai nayi ƙwafa dan ba ƙyaleshi nayi ba yanzu ta kaina kawai nake.
Zanyi lokacin shi, zai kuma gane yayi kuskuren maidani mace da yayi, wata sabuwa tsanarshi ta sake lunkuwa a zuciyata, naja jikina a hankali na hau gadon da towel ɗin na kwanta naja duvet har ka, bayan kusan minti ashirin na samu wani wahalallen bacci ya ɗauke ban sake bi ta kan Saraki ba.
Ina gaban mirrow ina shafa mai bayan tashina bacci da kuma ƙarfin jikina da naji, duk da cewa ban koma dai-dai ba amma dai ba kamar ɗazu ba, tunanikan banza da wofi nake naji buɗe ƙofar ɗakina, na juya ina kallo mai shigowar, kallo ɗaya nayi mashi na ɗauke kai dan ganin yarda yaci wankanshi yana sanye da shadda mai ruwan bula, ya tako har gabana ya sanya hannu a goshina da wuya jin babu zafi ya juya ya zauna bakin gadon yana faɗin ya jikin naki?
Na harareshi ta cikin madubin, murmushi ya yi yace hadda hararata lallai baki hukuntu ba, yanzu dai ni dai yunwa nake ji ki tashi kije kiyi mana abin kari, kinsan dai Jamila bayi zata yi ba, na ɗago ina mashi kallon mamaki ta cikin madubin, anya Saraki na da tausai ko imani, takaicin shi ya sake kamani na balla mashi harara tsaki na biyo baya.
Miƙewa ya yi ya iso inda nake, ya ɗagoni tsaye yana kallona da wani tsinannen murmushi saman fuskarshi, yace ni kike harara da yi ma tsaki, lalle baki huru ba, yanzu zanyi maganin wannan rashin kunyar taki, amma kafin nan yunwa nake ji daure ki sama mana wani abu mana, tureshi nayi daga kusa dani ina tura baki, nifa ba abinda zai sa nayi maka wani abin kari, banga dama ba kuma banyi niyya ba, na nufi wajen closet ɗin kayana in samu rigar da zansa ma jikina, ban ƙarasa ba naji an fisgoni sannan ya ciccibeni yayi sama dani zuwa kan gado.
Sai a lokacin naga ya cire shaddar jikinshi daga shi sai vest da boxer, hannu yasa da ƙarfi ya funcike towel ɗin jikina yana faɗin tunda ba zaki bani abinci ba ai sai inyi breakfast dake ni duk ɗaya ne a wajena, dan ma ki sani yau sai na fanshe bashin kwanaki uku da mukai kina sanya man maganin bacci, zuciyata tayi mummunan harbawa ganin da gaske yake maimaita man wannan azabar yake shirinyi, na hau kai mai duka jikina na rawa, ya kama hannayen nawa duka biyu ya danne da katifa sannan ya shiga kai man sumba ta ko ina, na saki kuka jikina na wani irin rawar tsoro.
Kafin wani lokaci nayi laƙwas sai hawaye kawai dake tsiyaya daga idanuwa na, a yau na tabbatar da cewa Saraki mugu ne na ƙarshe, dan harda mugunta yake haɗa mani ni na sani, ina kallonshi ya tashi ya shige toilet kafin ya fito a maimata irin na safe, wannan karon har busar man da kai shi yayi sannan ya ɗauko pant ya sanya mani da wata doguwar riga ta shan iska dan ko hannu bata dashi, ni dai rufe ido nayi kawai ina hawaye ban hanashi duk abinda yake yi ba, ya gama ya ɗaukeni ya kwantar kan gado yana faɗin kwanta ki huta bari in samo mana abinda zamu ci ina zuwa.
Yana fita na fashe da wani irin kuka, bazan iya wannan azabar ba gida zani kafin ya ƙarasani da raina, mintuna arba'in ya sake shigowa da ledar takeaway, yazo har kan gadon, ɗagani ya yi ya rungume na zame, ya sake mannani da jikinshi nan ma nayi ƙoƙarin zillewa amma yayi man kyakkyawar runguma dole na haƙura naci gaba da kuka.
Toh miye kuma na kuka Rumanah? Kiyi haƙuri da ciwo ko? Nace ni ka sakeni tunda ka gama da rayuwata zaka zo ka tasani da surutan banza, ni gida ma zan yau ɗin nan, gida kuma Rumanah, kofa sati ba ki yi ba, kiyi haƙuri da kaina zan kai in lokaci ya yi, jin ban ƙara cewa komai ba yasa ya soma maganarshi ta yadda ya iske daren jiya, zamewa nayi daga jikinshi na matsa can gefe naci gaba da kuka na, shima ya matso ya dafa man kai, kiyi haƙuri Rumanah ɗaure ki sauko ki karya, ya sake tallaboni zai rungume na maza na dire ƙasa ina nuna shi da ɗan yatsa, kada ka ƙara gigin taba jikina, ko an gaya maka ni ƴar iska ce, ya yi saurin dorowa shima ya nufoni.
Lafiyarki lau Rumanah, waya gaya maki iskanci muka yi? Na ƙara matsawa ganin so yake ya kamani, toh miye in ba rapping ɗina kayi ba? Subhanallahi! Rumanah kefa musulmace kuma nasan kinsan komai, ya kawo man cafka kafin na gudu ya kamani ya rungume, sai na kasa gudu daga jikinshi naci gaba da kuka, Rumanah dan Allah kiyi haƙuri wallahi gani nayi inba haka nayi maki ba, ba zaki taba yarda dani ba, kinsan kuma ke kaɗai nake so ban iya haɗa jikina da kowace mace idan bake ba, dan Allah ki daure ki soni nima, amma yanzu daure kici abinci dan ki samu ƙarfi sai ki sake shan drugs kinji, banyi gaddama ma na janyo ledar abincin.
Bayan azahar na sake yin wanka na saka wata atamfa mai buɗaɗɗen ɗinki, fridge na buɗe na ɗauko yoghurt na shanye sannan na zura hijab na rataya jakka na sa takalin flat, na fito na ƙulle ƙofata nasa key ajakkar, babu kowa falon dan haka na fice na shige motata na bar gidan.
Ko ɗar banji ba na shige gidanmu, babu kowa a gidan jamar yarda nayi zato sai Iyalle kawai, na gaisheta, maimakon inga ta hau ni da faɗa sai ma naga ta hau murna da zuwa na, nace Iyalle duk ina mutan gidan? Toh Ummu kowa ya yi ta kanshi ya koma cikin iyalinshi dama maganarku ta kawo su, anyi an gama kuma, na bata rai cikin rashin jin daɗi, yanzu ko su Aunty Khadijah basu tsaya ba tunda sun jima basu zo ba dan ba'a ƙasar suke ba.
Rumanah dole su tafi tunda sun bar yara a gida, na sauke ajiyar zuciya nace Baba fa? Yana ciki yau bai fita dan baya jin daɗin jikinshi amma yaji sauƙi dai, na miƙe da sauri zuwa sashen shi, a falo na sameshi yana duba Jarida, na duƙa ina gaisheshi, yace a'a amare ne har an soma fitowa?
Ɗan murmushi nayi nace Baba naji Iyalle tace baka jin daɗin jikinka?
Abinda jikin yayi sauƙi ma, dama ɗan zazzabi ne kawai, nace toh Allah ya sawwaƙe ya ƙara lafiya da nisan kwana yace amin.
Haka dai munata ƴan hirarraki har na wajen mintuna ashirin, daga bisani na gyara zama na sako abinda ya kawo ni, ''hmmm" daman Baba na zo ne kan alƙawarinmu, wane alƙawari kenan Rumanah?
Kai tsaye na dake nace raba mana aure mana, ya aje jaridar ya fuskanceni sosai, Umma naga ba'a wani jima da yin auren ba, Baba kwana huɗu kenan fa, ya yi murmushi yace ni ba kwanaki nake nufi ba watanni ko shekaru haka, na zaro ido, shekaru Baba? Baba ka taimaka mani, ni ba zan iya shekaru da auren Yaya Saraki ba, yace to naji daure kiyi ko ƴan watannin ne, nayi ɗan shiru ina tunani, amma Baba innayi watannin zaka raba ko?
Kwarai da gudu ma kuwa Rumanah, inde har na tabbar da baki son shi ba, daga nan yaci gaba da yi man nasihohi a kaikaice har na ɗanji wani iri araina na rashin kyautatawa.
Ban baro gidan ba sai bayan la'asar, ina cikin mota ina ta tunani, wai meke damuna ne, farkon zuwa na gidan Saraki akwai son jini da jini kuma ina tausaya mashi, amma daga baya sai naji ba wanda naƙi jini irinshi, to ko dai asiri akayi mani? Amma wa zai mani wani asiri ana zaune ƙalau, babu na ba kaina amsa, ko dai yane zanyi ƙoƙari yau inga nayi ma Saraki wani abu da zai yi mamakina.
Ina zuwa gidan kitchen na shiga inyi ma angona abinci, ganin tukunya bisa cooker gas nasan Jamila ce zata yi girki, na kalli ƙofar shigowa sannan na buɗe na iske dafadukan shinkafa da macaroni ce taji kayan haɗi, na maida na rufe ina daɗin ko yaushe su Jamila aka iya girki haka? Kamar in fasa nawa girkin amma wata zuciya tace kiyi mashi ɗan gidan mana wato kunun gyaɗa.
Kafin magriba na kammala damun kunun na soya mashi doya da kwai sai farfesun kidney da nayi mashi, duk da cewa mun haɗu da Jamila tazo duba girkinta nayi mamaki da ko kallon inda nake ba tayi ba, ni ce ma nace mata barka da yamma tayi mani wani kallo ta ɗauke kai, sai nima na ba banza ajiyarta harta gama abincin ta ta juye a warmer ta fita da abinta, maimakon in zauna sai na wuce kai tsaye toilet, wanka nayi na ɗauro alwalla, bayan na gabatar da sallah na shirya cikin wasu riga da wando ɗinkin Chaina pupple ne, na fesa perfumes masu sanyin ƙamshi, gashina na kama shi na ɗaure na saki yayi baya, ni kaina nasan nayi kyau sosai.
Ina jin dawowar Saraki, bai shigo ba nima ban fita ba, zuwa can ya turo ƙofa ya shigo da sallama, muna haɗa ido gabana ya fadi nayi saurin tashi tsaye, shi kuma ya shigo yana murmushi, amarya yaya gida? Maimakon in amsa sai na ratsashi nayi falo naje nayi zaune kan kujerar tebirin cin abinci, Jamila dake zaune wajen ta bini da kallo.
Shima ya fito ya zo ya zauna kusa dani a hankali yace kinyi kyau yau, duk kin canza mani, miƙewa bayi na ɗauko abinda nayi mashi ina faɗin ga abinci nayi maka, cikin mamaki yace ni Saraki kikayi ma girki, bance komai ba na hau zuba mashi, duk abinda nake ban yarda na kalleshi ba, na gama na tura gabanshi ina niyyar barin wajen ya kamo hannuna, zauna muci tare in kuma baki ci zauna ni na gama, banyi gaddama ba na koma na zauna.
Yana ci yana surutan yadda abincin yayi daɗi harya gama, ya ɗago fuskata dake duƙe muka haɗa ido, a take naji gabana ya sake faɗuwa, tsanarshi mai tsanani ta rufe dukan zuciyata, kumatuna ya sumbata nayi saurin miƙewa tsaye ina kallon inda Jamila ta ke, amma wayam sai kujerar kenan ta tashi tun ɗazu.
Ya tashi ya tsaya dab da ni, miye haka Rumanah, yaya kinyi man kwalliya tare da abinci mai daɗi, na ci zan nuna maki godiyata kin tashi, ya matso ya janyoni jikinshi yana shafa da sumbatar kafaɗuna, tureshi nayi ina nuna shi da yatsa, na gaya maka ni ba ƴar iska bace, ya dafe kai wai meke damunki ne Rumanah? Na balla mashi harara na juya na shige ɗaki harda sa ma ƙofata key, na faɗa gado na fashe da kuka, kukan da bansan na miye ba.